Faɗuwa Jarabawa A Makaranta Shima Jarabawa Ce

FADUWA JARABAWA A MAKARANTA SHIMA JARABAWA NE

Ka sani ya kai Dan'uwa Musulmi mai Imani, Allah da ya halicci mutum ba haka kawai kara zube ya barshi ba, kuma ba a hakan kawai za'a barshi ba, ba tare da an jarabceshi ko ana jarabtarshi ba, dole ne sai Allah ya jarabemu ta inda bama tsammani. Allah yana cewa:

"أَحَسِبَ النَّاسُ أَنْ يُتْرَكُوا أَنْ يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ"
"Ashe mutane sunyi zaton abarsu su ce: Munyi Imani, alhali kuwa ba za'a fitine su ba?" {Ankabut, 29:02}

Akwai lokutan da cin jarabawa ko faduwa bashi da alaqa da kokari ko rashin kokari, kamar yadda faduwar bata da alaqa da yin karatu da yawa ko rashin yi da yawa.

Zai yiwu mutum na da kokari kuma yayi karatu da yawa, amma kuma ya fadi jarabawa, mene ne sababi mene ne dalili? Shi kanshi faduwa jarabawa wata jarabawar ce daga wurin Allah, domin zai iya yiwuwa babu alkhairy a cin jarabawar, faduwar a wannan lokacin sai ya zama shine mafi alkhairi ga mutum. Allah yana cewa:

"عَسَىٰ أَنْ تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَنْ تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَكُمْ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ"
"Akwai fatan cewa ku ki wani abu, alhali shine mafi alkhairi a gare ku, kuma akwai fatar cewa kuna son wani abu, alhali kuma shine mafi sharri a gareku, Kuma Allah ne yake sani, ku baku sani ba". {Bakara, 2:216}

Faduwa jarabawa, jarabawa ce, fitina ce kuma musifa ce, kuma dukansu daga Allah ne (duk da a wani lokacin akan samu laifin daga wurin mu ne), abinda ake bukata ga wanda ya samu kanshi a wannan halin shine yayi tawakkali, yayi hakuri yayi Istirjaa'i ya maida al'amarinshi ga Allah, idan yayi haka; Allah zai taimake shi, Kuma zai kasance cikin masu rabauta in sha Allahu. Allah yana cewa:

"وَبَشِّرِ الصَّابِرِينَ، الَّذِينَ إِذَا أَصَابَتْهُمْ مُصِيبَةٌ قَالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ، أُولَٰئِكَ عَلَيْهِمْ صَلَوَاتٌ مِنْ رَبِّهِمْ وَرَحْمَةٌ ۖ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُهْتَدُونَ".

Allah muke roko ya jarabemu da abinda zamu iya dauka, ya kikaye mu tabewa da zarmiya, ya bamu ikon cin jarabawar duniya da ta lahira.


#AlbanyDabai,
Wadi Hof,
23/01/2019.
Post a Comment (0)