MUNGO PARK MABUDIN KWARA 26

26. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...


 
Daga wannan gari za mu shiga wani Kungurmin daji, wai shi Dajin Simbani. Isyaku, da ya ke shi dan kasa. ne, ya san dajin, kuma yana tsoron shiga cikinsa kwarai, ya ce da kyar ne ba za mu gamu da mutanen Bondu ba. Ya ce wai ’ya’yan Sarkin kasar suna basasa a kan maganar gadon sarautar ubansu. Labari kuwa ya watsu ko’ina, an san Nasara za su ratsa kasar dauke da dukiya takaka. Saboda haka ya tabbata ’ya’yan Sarkin nan za su yi rigen tare hanyarmu, don sun san cikinsu duk wanda ya sami kayan da mu ke dauke da shi zai ci nasarar yakin. Muna kara matsar dajin, Isyaku yana dada karya zuciyata. Ran da fa za a shiga, sai ya ka da wani bakin rago, ya tsaya ya ja doguwar addu’a a kansa tukuna, sa'an nan ya sa wuka ya yanka, ya bar shi nan, ya ce mu shiga.
Muna tafe har muka kawo wata mashayar ruwa da a ke kira Faraba, muka duba, amma babu ruwa. Ganin haka sai barorimmu suka tube, suka shiga hako ruwa. Nan da nan kuwa ya samu, muka sha, muka yi girki, muka yi ban ruwa. Daidai zuwammu wurin, muna cikin sauke kaya, sai farfadiya ta buge wani soja wai shi John Walters, ya fadi. Kafin sa’a guda, rai ya fita. Muka shiga hakar kabari, muka binne shi, kuma don gaba a tuna da shi, na sa wa rijiyar suna Rijiyar Walters. Da gari ya waye, muka yi aji, muka kuga kai cikin bakin daji. Mun yi ta ganin kashin zaki a hanya. In ya tsiba shi, sai ya taro kasa da kumbobinsa ya rufe, kamar yadda kyanwa ke yi.
AN DAURE ISYAKU
Mun tashi daga wani gari da a ke kira Jallakotta, ran 20 ga Mayu. Muka dauki hanya, muka yi ta yi har muka kai wani babban birni wai shi Bade. Sarkin garin babban Sarki ne, amma dagacin Sarkin Wulli ne. An ce azzalumi ne, ya kan yanka wa ayari kudin fito da yawa. Ashe kuwa za mu dandana zaluncinsa.
Da saukarmu, muka aiki ja gorammu ya fada wa sarkin mun sauka. Sai ya turo dansa da maraice tare da mutane ashirin da shida, kowa da bindiga, ga kuma mutanen gari takaka suna biye. Da dan ya zo, ya ce mu ba da abin da za mu bayar a kai wa ubansa. Na aiki Isyaku ya kai masa duwatsu goma. Da ya kai, sai ya wo kora da su. Sai na debi wadansu biyar na kara, na tashi da kaina sai wurinsa. Ko da na ga yawan bindigogin da suka yi wa dan Sarkin nan lifidi da irin duban da ’yan lifidin ke mini, sai na san bai zo da niyyar lalama ba. Da na ba shi duwatsu goma sha biyar, ko dubana bai yi ba. Na yi rarrashin duniyan nan, amma ya ki karba.
A nan gabana sai na sa hannu a aljihu na jawo farar takarda da fensir, na rubuta wa wani Hafsan Sojammu na ce ya shirya soja, kila za a buga a nan. Na sa kowa ya dura harsashi a bindigarsa, ya kafa banati. Na ce da tafinta, Isyaku ya fada wa dan Sarkin na ratso kasashen sarakuna da dama ba su hana ni wucewa ba, amma in ubansa bai yarda in shiga cikin kasarsa ba, to, sai in koma in dauki wata hanyar. Jin haka fa sai ya kama zage-zage. Bayan ya tafi ya gaya wa uban yadda muka yi, mu kuma muka daura niyyar komawa baya.
A daren ran nan sai mutanensa suka kama dokin Isyaku. Da muka tura shi ya je bin sawun maganar a cikin gari, sai suka kama shi, suka kwace bindigarsa da takobinsa, suka hada shi da itace suka daure, suka yi ta duka.
