30. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
Ran nan muna cikin tafiya sai muka iso wani babban kogi da mutanen kasar ke kira Bawulima, watau "Jan Kogi.'' Muka daidaita da masu fito zam biya amba sittin don a fid da mu da kayammu da dabbobi. Amma Isyaku ya ga alamar har dare zai yi mana ba a fid da mu duka ba, sai ya ce zai fid da jakuna da kansa. Aka daura wa jakunan igiya a wuya ya rike, ya shiga wani jirgi. Hannu guda yana tuki, guda yana jan jakuna. Suna kaiwa tsakiyar kogin sai kado ya taso wa Isyaku, ya kama shi a cinyar dama, ya ja shi sai karkashin ruwa. Mu da ke gaba sai ihu mu ke, wai don kadon nan ya saki.
Ashe shi Isyaku bai tsorata ba. A can karkashin ruwan sai ya laluba har ya sami kan kadon nan, ya kuwa danna yatsarsa guda cikin idon kadon. Da kado ya ji zafi sai ya saki, Isyaku ya taso bisa rawa, ya wo ninkaya yana neman gaba don ya karbi wuka. Amma kafin ya kawo, kadon ya sake juyowa ya kama shi a daya cinyar, ya sake nutsad da shi. Har wa yau shi kuma Isyaku sai ya koma ga dabararsa ta farko. Ya danna yatsunsa cikin idandunan kadon nan da karfin gaske, kadan ya sake sakinsa tilas. Kadon ya taso bisa ruwa, duk ya gigice, sai da ya marzaye kana ya bi tsawon kogi ya bace. Isyaku kuma ya taso bisa ruwa, ya yi ninkaya ya kai gaba.
Cinyoyin nan nasa biyu suka dinga zub da jini, bayan cije-cijen da ke bayansa. Zurfin ramin da hakoran kadon nan suka yi ya kai inci hudu. Nan da nan muka tura Isyaku gaba, don ya je ya sauka a wani kauye ya huta kafin mu zo.
Ni kuma a lokacin jante ya rufe ni, in na mike sai in ga dif, jiri yana daukana. Muka dai yi gaba sai Bulinkumbo, inda Isyaku ya ke jirammu. Muna zaune ina wanke ciwon Isyaku, kwaram sai muka hango wani farin mutum yana zuwa wajemmu tsirara, haihuwar uwa tasa. Ashe Ashton ne, daya daga cikin marasa lafiyan da muka bari a baya. Ya ce wai wadansu mutanen kasar su uku suka tare shi a daji, suka tube kayansa duka. Muka ba shi sutura ya sa.
Al'amari duk ya rude mana, ga rashin lafiya tana ta karuwa, ga dabbobin da ke daukar masu ciwo su kuma sai shiriricewa su ke yi. Wani jakina da na sayo amba 50, tafiyar mil uku kadai ya yi daga inda na sayo shi sai ya dage kafa. Muka yi juyin duniyan nan ya yi tafiya, ya ki, da taba shi sai ya kwanta. Ashe ba shi da lafiya ne da muka kai wani kauye sai ya mutu, mutanen garin suka yi ta shagali da namansa, kafin kyaftawa ba ko kashinsa, sun kwashe sun cinye.
Duk cikin taron babu wanda na fi jin ciwon rashin lafiyarsa kamar Isyaku. Ran nan muna zaune sai ya fara atishawa. Kafin dan lokaci sai idonsa ya kada ya yi ja, hancinsa na zubar majina, zufa na keto masa ta ko ina. Ciwo ya zama biyu ke nan, ga cizon kado, ga jante. Ba shi yiwuwa in tafi im bar Isyaku a baya, don za mu shige ta Kaminum ne, an kuwa ce duk bisa hanyarmu babu rikakkun barayi irin mutanen Kaminum. Ba shi kuma yiwuwa mu zauna wuri guda har Isyaku ya warke, don kuwa ciwon nasa babu alamar warkewa da sauri. Damina kuma tana kara zurfi, ruwa yana dada yawa. Har wa yau kuma duk cikin tarommu, da ’yan kasar da mu baki, babu wanda na yarda da shi kamarsa. Bugu da kari ga abincimmu ya kare, sauran na kwana biyu kadai ya rage mana, ga kasar suna fama da yunwa.
Na dai daure, na tsaya kwana uku ina jiyar Isyaku. Na tura mutanensa biyu da jakuna, da tsakiyar wuya biyar, na ce su je Sankara su sayo shinkafa. Ran 6 ga Yuli fa ran nan na ga tashin hankali. Dukammu muka tashi babu mai lafiya, sai mutum guda kadai. Ran 9 ga wata masu sayo shinkafa suka komo, Isyaku kuma ya sami sauki kwarai da gaske. Hankali ya fara kwanciya, kashegari sai muka yi harama muka tura gaba.
MUN TAKI NASIHA
A zuwana Afirka na farko, na gamu da sarakunan kirki kamar su Duti Mammadi, da Sarkin Sego, na kuma gamu da miyagu, kamar su Ali. To, a wannan zuwan ma haka. Amma duk cikin wadanda na ratsa kasarsu a yanzu ban ga mara kirki kamar Sarkin Mallabu ba, wanda a ke kira Mansa Numma. Da na sauka garin, na kwana, da safe muka tafi fada, da ni da Isyaku tafinta. Na kai wa Sarkin gaisuwar abubuwa kamar dari, da manya da kanana, don na ji an ce mugu ne. Ko madubi kurum biyar na kai masa, turmin jan siliki goma, dutsen wuya talatin da uku, da sauran tarkace. Duk wannan ban da gaisuwar Erujama kanensa, da ta dansa, da ta fadawa, da goron maroka.
