Fitinar Da Ta Ɓullo Wa Matanmu A Yau

*FITINAR DA TA ƁULLO WA MATANMU A YAU!*
.

Ina farawa da sunan Allah Mai rahama Mai jin 'Kai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Madaukakin Sarki. Tsira da aminin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta (ﷺ).

Ya 'Yan uwana musulmi, na tsara zan yi wannan rubutu ne ba don komai ba sai don in ankarar da 'Yan uwa musamman mata da iyaye dangane da wata annoba ta lalacewa da ta tunkaro matanmu a yau.

A kokarin kafirai na ganin cewa sun bata tarbiyyar yaran musulmi, sun cire kunya daga jikinsu wadda aka san mata da ita a addinance da al'adance, da kuma kokarinsu na kawar da manufar aure tare da hana auratayyar gaba daya, sun kirkiro wadansu abubuwa (tools) wadanda Mace za ta iya amfani da su don biyan bukatarta (sexual desires) ba tare da ta bukaci namiji ba. Hakika wannan haďarine mai girman gaske, kasancewar zai hana masu yin aure tare da cire masu kunya, kuma uwa ubama zai iya janyo masu matsaloli a jikinsu da kuma fushin Ubangiji.


Daga cikin waďannan abubuwa akwai abin da ake ce ma *Dildo,* shi wannan wani abu ne wanda ake qera shi da roba (rubber) kuma a yi mashi kirar (shape) irin na al'aurar namiji, suna amfani da shi ta hanyar zura shi a gabansu, wanda su kan sanya wani mai (oil) wanda zai ba su damar shigar da shi cikin al'aurarsu, a haka za su yi ta yi har su gamsar da kansu (Cum/ejaculate).

Sannan akwai *Vibrator,* shi kuma wannan akwai wanda ake jona shi da wutar lantarki (electric), akwai kuma wanda ke amfani da battery (manual), suna amfani da shi ta hanyar wasa da al'aurarsu da shi (masturbation), shi ma dai idan mace ta yi amfani da shi tana samun gamsuwa ba tare da ta bukaci namiji ba. Na'udzubillah!

Akwai *Strapon,* shi kuma wannan shi ma yana da kirar al'aurar namiji, Sannan akwai igiya a jikinshi kamar ďamara (belt), mace za ta daura shi a kugunta sai ta dinga yi wa wata macen irin yadda namiji ke yi wa Mace. Innalillahi wa inna ilaihi raaji'un!

Akwai sauran *Sex toys* kala-kala wanda duk an yi su ne saboda wannan manufar. Kuma mafi yawa daga ciki 'yan madigo (lesbians) ne suke amfani da su.

Asali wadannan abubuwa ana amfani da su ne a kasashen yammaci, wato yankin turawa kenan, amma a yanzu na samu labarin cewa wasu gur6atattu a nan kasar (Nigeria) sun fara yo safararsu (ordering) daga kasashen ketare zuwa wannan kasa tamu mai albarka, kuma ma har ya shigo yankin mu na arewa wanda yanki ne na musulmi, da kunnena na ji wata tana ikirarin cewa ta kusa fara yin safarar irin wadannan kayayyaki tunda ta fahimci cewa mazan hausawa ba su iya biya wa matansu bukata ba (Kun ji karya!), wannan abu ya tada min da hankali matuka, shiyasa na za6i in yi wannan rubutu don farkar da 'Yan uwa game da muni da illar wadannan abubuwa.

Amfani da irin wadannan abubuwa be tsaya a kan *'Yan mata* kaďai ba, da yawa a kan samu *Zawarawa* da *Matan aure* ma suna amfani da shi, musamman matan da mazansu ba su iya gamsar da su. Dayawa mata suna daukar wannan dabi'ar ne daga lalatattun Qawaye a gida ko a makaranta, ko ta hanyar shiga dandali (groups/pages) na 'yan maďigo da labaran batsa a yanar gizo, ko ta hanyar kallace-kallace na fina-finan nuna tsiraici (pornographic videos), da cakuduwa da matan Banza.
.

