MUNGO PARK MABUDIN KWARA 34

34. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...


 
Da ya ke yanzu mun nufi Sego ne, sai na yi shawara in aiki Isyaku da kyauta mai yawa ya kai wa Modibinne, Wazirin Bambara, don a ba Sarki, a kuma fada masa ga mu nan tafe. Shi Modibinne shi ne babba a kasar, ban da Sarki, kuma ko da ya ke Musulmi ne, amma bai cika kin Nasara ba. Abin da ya sa na aika gare shi kuwa, na san yanzu labari ya kai garin cewa ga ni nan tafe. Saboda haka Larabawa suna nan suna mini kulle-kulle iri iri, suna neman washe ni, ko su hada ni da Sarkin ya kashe ni, kamar yadda suka so yi mini a tafiyata ta farko. Isyaku ya tafi. Zan gan shi yau, zan gan shi gobe, shiru, ba Isyaku, ba labarinsa. Im mutane sun zo daga Sego muka tambaye su labarinsa, sai su ce wai Sarkin ya yanka shi da hannunsa, mu ma yana jirammu ne ya yanka. Muna nan dai ran nan sai ga Bukari, sankiran Sego, ya zo ya ce Sarki ne ya aiko shi gare mu. Ya ce Sarki ya ga gaisuwar da Isyaku ya kai masa, ya yi murna kwarai, ya kuma ji dadi. Amma ya ce ya fi so shi Bukari ya tafi da mu Sego tukuna, sa’an nan Sarki ya karbi kayan nan daga hannun Isyaku.
Da jin haka, muka shiga Shirin kaya. Nan da nan Bukari ya samo jirgin ruwa, aka lafta kayan a ciki, muka shiga sai Sego. Muka yini muna tafiya, tafiya kuwa mai ban sha’awa, don babu abin da ya fi Kwara kyaun gani. Muna tafe, muna bin igiyar ruwa suu, wani lokaci sai ka ce ba motsi mu ke yi ba, wani lokaci kuwa igiyar ruwa ta dam fizge mu kadan, mu tangada, amma har muka sauka saurin tafiyarmu bai kasa mil shida ko bakwai a sa'a guda ba.
Muka sauka a Sami, kusa da Sego, muka kwashe kayammu. Bukari kuwa ya wuce Sego a cikin wannan jirgin don ya gaya wa Sarki ga mu mun iso. Kashegari da safe sai ga Isyaku ya zo a jirgi da kayan nan duk da aka aike shi da su. Ya ce Sarkin Sego bai yarda ya ko duba ya gan su ba. Yanzu da ya ji ga ni a Sami, sai ya ce Wazirinsa Modibinne ya fada wa Isyaku ya komo mini da kayan a nan Sami, zai aiko a karba daga hannuna. Isyaku ya ce mini a cikin zamansa a Sego ya sami ganin Sarki sau da yawa, a kowane lokaci kuwa Sarkin ya kan fada masa lalle zai bar mu mu wuce. Amma Isyaku ya ce ya ga alamar Sarkin yana tsorommu, don kuwa bai taba nuna cewa yana son ganimmu ba.
Kwana biyu tsakani, bayan zuwan Isyaku, sai ga Waziri Modibinne da fadawa hudu, sun shigo jirgi sun zo Sami wurimmu. Can bayan sun sauka sai suka aiko in tafi. Da na tafi, Modibinne ya ce Sarki ne ya aiko shi don ya ji daga bakina irin abin da ya kawo ni kasar Bambara. Da yin wannan tambaya sai ya sallame ni, ya ce in je in yi shawara da zuciyata da dare, in gari ya waye mu sadu ya ji. Ya ba ni bajimi, ya ce ga shi nan saukata ke nan, in ji Sarkin Sego. Bajimin gawurtacce ne, mai kiba, kuma fari ne fat kamar madara.
Muna kare kalaci da hantsi sai ga su Waziri sun cim mini har gida. Bayan sun zauna mun gaisa, Waziri ya ce ya zo ya ji amsar tambayarsa ta jiya, watau ya ji abin da ya kawo ni kasarsu. Na amsa masa da harshen Bambara na ce, “Ni ne Baturen nan da ya taba zuwa kasar Bambara shekara tara da suka wuce. Na zo har Sego, na nemi iznin Sarki, na shige ta kasarsa na yi gabas. Ya kuwa ba ni izni, har ma ya taimake ni da tsabar kudi dubu biyar, ya ce in yi guzuri a kan hanya. Kun sani Larabawa sun washe mini kayana karkaf a lokacin. Wannan alheri da Sarkin Sego ya yi mini ya sa sunansa ya shahara a kasar Turawa. Sarkin kasarmu shi ya sake aiko ni zuwa kasar Bambara. To, im fa Sarkin Sego zai taimake ni kamar yadda ya yi da, ku kuma sarakunansa da mu ke zaune nan tare da ku, kun yarda da ni bisa amana, zam fada muku gaskiyar abin da ya kawo ni kasar Bambara.”
Waziri Modibinne ya ce sun amince da ni, sun kuwa yarda im fadi dalilina. Na ci gaba, na ce, “Kun sani mu Turawa mutane ne masu son ciniki, kuma hajjar da ku ke gani masu kyau wadanda Larabawa da mutanen Jinne ke kawowa Sego duk mu ke yi. In kun ga bindiga mai kyau, wa ya yi ta ? Turawa. In takobi kuka gani rantsattse, ko wani ajanaku, ko akoko, ko dutsen wuya, ko albarushi, duk wa ke yin su? Mu ke yi, mu sayar wa Larabawa, su kuma su kawo Tambutu su tsabga musu kudi su sayar. Su kuma mutanen Tambutu su kara musu kudi su sayar wa mutanen Jinne, na Jinne kuma su kara kudi su sayar muku.
