MUNGO PARK MABUDIN KWARA 32

32. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
....


 
Mun tashi Bangasi ran 27 ga watan Yuli wajen karfe tara na rana. Muka bar Mr. Inelli a hannun Sarkin garin, na ba shi kudin abincinsa. Da fitarmu garin sai mutum uku suka karya gindi suka zauna, suka ce su dai sai a bar su su mutu, amma ba za su iya tafiya ba. Su ne Frair da Thomson da Hercules. Tilas muka wuce muka bar su. Ba a ci rabin mil ba sai James Trott, daya daga cikin kafintocimmu, shi kuma ya kwanta, ya ce ba zai yi gaba ba. Na kora jakinsa, na ce ya koma Bangasi.
Ni kaina gajiya duk ta rufe ni, ga ciwo, ga wahalar tafiya a kasa ina kora dokina da ke dauke da kayan shinkafa, ina kuma kora jakin James Trott. Muna tafe sai hanya ta bi da mu ta kan wani tsauni. Muna kaiwa bisa, da na duba gabana sai na hango wadansu manyan duwatsu can can nesa. Na tabbata daga bayansu Kogin Kwara na nan yana gudu. Tuna haka sai ya sa mini wani sabon karfi a jikina, na manta da gajiya, na manta da ciwon da ke jikina. Muka kai Nummasulo, muka yi mugama. Da safe, kafin mu tashi, sai ga dan Sarkin Bangasi ya zo asukwane, ya ce mutanen nan uku da suka tirje a hanya sun koma Bangsi, shi ya sa ubansa ya aiko shi ya tambaye ni yadda na ke so a yi da su. Na kawo abin saya musu abinci na ba shi. Na kuma ba shi abin da za su yi guzuri su cim mana in sun warke. Na kawo kyauta na ba shi ya kai wa uban, shi kuma na ba shi nasa. Sa'an nan na jawo takarda da alkalami, na rubuta wa mutanen nan wasika, na ce :
Masoyana Soja,
Na yi bakin ciki da ciwo ya ci karfinku, har tilas kun koma Bangasi. To, saboda haka, ga shi na aiko wanda ya kawo muka takardan nan da kudin da za su ishe ku sayen shinkafa har kwana arba’in. Na aiko shi da kudin da za su ishe ku sayan kaji da madara na kwana arba'in. Na aiko shi da kudin da za su ishe ku guzuri a hanya, ha r ku iso bakin Kwara.
Ni ne naku,
M. PARK.
Ran 1 ga Agusta na sayi jaki, na biya da bindiga daya, da turmin akoko daya, da zane daya irin na Mandingo. Muna cikin tafiya sai muka iso wani rafi mai zurfi. Tilas muka sauke kayan jakuna, muka shiga dauka da ka muna ketarewa da su. Abakin rafin kuwa mun tarad da mutane da yawa, duk kuwa barayi ne. Sai na ce Isyaku ya tsaya ya duba kaya a lokacin da mutanena ke ketarewa don kada asace. Isyaku sai fada ya gama su da wani Bature, sai ya kai wa Baturen mari. A wannan mari fa Isyaku ya so ya maro wa kansa, don saura kadan ya tafi lahira. Bature da jin mari sai ya dauki bindiga ya kafa banati, ya kuwa tasam ma Isyaku haikan zai tsire shi.
Farat sai Mr. Anderson ya rike bindigar, sa'an nan ni kuma na zo na shiga tsakani. Da na raba, na yi wa Isyaku fada kwarai. Ashe ya yi fushi don na yi masa fada, zatonsa na bi bayan dan'uwana Bature, sai ya tara mutanensa suka yi gaba suka bar mu. Sai na zo na tsaya kan kayan har aka ketare da su duk, ba abin da aka sace. Sa'an nan na ba mutanen da muka tarar a wurin lada, suka fitar mana da jakunammu.
A ran nan, fitar rana faduwarta, babu wanda ya dandana wani abinci a cikimmu. Ana shirin yin abinci ke nan, har an girka, sai ruwa shaa, duk ya kashe wutar. Haka muka kwana. Kashegari na sayi raguna biyu a wani gari wai shi Balaudu, muka yanka muka ci nama muka koshi. Mun tashi daga wannan garin ke nan, sai wani cikin mutanena wai shi Lawrance Cahill ya kwanta, ya ce shi ya tabke, ba zai iya tafiya ba. Na kora jakinsa, na ce in ya ji dama ya same mu a gaba. Mr. Scott kuma ya kasa, na sauka na ba shi dokina, ni kuwa na shiga kora jaki a kasa. Mutum hudu kuma bayansa suka kasa kora jakunansu don rashin lafiya. Kai, abu dai ya yi mini muni Kwarai da gaske. Duk taron babu mai lafiya. Wadansu, don tsananin ciwonsu da rashin karfi, ko kaya ya fado daga kansu ba iya daga shi daga kasa, balle su kai ka. Da kyar dai muka isa Kulihori, wani dan gari a kan hanya. Muna gama kafa tanti sai ruwa, har gari ya waye bai dauke ba. Ba mu sami damar girka abin da za mu ci ba ma. A cikin dare har kyarkeci suka kashe jakimmu guda.
Daga Bangasi zuwa Kulihori karkara ce, sai daji jefi jefi. Tun da muka taso Bangasi ba mu ga shanu ba. Saboda haka, da muka ga mutanen Kulihori da safe sun sheko suna kokawa a kan sudin kyarkeci na naman jaki, sai muka tabbata suna da tsiyar nama. Da kyarkecin suka kashe jakin, kayan cikin kadai, suka ci da zuciyar. gangar jikin kuwa ba su taba ba. To, shi ne mutanen Kulihori suka samu suka yi ta kokawa a kai. Kowa ya debi rabonsa ya nufi gida, mai gashi na yi, mai dafa na yi, mai suya na suya. Kafin mu tashi, Lawrence Cahill ya rarrafo ya cim mana.
MUN KAI KWARA
Ganin yadda mutanena su ke, sai na yi hayar mutum biyu a Kulihori don su taimake mu kora jakuna. Muka tashi muka nufi Ganifara. A hanya muka sake barin mutane uku, sun tabke, da L. Cahill, da J. Bird da William Cox. A Ganifara muka yini, muka shanya kayammu da suka jike, muka shafa wa bindigogi man kadanya, maganin tsatsa. A cikin dare wani soja wai shi Michael May ya rasu. da safe muka binne shi, muka tashi. Muna cikin tafiya, ina taitaya wani wai shi William Ashton da ya kasa, sai na sami Mr. Anderson a gindin wata itaciya ya yi rangaranga. Shi kuma na dauke shi bisa doki, muka yi gaba da kyar. Can gaba kuma muka sami wani jaki mai dauke da albarushi yana kiwo a kan hanya, ga mai kora shi Dickinson a kwance. Na koro jakin, muka wuce muka bar shi, don ya ce ba zai wuce ba. Rabommu da shi ke nan ban sake jin ko labarinsa ba.
Muna cikin tafiya a daji, Mr. Anderson yana bisa dokina ni ina kasa ina jan dokin, sauran ayari kuwa ya yi gaba, Sai muka ji wata irin kara mai ban tsoro daf da mu. Na ce da Mr. Anderson kila birai ne ke ba mu tsoro. Muna fita wani dam fili, sai na hango zakoki guda uku sun yi banga-banga, sun nufo inda mu ke. Suna tafe suna gurnani, suna kada wutsiya. Na firgita kwarai.
....
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2bddd505
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)