MUNGO PARK MABUDIN KWARA 36

36. MUNGO PARK MABUDIN KWARA
Na Malam Nuhu Bamalli
www.bukarmada.blogspot.com
...


 
Gwamnatin Ingila ta umurci tabbatar da labarin mutuwar Mungo Park. In gaskiya ne, a samo dalilin mutuwar da yadda ya mutu, da inda ya kai cikin tafiyarsa. Gwamna Maxwell ya cigita ko zai sami wani mutum mai gaskiya wanda za a iya yarda da magana tasa. Aka yi katari, aka sami lsyaku. Gwamna ya yi masa magana, Isyaku kuwa ya yarda zai tafi bin sawun.
Aka yi wa Isyaku shiri cif, aka ba shi 'yan rakiya. Gwamna Maxwell kuma ya ba shi badujala, da bindiga biyu, da gadon karfe, da alade biyu, da turamen ajanaku, da karnuka biyu, aka ce ya kai wa Sarkin Sego. Isyaku ya kama hanya. Ya kwana ya tashi har Sego. Da ya tafi ya tarar wancan Sarkin ya mutu, babban dansa Da shi ya zama Sarki. Ya sauka a gidan wani bafade da a ke kira Ciyawe, wanda ya je ya fada wa Sarki ga shi ya iso. Da safe bayan an dauke ruwa, Sarki ya aiko ya ce Isyaku ya tafi, amma ya tafi tare da aladen da ya kawo masa a daure, yadda ya taho da su.
ISYAKU YA SAMU LABARI
Bari mu ji duk yadda aka yi daga bakin Isyaku :
Da shigata zauren farko na fada sai na sami dakarai su arba'in, duk kuwa samari ne karfafa. Na wuce su, na shiga wani kuma sai ga wadansu, kowa na rike da makami a hannunsa, sun zuro mini ido. Da wuce su sai muka kai inda Sarki ke zaune. A kusa da shi, dama da hagu, ga takubba zararru an kafa tsininsu a kasa, ga wani kuma a bayan Sarki. Duk takubban nan uku Mungo Park ya ba shi lokacin da mu ke zaune a Sansandin, yana shirye-shiryen wucewa. A wuyan Sarkin ga rigarsa ta yaki, wadda ya ke kwana yana tashi da ita. Wata al’adarsu ce in kasar tana yaki da wata kasa, Sarki ba ya tube rigan nan sai ran da mutanensa suka komo daga wurin yaki.
Da muka shiga, na fadi na yi gaisuwa, na koma waje guda na zauna, mai masaukina kuma haka. Na baza masa kayan nan da aka aiko ni in kawo wa uban, amma a cikin karnuka biyu daya ya salwanta a daji. Na ce masa, “Ran Sarki ya dade, Mr. Maxwell, Gwamnan kasar Senegal, ya ce in yi maka gaisuwa. Kuma ga wadannan kayan ya ce a kawo wa Sarki marigayi, bai san ya mutu ba. Watau su ne abin da ya tambayi Baturen nan Mungo Park da muka zo da shi, shi kuwa ya yi alkawarin zai kawo masa."
Sarki ya ce, “Gwamna yana nan lafiya ?"
Na ce, “Yana nan lafiya, ran Sarki ya dade. Ya ce in zo gare ka, ka taimake ni sanin abin da ya sami Mungo Park, don labaru suna kai mana a Gambiya cewa an kashe shi. To, shi ne ya turo ni in zo im bi sawu, in tabbata in gaskiya ne. Ya ce yana so ka ba ni jirgi wanda zai kai ni har iyakar inda Mungo Park ya kai, shi kuma zai ba ka ladanka."
Sarki ya ce, “Me Gwamna zai ba ni ?"
Na ce, “In dai am ba ni duk taimakon da na ke bukata, Gwamna zai ba ka amba metan."
Ya ce ya ji ya yarda, amma bai ga yadda Gwamna Maxwell zai ba shi amba metan daga Senegal a kawo Sego ba. Na ce lalle tsakaninsu da nisa, amma tun da ya ke ga ni, ai sai in zama wakilinsa, in karba in aiko masa da shi. Da ya ji haka sai ya yarda, ya ce zai yi mini duk abin da na tambaya. Ya sa aka yanka mini sa dungum, ya ce in huta har wata ya mutu tukuna.
Da wata ya mutu, wani ya tsaya ya kwana goma, ran nan Sarki ya ba ni jirgi, ya hada ni da masunta uku, na tashi na bi sawun Mungo Park. Ga mu nan muna bin igiyar ruwa sai Sansandin, muka kwana.
