MUNGO PARK MABUDIN KWARA 31

31. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...


 
Muka dai yi gaba. Hanyar duk duwatsu ce, babu dadin bi ko ga mutum ko ga dabba. Na gaya wa sojammu su harbi duk bakon idon da suka ga ya matso wurin kayammu. Muna tafe har zuwa wani babban dutse. In ta da kaina haka sai na hango barayi a kan dutsen, sun shige wani sako suna leko mu. Muka dai wuce lafiya, har muka isa wurin sauka. Muka kwana a dokar daji, kafin safe duk mun jike da raba. Kai, ni dai ban taba tashi tafiya a kan rashin sa’a kamar tasowarmu daga Mallabu ba.
"KADA KA KASHE NI, BATURE!"
Kowace irin sana’a ta kan fi kyautatuwa in an yi ta da ilmi, ko da sata ce. Amma barayin da muka ci karo da su yau, tasu satar da rashin kunya su ke yinta, ba da gwaninta ba. Da muka fito daga kofar Seransang, ba mu yi tafiyar da ta fi ta mil daya ba sai ga wadansu mutum biyu, su kuma sun fito daga garin suna take da sawummu. Da suka cim mana, sai dayan ya wuce da sauri kamar mai sammakon da rana ta yi masa, dayan kuwa shi ya rika jan burki yana bimmu a baya. Sai na ce da Mr. Anderson ya rika lura da na bayan ni kuwa na yi kaimi na bi na gaban, ina dubansa. Ga mu nan har muka zo inda hanya ta yi kwana, itatuwa suka hana ni ganinsa. A dan tsakanin nan, kafin in karya kwanar, ashe har ya fizge wata babbar rigar sanyi da ke daure a kayan wani jaki, ya tsere. Mai kora jakin ba ya iya binsa saboda rashin Iafiya, sai yana dubansa kurum yana cewa, “Kai, kai, kai!” Aka yi sa’a sai ga ni na bullo, na hange shi ya fada daji yana ta gudu. Na tausa linzami na sha kansa, na zo kusa da shi sai ya yi tsalle ya fada wata sarkakiya. Kafin in zagaya, shi kuma ya fita ta wata kafa ya sheka, na kuwa bi shi. Ya kurda nan, in kurda, ya yi kwana can, in yi, ban dai yarda ya bace mini ba. Can sai ya ga wata katuwar itaciya sai ya rabe da jikinta, wai shi ya yi mini burtu. Ni kuwa na ga kila in na sake barinsa yanzu zai tsere, saboda haka na kwarara bindiga daidai itaciyar. Na rataye bindigar a sirdina, na jawo karama na aune shi, na ce masa in ya kuskura ya motsa daga wurin zan kashe shi har lahira. Jin haka fa sai ya tsaga kara yana kwance, yana afi da hannunsa, yana cewa, “Ka yi mini rai! Kada ka kashe ni, Bature! Kada ka kashe ni, Bature ! Ba zan iya tsere maka ba, ka karya kafata !" Ko da na duba kafar sai kuwa na ga jini yana tarara kamar an yanka dan akuya. Da ya janye wandonsa na duba, sai ga harsashi ya fasa kwaurin a kusa da gwiwa, har ya zarce ya tafi. Na ce ya tashi ya fita. Ya tashi yana dingisawa da kyar, yana kara, yana waigo ni yana cewa, "Kada ka kashe ni, Bature!" Tafiya dai ta gagara, ya fadi a gindin wata itaciya.
Da ayari suka ji kararsa, wadansu suka rugo suka zo. A cikinsu har da yaron Sarkin Mallabu wanda ya hado su tare da dansa su yi mana jagora. Da ganin abin da ya faru, yaron Sarkin nan ya tsaya kai da fata sai in kashe barawon nan. In kuwa na ki, to, na ketare umurnin shugabansa, dan Sarki ke nan, gama ya ba ni iznin in harbi duk wanda ya zo kusa da mu, ya yi mana sata. Na ce ba zan kashe shi ba, wannan wahalar da ya ke sha ma ta isa. Yaron Sarkin nan ya ce to, in ni na ki kashe shi, shi zai kashe shi da hannunsa. Na rarrashe shi, na rarrashe shi, sai da kyar na ciwo kansa. Muka tafi muka bar barawon a kwance, kafa tana tsiyayar jini. Ko ya yi rai ko ya mutu, oho.
Daga nan ba mu kuma sake ganin wani barawo ba har azahar. Ana nan sai hadari ya daura baki kirin, can sai ruwa ya zo. Ana cikin ruwan nan sai wani Bature mara lafiya ya kasa. Muka wuce shi, muka ce in ya sami sauki ya cim mana. Ashe wucewarmu kadan sai barayi hudu suka fito daga cikin daji, suka kwace masa rigarsa. Ya yi kururuwa muka ji, da ni da Mr. Anderson muka juyo. Muna zuwa suka ruga a guje muka bi su har wajen mil uku. Da suka ga ba dama suka jefad da rigar, suka shige daji. Muka dauko, muka komo kan hanya. Ga mu nan har muka kusa da Nummabu. Da muka duba sai muka ga Mr. J. Bowden bai iso tare da mu ba muka zaci kila ko ya kasa a hanya, barayi sun yanka shi.
