MUNGO PARK MABUDIN KWARA 23

23. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
bukarmada.blogspot.com
...


 
Ga mu nan har muka isa Tendakoba, a nan wani bawa ya kasa. Da ubangijinsa ya ga alama ba zai iya ci gaba ba, sai suka shirya da wani mutumin garin a kan musaya. Ya ba da bawan, aka ba shi wata yarinya baiwa. A nan kuma na sake ganin abin tausayi. Ita dai baiwan nan ko kadan ba ta san am musayad da ita ba. Sai da gari ya waye, mun shirya, ayari yana shirin tashi, sai ta zo tare da bayi 'yan'uwanta mata. Sun zo su yi kallommu, su kuma yi mata ban kwana. Tana tsaye, sai ta ga ubangijinta ya fizgo hannunta kurum, aka dibiya mata kaya, aka yi mata kangi da igiya a wuya, sai tafiya. Bacin ranta a lokacin ba ya misaltuwa. Nan da nan idanunta suka cika da hawaye, da kuka ta yi ban kwana da abokan bautarta.
Daga wannan garin, bayan mun taba ’yar tafiya mun ketare wani rafi, sai na ji mawakan nan da ke tare da ayari duk sun garke da waka. Dalili wai ashe mun shiga kasar Gambiya ke nan. Kuma al’adace, in ayari ya iso nan wurin lafiya, sai a yi ta murna da shiga “kasar da rana ke faduwa," watau yadda a ke kiran Gambiya a Afirka.
Ran nan, ko da na duba haka, sai ga Kogin Gambiya yana malala. Na yi ajiyar zuciya, farin ciki ya rufe ni. Rabona da in yi murna haka tun ran da na ga Kogin Kwara a bara. Kila mai karatu zai ce na cika gishirin baka, amma in na tuna irin masifar da na sha, da wadda na ke cikin sha game da ciwo, da yunwa, da huntanci, da wulakanci, da halaka iri iri, lalle in yi murna da godiya da ganin Kogin Gambiya. Saboda haka, da na ji an ce mun shiga kasar Gambiya, sai na ji kamar na shiga kasar Turai ne.
Kashegari, da muka taba tafiya sai muka shiga Wulli. Kamar dan hantsi kankane muka isa babban birninsu Madina. A farkon littafin nan na fadi yadda Sarkin garin ya karbi bakuntata, ya yi mini karimci a bara lokacin da na ratsa ta cikin kasar. Sai aka ce mini Sarkin Wulli ba shi da lafiya. Da ya ke Karfa bai yarda a yi mugama a Madina ba, ban sami ganin Sarkin ba, amma na aika a gaishe shi, kuma gaya masa na komo, na wuce zuwa gida. Na ce a gaya masa na ji ba ya da lafiya, Allah ya sawwake.
Muna tafe har muka isa Jinde, watau inda Dr. Laidley ya tsaya muka yi ban kwana da ya zo yi mini rakiya, a lokacin da zan shiga Afirka. Da na zo wannan gari sai na yi hamdala, don ina ji kamar mutumin da ya yi shekaru ne cikin daki mai duhu, sa'an nan aka zo da shi bakin kofa za a bude masa ya fita ya ga haske. A Jinde nan ne karshen ganina da wani mutumin kasarmu, a nan ne karshen yin maganata cikin harshen Turanci, yau wata goma sha takwas.
Da ya ke an ce yanzu kasuwar bayi ta fadi, sai na yi wa Karfa shawara, na ce ya kamata ya bar bayinsa a nan, har lokacin da za su fara kadari kana ya kai su Gambiya. Ya yarda, ya sami aron wuri ya yi bukkoki, ya kuma sami gonar noma. Za mu yi sallama, amma Karfa ya ce a'a, shi ba zai bar ni ba sai ya ga fitata Afirka lafiya lau zuwa Turai. Saboda haka muka dauki hanya sai Pisania, garin Dr. Laidley. Amma ko da ya ke ina cike da dokin ganin Pisania, duk da haka da na zo rabuwa da bayin nan abokan tafiyata, sai duniya ta yi mini baki kirin. Na dubi halin da su ke ciki, na kuma tuna sun rabu da ’yancinsu ke nan har su tafi kabari, sun rabu da kasarsu ke nan, da iyayensu da 'ya'yansu da 'yan'uwansu da masoyansu. Cikin tafiyar da muka yi da su ta wajen mil dari shida, ko da ya ke suna cikin bacin zuciya, cikin kangi, ga rana, ga kaya a kansu, da dare su kwana cikin sarka, ga duka, ga zagi, amma duk zamansu cikin wannan hali har su kan ji tausayina su taimake ni. Sau da yawa sun danne nasu kishin a kan hanya, sun kawo mini ruwa na sha. Sau da yawa, ba tare da an sa su ba, sun karyo ganyaye sun shimfida mini a zango, lokacin da kwana ya same mu a daji. Sau da yawa sun nuna mini halaye nagargaru, wadanda ba na tsammanin samunsu wurin mutumin da ke cikin duhu, mara addini. Ko a wurin mai addini ma sai nadiran. Hasali dai su ne abin tausayi, abin a taimaka. Muka dai rabu, su hankalinsu a tashe, nawa a tashe. Ba ni da kome da zam ba su, sai addu'a na yi musu, na roki Allah ya ba su iyayen gida nagari ya kuma kawo ranar da wannan masifi ta bauta za ta kare a Afirka.
Muka isa Tendakunda da maraice, muka sauka a gidan wata tsohuwa ana kiranta Seniora Kamilla. Da can ta zauna a kusa da Turawa a Gambiya, har tana jin dan Turanci. Ta san ni sosai kafin in shiga Afirka, amma yanzu ganina cikin tsumma da takalma fade, ga suma duguzum, ba ta iya gane ni ba. Ba ta ma yarda ni Bature ne ba da farko, zatonta ni wani tsohon Balaraben Hamada ne wanda duniya ta juya masa baya. Da na ce mata ni ne Mungo Park, mutumin Ingila, sai ta dube ni shiru, tana mamaki. Ta ce mini duk Turawan da ke Gambiya sun zaci na halaka, ba wanda ya sa zuciyar ganina. An gaya musu wai Larabawan Ludamar sun kashe ni, kamar yadda suka kashe Manjo Houghton. Na tambaye ta labarin yarana, Johnson da Demba, ta ce ai har yau babu dayan da ya komo cikinsu.
Da muka shiga tadi da Turanci, sai Karfa ya tsaya kurum yana kallommu, yana mamaki, don bai taba jin harshen Ingilishi ba. Da ya dubi kayan da ke cikin dakin matan nan, sai duk ya rude. Ya ga kamar a wata duniya ya ke dabam. Bai taba ganin kujera ba sai a ran nan, bai taba ganin gado da labule da sauran kaya irin na Turawa ba. Aka kawo mana ruwan wanka, da muka yi muka kare aka ba mu abinci. Bayan mun ci mun taba dan tadi, sai muka kwanta.
Kashegari da safe, sai ga Mr. Robert Ainsley. Ashe ya sami labari na zo, ya zo tariyata. Cikin wata goma sha takwas sai ran nan na ga dan’uwana Bature, sai ran nan na kaje muryata, na yi ta sheka Turanci Mr. Aisnley ya ba ni dokinsa na hau, ya gaya mini Dr. Laidley ya yi kaura daga Pisania, ya koma wani gari wai shi Kaye Ya ce amma shi har yanzu yana Pisania, kuma da ya ke Dr. Laidley ya yi ’yar tafiya, sai mu je gidansa in sauka har ya dawo. Muka dunguma, da ni da shi da Karfa. Can zuwa sha biyun rana sai Dr. Laidley ya komo. Da ganina ya zo da hannuwa bude, ya rungume ni saboda murna da farin ciki.
Ya kawo mini tufafina da na bari a hannunsa, na cire garen farin da Karfa ya ba ni da wandon fari, na shiga kaya irin na Turawa. Aka ba ni aska, na yi gyaran fuska, na share dogon gemun da ke habata da saje. Da Karfa ya gan ni cikin wannan hali sai ya yi sha'awa kwarai, amma ya ji zafin aske gemuna da na yi. Ya ce cire gemun nan ya tashe ni daga dattijo, ya zama da ni karamin mutum !
