22. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...
Da ranar tashi ta zo, Karfa da sauran duka, kowa ya fito da bayinsa. Aka cire musu sarka a kafa, aka yi musu kangi da kiri a wuya. Aka rarraba su hudu, ko wadanne kanginsu guda. Bayan kangin nan, ko wane bawa yana dauke da kayan ubangijinsa. Nan da nan ayari ya hadu, mu duka mutum saba'in da uku. Daga cikin talatin da biyar bayi ne, shida maroka ne masu waka. wadannan hayar su aka yi musamman, don wakarsu tana kara karfi a zuciya, yadda za a manta da gajiya. In an zo wani gari kuma, da shiga sun dinga yi wa mutanen garin kirari ke nan, yadda za su ji dadi su ba fataken nan masauki.
Da shiri ya gamu cif, sai aka tashi. Mutanen Kamaliya duk, babba da yaro, mace da namiji, suka fito rakiyarmu. Masu addu’a suna yi, masu bacin zuciyar rabuwa da ’yan’uwa suna yi, mata kuwa suna ta rusa kukan rabuwa da mazansu. Da muka bar garin kamar rabin mil sai aka yi ban kwana muka ci gaba. A ranar farko wadansu daga cikin bayi suka tabke, sun yi watanni ba su tafi ko’ina ba, suna cikin sarka. Har na tuna wadansu bayi mata, daya babbar mace daya budurwa, da suka kasa a hanya. Ubangijinsu ya jawo bulala ya yi ta bugunsu sai da suka fadi, sa’an nan ya bar su tare da yaransa uku, ya ce in sun ki tafiya su daure su su ja su a kasa da karfi. Wai a ja mutum kamar yadda a kan ja mushen jaki!
Ita babbar wadda ta fi tabkewa, ana kiranta Nili. Labarin Nili yana da ban tausayi, kuma ya isa ya tausasa zuciya kome karfinta, ya kuma isa ya nuna iyakar muguntar bauta. Domin kashegarin ran da Nili ta kasa, muna cikin tafiya har da ita, sai ta sake gajiyawa, kafafunta duk suka kumbura. Karfa ya ce a karbi kayanta, amma duk da hakanan dai inda ta cire kafa nan ta ke mayarwa don gajiya. Can wajen tsakar rana, an sauka ana hutawa, sai muka ga zuma a kogon wani ice.
Wadansu suka doshi wurin, zuma kuwa ta ce ga ta nan a kammu, ta rufe mu da harbi, duk muka watse. Nili ba ta da damar gudu, tiias ta tsaya zumun nan suka yi ta harbinta. A taron dai duka ni ne kadai ba ta taba ba, don kuwa ni na fara garzayawa a guje na tsere. Bayan zuma ta lafa, aka zo aka sami Nili jikinta duk ya kumbura. Bayan an cire mata karin daga jikinta, aka yi aka yi da ita ta tafi, ta ce sai dai a kashe ta, amma ba ta dagawa daga nan. Ta ce ta fi son mutuwa ma da ranta. Aka buge ta, aka buga, amma ta cije. Daga nan sai Karfa ya ce a dibiya ta bisa jaki. Amma ba ta iya mikewa bisa jakin, don ciwo. Saboda haka aka sari itatuwa biyu dogaye aka daure su kamar amuku, aka dibiya ta, bayi biyu suka dauke ta har inda aka sauka.
Kashegari da safe aka tashe ta daga barci. Amma ba ta iya ko mikewa tsaye, balle tafiya. Sai aka ciccibe ta, aka dora a kan jaka, aka nemi a kwantad da ita rub da ciki a bayan jakin, a rutsa wuyan jakin da hannuwanta a daure, kafafuwanta kuma a gama su a dame a cikin jakin. Amma jakin ya ki tafiya, in an taba shi sai ya dinga tutsu, har dai ya jefad da Nili. Aka yi da ita ta yi tafiya, ta kasa. Wadansu sai cewa su ke, “A yanka ta, a yanka ta.” Da na ji haka, na ce a raina ni kuwa in Allah ya so ba na ganin yadda za a danne mutum a yanka kamar rago. Saboda haka sai na yi gaba. Bayan an yi dan nisa, sai ga daya daga yaran Karfa ya zo yana rataye da zanen Nili a sandarsa. Na tambaye shi irin abin da aka yi wa baiwan nan, sai ya ce, “Ai Nili kuma sai wata !"