Muna cikin tafiya muka iso bakin Kogin Bawulima. Ko da yake ba fadi gare shi ba amma ya wo cikowa ga shi kuma bahagon kogi ne. Muka ga dai ba shi yiwuwa mu shiga, sai muka yi hayar mutanen wurin muka ce su yi mana kadarko. Nan da nan suka saro itatuwa suka shiga aiki. Kafin dan lokaci kadarko ya samu, muka bi. muka wuce. Ammaa cikimmu wani wai shi Franci s Beedle zazzabi ya rufe shi ainun ya ce shi ba zai ketare ba, ya fi so a bar shi ya mutu a bakin kogin. Muka wuce muka bar shi, na kuwa tabbata zai mutu zuwa dare. Ba a dade ba kuma sai Mr.Scott ya kasa, jim kadan kuma Mr. Martyn ya tabke. Duk ciwo ya rufe su. To, ni kaina a kasa nake tafiya, an sa wa dokina kaya, yana gaba ina korashi, balle in ce zan taimake su. Sai muka wuce muka bar su. Zuwa can sai muka hango ganuwar Marina. Saboda haka na aika da mutum biyu su koma su taitayo Scott da Martyn.
Iabari ya rigaya ya kai wa mutanen Marina irin yadda ake washe mu a kasashen da muka biyo. An ce musu kayammu wai "dummulafo" ne, watau “kayan banza ne, wanda bai debi rabonsa ba, shi ya so." Saboda haka mutanen wannan gari suka yi niyyar zuwa su debi nasu rabon ga banza ta fadi. Dare na yi fa suka lababo, suka shiga dauke-dauke. Suka sace jakuna biyar, amma da gari ya waye suka ciji hannu don haushi. Don kuwa safe na yi sai muka aika Bangasi, babban garinsu, muka sanad da Sarkin irin abin da suka yi mana. Da jin haka sai barayin suka komo mana da jakuna uku, amma ba su komo da biyun ba Muka tashi sai Bangasi. Sarkin ya aiko mana da liyafa, kuma da jaki guda cikin wadanda mutanen Marina suka sace. Ni kuma na debi kayan gaisuwa, na dauki Isyaku sai fada, muka yi gaisuwa. A cikin tadi, bayan mun gaisa, Sarki ya tambayi Isyaku ko ni ne Baturen da na shige ta kasarsa bara waccan. Aka ce masa ni ne. Ya ce har yanzu dai ban daddara da wahalar da na sha ba, na sake komowa? Na ce a gaya masa abin da ya kawo ni da, shi ya sake kawo ni yanzu, watau sanin yadda Afirka ta ke kurum. Ban zo don in sayi bayi ba, ban kuwa zo in kashe wa wani mutum sana'arsa ko cinikinsa ba. Ban zo don kwashe kudi ba, sai ma don in kashe su a Afirka. In kuwa yana shakkar gaskiyar maganata, na yarda ya tambayi duk mutumin da ya san ni, ko wanda ya taba tafiya tare da ni. Na ce masa ko yanzu kuwa ma na zo ne in roki iznin shigewa cikin kasarsa zuwa kasar Bambara. Ga kuma gaisuwata na kawo don in sami wannan izni. Isyaku ya baza kayan nan a gabansa. Sarki ya kalle su sau daya a wulakance, watau dai irin kallon nan na mutanen Afirka na gado wanda su kan yi wa abu, ko ba su taba ganin irinsa ba. Domin mutumin Afirka shi ke da wannan hali, kome sha'awarsa da abu, kome mamakin da ya ji, ba ya yarda ya nuna maka ya ji sha'awar, ko ya ji mamakin ko kadan.
Zuwa can dai sai Sarkin ya ce ya yarda in wuce, har ma zai sa dansa ya yi mini rakiya, amma ba nan da nan ba. Na ce masa ni kuwa na kosa in shiga kasar Bambara, don kuwa galibin mutanena ba su da lafiya. Na ce ina so in ya yarda ya hada ni da wani ya kai ni kan iyaka. Ya ce ya yarda, zai ba ni.
AL'AMARI YA RUDE
Kafin in tashi Bangasi na sa aka kawo jakuna biyu masu kyau na saya, na kara. Bangasi gari ne mai wadatar abinci, saboda haka duk zaman da muka yi a kullum na kan sayi wa mutanemmu madara da yawa don su sha, karfinsu ya karu yadda za mu sami kai wa Kwara da sauri. Amma ciwo ya rigaya ya ragargaza jikimmu. Ga jante ya kwantad da Kofur Powel riris, ga atini ya cinye karfin Mr. Inelli. Ban kuwa yi zaton dayansu zai tashi ba. Gari na wayewa Kofur Powel ya cika, muka binne shi. A cikin aljihunsa na sami dala biyu da sule daya, suna hannuna.
Mun tashi Bangasi ran 27 ga watan Yuli wajen karfe tara na rana. Muka bar Mr. Inelli a hannun Sarkin garin, na ba shi kudin abincinsa. Da fitarmu garin sai mutum uku suka karya gindi suka zauna, suka ce su dai sai a bar su su mutu, amma ba za su iya tafiya ba. Su ne Frair da Thomson da Hercules. Tilas muka wuce muka bar su. Ba a ci rabin mil ba sai James Trott, daya daga cikin kafintocimmu, shi kuma ya kwanta, ya ce ba zai yi gaba ba. Na kora jakinsa, na ce ya koma Bangasi.
....
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2bddd505
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)