Bayan mun komo masauki muna zaune, sai ga yaron Sarkin ya komo da abubuwan nan duk. Na tambayi dalili, ya ce wai Sarki ya ce ba ya so sai na kara masa da bindiga mai daurin azurfa.
Da dai na ga babu dama, sai na ba da bindigar. Amma kuma na yi wata babbar sa'a, Mansa Numma da kansa ya aiko ya ce yana son ganin sojana. Saboda haka sai na sa masu 'yar lafiyar jiki suka yi ado, suka saba bindiga, su ka daura macin oda sosai, na tura su cikin gari suka yi maci. Inda suka ga wani karamin itace mai dan kauri, sai su rusa masa bindiga nan da nan su yi ratsa-ratsa da shi. Dabarata da yin haka wai in nuna wa Mansa Numma muna da karfin tsare kammu. In kuma yana shawarar fada mana ne, to, ya fasa.
Duk muka kosa mu sami sallama mu tashi, don mutanen Mallabu manyansu da yaransu, mazansu da matansu, duk barayi ne. Ni dai ban taba ganin gari da satar wannan ba. Amma ba abin mamaki ba ne, tun da ya ke Sarkinsu shi kansa muguntarsa ta fi ta barawo. Yana kuma da 'ya'ya sun fi talatin wadanda ke duban kansu 'ya'yan Sarki ne su, saboda haka suna iya kwace kayan kowa, ba kome.
Ban tabbatar da muguntar Mansa Numma ba sai da na gangara bakin wani rafi na kusa da garin. Me na gani? Kasusuwan mutane ne har ga kawuna wajen talatin. Na tambayi dalili, aka ce wai duk kasusuwan wadanda suka yi wa Sarki laifi ne, ya sa aka kashe su.
Asalatu na yi kashegari sai muka tashi. Amma duk da sammakon nan namu, mutanen garin sai da suka taru mana a lokacin da mu ke ajin kaya, ko barci ba su yi ba suna jirammu. A kwanan nan daya da muka yi sai da suka nuna halin nasu, suka sace mana riguna huda, daurin tsakiya daya, bindiga daya babba, biyu kanana, da dai abubuwa da dama.
Tun jiya, da na ga son satar mutanen Mallabu ya yi yawa, sai na ce da Sarkin ya ba mu dan rakiya. Ya hada mu da babban dansa. Da muka bar garin, ga mu fa tare da dan Sarkin, amma sai da mutanen nan suka bi mu suka fizge kaya a bayan jaki guda. Da ni da dan Sarkin da Mr. Martyn muka cim ma dam fizgen nan, muka kwato kayan. Kafin kuma mu juwo gun ayarimmu wani barawon da ke labe a bakin hanya ya fizge bindiga, ya fada daji da ita.
Kai, haka dai muka dinga fama da barayin nan marasa kunya. Na tuna lokacin da muka tasam ma wani kauye, jakunammu suka yi ta faduwa saboda rashin dadin hanya. Na ratse daji wai don in duba ko akwai wata hanyar mai saukin bi. A lokacin kuwa ina rike da bindigata, amma da hannu daya kurum. Can sai ga 'ya'yan Mansa Numma su biyu. Sai dayan ya zo gabana, dayan kuwa ya tsaya daga bayana ya ce in dam masa taba. Na juya wai don in gaya masa ba ni da ita, sai na ji fit, na gaban ya fizge bindigata, suka ruga cikin daji. Ni kuma ban tsaya wata-wata ba, sai na yi titif na diro daga dokina, na zaro takobina, na bi su. Kama kama kama, af, ina? Wannan bindigar ta hallaka. Na koma na fada wa wansu wanda ke tare da mu. Na tambaye shi abin da ya kamata in yi im mutanensu sun sake zuwa kusa da mu don su zambace mu haka. Ya ce lalle abin ya kai matuka, saboda haka ya halatta mini ran duk wanda ya sake matso mu.
Mun sauka muna girka abinci, sai wani cikin mutane Isyaku ya tsaga ihu. Ko da muka duba, sai muka ga barayi uku sun lababo suna kora jakunammu. Na bi su, suka tsere, suka haye dutse. Na koro jakunan, na komo da su zango. Da muka kare kalaci sai muka shiga ajin kaya. Wani jakin, bayan an yi masa aji yana kiwo, ciyawa ta ja shi har yayi dan nisa da mu kamar yadi metan. Kawai sai muka ga wani mutum ya fito daga cikin sagagi, ya sauke kayan, ya sa wuka yana farke daurin. Da dai ya ji mun ce kai kai kai, sai ya ruga cikin daji, bai dauki kome ba.
Muka dai yi gaba. Hanyar duk duwatsu ce, babu dadin bi ko ga mutum ko ga dabba. Na gaya wa sojammu su harbi duk bakon idon da suka ga ya matso.
....
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2bddd505
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada