33. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...
MUN KAI KWARA
Ganin yadda mutanena su ke, sai na yi hayar mutum biyu a Kulihori don su taimake mu kora jakuna. Muka tashi muka nufi Ganifara. A hanya muka sake barin mutane uku, sun tabke, da L. Cahill, da J. Bird da William Cox. A Ganifara muka yini, muka shanya kayammu da suka jike, muka shafa wa bindigogi man kadanya, maganin tsatsa. A cikin dare wani soja wai shi Michael May ya rasu. da safe muka binne shi, muka tashi. Muna cikin tafiya, ina taitaya wani wai shi William Ashton da ya kasa, sai na sami Mr. Anderson a gindin wata itaciya ya yi rangaranga. Shi kuma na dauke shi bisa doki, muka yi gaba da kyar. Can gaba kuma muka sami wani jaki mai dauke da albarushi yana kiwo a kan hanya, ga mai kora shi Dickinson a kwance. Na koro jakin, muka wuce muka bar shi, don ya ce ba zai wuce ba. Rabommu da shi ke nan ban sake jin ko labarinsa ba.
Muna cikin tafiya a daji, Mr. Anderson yana bisa dokina ni ina kasa ina jan dokin, sauran ayari kuwa ya yi gaba, Sai muka ji wata irin kara mai ban tsoro daf da mu. Na ce da Mr. Anderson kila birai ne ke ba mu tsoro. Muna fita wani dam fili, sai na hango zakoki guda uku sun yi banga-banga, sun nufo inda mu ke. Suna tafe suna gurnani, suna kada wutsiya. Na firgita kwarai. Na ga in na bari sun zo kusa, kila bindigata ta ki tashi da sauri, su yi tsalle bisa kammu su kashe. Sai na saki linzamin dokina, na ce Mr. Anderson ya rike, ya tsaya kurum. Ni kuwa na dura harsashi, na sake kama linzamin, na yi gaba, na nufi inda su ke, su kuma suna tahowa, ba ko tsayawa. Sai na auni na tsakiyar, na sakam masa wuta kwararam! Ban zaci dai na same shi ba, amma na ga duk sun tsaya, kuma sai suka dubi juna, suka juya. Har sun taba 'yar tafiya, sai na ga guda ya tsaya ya juyo ya dube ni. Ni kuwa a lokacin ina kici-kicin dura harsashi. Kafin in gama, ko da na duba, sai na hange su can sun shiga daji, suna takama. Mun yi tafiya kamar ta rabin mil, sai kuma muka sake jin gurnani kurkusa da mu. Na tabbata daya daga cikin zakokin nan ne, kuma na san haka za su dinga bimmu har dare ya yi, su yi mana lalata. Sai na karbi usir wurin Mr. Anderson, na yi ta hurawa firr, fifirr, firr! Daga nan ba mu sake jin motsinsu ba, har muka kai Kumikumi. A nan mutum guda cikimmu ya mutu, sunansa Jonas Watkins.
Kafin mu kai Dumbila muna cikin bakin ciki. Duk ayarin, ban da mutum uku rak, babu mai lafiyar da zai iya tafiya. Amma da muka shiga garin, mun ji dama, don kuwa mun huta. A garin ne muka sadu da abokin nan nawa Karfa Taura, wanda na zauna wata uku a gidansa, ya yi mini riko mai kyau a tahowata Afirka ta farko. Ya ce mini tun a wani gari wai shi Buri, inda ya ke zaune yanzu, ya sami labari aka ce ayarin Turawa yana wucewa ta kasar Fuladu zuwa Bambara. Madugunsu kuma wani Bature ne mai jin harshen Mandingo, wai shi Park. Jin haka shi ya sa shi Karfa ya zo don mu sadu, kuma har ya zo da bayinsa uku don su taimake ni daukar kaya zuwa Sego.
Da gani na Karfa ya gane ni, ni kuma murna a gare ni ba sai na fada ba. Don kuwa duk yadda a ke taimakon gajiyayye, Karfa ya taimake ni lokacin da na ke cikin gajiyawa. Ba na mantawa da Karfa har im bar duniya, ba na kuwa fasa gode masa. Na karbi bayi, na yi godiya, muka rabu da Karfa.
Daga nan zuwa gaba hanya ba ta cika kyau ba. Muka dai yi ta fama hakanan, mu fadi mu tashi, har Toniba. Da na hau wani tudu a hanya, ko da na duba gabana sai na hango Kogin Kwara. Ganin wannan kogi lalle babban abu ne gare mu, don kuwa ko bai nuna iyakar tafiyarmu ba, ya dai nuna raguwar wahalarmu. Amma kuma in na tuna a cikin mutanen da muka taso da su, yanzu abin da muka rage ba mu kai kashi daya cikin hudu ba, sai in yi ajiyar zuciya. Babban abin da ke bata mini rai kuma, bayan mutuwar wadannan 'yan'uwa nawa, shi ne duk cikimmu yanzu babu sauran kafinta wanda zai sassaka mana jiragen da za mu shiga, mu ci gaba da tafiyarmu a kan Kwara. Abin da ya yi mini dadi game da wannan tafiya daya ne tak, watau yadda na ratso kasar Afirka da Turawa masu yawa haka da dukiya niki, muka yi tafiyar wajen mil dari biyar amma ba mu yi wani tashin hankali da mutanen kasar ba. Wannan ya nuna mini abu biyu. Na daya, in an kula da kyau, ba a yarda an yi tashin hankali da mutanen Afirka ba, ana iya ratso kasarsu da kaya, kome yawansa, daga Gambiya har zuwa bakin Kwara. Na biyu, in da ba cikin damina muka yi tafiyan nan ba, da kila hasarar da za mu yi ba za ta fi ta mutum uku ba, intaha hudu, a cikin mu hamsin.
To, mu komo kan labarin Kwara. Ko da ya ke tana cike ne a yanzu, amma ba ta tumbatsa ta ba fadamunta ruwa ba. Sai dai a nan girmanta ya fi yadda ta ke a kasashen Gambiya da Senegal. Daga cikin soja talatin da hudu da kafinta hudu da muka taso Gambiya da su, sai soja shida da kafinta daya kadai suka ga Kwara, sauran duk sun mutu a hanya.
Da ya ke yanzu mun nufi Sego ne, sai na yi shawara in aiki Isyaku da kyauta mai yawa ya kai wa Modibinne, Wazirin Bambara, don a ba Sarki, a kuma fada masa ga mu nan tafe. Shi Modibinne shi ne babba a kasar, ban da Sarki, kuma ko da ya ke Musulmi ne, amma bai cika kin Nasara ba. Abin da ya sa na aika gare shi kuwa, na san yanzu labari ya kai garin cewa ga ni nan tafe. Saboda haka Larabawa suna nan suna mini kulle-kulle iri iri, suna neman washe ni, ko su hada ni da Sarkin ya kashe ni, kamar yadda suka so yi mini a tafiyata ta farko. Isyaku ya tafi. Zan gan shi yau, zan gan shi gobe, shiru, ba Isyaku, ba labarinsa. Im mutane sun zo daga Sego muka tambaye su labarinsa, sai su ce wai Sarkin ya yanka shi da hannunsa, mu ma yana jirammu ne ya yanka.
....
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2bddd505
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada