JAHILCI KO HUDUBAR SHAIDAN?!
*MALWAHDE ❌❌*
'Yan uwa haqiqa wannan jahilcin da gidadanci da ya bullo mana a wannan zamanin ba qaramar fitina bace ga musulmai.
Wata kalar rawane wai ita MALWAHDE. Asali yahudawa ne suka tsiro da wannan rawar, wata waka ne ake yi da wani yare wadda har yanzu na kasa gane hakikanin fassarar waqar, sai ku ga masu rawar suna faduwa suna tashi. To amma saboda tsabar JAHILCI, GIDADANCI da yake damun wasu daga cikin samarinmu da 'yanmata a wannan lokacin, har an samu wasu na kwaikwayon irin wannan rawar, babban abin takaici ma wai har da mata. Na'udzubillah!
'Yan uwa wallahi mu ji tsoron Allah, ba komai ke damun mu ba sai rashin ilimin addini da son zuciya, na rantse da Allah sam-sam wannan ba waye bane, babu abin da koyi da yahudawa zai jawo mana face halaka da fushin Ubangiji.
Sannan kuma iyaye Wallahi ku ji tsoron Allah! Ku sa ido a kan yaranku domin wallahi za a tambaye ku a kan su domin kiwo ne Allah Ya ba ku!
Ya Allah Ka sa mu fi karfin zukatanmu.