Allah Madaukaki bai yarda Ingantacciyar Aqida ta kasance tare da kowace kungiya ba sai Ahlus Sunna Mabiya Hadisai da Sunnonin Manzon Allah (ﷺ). Saboda su ne suka dauko Addininsu da Aqidunsu na baya daga na farko, karni bayan karni, har zuwa kan Tabi'ai, Tabi'ai kuma suka dauko daga Sahabbai (R.A), Sahabbai kuma suka dauko daga Manzon Allah (ﷺ). Babu wata hanya ta sanin abin da Manzon Allah (ﷺ) ya kira mutane zuwa gare shi na Mikakken Addini, da Hanya Madaidaiciya face ta wannar hanya da Ahlus Sunna suka bi.
Amma sauran Kungiyoyin Bidi'a kuwa, sun nemo Addini ne ba ta hanyar Annabi (ﷺ) ba, saboda sun dogara ne a kan hankulansu da tunaninsu da ra'ayoyinsu. Idan sun ji wani abu daga Qur'ani da Sunna to za su auna shi ne a kan ma'aunin hankalinsu, in ya dace da hankalin nasu sai su karba, in kuma bai dace ba to za su yi watsi da shi ne, bisa da'awar ya saba wa hankali, ko kuma dalili ne na zato ba yakini ba, ko kuma zato ne wanda ya yi karo da yakini, ko su ce: Hadisi Ahaad ne da ya yi karo da Mutawatiri. Da dai sauran ma'aunai na ra'ayi da suke da su don watsi da Nassoshin Wahayi.
In kuma ya zama dole sai sun karba, saboda babu yadda za su yi, kamar in Ayar Qur'ani ce, ko kuma Hadisi ne Mutawatiri to sai su yi tawilinsa, su canza masa ma'ana. Da wannan sai suka karkace daga gaskiya, suka jefar da Addini bayansu, suka sanya Sunna a kasan kafafunsu suka take ta.
Wannan shi ne Manhajin 'Yan Bidi'a da son zuciya, amma su Ahlus Sunna kuma ga bayanin nasu Manhajin daga Abul Muzaffar Al- Sam'aniy inda ya ce:
ﺃﻣﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺤﻖ ﻓﺠﻌﻠﻮﺍ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﺇﻣﺎﻣﻬﻢ، ﻭﻃﻠﺒﻮﺍ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻬﻤﺎ، ﻭﻣﺎ ﻭﻗﻊ ﻟﻬﻢ ﻣﻦ ﻣﻌﻘﻮﻟﻬﻢ ﻭﺧﻮﺍﻃﺮﻫﻢ، ﻋﺮﺿﻮﻩ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺈﻥ ﻭﺟﺪﻭﻩ ﻣﻮﺍﻓﻘﺎ ﻟﻬﻤﺎ ﻗﺒﻠﻮﻩ، ﻭﺷﻜﺮﻭﺍ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﻴﺚ ﺃﺭﺍﻫﻢ ﺫﻟﻚ ﻭﻭﻓﻘﻬﻢ ﺇﻟﻴﻪ، ﻭﺇﻥ ﻭﺟﺪﻭﻩ ﻣﺨﺎﻟﻔﺎ ﻟﻬﻢ ﺗﺮﻛﻮﺍ ﻣﺎ ﻭﻗﻊ ﻟﻬﻢ، ﻭﺃﻗﺒﻠﻮﺍ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ، ﻭﺭﺟﻌﻮﺍ ﺑﺎﻟﺘﻬﻤﺔ ﻋﻠﻰ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ، ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻻ ﻳﻬﺪﻳﺎﻥ ﺇﻻ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺤﻖ، ﻭﺭﺃﻱ ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ ﻗﺪ ﻳﺮﻯ ﺍﻟﺤﻖ، ﻭﻗﺪ ﻳﺮﻯ ﺍﻟﺒﺎﻃﻞ
ﺍﻟﺤﺠﺔ ﻓﻲ ﺑﻴﺎﻥ ﺍﻟﻤﺤﺠﺔ ( /2 237 - 238 )
"Amma Ahlus Sunna fa, Mabiya gaskiya, su sun sanya Littafin Allah da Sunnar Manzonsa (ﷺ) ne a matsayin jagoransu, sai suka nemi Addini ta wajensu. Duk abin da ya fado musu a cikin hankulansu da tunaninsu to za su bijiro da shi ne ga Qur'ani da Sunna, idan sun samu ya dace da su to sai su karba, kuma su gode ma Allah ta yadda ya nuna musu hakan, kuma ya sa suka dace gare shi. In kuma suka samu ya saba musu to sai su bar ra'ayin nasu, sai su fiskanci Qur'ani da Sunna, sai su koma suna tuhumar kawunansu da tunaninsu. Saboda Littafin Allah da Sunna ba sa shiryarwa zuwa ga komai sai zuwa ga gaskiya, amma ra'ayin mutum kuwa, zai iya hango gaskiya kamar yadda zai iya ganin karya".
Saboda haka, wannan shi yake nuna mana hakikanin banbanci tsakanin Tafiyar Ahlus Sunna wacce ta ginu a kan Biyayya ga Qur'ani da Hadisan Annabi (ﷺ), da kuma Tafiyar 'Yan Bidi'a da Mabiya son rai, wacce ta ginu a kan Biyayya ga Falsafa da Ra'ayi da Tunani da Hankulan 'Yan Adam masu rauni.
Daga:- Dr Aliyu Muh'd Sani.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.