29. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
....
Ga mu nan tafe gabas sak, har muka iso Kimbiya. To, a lokacin ni ina can baya ina koro jakunan da suka zubad da kayansu, saboda haka mutanena sun riga ni isa garin. Ko da na iso sai na ga duk gari ya yamutse, mutanen garin kowa sai gudu ya ke yi zuwa gida, yana jawo kwarinsa da baka. Na tambaya me muka yi musu, aka ce ba kome. Ashe wai burga ce, kudi su ke so. Sun sami labari, tun kafin isowarmu, ga mu nan tafe dauke da dukiya mai yawa, amma duk cikimmu babu mai lafiya, saboda haka da fada mana sai mu bi kurum. Da suka ga mun ki kula su, mun wuce, sai suka tare mu, suka ce ba mu da ikon wucewa sai da yardar Sarkinsu. Suka tsaya sai mu koma gari, mu kuma muka ce mun ki komawa. Sai wani cikinsu ya yi wuf ya rike kalfazurun dokin sojammu, ya nufi gari yana ja. Amma da ya ga sojan ya dura harsashi a bindigarsa ya aune shi, sai ya saki. Wadansu mutanen kuwa suka tasa jakunammu a gaba suna korawa, suka nufi gari.
Kai, sha'ani dai duk ya rude mana. Sai sojammu suka dura wa bindigarsu harsashi, suka soka banati. Ganin haka sai muka ga mutanen nan suna togewa nesa. Sai soja suka sake koro jakunan da aka nufi da su gari, suka komo da su. Mutanen garin suka taru a kofar garinsu. Da na isa, na tarad da Sarkin da Isyaku suna magana fada fada. Da na tambayi dalili, Isyaku ya ce wai niyyar mutanen garin su kwace kayammu ne. Na juya, na ce da Sarkin ko ya san wa suka yi wannan niyya? Ya nuna mini kamar mutum talatin masu kwari da baka sai na yi dariya, na ce yana zaton wadannan mutane su iya fada da mu? Na ce amma in Sarkin yana zaton za za su iya, to, ya fada musu su je su sake taba jaki daya tak da hannu kurum, yanzu su ga fada da cikawa.
Jim kadan sai na ga kowanensu ya ajiye bakansa a kasa, suka ce ba su iyawa. Sarkin ya ce a gaya wa mutanena su kora jakunansu su tafi abinsu. To amma da ya ke da yawa cikimmu ba mu da lafiya, har kila wani zai kasa ci gaba, ya komo ta wannan garin, sai na ga wauta ce in yarda mu rabu da Sarkin barambaram. Saboda haka na ba shi amba hudu, na ce da shi mu girma da arziki ya kawo mu, ba mu zo yaki ba. Amma fa kowa ya taba mu, ba za mu kyale shi ba, sai karfimmu ya kare. Muka yi sallamar arziki.
Muka kama hanya, muna tafe jakunamamu suna faduwa don santsin duwatsu. Ga mu nan dai, har Sullo. Da isarmu sai dokin Martyn ya fadi ya mutu. Abin mamaki, muna kicikicin haka rami mu binne, sai mutanen garin suka zo suka ce sun hutasshe mu, mu bari. Har na fara yaba kirkinsu sai na ga ashe ba kirki ba ne nama ne Allah ya kawo musu, don suna cin doki. Nan da nan duk sai wuri ya yamutse, sai ji ka ke kakas, kas, kas, wukake na gamuwa, ana ta ture-turen juna! Kafin dai a yi haka da tsokar dokin nan da kayan cikinsa babu ko daya duk an wasashe, sai kashi. Mu dai sai muka tsaya kurum muna kallo.
Daga wannan gari abin da ya yi gaba duk kasa ce mai ban sha'awa, da kauyuka masu kyaun zama, da karkara mai alabarka kewaye da su. Akwai kuma rafuka da koguna masu zurfi, ga duwatsu masu kyaun gani. Babban abin da ke damuna da kogunan Afirka shi ne rashin dadin kan masu fito a cikinsu. Ko ina muka cin musu sai sun yi ta ja mana rai, suna tsuga mana kudi.
A wani gari wai shi Sakoba nan na ga yadda mutanen Afirka ke narka zinariyarsu, suna kera ta. Na fada a baya cewa ni ban taba sayen zinariya ba, amma Isyaku ya saya da dama. To, ita ya ba wani makerin farfaru a nan garin, ya ce ya kera masa zobe. Nan da nan sai na ga makerin ya debi yumbu, ya yi wani dan karamin kasko, ya shanya a rana har ya bushe. A ciki ya zuba zinariyar tsabarta, bai hada ta da kome ba. Ya zuba gawayi a wurin zuga, ya dibiya dan kaskon nan mai zinariya a bisa gawayin, ya shiga zuga. Can wuta ta kama kasko sosai, ya yi ja zir, sai muka ga zinariyar ta fara motsi. Daga nan dai har ta narke ta zama ruwa. Makerin ya dauke, ya juye a wani dan dogon rami da ya yi a kasa da tsinke. Ruwan zinariyan nan ya bi tsawon ramin, ya daskare. Da ta yi sanyi, ya sa hantsaki ya dauko ta, ya rike ta a kan wuta da hannu guda, yana zuga da hannu guda, har ta sake yin zafi. Sai ya aza ta a kan uwar makera, ya sa hama ya buga ta a hankali, ya maishe ta kusurwa hudu. Da ta zama haka, ya sake maishe ta cikin wuta ta yi zafi, sa'an nan ya kama ta da hantsaki biyu ya yi ta murdawa, ya tankwasa ta ya gama bakin, sai ga zobe ya tashi.