*ILLOLIN IRIN WADANNAN ABUBUWA.*

—Yin amfani da wadannan abubuwa haramun ne, kasancewar ya sa6a wa hanyar da shari'a ta taskance don biyan bukata, wato *aure* tsakanin mace da namiji.

—Sannan wannan abune da zai iya barazana ga lafiyar mace, kasancewar tana shigar da wani abu jikinta sa6anin wanda aka yi gurin don shi.

—Yin amfani da su yana zubar wa mace da budurcinta tun kafin ta yi aure, wannan zai iya sa koda ta yi aure mijinta ya sake ta ko zargi ya shiga tsakaninsu domin ba ta da wani bambanci da bazawara. Kasancewar tsokar da ke rufe da farjinta (hymen) wanda ke da alaka da budurci (chastity/virginity) zai fita daga lokacin da ta fara amfani da irin wadancan abubuwan.

—Yana cire wa mace son aure gaba daya, sai ka ga mace ta manyanta amma ko maganar aure ba ta yi, domin a nata tunanin ai tana samun duk abin da za ta iya nema daga namiji.


—Ga matar aure, zai cire mata sha'awar mijinta, domin za ta ji ba ta iya samun gamsuwa daga mijinta har sai ta yi wancan abin da ta saba.

—Yana janyowa matsala daga kwakwalwa kamar yawan mantuwa, kasancewar akwai ragowar ruwa (sex fluid) wanda ba ya samun fita sai ta hanyar saduwa da namiji, to wannan ragowar yana komawa ya shafi (affecting) din kwakwalwarta (Central Nervour System).

—Baqaqen aljanu (Jinnul ashiq) za su iya shiga jikinta a lokacin da take wannan abin, kuma za su janyo mata matsaloli masu girma a rayuwarta, ko dai su aure ta su hana ta aure da dan adam, ko kuma ko ta yi auren ta ki samun haihuwa ko kwanciyar hankali.

Wadannan wasu kenan daga cikin illolin wadannan abubuwa.
.

*HANYOYIN MAGANCE WANNAN MATSALA*

—Wajibi ne Iyaye su sa ido sosai a kan kaiwa da komowar yaransu, su san abin da suke yi idan sun kaďaitu a ďaki, su dinga yawan duba (searching) na jakarsu domin mafi yawan 'yan mata masu yin wannan yawo da shi a jaka.

Sannan Uwa ta dinga kokari wajen nuna wa 'yarta darajarta da abin da zai kai ga zubar mata da kimarta tare da kai ta ga fada wa cikin fushin Ubangiji.

Uwa ta koya wa 'yarta ayyukan cikin gida domin ta shagaltar da ita da aikace-aikace, wannan zai sa sha'awa ba za ta dinga mata barazana ba.

—Iyaye su ji tsoron Allah su dinga aurar da yaransu daga lokacin da suka balaga matukar sun samu manemi. Kada a bijiro da wani al'amarin duniya kamar gama karatu d.s.

Mazan da ba su iya gamsar da iyalinsu sakamakon wata lalura su ji tsoron Allah su nemi magani.

—Ki kare idanunki daga kallace-kallacen videos da pics na tsiraici ko karatun littafai na batsa.

—Ki Shagaltu da ambaton Allah, karatun Alqur'ani da salloli na nafila da azumin nafila.
.

Sannan daga karshe ina shawartar hukuma da masu fadi a ji da su sa ido a kan masu shigo da irin wadannan kayayyaki, fasa kauri (smuggling) na shinkafa da makamai ba shi kadai bane matsalarmu, makomar tarbiyyar 'ya'yanmu ma abin dubawa ce.
.

Ya Allah Ka shiryar da mu.
.

*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*

Daga Zauren
*🕌ISLAMIC POST.*

Ku yi sharing don wasu su amfana ta sanadiyarka!
Post a Comment (0)