MUNGO PARK MABUDIN KWARA 37

37. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
...


 
“Kashegari, ran Asabar, muka yi sallama da Mungo Park, ya tashi, ni kuma na kwana a Yawuri. Da gari ya waye na tafi garin da Sarkin Yawuri ya ke don in yi gaisuwa. Da shiga gaban Sarki sai na sami barade biyar wadanda dagacin Yawuri ya aiko su. Ina zama sai suka ce da Sarki, “Allah ya ba ka nasara, dagacin Yawuri ne ya aiko mu mu gaya wa Sarki Turawan nan sun wuce, ba su ba Sarki kome ba, balle fa shi da bai dada kome ba. Jirginsu yana makare da dukiya iri iri. Ya kuma ce a gaya maka, Allah ya ba ka nasara, kada ka yarda da Amadi Fatuman nan, lalatacce ne. Shi ne ya hana Turawan nan su ba ka wani abu.'
“Da rufe bakinsu Sarki ya sa aka buge ni aka daure. Aka cika ni cikin sarka, wadansu suna a kashe ni, wadansu suna a kyale ni. Gari na wayewa sai Sarkin ya aika da mayaka wani gari wai shi Busa a bakin Kogin Kwara. mayaka wani gari wai shi Busa a bakin Kogin Kwara. Daga gaban garin kadan, akwai inda wani dutse ya datse Kogin Kwara, ya taso tun daga wannan gaba ya dangana da waccan. Dutsen nan yana da bisa ainun a waje guda, kuma daga tsakiyar kogin ya bar wata 'yar kofa. Ta nan kadai ruwa ke wucewa, yana kuwa da karfi kwarai. Mayakan nan na Sarkin Yawuri suka haye bisan dutsen nan daidai bakin kofar, kowa ya jawo bakansa, ya dana kibiya, ya cije wadansu, suka jira zuwan Mungo Park. Zuwa can sai ga su Mungo Park sun iso a jirginsu, suka ce kuwa suna neman wuce 'yar kofan nan. Mutanen Yawuri suka fada musu, mai kibiya na harbi, mai jeho mashi na yi, mai jeho dutse na jehowa. Su Mungo Pask kuma suka yi kokarin tsare kansu.
“Mutanen suka fara kashe bayin Mungo Park da ke zaune nan a baya, daga gindin jirgin. Da Mungo Park ya ga ba za su kai ba, sai ya ce da mutanensasu kwashe duk abin da ke cikin jirgin su zuba a ruwa. Suka tsaya daga su sai bindigoginsu, suka bude wuta, suka yi harbi, suka yi harbi. Kayya! An ce. Sarkin yawa ya fi Sarkin karfi! Mutanen Yawuri sun fi karfinsu, kuma ga , jiya, igiyar ruwa tana fiffizga musu jirgi. Mungo Park dai ya tabbata su kuma tasu ta kare, sai ya kakume wuyan Bature guda. Mr. Martyn kuma ya kakume wuyan guda, suka bar jirgin, suka tsunduma cikin ruwa. Suka yi kokarin fid da kansu da ninkaya, a nan ruwa ya ci su, suka halaka. Sauran bawa daya da ya rage a cikin jirgin, da ya ga mutanen ba su daina harbin jirgin ba, sai ya mike, ya ce, “Ku daina harbi haka nan, babu abin da ya rage cikin jirgin sai ni. Ku zo ku kama ni da jirgin duka, amma kada ku kashe ni." Suka kama shi suka kai wa Sarikin Yawuri har da jirgin.
“Ni kuwa aka bar ni a daure cikin sarka har wata uku. Ana nan sai Sarki ya sake ni, har ya ba ni kuyanga. Da samun kaina, sai na je wurin bawan nan da aka kamo daga jirgin Mungo Park, shi ya gaya mini irin abin da ya sami Mungo Park, da irin halin da ya mutu a ciki. Na tambaye shi in ya tabbata babu abin da aka samu a cikin jirgin, ya ce babu abin da ya rage daga shi kansa sai wata hamilar takobi. Na tambaye shi ko ya san inda aka kai hamilar, ya ce tana wurin Sarki, har ya yi majayin sirdin dokinsa da ita.