Kashegari sai Madina. A can na sami Amadi Fatuma, mutumin da na hada shi da Mungo Park suka tafi tare. Na aika a gaya masa ga ni, nan da nan kuwa ya iso masaukina. Bayan mun gaisa, na ce masa abin da ya kawo ni ina neman sahihin labari ne na Mungo Park. Da jin na ambaci sunan Mungo Park sai na ga kwalla sun faso masa. Da ya bude baki, abin da ya fara ce mini shi ne, “Ai duk sun mutu."
Na ce masa, “Share hawayenka, ko da kai na zo nema, na kuwa yi niyyar duk inda ka shiga sai na gan ka, don in sami labarin gaskiya game da mutuwarsu." Ya ce sun halaka har abada, saboda haka ba shi da amfani in wahal da kaina in je nemansu, don neman abin da ba shi, bata lokaci ne kurum. Na ce masa, na yarda da maganarsa, zan juya da baya in koma Sansandin, amma ina so mu gamu da shi a can. Na koma Sansandin na kwana, da gari ya waye na aika wa Sarkin Sego da jirginsa Amadi Fatuma kuma ya zo ran 10 ga Oktoba 1810. Da zuwa na ce masa abin da na ke so shi ne ya fada mini irin abin da ya sani ya faru ga Mungo Park, daga tashinsa Sansandin har halakarsa. Ga abin da ya rubuto da Larabci ya ba ni :
LABARIN AMADI FATUMA
“Mun tashi daga Sansandin a jirgin ruwa ran 27 ga watan sama, da ni da su Mungo Park. Bayan kwana biyu muka kai Selli, inda Mungo Park ya tsaya a tafiyarsa ta farko, daga nan ya juya da baya. Mungo Park ya sayi bawa don ya taimake mu taka jirgi. Bayan Mungo Park akwai Mr. Martyn, da wadansu Turawa uku kuma, da bayi uku, da ni jagoransu kuma tafintansu, mu tara ke naa. Da muka wuce Selli, muna waigawa sai ga jirage uku a guje suna biye da mu, mutanen ciki kowane da kwari da baka, amma babu mai bindiga cikinsu. Da dai muka gane mu su ke hari, sai muka ce musa su koma, suka ki. Muka bude wuta, tilas suka koma. Da muka wuce wani gari kuma wai shi Gauraumu, sai ga jirage bakwai, makil da mutane da kwari da baka. Su kuma muka maishe su baya. Bature daya cikimmu ya mutu, amma ciwo ya kashe shi, ba wani abu ba. Muka rage saura mu takwas. Muka wace wani kauye wanda na manta da sunansa, amma a nan Sarki Gotojege ya ke zaune. Muna wuce kauyen sai muka hango jirage sittin suna biye da mu a guje. Muka bude musu wuta muka kashe su da yawa. Da sauran suka ga haka, sai suka juya. Ganin yadda a ke kashe rayuka haka sai na kama hannun Mr. Martyn, na ce, ‘Mr. Martyn, ya kamata mu daina harbi haka nan, rayukan da muka kashe sun isa.’ Da jin haka Mr. Martyn ya ta so mini yana neman kashe ni, sai da Mungo Park ya shiga tsakani.
“Da muka yi dan nisa, har wa yau sai muka sake gamuwa da wata babbar runduna a gabar kogi suna hutawa. Muka wuce su ko sannu ba su ce mana ba. Muna cikin tafiya sai muka yi karo da dutse. An jima kuma kadan sai ga dorina ta taso, tana neman kabar mana da jirgimmu, muka harbe ta da bindiga, ta gudu. Ran nan dai ba mu tsaya ba sai da muka kai Kaffo, a nan muka kwana. Tun kafin mu taso, sai da muka wo guzurin abinci iri iri a Sansandin, don gudun yawan tsayawa a garuruwa muna neman abinci. Jirgimmu babba ne, don zai iya cin mutum dari da ashin'n. Da muka tashi daga Kaffo, tun ba mu yi nisa ba, sai ga jirage uku suna bim mu. Muka kore su.
“Mun isa wata maciya gabar kogi, sai aka tura ni tudu in sayo madara. Ina tafiya sai mutanen maciyar suka kewaye ni suna neman kashe ni. Har wani cikinsu ya rike ni kam, ya ce wai na zama fursuna. Da Mungo Park ya ga haka, ya ce da mutanen kul suka kuskura suka taba ni zai kashe su duka, ya kwashe jiragensu da kayansu. Sai suka sako ni. Bayan mun tashi daga nan, mun taba 'yar tafiya, sai ga jirage ashirin sun taso daga maciyan nan a guje. Da suka zo kusa da mu sai daya cikin mutanen ya mike, ya ce, ‘Kai Amadi Fatuma, yaya za ku shige cikin kasarmu ba ku ba mu kome ba ?’ Na gaya wa Mr. Park abin da suka ce, sai ya ba su amba da dutsen wuya, suka juya.
“Da muka kai wani gari wai shi Gormon, muka sauka muka kara guzuri, muka yi gaba. Har mun yi dan nisa, sai Sarkin garin ya aiko a gaya mana akwai wadansu miyagu suna can gaba, sun labe a kan wani tsauni suna jiram mu. Saboda haka ya kamata ko dai mu komo da baya, ko kuwa mu kula da kammu. Da jin haka sai muka tsai da jirgi, muka yini a wurin, muka kwana. Gari na wayewa muka yi gaba Muna zuwa daidai tsaunin, sai kuwa ga mutanen nan suna jirammu. A cikinsu muka ga har da Larabawa bisa rakuma, amma babu mai bindiga, duk taron. Ba mu ko kula su ba, su kuma ba su ce mana kome ba, muka wuce muka shiga kasar Hausa, nan muka tsaya.
“Da shigarmu wannan kasa sai Mungo Park ya ce mini, “To, Amadi Fatuma, ka fa zo iyakar tafiyarka. Mun yi alkawari nan za ka kawo ni, ka kuwa kawo ni, yanzu kuma sai ka bar ni. Amma kafin mu rabu ina so ka fada mini abubuwan da zam bukata da yadda a ke fadarsu a harshen kasar da za mu ratsa." Na yarda zan gaya masa a kan hanya kafin mu rabu. Bayan mun yi tafiyar kwana biyu muka iso Yawuri. Tun da muka taso daga Sansandin har Yawuri ni kadai ne na taba sauka kasa.
MUMMUNAN KARSHE
“Da gari ya waye Mungo Park ya ba ni bindiga da takobi, ya ce in kai wa dagacin Yawuri. Ya kuma ba ni turmin akoko uku, ya ce a ba shi ya raba wa mutanensa. Na tafi na ba dagacin nasa, na kuma ba wani wai shi Alhaji turmi daya, na ba Alhaji Biro turmi daya, dayan kuma na ba wani amma na mance sunansa, amma dukansu Musulmi ne. Dagacin ya aiko mana da sa, da rago, da tukunyar zuma uku, da kayan kato hudu na shinkafa. Mungo Park ya sake aikena gun dagacin in kai masa zobba biyar duk na azurfa, da albarushi, da kyastu, ya ce in gaya masa wadannan gaisuwarsa ce zuwa ga babban Sarkin kasar. Sarkin Yawuri, babban Sarkin kasar, a lokacin yana zaune nesa da kogi. Mungo Park ya ce dagacin ya gaya wa Sarkin wannan gaisuwa daga wani Bature ne wanda ke neman izni ya shige ta cikin kasarsa.
“Bayan dagacin ya karbi kyautar, sai ya tambaya ko ta wannan hanyar Mungo Park zai biyo in zai koma gida. Da aka gaya wa Mungo Park sai ya ce, ‘In na wuce na wuce ke nan, ba zan sake komowa ta nan ba.’ Fadar haka ita ta kawo mutuwar Mungo Park. Don da dai dagacin ya ji ba zai biyo ta nan ba, sai ya ki kai wa Sarkin Yawuri kyautar da aka ce ya kai.
“Ni kuma na ce da Mungo Park, ‘Mun yi alkawari zan kawo ka kasar Hausa ne daga Sansandin. To, ga mu a kasar Hausa. Na cika alkawarina, saboda haka zam bar ka nan, in koma.’
“Kashegari, ran Asabar, muka yi sallama da Mungo Park, ya tashi, ni kuma na kwana a Yawuri. Da gari ya waye na tafi garin da Sarkin Yawuri ya ke don in yi gaisuwa. Da shiga gaban Sarki sai na sami barade biyar wadanda dagacin Yawuri ya aiko su. Ina zama sai suka ce da Sarki, “Allah ya ba ka nasara, dagacin Yawuri ne ya aiko mu mu gaya wa Sarki Turawan nan sun wuce, ba su ba Sarki kome ba, balle fa shi da bai dada kome ba. Jirginsu yana makare da dukiya iri iri. Ya kuma ce a gaya maka, Allah ya ba ka nasara, kada ka yarda da Amadi Fatuman nan, lalatacce ne. Shi ne ya hana Turawan nan su ba ka wani abu.'
“Da rufe bakinsu Sarki ya sa aka buge ni aka daure. Aka cika ni cikin sarka, wadansu suna a kashe ni, wadansu suna a kyale ni. Gari na wayewa sai Sarkin ya aika da mayaka wani gari wai shi Busa a bakin Kogin Kwara.
....
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com/
http://bukarmada.wordpress.com/
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)