MUNGO PARK MABUDIN KWARA 16

16. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
...


 
Ana cikin wannan harmutsi, sai Sarkin Sansandin, ana kiransa Kunti Mammadi, ya fito. Ya ce musu su rabu da ni, don kuwa ni bakon Sarkin Bambara ne, tun daga Sego ya sa yaronsa ya roko ni, saboda haka ba su da ikon taba bakon Sarki. Su bar ni in kwana, gobe wucewa zan yi. Da suka ji haka suka kyale ni amma suka ce lalle sai in hau wani mataki don duk mutanen garin su gan ni. A kan matakin nan aka tilasta ni na zauna har zuwa faduwar rana, mutane kuwa sai turereniya su ke yi don su gan ni, sai ka ce wanda za a kashe.
Zuwa can Kunti Mammadi ya ga abin ya kai iyaka sai ya kori mutane, ya ce in tashi im bi shi. Ya Shiga da ni wata taska a gidansa, ya rufe kofofin, ya nuna mini wani soro, na shiga. Duk da haka dai ban tsere wa Larabawan ba, sai da suka haura katangar gidan Sarkin, suka bi ni har daki. Suka ce wai sun zo ne su ga yadda na ke irin tamu sallar, da yadda na ke cin kwai. Na ce maganar kwai su kawo, za su ga yadda na ke ci. Suka gaya wa Kunti Mammadi. Jim kadan, sai ga kwan kaza guda bakwai, amma danyu. Na ce ban saba da cin danyen kwai ba, sai an dafa. Sai na ga duka sun kalli juna. Ashe wai sun ji Turawa ba su cin dafaffen kwai, sai danye su ke sha. Na ce da Mammadi wannan karya ne, in dai yana sona da cin abinci, kome ya kawo mini sai in ci, amma ban da danyen kwai. Ya sa aka yanke rago, aka yi mani abinci mai kyau. Kashegari da sassafe na bar garin.
Na isa wani garin Filani wai shi Nyamai. Amma Sarkin garin ya sa aka tare ni daga kofa, ya ce kada in kuskura in shiga masa gari. Ya hada ni da dansa ya raka ni, don daga gaba hanyar ba ta da kyau, akwai namun daji masu barna. Muna tafe, sai muka yi kicibis da zaki. Sai na ji dan Sarkin nan ya yi wata magana da harshensa, ya juyo dokinsa, yana nuna mini da hannu wai ni ma in juya mu gudu. To, ni dokina ya gaji, sai na yi kwakkwafa muka wuce, ba mu koma ba. Ni da ban ga zakin da idona ba, sai na zaci dan Sarkin nan ya firgita ne kurum, bai ga wani zaki ba. Can an jima sai na ji ya sake cewa, “Subuhana lillahi !" In duba haka sai ga katon zaki ja, kusa da mu, ya sunkuyad da kansa tsakanin kafafunsa kamar zai yi tsalle ya diram mana. Gabana ya fadi, na yi shawarar in sauka in kwanta a karkashin cikin dokina, ko da zakin zai wo tsalle, ya zama ya fada a kan dokin ne, ba a kaina ba. Sai dai na cije, na bi dan Sarkin muka wuce. Amma don tsananin tsoro, tun da na kafa wa Sarkin dawan nan ido ban iya cirewa ba sai da muka bace.