In aka tashi wannan gari, akwai wani babban kogi ana fito a cikinsa. A can muka daidaita abin da za mu biya a fisshe mu da kayammu da dabbobimmu. Jiragen kanana ne, ba su daukar abin da ya fi kayan jaki guda da rabi, mutane kuma ba su wuce uku, ban da mai tuki. Ta haka aka yi ta ketarewa da mu, a kai a zube, a komo a kwashi wadansu. Wani jirgin da ya dauki bindigogi da wani Bature wai shi Mr. J. Cartwright, yana zuwa tsakiyar kogin sai ya kife. Nan da nan masu
jiragen nan suka zo suka yi nitso, suka yi ta nema, da kyar suka samo bindigogin, da shi Mr. J. Cartwright. Suka saka shi cikin jirgi, suka tuko shi tudu. Ko da suka ajiye shi, na duba, sai na ga ba rai. Na shimfide shi, na daddanna cikinsa yadda Likitawa suka ce, amma a banza. Ya mutu. Muka haka masa kabari a bakin rafin, muka tsaya har maraice, muka binne shi.
Tun ran da na ke ban taba ganin mutane barayi irin mutanen wajen nan ba. Kome namu sai so su ke su sace. Da ce dare ya yi, mun shiga fama da barayi ke nan. Ga namun daji da ke kewaya mu ko yaushe, suna neman mutum ko dabba.
Muna cikin tafiya muna iso wani dutse da a ke kira Sankari. A nan na ga wani abin da ban taba gani ba. A gindin dutsen na yi ta ganin tarin duwatsu kanana da madaidaita, kamar yadda a kan fasa don aikin ginin sumunti. Da na tambayi wani dan kasar dalilin wannan sai ya gaya mini wai a da akwai babban birni a wurin ana kiransa Madina. Wai mutanen birnin suna zaune, wata rana sai kwaram Sarkin Ka'arta ya zo ya fada musu da yaki ba shiri. Suka tsere, amma mutanen Ka'arta sun yi ta binsu, suna kisa a kan hanya. To, wadanda suka mutun nan sai aka yi musu kabari a inda kowa ya fadi. Tun lokacin nan in danginsu sun zo wucewa, ko su nawa ne, sai kowane ya jefa dutse a kan kabarin dan'uwan nan nasa, don ya rika tunawa da shi.
Wannan tafiya tamu cike ta ke da bakin ciki. A kullum daga ciwo sai binne gawa. Wadansu har ciwonsu kan yi tsanani, su zauna a hanya su ce a bar su nan a daji su mutu. A cikin irin wadanda muka bari a baya har da wani soja da a ke kira Roger M'Millan. Ran 2 ga Yuli ya tashi da zazzabi mai zafi har yana maganganu. Saboda haka na ga ba shi yiwuwa mu wuce tare da shi. Sai na bar shi a wani kauye wai shi Sanjikotta. Na ji zafin barin mutum irin Roger, wanda tun yana yaro karami ya ke bauta wa kasarsa, Ya shekara talatin da daya yana soja, sau goma sha biyu yana daura kofur, ya kuma daura saje sau tara. Amma kowane lokaci sai a fizge igiyar ya komo farabiti. Dalilin da ke sa haka kuwa shi ne abutar da suka daura da giya. An yi, an yi, ya kwance wannan abuta, ya ki. Mashayi ne kwarai. In ya dinga kwarara giya a cikkinsa sai ya bugu idonsa ya rufe. Daga baya labari ya same mu wai Roger ya rasu.
Ran nan muna cikin tafiya sai muka iso wani babban kogi da mutanen kasar ke kira Bawulima, watau "Jan Kogi.'' Muka daidaita da masu fito zam biya amba sittin don a fid da mu da kayammu da dabbobi. Amma Isyaku ya ga alamar har dare zai yi mana ba a fid da mu duka ba, sai ya ce zai fid da jakuna da kansa. Aka daura wa jakunan igiya a wuya ya rike, ya shiga wani jirgi. Hannu guda yana tuki, guda yana jan jakuna. Suna kaiwa tsakiyar kogin sai kado ya taso wa Isyaku, ya kama shi a cinyar dama, ya ja shi sai karkashin ruwa. Mu da ke gaba sai ihu mu ke, wai don kadon nan ya saki.
....
(c) 2016 Waziri Aku
(c) 2016 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada