Falalar Yin Sallar Nafila A Gida

FALALAR YIN SALLAR NAFILA A GIDA

Nafila mafi tsada da daukakar daraja a wajan Allah itace wadda akeyinta a gida,kamar yadda mafi yawan nafilolin Annabi s.a.w yana yin sune a gidansa, kadan ne yakeyi a masallaci.

Annabi s.a.w ya kwadaitar da mu akan yawaita nafila a gida yayi hakan a aikace kuma ya fada da dama ga kadan daga cikinsu;-

1-Sallar nafila a gida tafi falala akan wadda akayita a wani guri da daraja ashirin da bakwai.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Sallar mutum ta nafila a gidansa inda mutane basu ganinsa,tafi sallar nafilar da mutum yayi inda mutane suke ganinsa da daraja ashirin da biyar).
@صححه الألباني في
صحيح الجامع - رقم: (3821)

2-Yin sallar nafila a gida sabawa Yahudawane da Nasara,kuma tana korar shaidhan kuma Mala'ikun sama suna kallon gidan.

Annabi s.a.w yana cewa:
(Ku sanya wani yanki na sallar nafila a gidanku,kada ku sanya gidanku ya zaman maqabarta kamar yadda Yahudawa da Nasara suka riqi gidanjensu a matsayin maqabarta,domin gidan da ake karanta alqurani acikinsa ma'abuta sama "wato mala'iku" suna ganin kamar yadda ma'abuta kasa"wato mutane"suke hangen taurari a sama).
@السلسلة الصحيحة - رقم : (3112) قال الألباني إسناده جيد .
3-Sallar nafila a gida itace mafi alkhairin nafilar bawa kuma Allah yana sanya mata alkhairi.

Manzon Allah s.a.w yace:
(Idan dayanku yagama sallolinsa a masallaci,to ya sanya wani kaso na sallar nafilarsa agidansa, domin Allah ya sanya albarka a sallar ta gida).
صحيح مسلم - رقم: (778)

4-Annabi s.a.w yayi mana umarni da yin sallar nafila agida.

Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Kuyi sallar nafila a gidajenku,kada ku bar yin sallar nafila a gidajenku).
@صححه الألباني في صحيح الجامع - رقم: (3786)

Allah ka bamu dama da ikon yin sallar nafila da kyakkyawar niyya da ikhlasy a gidajenmu.

Post a Comment (0)