Na fa rasa abin da zan yi. Ga matar Isyaku da dansa suna ta kuka, ga mutanensa sun firgita, suna shirin watsewa. Muna da karfin da za mu fada wa garin mu kona shi cikin dare, amma na ga im mun yi haka za mu karkashe talakawa wadanda babu ruwansu cikin wannan sha’ani. Sai muka daidaita shawara da ni da Mr. Anderson da Laftana Martyn, muka ce mu bari sai gobe. Im ba su sako Isyaku ba, mu fada musu da rana kirikiri, mu kona su.
Gari na wayewa sai ga Isyaku, sun sako shi. Kuma sai ga mutane Sarkin ya aiko su su gaya mini shi ba ya son fada da ni, amma ba shi yiwuwa ayari ya shige kasarsa ba tare da biyan kudin fito ba. Saboda haka yana so in tafi Bade in kai masa abin nan da na bayar jiya. Da na ji haka, ni kuma na ce ban yarda in tafi ni kadai ba, tun da ya ke bai san girman amana ba, ga Isyaku ya shiga garin jiya ya kama shi ya daure. In yana so in zo, to, zan zo da soja ashirin ko talatin. Bai yarda da haka ba, sai ya ce zai aiko da dokin Isyaku, ni kuma in tafi da gaisuwar da zam bayar, mu gamu da manzonsa a tsakanin garin da zangommu in karbi dokin, mutanensa su karbi gaisuwar, kowa ya juya. Na ce na yarda. Muka gamu a tsaka da mutanen Sarki, na ba su kudin fito, suka ba ni dokin Isyaku, suka juya, na juyo. Amma sun hana bindigar da takobin, suka ce wai tun daren jiya aka kai su wani kauye, amma an aika a komo da su, ko mun tashi yaro zai same mu da su a hanya. Har yau ko labari !
Muka yi ta tafiya har muka kai Jeningalla. Na ce mu yi zango a nan, ba don wai mun gaji ba, don dai ina da labarin shaharar garin wajen aikin tama. Ina so in ga yadda su ke yi. Na tafi inda su ke aikin na gani, amma na ga su tasu rahoniyar ta narka tama ta bambanta da irin ta Mandingo.
Da muka tashi muka yi ta tafiya har dare ya yi, kana muka sauke kaya a dokar daji. Cikin dare sai ga kyarkeci suka zo suka kama jaki guda, suka cinye. Daga inda suka kama jakin zuwa inda mu ke kwance da ni da Mr. Anderson bai fi yadi ashirin ba. Da gari ya waye muka yi gaba, har muka wuce wani gari wai shi Koba, inda na taba kwana a zuwana na farko. Yanzu garin duk ya zama kango, don a ture ma maganar mutum, ko itaciyar dandalin tsakiyar garin an kone ta. Ka ji sharrin yaki !
Bayan mun taba 'yar tafiya kadan sai muka iso wani dogon dutse. Hanyar da ta hau bisa kansa tana da kyau, amma da wuyar hawa, tun ba ga jakuna ba. Da muka hau muka kai tsakiya, muka duba kasa, sai muka ga kewayen dutsen karkara ce mai ban sha'awa ta milla ta tafi. Don kyaun gani, har na sa wa dutsen suna Dutsen Kallo. Da muka gangare muka sake tarad da wani garin da yaki ya mayar kango. Mun kuma yi ta ganin kafar giwa, da kashinsu danye wanda bai dade da yi ba.
Muna cikin tafiya sai muka gamu da wani ayari za shi Gambiya. Mutanen suka ce mana wai za su su fanso wani ne da aka kama, aka ce in ba a kai fansarsa cikin 'yan watanni ba, za a sayad da shi a bauta. Suka sauke, aka yi zango a nan, aka shiga shirin girkin kalaci. Ashe ba mu sani ba, a lokacin mutanen Isyaku sun ga zuma, sai suka tasam ma sha. Mu dai ba mu farga ba sai muka ji harbi kurum ! Muka watse, dabbobi kuma suka fashe da mu da su kowa ya kama gabansa. Aka yi sa'a, a Iokacin duk an sauke wa jakuna kayansu, amma mutane da dawaki sun sha harbi da kyau. Wutar da aka hura don girki kuma ta kama ciyawar wurin, kafin a yi haka dajin duk ya kama wuta.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)