Sai na ji gabana ya fadi, tausayi ya kama ni. Na ce, “Am ba ka zanenta ladan yanka ta da ka yi ne ?"
Ya cc ai Karfa ya ki yarda a danne ta a yanka, sai dai am bar ta ita kadai a hanya. Na tabbata cikin biyu daya ya faru ga Nili, ko dai ta mutu, ko kuwa wani naman daji ya cinye ta. Don ba ta ko iya tashi tsaye, balle ta gudu.
Wannan abu ba na mantawa da shi har abada. Ko yaushe na tuna sai hankalina ya tashi, don kome karfin ran mutum, in ya ga irin halin da Nili ke ciki, da yadda aka yad da ita a dajin Allah, lalle jikinsa ya yi sanyi. Babu wanda tausayinta bai kama shi ba a cikin ayarin duka, da bawa da da. Raina bai taba baci game da bauta ba kamar ran nan. A cikin wannan hali muka wuce, muka bar Nili. Ko me ya same ta bayammu? Sanin wannan hali sai Allah !
Muka yi ta ratsa daji da kurama, mu hau wannan dutse, mu gangare wannan fadama, har dai muka iso wani gari wai shi Tambakunda. A nan muka yi mugama kwana hudu, muka huta.
A lokacin hutun nan aka yi wata gawurtacciyar shari'a tsakanin daya daga cikin fataken da mu ke tafe tare da wani mutumin garin. Shi farken nan ya auri wata mace, ’yar mutanen garin. Sun haihu ’ya’ya biyu, sai ya yi tafiyarsa, ya bar ta har shekara takwas, ba shi ba labarinsa. Da ta gaji da zama ba miji, sai ta yi aure. Ta haifi ’ya’ya biyu da sabon mijin. Ran nan kwaram sai ga mu mun sauka. Farke ya nemi matarsa a wurin iyayenta, suka ce ta yi aure. Da jin haka, sai gaban muhukunta. Manyan gari da sauran jama’a duka aka taru a gindin babbar itaciya tsakiyar gari, yadda suka saba bisa al’ada. Nan aka bude shari’a, da farke da sabon miji, kowa ya fadi tasa maganar. Muhukunta suka gaya wa farke cewa ba shi da ikon karbar matarsa, don kuwa ya guje mata har shekara takwas.
Bisa al'adarsu kuwa, im mutum ya guje wa matarsa ta shekara uku tana jiransa bai komo ba, tana iya auren wanda ta ga dama. Suka ce amma ba za su yanke hukunci ba sai irin abin da matar ta zaba. Mace fa ta rasa ta cewa. Shi dai farke, ko da ya ke ya fara tsufa shi ne mijinta na fari, kuma ga shi da samu. Shi kuwa wannan, ko da ya ke shi ba shi da wadata, amma ga shi yaro ne. Can dai sai dukiya ta yi rinjaye, tsoho mai samu ya datse yaron da ba wuri. Matar farke ta komo wurinsa. Wannan hanya ta shari'a ta ba ni sha'awa don ko a cikin al’ummar da kansu ya waye masu rubutacciyar shari’a, ba za a yi wadda ta fi wannan adalci ba.
Ga mu nan har muka isa Tendakoba, a nan wani bawa ya kasa. Da ubangijinsa ya ga alama ba zai iya ci gaba ba, sai suka shirya da wani mutumin garin a kan musaya. Ya ba da bawan, aka ba shi wata yarinya baiwa. A nan kuma na sake ganin abin tausayi. Ita dai baiwan nan ko kadan ba ta san am musayad da ita ba. Sai da gari ya waye, mun shirya, ayari yana shirin tashi, sai ta zo tare da bayi 'yan'uwanta mata. Sun zo su yi kallommu, su kuma yi mata ban kwana. Tana tsaye, sai ta ga ubangijinta ya fizgo hannunta kurum, aka dibiya mata kaya, aka yi mata kangi da igiya a wuya, sai tafiya. Bacin ranta a lokacin ba ya misaltuwa. Nan da nan idanunta suka cika da hawaye, da kuka ta yi ban kwana da abokan bautarta.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: D61EAFAE
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada