28. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
....
Kashegari muka yi gaba. A hanya wani kafinta Bature cikin mutanena, ana kiransa James, ya kasa. Yana fama da atini, ba ya iya ko zama kan jakinsa. Tilas na sa wadansu soja su rika shi a kan jakin kada ya fado. Da ciwo ya ci karfinsa sai ya debe zuciya ga warkewa, ya sa rai ga mutuwa. Ko an rika shi a kan jakin sai ya kwace ya fado kasa. Kai, har dai ya ce shi a bar shi, ya gwammace ya mutu. Da dai na ga zai hana mu sauri, kuma ga alama mutuwar zai yi, sai na bar shi a wani kauye. Na sa shi a hannun sarkin garin, na ba da abin likkafani, na ce in ya mutu a binne shi, mu kuwa muka wuce. Kashegari da safe sai ga yaron sarkin ya zo ya gaya mana wai James ya rasu tun jiya da yamma.
ASALIN BAKIN CIKI
Ran nan muka sauka a kofar wani gari, muka kafa tanti. Zuwa can sai ga iskar ruwa ta taso, ta daddaage tantin nan duk, ruwa kuwa ya dinga rangada mana duka. Muka jika sharkaf, ga gajiya, ga yunwa, ga duhu. Ba a ko ganin tafin hannu, balle mu nemo tantimmu daga inda iska ta jefar, mu sake kafawa. Malafata kuwa ta bi iska, ban sake ganinta ba. Muka dai hakura, muka kwanta haka nan cikin jikakkun tufafimmu, ruwa bisa, ruwa kasa. Can da asuba kuma wani ruwa ya sake saukowa kamar da kwarya, ya kare duk a kammu. To, ruwan nan na farko shi ne asalin bakin cikimmu a wannan tafiya, don shi ne asalin rashin lafiyar mutanemmu duk.
A da, ina ta murna za mu kai bakin Kwara ba tare da ko ciwon kai ba. Kwaram John Watlers ya mutu, kafinta, James ya mutu. Ga shi kuma ruwa ya buge mu, duk ba mu da lafiya. Da faduwar ruwan farkon nan mutanena duk sai ji ka ke ha, ha, sun kece da amai. Rashin lafiya dai ya shigam ma kowa tun daga ran nan. Wadansu suka murmure, wadansu kuwa shi ne sanadin barinsu duniya. Babban abin da ya ke kara karya ni a zuci, shi ne ganin duk tafiyar da muka yi har yanzu ba mu fi rabi ba.
Da safiya ta yi, na shiga gari, na gaisa da Sarkin, na kuma ce masa in ya yarda ina so in ga wurin da a ke hakar zinariya. Ya yardam mini, ya hada ni da wata mace, ta kai ni na gani, na ba ta lada. Da muka isa sai na ga wani fili da ramuka ko ina a ciki, ashe wai shi ne ramin zinariyar. A bakin ko wane rami babu kome sai tsakuwa kurum, wadansu farare, wadansu bakake, wadansu ja.
Sai na ga matan nan ta rusuna a bakin wani rami. Ina zaton dai raminta ne. Sai ta dauki kore biyu, ta sa guda ta debi kasar da ke tare bakin ramin, ta kuma debi ruwa da daya ta shiga riga, kamar yadda a ke rege shinkafa. Ni dai ina tsaye ina kallo kurum. Can sai ta ce mini da harshen kasarsu, “sanu mira," watau, “Dubi kurar zinariya" Ko da na duba, ni ban ga kome ba sai wadansu 'yan duwatsu ja-ja kamar albarushi. Har na fara karyata ta a zuciyata, ina zaton wannan tsakuwar banzar ita mutanen Afirka ke kira zinariya, sai na ji matar ta ce, “Sanu affilli" wai “Dubi zinariya." In duba haka sai kuwa ga zinariya ta asalin, kamar ruwan kwai a hannunta. Na karba na juya ta a hannuna, na sake juyawa. Na ce ta sake wanke wani, ta sake, sai ga kwayoyin zinariya har ashirin da uku. Ta ce wani lokaci in an yi sa'a a kan sami dunkulen zinariya daya kamar dunkulen hannun mutum.
Ba na iya fadin yawan zinariyar da a ke hakowa a kasan nan, amma na tabbata tana da yawa. A nan kasar duka ma’auninsu na sayad da zinariya wahi abu ne da su ke kira minkilli. Shi kuwa minkilli, abin da ke yinsa tili kissi, watau ’ya’yan wani itace na kasar. Nauyin tili kissi guda shida shi ne daidai da nauyin minkilli daya. A kasar Ka’arta su ma nasu ma’aunin ’ya’yan itace ne, ana kiransu jabace kissi. Shi kuma guda ashirin da hudu ke yin nauyin minkilli guda. A Kasson ’ya’yan tsamiya ne nasu ma'aunin, tsabarsu guda goma sha biyu ke yin minkilll guda. Ni ban sayi zinariya ba, amma Isyaku ya saya da yawa, ya biya da albarushi.
Mutanemmu marasa Iafiya ko yaushe karfinsu sai raguwa ya ke ta yi. Tilas dai muka sauka a dawakimmu, da ni da Mr. Anderson, muka dora su, mu kuma muka shiga kora jakuna. Da muka isa masauki aka kirga jakuna,sai aka ga ba guda. Batan wannan jaki zai fi batan kome zafi a gare ni, don shi ke dauke da madubin da na ke duba taurari, na ke sanin lokaci, da kuma wanda ke nuna mana hanya. Saboda haka sai muka koma muka shiga nema, amma ba mu gan shi ba. Sai na ce da Sarkin garin ya sa a nemo, in an samo, zam ba shi dutse goma, wanda ya samo kuma zai sami ladan dutse ashirin. Yamma na yi sai ga dan Sarkin ya zo ya ce an sami jaki. Na shiga gari na biya ladan na kamo abina. Don kada haka ya sake faruwa, sai na kwance kayan daga kan jakin na daura a kuturin dokina. A lokacin nan sauran ayari sun yi gaba, sai ni kadai, sai wadansu soja uku marasa lafiya da na tsaya ina rarrashinsu su yi gaba. Karfinsu ya kare kwarai, ga ciwo, ga gajiya. Saboda haka, ko wane gindin itace muka zo sai su ce za su kwanta nan su mutu. Tilas in tsaya im ba su magana, im ba su magana, sai da kyar sa’an nan su kan yarda su ci gaba. Im muka isa wani itacen kuma su nemi kwanciya. Da haka dai har muka kai Fankiya inda ayari ya ke, muka yi zango.
Ran 16 ga watan Yuni na tashi daga wani gari wai shi Tumbi. Bayan kaya ya yi gaba, ni kuma na sa kafata guda a likkafa zan hau doki, sai na ji gaisuwa daga bayana. Na waiga, sai ga wani aminina wanda ya nuna mini mutunci a Iokacin da na zo Afirka da farko. Shi malamin makarantar Alkur'ani ne. Ya kula da ni ainun, ya yi mini kyakkyawar karba a gidansa. Ya ce ya sami labarin na sake komowa kasarsu zan wuce, shi ya sa ya zo don mu gaisa. Na yi murna da ganin wannan mutum, amma da ya ke kayana duk sun yi gaba, ban sami abin ba shi ba. Sai nace ya raka ni har inda za mu sauka, dabarata watau in yi masa 'yar kyauta don alherin da ya yi mini da. Muka kama hanya, muna tafe muna tadin rabuwarmu.
