WANNAN RAYUWA INA ZAKI DA MU?

Ta Mutu A Dakin Otel Bayan Sun Yi Sallama Da Mijinta Da Sunan Zuwa Bikin Dangi 


Daga Comrade Zakari Adamu Y Kontagora 

Kwanaki kafin tafiyarta, ta roki mijin cewa tana da bikin dangi a Kaduna, ya yarda da cewa ta je.

Ranar tafiyar bayan sun karya kumallo, da zai tafi kasuwa sai yace ta shirya ya ajiyeta a tashar mota. Tayi godiya ta kimtsa. Ta goya jaririnta da bai karasa cika shekara ba. Suna hira har suka isa tashar mota.

Aka saka kayanta ya kawo kudin motar ya bawa dan kamasho, daman tun a gida ya ba ta na tsaraba. Suka yi sallama yayi kwana da motarsa ya tafi kasuwa.

Fitarsa tasha ke da wuya ta yi salati ta ce ma dan kamasho ta yi mantuwa, ta ce don Allah don kada a jira ta a ba ta kayanta da kudinta za ta koma gida ta dauko abin da ta mata din, maimakonn ka da ayi ta jiranta idan motar ta cika, in yaso idan ta dawo sai ta hau mai lodin lokacin 

Fitar ta tasha ke da wuya sai ta tare keke napep (a daidaita sahu) ta ba shi adreshin otel din da zai kaita.

Daman ashe sun shirya da farkanta har ya kama masu daki na iya kwanakin da ta roki mijin ya ba ta a wajen bikin. Tana isa ta karbi mabudi ta shiga, dan kwantawar da ta yi tana jiransa, ashe aikin kaddara, sai rai ya yi halinsa.

Can ba a dade ba sai shi farkan nata ya shigo ya wuce dakin kansa tsaye, yana shiga ya yi magana ya ji shiru, ya buge ta irin na wasa ya ga ba ta motsa ba, ya tabata yaji jikinta sanyi kamar qanqara, anan ya fahimci ba ta da rai. Sai ya yagi takarda a irin wacce ake bari a teburin rubutu na dakin otel ya rubuta yadda suka yi da ita ya ajiye a gefenta da kudin da suka yi alkawarin zai ba ta, ya fice yayi tafiyarsa.

 Ba a ankara ba sai da mai karbar baki na otel din ya ji jaririn da ta zo da shi nata tsala kuka amma bai ji alamun rarrashi ba, ya zo ya kwankwasa kofa, Hajiya, Hajiya? Ya ji shiru, sai ya bude kofa domin ya duba ya ga me ke faruwa, shima ya ankara cewa rai ya yi halinsa, ya fito ya fadama manaja, shi kuma ya kira 'Yan Sanda, suka zo, aka bibiyi wayarta har aka gano lambar mijinta.

Da aka kira shi aka fada masa ya zo ga halin da matarsa ke ciki, ya ce shi kam matarsa tana Kaduna, da aka matsa dai ya zo, lallai ko ya tabbatar matarsa ce, sai ya sa aka kira iyayenta ya ce suje da ita gidansu in 'yan sanda sun gama bincike ayi mata sallah a can, baya ma son a adawo da ita gidansa.

Allah Ka ba mu ikon jin tsoronKa, Ka sa kuma mu iya rike amanar da ke kanmu.
©Zuma Times Hausa.
Post a Comment (0)