“Iyakar abin da na sani ke nan game da mutuwar Mungo Park.”
ISYAKU YA CI GABA DA LABARINSA
Da jin wannan labari daga bakin Amadi Fatuma, sai na tashi manzo na aike shi gun Sarkin Yawuri. Na ce ya gaya wa Sarki ya ba da hamilan nan ta Mungo Park kuma za a biya shi ko nawa ya sa mata kudi. Manzo ya tashi, ni kuma na bar Madina, na koma Sansandin, daga can na wuce Sego. Na tafi na fada wa Daca, Sarkin Sego, duk irin abin da na ji. Ya yi fushi, ya yi fada, ya ce ba don kasar Hausa ta yi nisa ba, da ya tafi da kansa ya halaka Sarkin Yawuri. Amma duk da haka, nan da nan ya tara runduna, ya wuce gabanta sai Banankoro. Daga can ya ce mutanensa su je su kone kasar Hausa. Rundunar ta tafi, suka wuce Tambutu, ba su ya da mashi ba sai da suka kai Saca. Daga can suka aiko wani barde ya zo ya gaya wa Sarki ga inda su ke. Kuma a gaya masa kasar Hausa ta cika nisa, har bai kamata a tura 'yan yaki su tafi ba. Sai Sarkin ya ce to su komo da baya, amma su biya kasar Masina su kwaso duk abin da suka samu, mutum da dabba. Suka shiga, suka kwaso shanu tururu. Kafin masu koro shanun su iso Bambara sai da suka dade a hanya, rundunar kuwa wata hudu ta yi daga fitarta Bambara zuwa komowarta.
“Sarki ya yi fushi da Sarkin Yakinsa, don rashin bin umurnin da ya ba shi, ya komo da baya tun bai kai inda ya ce ya je ba. Sarkin Yakin ya ce abin da ya sa ya komo da baya, gani ya yi sun yi nisa da kasarsu inda za su sarni taimako in sun kama yaki. Saboda haka ya ga ya fi amfani su juyo, da su tura kai a halaka. Amma a kan tilas ya juyo, ba da son ransa ba. Muka taso har da Sarki da rundunar duka, muka komo Sego.
“Na sake komawa Sansandin, don in jira wanda na aika gun Sarkin Yawuri ya karbo mini hamila. Bai komo ba sai da ya yi wata takwas a can, kuma ya sha wuya kwarai. Ya kawo mini hamilar, amma ya ce ba Sarkin Yawuri ya ba shi ba. Wata yarinya kuyangar gidan Sarkin ta sato masa ita. Kuma yarinya kuyangar abin da ta iya samowa ke nan na su Mungo Park, ban da hamilar babu kome a hannun Sarkin Yawuri. Na karbi hamilar, na tashi Sansandin na je Sego, na fada wa Daca irin abin da ke akwai, na kuma ce masa zan koma Senegal. Sarki ya ce tun da ya ke damina ta matso, ya kamata im bari sai kaka in tafi. Na ce masa ba na iya tsayawa, tun da ya ke abin da na zo nema labarin Mungo Park ne, na kuwa samu, zan tafi gida nan da nan. Na gaskata labarin Amadi Fatuma, don ko da ma, saboda nagartarsa da gaskiya tasa, na hada shi da Mungo Park. Kuma bai ba ni wannan labari ba sai da ya rantse. Ni kuwa ba wani abu na ce zam ba shi ba, ban kuma yi masa alkawarin kome ba, balle in ce don kwadayi ne ya yi mini karya. Kuma Mungo Park ba shi a duniya, dukiyar da ya ke dauke da ita kuma ta halaka, balle in ce kwadayin boye ta ya sa Amadi ya yi mini karya ya ce Mungo Park ya mutu. Matafiya kuma da yawa sun fadi labarin mutuwan nan kamar yadda Amadi ya fada. To, saboda gaskata labarin nan da ya fada mini, da hatsarin da zan shiga in na ci gaba, su suka sa zan koma Senegal. Ga hamila na samu, ta zama shaidata. Iyakar labarin da na samo ke nan na Mungo Park.”
