NEMAN SHAWARA!



​Matan sirri pls kutaimakama qawata da shawara,tazo wurina Neman shawarane amma ni ba wani wayo bane dani shine nace bara in nemi shawaranku...Ita dai wannan ta auri mai mata kuma uwargidan tana da kirki sosai domin kowa yana yabonta amma wasu lokutan takan nunama amaryar alamun kishi,Itakuma amaryar tana sonta tana bata girma kuma tana gudun bacin ranta domin tana tausaya mata tasan tana son mijinta sosai kuma ta amince ya Aurora..duk wadannan abubuwan ne amaryar take tunani shiyasa bata treating dinta kamar uwargidanta,asalima bata yiwa mijinta abubuwan da zai nuna cewa ita matarshice idan suna tareda uwargidan, Misali bata iya kwalliya Idan suna tare kuma bata iya zama da mijin da uwargidan suyi hira wai tana jin kunya...To matsalar itace mijin bai damu da itaba,Ita yanxu tana wani gari tana karatu said mijin yayi wata biyu baixo ya dubata ba kuma Idan yaxo baxai wuce kwana hudu/biyar ba,wani abin haushi Idan yana tareda ita karfe Tara na dare itama uwargidan ana sallar asuba zakiga ta kirashi tana tambaya yaci abinci ko me zaici kuma susha hirarsu kamar ba daga wurinta yakeba amma Idan amaryar ce takirashi karfe bakwai da rabi sai kiga yana magana kamar ta dameshi,Wallahi ni nasan amaryar batada matsala,Kamar yadda ta fadamun kafin tatafi karatu wai duk ranar kwananta dayake kusan kullum saita kira uwargidan ta gaisheta to Idan had tanar kwananta xakiga uwargidan na amsawa cikiciki shine data lura da haka sai wani lokacin tace maigidan yaje ya kwana can,akwai wani lokacin ma data ce yaje ya kwana can har na sati days kuma bece komaiba itama kuma uwargidan haka,amma wani abun haushi akwai lokacin datakeda tsohon ciki aihuwa yau ko gobe ga uban wahala da ciwo kuma ita kadaice gidan amma ko sau daya bata taba cewa mijin ya kwana ba asalima Idan uwargidan taga mijin be shigo gida ba xuwa biyar da rabi xata ringa nemanshi awaya tana tambaya ina yake kuma dayace yana wurin amaryar xata katse wayar..Gata amaryar yarinyace baxata wuce 23 kuma uwargidan xata haifeta don Allah kutaimaka tanaso ta shawo kan mijinta amma kuma batason ta bakanta ma uwargidan ta,pls kubata shawara yadda mijinta xai rinqa bata kulawa kuma baxai baqanta wa uwargidan ba​

Post a Comment (0)