“To, ganin yadda ku ke sayen hajja da tsada haka, shi ya sa Sarkin Turai ya ke so a sami hanyar da za a rika aiko muku da kayan nan yadda za ku sayi kome da araha. Saboda haka, in Sarki ya yarda, zam bi kan Joliba (Kwara), in yi ta tafiya har in kai inda ruwanta ya gauraya da ruwan gishiri. In kuwa na kai lafiya, ban yi karo da dutse ko wani hadari ba, za ku ga jirgin Turawa ya zo muku da hajja Sego, amma fa sai in Sarkin Sego yana bukatar haka. Amma wannan magana fa asiri ce, daga ni sai ku, ba na son ku fada wa kowa sai Sarki da dansa. Dalili kuwa, in Larabawa suka ji haka, lalle za su kashe ni, kafin in kai ruwan gishiri."
Da na gama, Waziri Modibinne ya amsa ya ce, “Mun ji abin da ka fada. Tafiyarka lalle ta alheri ce, Allah ya ba ka sa'a cikinta. Sarkin Sego zai ba ka iznin shigewa, kuma zai ga babu abin da ya cuce ka. Za mu fada wa Sarki duk abin da ka fada a yau, gobe kuwa za mu komo mu fada maka abin da ya ce.” Da ya gama, Isyaku ya nuna musu irin abubuwan da na kawo wa Sarki da dansa. Suka yi murna, suka ce duk kayan nan suna da kyau kwarai.
Shi kuma Wazirin, da sauran fadawan duka, na ba ko wanne turmi na ajanaku. Bayan sun karba, sai Waziri ya ce, “To, mun ga gaisuwar da ka kawo wa Sarki, ta kuwa isa. Amma Sarki ya sami labarin kana tafe da dukiya mai yawa, saboda haka ya ce mu yi cajin kayanka duka, duk kayan da aka kunshe a jakar fata, kada mu kwance, in dai ka gaya mana abin da ke ciki ya isa." Na ce musu ni ba na dauke da wata dukiya sai irin abin da zai ishe ni sayen abinci kurum kuma ina rokonsu kada su barbaza mini kayana. Amma ba su yarda ba. Saboda haka na ce da mutanena su fito da adilu, amma na gaya musu da Turanci kada su fito da kayan amba da duwatsun ado. Da aka kwance aka baza duka suka duba, sai na tambayi Waziri ko maganata ta tabbata gaskiya, ko kuwa yana da sauran shakka. Ya ce lalle bai ga wani abin kirki ba, sai abin guzuri kurum. Muka yi sallama, suka mika Sego, amma suka ce ba za su dauki gaisuwar Sarki ba sai sun ji abin da ya ce tukuna. A daren wannan rana muka sake rasa soja biyu, da Mr. Seed da Mr. Barber, daya zazzabi ya kashe shi daya kuwa atini.
Kashegari Waziri Modibinne da fadawan nan na jiya duka suka komo. Ga jawabin da suka kawo mini daga wurin Sarki : “Sarki ya cw a gaishe ka. Ya ce zai lura da kai, babu abin da zai cuce ka, kana iya bi ta ko'ina cikin kasarsa. In gabas za ka nufa daga Sego, babu mai taba ka har ka wuce Tambutu, in yamma ka yi har ka wuce Fuladu da Mandin da Kasson da Bondu. Da ka ce kai bakon Sarkin Sego ne, babu mai taba gashin kanka. In a Sami ka ke so ka sassaka jiragenka, ko a Sego, ko a Sansandin, ko a Jinne, sai ka fada, Sarki zai aika a kai ka can, a kuma kula da kai." Da ya kare, ya ce amma Sarki yana so in sayar masa da wata bindiga, da takobina da molon Mr. Scott, da wadansu duwatsun wuya. Ya kuma aiko mana da bajimi, dansa kuma ya aiko mana da bajimi da rago. Na yi godiya, na ce da Waziri alherin Sarki a gare ni ya fi wadannan abubuwa da ya ce in sayar masa, saboda haka ya kwashe abubuwan ya kai wa Sarki kyauta.
Wajen maganar garin da na ke so in zauna saboda sassaka jirgi, na ce na zabi Sansandin. Tun da ya ke Sarki bai ce yana son ganina ba, kuma a Sansandin ba zan sha fitinar roke-roke kamar yadda zan sha a Sego ba, na fi son can.
Muka shirya, muka tashi cikin jiragen ruwa daga Sami zuwa Sansandin. Da ya ke a ran nan babu iska, kuma jiragen babu rumfa, mun yi fama da zafi kwarai. Zafin ya yi zafi har kaina ya rika ciwo. Ni dai ban taba jin zafin rana irin na ran nan ba, don kamar a gasa nama a ciki. Mun shige ’yan tsibirai, da masunta da yawa a cikinsu, har dai muka kai Sansandin da hantsi karfe goma. Muka cim ma bakin ruwan dankare da jama’a wadanda suka zo ganimmu. Muka nemi yadda za mu sauke kayammu ma, muka rasa, saboda yawan jama’a, sai da Sarkin Sansandin, Kunti Mammadi, ya sa aka yi ta duka, ana kora. Nan da nan Mammadi ya sa aka kai mu masauki, muka zuba kayammu. A daren ran nan soja biyu kuma suka mutu, da Marshall da W. Garland. Amma kafin safe kyarkeci sun dauke gawar Garland, sai Marshall kadai aka tarar.
....
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
BBM: 2bddd505
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)