Da tafiya da komowa, Isyaku ya yi shekara daya da wata goma wajen bin sawun Mungo Park. Duk abin da ya ji ya rubuta da Larabci, ya hada da takardun da Amadi Fatuma shi kuma ya rubuta da Larabci a kan mutuwar Mungo Park, ya kawo wa Gwamna Maxwell a Senegal. Shi Gwamna Maxwell ya sa aka fassara da Turanci, ya aika wa manyansa a lngila. Aka shirya su duka, aka maishe su littafi, don duniya su karanta su a irin yadda wannan taliki ya yi ta kutsa kai a halaka, har ya halaka, don ya yaye wa duniya duhun jahilci.
MU GODE WA MASU HIMMA!
Allahu Akbar! Haka wannan tafiya ta Mungo Park ta kare cikin masifa, mutum arba’in da hudu, amma babu wanda ya koma gida, balle ya kai labari! Duk da wannan babbar hasara ta rai kuwa, ga shi abin nema bai samu ba. A tafiyar farko duniya ta karu kwarai da kokarin Mungo Park. Ya fito don ya ga Kogin Kwara ne da jihar da ya nufa, ya kuwa gani, har ya koma gida ya warware gardamar da aka shekara wajen dubu ana yi. Amma manufar tafiya ta biyu, ita ce ya zo ya sake warware gardamar inda Kwara ta kare. Ayya! Haka bai samu ba. Iyakar labarin da aka ji daga bakinsa shi ne takardar da ya rubuta da hannunsa, ya fadi tashinsa Sansandin. Daga wannan ba a sake jin ko duriyarsa ba, sai dai kwaram aka ji ya halaka a Busa. A lokacin kuwa mutanen Ingila suna zaton Busa ba ta wuce mil tamanin daga Sansandin ba. Saboda haka, da suka ji iyakar tafiyar ke nan kadai Busa ba su cika yabawa ba. Nan kuwa ba su sani ba ne, Busa, wajen mil dari takwas ce daga Sansandin. Kuma inda Mungo Park ya rayu, da ya nuna wa duniya bai yi tafiyar banza ba. Don tun kafin ya isa Busa ya fara ganin ashe Kwara ba mikewa gabas sak ta yi ba, ta karya kudu ne.
An dai ji irin tsinci-fadin da kowa ke yi a Turai a lokacin game da jihar da wannan kogi ya bi, da inda ya kare. Wadansu sun ce ya fada a Kogin Nil, wadansu sun ce a'a, da Kwara da Kongo kogi guda ne. Ko Mungo Park kansa haka ya zata. Wadansu ma dungum cewa suka yi bai fada teku ba, ya kafe ne kurum a tsakiyar Afirka! To, halakar Mungo Park ita ta hana mutanen Turai su san Kwara ta karya kudu ne, ta fada teku a wurin da muka sani yanzu.
Mu koma kan dalilin bacin ranar wannan tafiya ta Mungo Park. Akwai dalilai biyu. Na farko dai, bai taso cikin lokacin da ya kamata a yi tafiya a Afrka ba, don da farkon bazara ya taso, kafin tafiyar ta yi nisa kuwa damina ta sauka. Zafin bazara da dukan ruwa su suka rage karfin mutanensa, har cuta ta shiga ta karasa su. Ko shi kansa kuwa ya fadi haka. Amma wannan kuskure na lokacin tasowa ba laifinsa ba ne, don ya sha fadin haka a gida, manyan ne dai ba su sallamo shi da wuri ba.
Dalili na biyu, babban kuskure ne a ratso da Turawa cikin Afirka, ba tare da samun mutanen kasar wadanda za su taimake su wajen hidima da daukar kaya ba. Bugu da kari, su Turawan nan da ya dauko ba lafiyayyu ne irin na Ingila ba. Su da ma Soja ne, a nan Afirka su ke zaune, duk kuwa cuce-cucen kasar, kamar su zazzabi da atini, sun rigaya sun raunana su. Yanzu ma ke nan da ilmi ya watsu ko’ina, lafiyar kasa ta karu, amma ana fama da wadannan irin cuce-cuce, balle a Afirka ta shekara dari da arba'in da suka wuce?
Amma Mungo Park yana da hali mai ban mamaki. Dauriyarsa da himma tasa su ne karfin tafiyar, don shi kadai ne cikin taron bai fid da rai ga samun bukata ba, har ran da ya mutu. Raki ya sa galibinsu sun kwanta a hanya, sun zabi a bar su su mutu. Shi kadai ne bai kawo mutuwa a zuciyarsa ba. Har ma ya kan tsaya ya dauki wadanda suka kasa, ya dibiya bisa dokinsa, shi kuwa ya bi kasa. Ko ya dauki kayansu, su kuwa su huta. Babu dai abin da ba ya yi, shi ne rarrashi, shi ne taimakon marasa lafiya, shi ne bin barayi a guje ya kwato kaya, sauran kuwa ba sa iya kome sai ko ihun “barawo"! daga kwance.
A lokacin da Munga Park ya shiga jirgi daga Sansandin ya bi tsawon Kwara, cikin Turawa arba'in da uku da ya taso da su, Soja uku da Laftana Martyn kadai suka rage. Sauran talatin da tara duk sun zama gawa a kan hanya da dai dai. Ko su hudun ma akwai-ya-babu ne, don soja daya ya haukace, Laftana Martyn kuwa gwamma ma rashinsa da shi. Amma duk wannan bai karya Mungo Park ba. Shi dai ya yi niyyar ci gaba. Ko fa ya kai ga bukatarsa, ko kuwa ya mutu a cikin Kwara. A kan ce duniya ba ta da gwani. Domin duk wannan wahala da Mungo Park ya sha, har ta kai shi ga halaka, wadansu mutane ba su gani ba, sai da suka zarge shi. Sun ce shi ya jawo wa kansa halaka, don wai duk inda ya ratsa shi ke fara neman fada da mutanen wurin, ko da ya ke su niyyar taimakon sa su ke yi. Amma tun daga tafiyarsa ta farko har wannan, duk wanda ya karanta yadda ya yi ta neman lalama da mutane, zai tabbata bai yi wa kowa tsiwa ba. Don taushin zuciya, ba ya son dan'uwansa mutum da wahala, balle ya raba shi da ransa. Im fada ya gama mutanensa da mutanen kasa, sai ka gan shi maza ya shiga tsakani, don kada a zub da jini. Bai taba butulce wa wanda ya yi masa alheri ba, ko mace ko namiji. Tun daga Sarkin Sego da ya ba shi tsabar kudi, har zuwa tsohuwar baiwar da ta ba shi dankin gyada, a kullum yana gode musu.
Ko da ya ke Mungo Park bai sami biyan bukatar tafiyarsa ba, amma kuma bai yi rayuwar banza a duniya ba. Ya dai sami baiwa biyu, daure wahala da himma, ya kuwa nuna wa duniya amfaninsu. Saboda haka duk wuyar da ya sha, da mummunan karshen da ya yi, ba su karya zuciyar masu himma kamarsa a Ingila ba. Sai ma kara musu karfin halin zuwa Afirka suka yi. Labarin da ya bayar na zaman mutanen Afirka, da halayensu, da al'adunsu, ya ba mutanen Ingila sha'awa, har wadansu sun yi kasada sun zo, don su karasa babban aikin da ya fara. A cikinsu ne, bayan ’yan shekaru kadan, wani ya bi tsawon Kwara har ya ga inda ta fada a teku. Amma wannan labari, sai a wani littafin kwa ji.
To, Turawan da suka tako sawun Mungo Park, su ne suka fito da kome a fili game da Kwara. Da ji, sai Turawa suka rika shigowa Afirka da dai dai, suna kara duba zamammu, da irin abubuwan da mu ke bukata, suka rika taimakommu da su. Ta haka arzikin kasar ya rika karuwa, kan mutanenta yana wayewa, lafiya da ilmi suna daduwa mana kullum. Duk wadannan kuwa, kusan Mungo Park ne, mabudinsu gare mu. Mun gode masa. Allah ya yi albarka!
KARSHE
Post a Comment (0)