Ga mu nan sai wani gari wai shi Modibbo, a bakin Kwara. Wannan gari yana da ban sha’awa kwarai, ga kifaye iri iri. Amma kuma tun da na ke ban taba jin gari mai yawan sauro kamarsa ba. Duk tsawon dare na kasa runtsawa saboda sauro. Kai, kwanciya ma wannan ta gagara. Sai na tashi tsaye, in kai gwauro in kai mari a cikin daki, ina ta kora da malfata ina bugun jikina bif bibif! Da gari ya waye jikina duk ya yi burr da cizonsu, domin ba ni da abin rufa. Tufafina duka sun TAPIYA u FARKO 65
zama tsumma. Cizon sauron nan ya sa na tashi da zazzabi mai zafi. Sarkin garin ya ce bai yarda in sake kwana masa a gari ba, kada im mutu. Muka wuce tilas. Dokina ya kasa, ga shi ba shi da lafiya, ga yunwa. Mun kai wani rafi, sai ya fadi. Da ni da mai rakiyana muka yi iyakar kokarimmu ya tashi, muka kasa. Na zauna waje daya, ina duban wannan abokin shan wahala nawa. Da na sake kokarin tashe shi, na ga dai babu dama, sai na cire linzamin, na kwance sirdin na dauka, na zuba masa ciyawa a gabansa, na bar shia wurin. Ganin wannan hali da ya ke ciki ya sa tausayi ya kama ni, tsoro kuma ya kama ni. Don na kyauta zaton ba za a dade ba irin abin nan da ya same shi, ni ma zai same ni. Yunwa da ciwo da gajiya za su sa in kasa, im fadi, in halaka, kamar yadda suka halaka dokin nan!
Da wannan bacin zuciya na bar dokin tilas, na bi dan rakiyana. Shi yana bisa, ni ina kasa dauke da sirdi da linzami. Muka yi gaba, sai Kea. Muka sami Sarkin a kofar gidansa, wani tsoho ne mara fara'a, mara imani, mara son mutane. Da na fada masa irin halin da nake ciki, sai ya ce shi dadin baki ba ya kwashe shi, im bar masa garinsa. Rana ta fadi, ga yunwa, ga gajiya, ga ciwo, kuma bugu da kari ga rashin wurin kwana. Ana cikin haka, sai ga wani mai jirgi ya nufo garin zai wuce a kan Kogin Kwara. Sai Sarkin ya daga masa hannu. Da ya zo, ya ce ya dauke ni ya kai ni garinsu. Na yi sallama da dan rakiyana, na ce ya duba mini dokina, in ya wartsake ya ba Sarkin Modibbo ya ajiye mini. Na Shiga jirgi sai wani babban gari wai shi Silla. Sarkin Silla shi kuma ya hana ni wurin kwana, ga shi kuwa ana ruwa. Da kyar ya yarda na shiga wani dabi, wanda don danshi in an shuka dawa a ciki sai ta tsira. Cikin daren sanyi ya kama ni, kafin gari ya waye sai zazzabina ya dawo.
Can dare ina kwance, ga sanyi, ga jante, ga gajiya, ga yunwa duka sun rufe ni, ga ni kusan tsirara, kuma babu abin sayen abinci ko sutura, sai na ji wani abu ya tuko mini a zuciya, raina ya baci. Tun ran da na baro gida, sai yau ne kadai na ji lalle na karai a zuciya. Yau kadai na ji ba na iya ci gaba cikin tafiyan nan tawa. Akwai abubuwa da yawa wadanda za su hana in wuce Silla. Na farkonsu dai, damina ta fara zurfi, tafiya ba ta yiwuwa sai a jirgin ruwa, tsabar farin kudin da Sarkin Sego ya ba ni kuwa ba su isa in yi hayar jirgi ba. Na biyu, wauta ce in ce zan ci gaba tun da ya zama ba ni da lafiyar jiki isasshiya, yadda zan iya daure wahalar da ke gabana. In da domin rashin kudi ne, ko guzuri kurum, ba zan ko yi shawarar komawa baya ba. Ban da rashin lafiya kuma, kullum hadarin gamuwa da Larabawa sai karuwa ya ke yi. Ganin yadda suka tasam ma halaka ni a Sego da Sansandin, sayad da rai zan yi a banza, ban kai ga bukatata ba. Saboda haka na ce gwamma in koma gida da dan abin da na gano, don kada im mutu ya bace. Amma kuma sai na zama gaba zaki, baya sayaki. Ba na iya ci gaba, kuma ba na iya komawa baya. Tsakanina da Gambiya ya kusa mil dubu, ga shi ba ni da lafiya, ba ni da doki, ba ni da kudin saye, ga damina ruwa ko yaushe. To, amma kuma im ban koma ba, wurin wa zan zauna ?
...
(c) 2016 Waziri Aku
Post a Comment (0)