Da muka zauna da Dr. Laidley, na kwashe labarina duk na gaya masa. Na kuma fada masa irin karimci da taimako wanda na samu a wurin Karfa, tun daga ran da na sauka gidansa har yau. Dr. Laidley ya yi masa godiya, ni kuma na ce ya ba shi dukiya, ta bayi biyu, goron godiyata gare shi ke nan. Karfa ya yi murna, amma babbar murnarsa ita ce da na zo da shi wurin Turawa, ya ga abubuwa masu ban mamaki. Im muna tadi wani lokaci ya kan yi shiru, sai kuma ya ce da harshen garinsu, “Fato fing inta fang," watau wai “Lalle Bakin Mutum bai san kome ba." Ya tambaye ni irin abin da ya isa gani a Afirka, wanda har ya sa na taso daga Kasar Turai na zo don in gani. Ya ce shi a ganinsa mutumin da ke kasa inda a ke yin kaya masu kyau da ban mamaki, irin wadanda ya gani a gidan su Dr. Laidley, me kuma zai yi kwadayin gani a Afirka, dajin Allah kawai ? Na ce masa akwai abin gani a Afirka da yawa, da cikin mutanenta da cikin dajinta. Muka yi sallama, ya koma wajen bayinsa a Jinde. Muka rabu muna marmarin juna, yana godiya ina godiya. Lalle na gode masa.
Bayan na huta, na fara mai da karfina da jikina, ran nan sai ga wani jirgin bayi ya zo daga Amirka. Da ya ke babu jirgi daga Turai, babu kuma labarin zuwansa, sai na yi shawara zan shiga wannan jirgin im bi ta Amirka, daga can in nufi Ingila. Na kare rubuce sauran abin da ban rubuta ba, watau irin abin da na gani, da abin da ya faru tun daga tasowarmu daga gidan Karfa, a Kamaliya zuwa Gambiya. Na hada da sauran takarduna, na shirya labarin tafiyata cikakke, babu abin da ya bace. Da jirgin nan zai tashi na shiga. Muka yi sallama da Dr. Laidley da sauran abokaina Turawa na Gambiya. A cikin jirgin akwai bayi 130. Daga cikinsu akwai Musulmi ashirin da biyar, wadanda kwanan nan bauta ta same su. Sun iya rubutu da karatun Larabci.
Na tabbata tafiyata a cikin wannan jirgi tare da bayin nan ta yi musu amfani. Don kuwa duk yadda mutum ya kan firgita sun firgita, sun gigice, don ba su san inda za a kai su ba. Ba su san irin abin da zai same su ba. A Afirka ana ba su labari wai Turawa suna sayen bayi, suna tafiya da su can bangon duniya, suna sayar wa wadansu Arna ne masu cin mutane. Kome kuwa karfin halin mutum, tilas ya yarda da wannan labari, domin ba su taba ganin wanda aka tafi da shi ya komo ba. Saboda haka bayin nan suka rika jin kamar wadanda za a tafi da su jakara a yanka. Amma na yi iya kokarina bisa in karfafa musu zuciya, su yarda ba kashe su za a yi ba. Duka cikinsu ba wanda ya gaskata ni, ban kuwa zarge su ba. Su a zatonsu kome na ke fadi karya ne, na fi son ’yan’uwana Turawa da su. Amma ni dai ban fasa ba, kullum na kan zo wurinsu mu yi ta tadi, da haka har muka kai wani tsibiri cikin Tsibiran Indies na kusa da Amirka. A nan na sauka, muka yi ban kwana da bayin nan. Daga nan ban san kuma abin da ya same su ba. Daga Afirka zuwa Amirka mun yi kwana talatin da biyar a cikin bahar.
Bayan na huta kwana goma a tsibirin nan, ran nan sai jirgi mai tafiya har Ingila ya samu. Na shiga ran 24 ga Nuwamba, muka ratsa bahar, muka iso Falmouth, wata tashar jiragen ruwa a Ingila, ran 22 ga Disamba. Sai ran nan kafata ta taka kasar Ingila. Na yi wa Allah Ubangiji godiya da ya kai ni Afirka ya fito da ni, har na komo gida lafiya. Yau rabona da Ingila shekara biyu da wata takwas.
...
WANNAN SHI NE KARSHEN LABARIN TAFIYAR MUNGO PARK TA FARKO A AFIRKA.
RANAR ASABAR MAI ZUWA, ZA MU SO JIN RA'AYINKU A KAN KO DAI MU CI GABA DA LABARIN TAFIYAR MUNGO PARK TA BIYU, KO KUMA MU JINGINE WANNAN LABARI SAI ZUWA GABA, MU ZAKULO MUKU WANI LABARIN DAGA KANDAMIN LITTAFIN NAN NA DARE DUBU DA DAYA?
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: D61EAFAE
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)