MAGANIN SAMUN HAIHUWA IN SHAA ALLAAH

MAGANIN SAMUN HAIHUWA IN SHA ALLAH :



TAMBAYA TA 2443
*******************
Assalamu alaikum Malam Allah ya saka da Alkairi Amin. Na dan kwana biyu da Aure Allah be bani haihuwa ba se aka bani wani magani wai inhada da gashin kan mijina ko na danshi inyi turare a gabana (private part) . 

1 Zan daukeshi a matsayin magani ne ko me ?

2 Yaya matsayinshi a addini? Nagode

(daga wata baiwar Allah) 

AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. 

Hakika kinyi nisan hankali da kikayi tambaya kafin ki gudanar da wannan abu. Domin kuwa tabbas ire-iren wadannan magungunan da za'a ce ki dauki farce, ko gashin kai, ko gshin gabanki ko na Mijinki ki rika hadawa kinayi, duk ba daidai bane. Sau da yawa irin wadannan abubuwan sukan hada da abubuwan tsafi ko champi wadanda auwatar dasu zai iya kaiki ga shirka da kafirci. 

Ina yi miki wasiyyah da jin tsoron Allah ako yaushe, aduk in da kike. Tare da bin halastattun hanyoyi domin samun biyan bukatunki na alkhairi. Kuma ki nisanci irin wadannan bokaye masu Kiran jama'a zuwa ga bin hanyoyin shaidan (L. A). 

Ga wasu magunguna nan ki jarrabasu domin samun haihuwa in sha Allahu. 

1. Ki samun 'ya'yan Habbatus sauda (wanda ba'a daka ba) ki rika turara gabanki dashi. In sha Allahu koda Aljanu ne sukayi ajiya acikin mahaifarki, to farjinki, to ajiyar tasu zata lalace kuma mahaifar zata budeq kuma ki samu haihuwa bi Iznil Lahi. 

Alamar ajiyarsu acikin farjinki ko mahaifarki, zaki ga idan kina jima'i da mijinki kina jin zafi, ko kuma babu dandano ko kadan. Amma idan aljanin ne yazo saduwa dake (a mafarki) kina jin dadi. 

Kuma idan kin gama jima'i da mijinki zaki ga maniyyin yana fitowa waje (kamar ana tunkudoshi). To in sha Allahu zaki samu waraka da zarar kin dukufa da yin turaren nan. 

2. Ki samu kwayoyin habbatus sauda din ki soyasu a kasko (sama-sama) sannan ki samu zuma farar saqa mai kyau ki hadasu ki gauraya kina shansu har tsawon sati shida zuwa takwas. In sha Allahu zaki samu rabo. Domin na san wadanda suka jarraba kuma suka dace daga cikin dalibanmu na Zauren Fiqhu. Yanzu haka sun samu haihuwa tun ashekarar da ta gabata. 

3. Ki samu Man Zaitun da Man Habbah da Man Albabunaj ki hadasu waje guda (daidai da juna) sannan ki karanta Ayatur Ruqyah acikinsu tare da Suratu Aali Imraan da Suratul Anbiya'i baki dayansu. Sai ki rika shafawa duk jikinki kuma kina shan cokali guda safe da yamma Kullum har sati shida zuwa takwas. In sha Allahu za'a dace. 

4. Ki samu Man Albabunaj mai kyau ki rika jansa acikin sirinji (bayan an cire allurar) kina matsawa (3 ml) kullum acikin gabanki, sannan ki kwanta tsawon minti 15 har ya ratsa jikinki. 

Shima wannan yakan magance matsalar toshewar mahaifa, ko matsalolin tsiron mahaifa (Fibroid). Ko toshewar Qahon mahaifa (Fallopian tube), kuma koda Aljanu ne suka toshe mahaifar to zata bude da izinin Ubangijin Baiwa. (Shima wannan akwai Daliban Zauren Fiqhu da yawa sun jarraba kuma sun dace. Alhamdulillah). 

5. Ki samu Saiwar Shajaratu Maryam, Kaffu Maryam, ko Shajaratur Ruhban (Duk sunayenta ne) Ki jiqashi acikin ruwa ki rika shansa ko yaushe. 

In sha Allahu koda kina da matsalar rikicewar jinin Al'ada to jininki zai daidai kuma mahaifarki zata bude. Kuma zaki samu haihuwa in Allah yaso ya yarda. 

6. Ki yawaita istighfari mai yawa da Salatin Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Sannan ki rika yawaita sallolin Nafila tare da addu'o'in Annabi Zakariyya (alaihis salam) 

"Robbi Hablee min Ladunka Dhurriyyatan Tayyibah, Innaka Samee'ud Du'a'i".

"Robbi Laa Tadharnee Fardan wa anta Khayrul Waritheen".

Har cikin sujadarki ki rika yinsu. In sha Allahu zaki ga abun mamaki wajen samun ijabah da yardar Allah. 

NOTE : Matar da take yawan bari, ko wacce haihuwar ta dakata gareta ma zata iya jarrabawa. Idan kuma akwai Jinnu lallai tare da ita, za'a iya kiran lambobin Zauren Fiqhu domin samun Qarin wasu shawarwarin (07064213990, 09094623006, 08163621213).

WALLAHU A'ALAM. 

DAGA ZAUREN FIQHU (04/02/2017 18/05/1439).

Idan kina da iko zaki iya bugawa ki rarraba a Masallaci ko Islamiyyah domin amfanuwar jama'ar Musulmai. Amma Don Allah kada agoge mana koda harafi guda kuma kada a chanza wani abu daga cikin rubutun nan.
Post a Comment (0)