Mun ci kamar mil guda sai muka sami Hinton, daya daga cikin mutanena, yana kwance rashe-rashe, ba shi da lafiya, kusa da shi ga dokinsa yana kiwo. Muka tarar mutanen wurin sun sace bindigar da ke rataye a sirdinsa, sun kuma sace rigata da na ba shi ya rike mini. Na raba kafa na sauka, na dauke shi na aza bisa nawa dokin, ni kuma na hau na rike shi, na kora nasa dokin a gaba kamar jaki. Muna cikin tafiya sai in ga Hinton ya yi nan lau, zai fadi, in tarbo shi, sai kuma ya yi nan lau, in tarbo shi. Ya dai kasa zama a sirdin, ni kuma hannuwana duk sun gaji. Da kyar muka ci kamar mil shida. Da na ga abin ba shi yiwuwa, tilas sai na sauke shi, na bar shi nan, muka yi gaba da ni da malamin makaranta. Bayan mun bar Hinton da kamar mil daya sai muka sake tarad da wadansu mutanena biyu, su ma sun kasa. Na hau da daya kan dokin Hinton, na dora dayan kan nawa na rike shi. Can gaban rana tsaka sai muka isa wani gari wai shi Sarimanna. Da sauka na tura mutum guda da doki, na ce ya je ya zo da Hinton. Aka zo da shi a rirrike, har yanzu dai yana jin jikin nasa.
Na kwance kayana, na ba malamin makarantar rawani da liyari biyu da duwatsun wuya, na ce ya kai wa iyalinsa. Ya yi murna kwarai da gaske, ya yi mini godiya matuka. Da za mu rabu kuma na kawo Linjila ta Larabci na ba shi, ya ce in Allah ya so sai ya karance ta daga farko har karshe. Muka yi ban kwana. Da gari ya waye muka shirya, sai na ga alamar Hinton da Sparks ciwonsu ya yi zafi kwarai. Saboda haka na sa su a hannun dagacin garin, na bar masa kudin saya musu abinci. Na ce in sun warke, to, ya hada su da wani ayari su koma Gambiya, in kuma rai ya yi halinsa, ga kudin binne su.
Da muka tashi sai Tajemmiya, dan gari ne, amma da mugun Sarki. Da ya yanko mana kudin fito sai muka ga im mun yarda mun biya, mun kar kammu, don ya washe mu ke nan. Sai muka ki, shi kuma ya hana mu wucewa. Kwana uku muna ja-in-ja da shi, sai da kyar ya ce mu wuce. Cikin kwanakin nan uku jante ya rufe ni. Ko fita ba na iya yi, haka kuma galibin mutanemmu. Safe duk sai mun bararraka bawon itacen kuni da muka yiwo guzuri, am ba kowa ya kurba. Da muka sami hanya, sai muka yi gaba. Amma mutum guda cikimmu ana kiransa Rowe, ya tabke da zazzabi, saboda haka na debi abincin kwana goma sha takwas na ba wani mutumin kirki a garin na ce ya yi jiyyarsa. Na ba shi ladansa na amba goma. Daga baya na sami labarin Rowe yana samun sauki a kullum. A wannan tsakanin ba a yi tafiya mai nisa sai mun tarad da gari ko kauye. Wannan ya taimake mu kwarai da gaske, don marasa lafiya da dabbobi kan samu su dan huta.
Ran nan mun isa wani kauye, sai wani cikin mutanemmu wai shi William Roberts ya sake kasawa. Na yi rarrashin duniyan nan, amma ya ce ba zai iya yin gaba ba, ya fi so a bar shi a nan har ajalinsa ya sauka. Na ba shi takarda ya sa hannun cewa ba ni ne na yashe shi ba, shi ne don kansa ya zabi a bar shi. Muna tafe har muka kawo wani babban tsauni da a ke kira Kullali. Tsaunin nan dogo ne kwarai, ba ya hawuwa ga mutum. Daga can samansa ya yi fadi, sai ciyawa a ke gani kore shar ko yaushe. Mutanen kasar sun ce wai wani tabki ne a can bisan, don da damina su kan tafi gindin tsaunin su rika samun kunkuru wadanda ruwa ya turo daga can sama.
Ga mu nan tafe gabas sak, har muka iso Kimbiya. To, a Iokacin ni ina can baya ina koro jakunan da suka zubad da kayansu, saboda haka mutanena sun riga ni isa garin. Ko da na iso sai na ga duk gari ya yamutse, mutanen garin kowa sai gudu ya ke yi zuwa gida, yana jawo kwarinsa da baka.
...
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi