MUNGO PARK MABUDIN KWARA 18

18. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...


 
Da tashi na isa wani gari wai shi Song da yamma, amma da ganina mutanen garin suka rufe kofar garinsu. Na kwanta a gindin wata itaciya daga wajen gari. Zuwa can dare sai na ji rurin zaki yana kusato ni. Na firgita, na sheka sai kofar garin. Na bugi kofar, na buga, na yi @bukarmada kururuwa, na ce da mutanen su bude mini, ga zaki zai cinye ni. Sarkin kofa ya ce in tsaya sai ya fado wa Sarki tukuna. Suka bar ni tsaye har wani lokaci, ga zakin yana gewaya ni. Can zuwa tsakar dare sai ga Sarkin da kansa ya zo, ya ce za a bude mini kofa, amma lalle in kwana a ruwan kofa ne, ban da shiga gari. Suka bar ni tsaye har wani lokaci, ga zakin yana gewaya ni. Can zuwa tsakar dare sai ga Sarkin da kansa ya zo, ya ce za a bude mini kofa, amma lalle in kwana a ruwan kofa ne, ban da shiga gari. Aka bude mini, muka shiga da dokina, muka karasa dare a kofa, da safe na wuce.
NA ZAMA MALAMIN TSIBBU
Ina cikin tafiya, ran nan na isa Taffara. Na tarar Sarkin garin ya mutu, 'yan Sarki ana ta kokawa, kowa yana neman ya hau gado. Kila saboda bakin cikin mutuwar Sarki da harmutsin masu neman sarauta, shi ya sa mutanen garin babu wanda ya shiga harkata. Ko’ina na tafi neman wurin kwana sai a kore ni, ko'ina na tafi baran abinci sai a hana ni. Tilas na zauna a waje, a gindin wata itaciya, ruwa ya yi ta ba ni kashi, ga yunwa. Zuwa can sai wani mutum da muka zo garin tare ya zo ya yi kirana. Na bi shi har masaukinsa, sai ya fito da abinci, ya tsuguna a kofar zaure daga ciki, ni kuwa ya ce in tsuguna daga waje mu ci ga shi kuwa ana kwara ruwa. Na yi mamakin wannan abu. Na ga dai mutumin da ya kira ka ya ba ka lomar tuwo lalle kaunarka ya ke, amma kuma mutumin da ya bar ka a waje cikin ruwa shi yana zaure, ba ka sa shi cikin @bukarmada masoyanka. Amma da na tambaya sai ya cc mini tun da ya ke shi bako ne, ba daidai ne ya shiga da kowa cikin zauren gida ba, sai da iznin mai gidan. Tilas dai haka nan na kwana bisa tarin wata danyar ciyawa.
Da gari ya waye na yi gaba sai Suha. Na sami Sarkin ya kame bakin kofar zaure, yana tsaye da fuska mirtik. Na tambaye shi dawar sayarwa, ya ce mini babu. Na ce to, ya taimake ni da dan abin karin kumallo, ya ce ya hana. Na zura wa wannan bakin mara imani ido, na yi zaton kin bako ya sa shi daure fuska haka. Sai na ji ya kira wani bawansa da ke noma a gonar kofar gida. Har na fara murna a zuci, ina zaton zan sami biyan bukata ne.
Da yaron ya zo sai na ji ya ce masa ya haka rami. Yaro yana haka, shi kuwa yana tsaki yana cewa da harshensu, “Dankatu, jankara Iemen" wai “aikin banza, wannan masifa ke nan.” Sai na yi zatoa da ni ya ke yi, kuma ga rami ana hakawa mai zurfi kamar kabari. Kada ka so ka ji yadda zuciyata ta ke harbawa a lokacin, jikina ya dauki kadawa, don na yi zaton zai tura ni ne a ciki ya rufe ni da raina ! Wata @bukarmada zuciya ta ce im bar dokina in tsere. Na taka likkafa zan dare in tsere, sai ga gawar wani yaro an dauko rabe rabe. Da zuwa sai aka warba ta a cikin ramin yaraf, kamar mushen jaki. Sai na ji Sarkin ya yi zagi ya cc, “Nafula attainiyata," wai hasarar kudi. Ashe wai yaron nan bawansa ne ajalinsa ya sauka, shi ya sa Sarkin ke jin haushi bai samu ya sayar ba. Ko juyayin rai bai yi ba, sai kukan kudinsa kurum.
Na dai haye dokina, na rabu da mugu. Ga ni nan sai Kulikorro. Garin duk Arna ne, amma na sauka a gidan wani wanda ya musulunta, don da can ya yi wa Larabawa bauta, sun shigad da shi Addinin Musulunci. Sana’arsa kiri ne, ya tashi wannan gari ya sauka wancan, yana sayad da tufafi. Ya kai ni daki, ya kawo mini abinci mai kyau da madara. Zuwa can sai ga shi ya zo ya ce wai ya ji an ce ni Kirista ne. Ya kuwa sami labari Kirista suna da maganin kome na duniya, saboda haka yana rokona in rubuta masa maganin mahassada da makiya. Ya kawo mini allo da alkalami. Na fa rasa ta cewa, in na ce ban iya ba, ya ce na ki ne. In kuma na yarda, to me zan rubuta? Na dai kama allo na rubuce kaf da irin @bukarmada rubutummu, na mika masa. Nan da nan ya samo dan ruwa a kwarya, ya wanke rubutun nan ya shanye kakaf, har ya lashe allon da harshensa. Ya yi godiya, ya yi mini abinci mai kyau.
A karshen wannan jiha ta Afirka, mai rubutun saifi ba ya boyuwa. Saboda haka nan da nan labari ya bazu a gari, har kunnen Sarkin garin. Zuwa can sai ga dan Sarkin, uban ya turo shi da abinci da kudi wai in rubuta masa maganin samun kudi. Na rubuta, na karanta masa da Turanci da karfi ya ji, ya yi murna ya yi godiya. Can sai kuma ga wani ya zo. Shi kuma ya ce maganin makiya ya ke nema, na rubuta na ba shi. Kai, kafin kwanciyar barci dai ban yi sukuni ba, masu neman magani iri iri suka yi ta duruwa mini. Na sha rubutu har yatsuna suka gaji. Na dai zama malamin tsibbu sosai. Da gari ya waye aka kawo mini shinkafa tana tururi, ga madara cike da kwarya, na ci na sha, na yi sirdi na bar garin.
Duk tafiyan nan a cikin fadamu na ke yi, wani wurin in shiga ruwa iya gindi, wani wurin iya kirji, wani wurin in kafe a tabo, sai da kyar zan zaro kaina in zaro dokina. Ina cikin tafiya a cikin kungurmin daji, na tasam ma wani gari wai shi Sibidulu, sai na ga mutum ya fito daga sagagi ya kama linzamina. A jima kadan sai ga wadansu ’yan’uwansa. Suka ce sai in sauka. Na sauka, suka caje jikina kaf, @bukarmada suka tube ni tsirara, suka tafi da kayana duka, har dokina. A haka suka bar ni tsirara haihuwar uwata. Amma ni duk wannan bai taba mini rai ba kamar hulata da na rasa, domin duk takardun da na rubuta labaran tafiyata a ciki su ke.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: D61EAFAE
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)