SHARHIN FIM ƊIN CAPTAIN AMERICA: THE WINTER SOLDIER

SHARHIN FIM ƊIN CAPTAIN AMERICA: THE WINTER SOLDIER 


Captain America: The Winter Soldier fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2014 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Captain America wanda Joe Simon da Jack Kirby suka wallafa a ƙarƙashin Kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne ya ɗauki nauyin Fim ɗin Yayinda Kamfanin Walt Disney Motion Pictures ya rarrabashi. 

 Fim ɗin shi ne na biyun Captain America: The First Avenger (2011) kuma Fim na tara daga cikin Fina Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU). Anthony da Joe Russo sune suka bada umurnin Fim ɗin, yayin Christopher Markus Stephen McFeely suka rubuta kuma suka tsara. Anyi na ukun Fim ɗin mai suna Captain America: Civil War. 

An fara Ɗaukar wannan Fim ne a cikin watan Afrilu 2013 a birnin Los Angeles, California, Kafin daga baya aka koma Washington, D.C. da Cleveland, Ohio .
 
An fara kallon Captain America: The Winter Soldier ne a birnin Los Angeles a Ranar 13 ga watan Maris 2014, sannan aka sake shi a ranar 4 ga watan Afrilu 2014 a zubin 2D, 3D , da IMAX 3D. Wannan Fim ya samu gagarumar nasara kuma an yaba masa sosai ba kaɗan ba musamman a fannin sauti, faɗa Kafce bada umurni, labari da dai sauran su. Bugu da ƙari, fim ɗin ya kawo kuɗi kimanin Dala miliyan $714 a harkar Kasuwancin Fina Finan duniya baki ɗaya, hakan yasa ya zama Fim na bakwai da yafi kowanne kawo kuɗi a 2014. Har wa yau, fim ɗin ya samu damar shiga gasannin Fina Finai da dama. 

LABARIN FIM ƊIN 


Shekaru biyu bayan artabun New York,
Yanzu Steve Rogers yana aiki ne a Washington, D.C. Wa Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. a ƙarƙashin Darakta Nick Fury , Yayin da yake koyon ci gaba da rayuwa a cikin wannan al'umma ta yanzu. 

Watarana sai aka aika Rogers, Natasha Romanoff da wata tawagar yaƙi da ta'addanci ta ɓangaren S.H.I.E.L.D. Mai suna S.T.R.I.K.E. Wace Rumlow yake Jagoranta domin su tseratar da wasu Kamammu daga wani jirgin ruwan S.H.I.E.L.D. Wanda Georges Batroc da muƙarraban sa suka kama. 

Ana tsaka da aiki, sai Rogers ya gano cewa Romanoff tana da wani aikin kuma da aka bata, wanda shi ne ta kwashi wasu bayanai daga Na'ura mai ƙwaƙwalwar jirgin ta kaiwa Fury. 

Daga nan sai ya tafi Hedikwatar S.H.I.E.L.D. domin ya ƙalubalanci Fury, anan ne aka yi masa bayani dangane da shirin INSIGHT, wasu Jibga-jibgan jiragen yaƙi ne guda uku waɗanda aka haɗa su da tauraron ɗan adam domin yin leƙen asiri waɗanda umurni kawai za'a basu nan take zasu kashe duk wani wanda zai kawo wa al'umma hari. 

Ganin cewa ya kasa buɗe waɗannan bayanai da Romanoff ta kawo masa, sai Fury ya fara zargin wannan shiri na INSIGHT don haka sai ya nemi wani babba daga cikin Jami'an S.H.I.E.L.D. Wanda shi ne Sakataren kula da harkar tsaro na ƙasa wato Alexander Pierce da ya Jinkirtar da shirin. 

Yayinda ya fita domin yin wata tafiya tare da Maria Hill , sai wasu mahara suka kaiwa Fury hari, wanda ke Jagorantar su kuwa wani Fitaccen Masheƙi ne mai suna Winter Soldier. Fury dai ya samu ya gudu izuwa mazaunin Rogers inda ya sanar da shi cewa an samu matsala a Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. Inda a nan take Winter Soldier ya harbe Fury a dai dai lokacin da yake bashi wani matattarar bayanai wanda ke ƙunshe da bayanan da Romanoff ta samo daga cikin wannan jirgi. 

An bayyana Fury a matsayin matacce yayin da ake yi masa aiki, Inda Maria Hill ta tafi da gangar jikin sa. Washe gari sai Pierce ya kira Rogers izuwa Hedikwatar su, da Rogers yaƙi basu bayanan Fury, sai Pierce ya bayyana shi a matsayin ɗan gudun Hijira sannan yasa tawagar S.T.R.I.K.E. su kama shi, daga nan sai Rogers ya haɗu da Romanoff bayan sun yi amfani da bayanan da ke ciki, sai suka gano wani ƙaramin Sansanin S.H.I.E.L.D. da ke ɓoye a New Jersey. 

A can ne suka kunna wata Na'ura mai ɗauke da hankalin Arnim Zola. A nan ne Zola yake bayyana musu cewa ai tun lokacin da aka kafa Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. bayan yaƙin duniya na biyu, Jami'an Hydra suke ta aiki a cikin ta ba tare da an sani ba, suna ta jawo Bala'i a duniya don akai matakin da jama'a zasu miƙa ƴancin su domin a basu kariya. 

Da ƙyar Rogers da Romanoff suka tsira sakamakon wata nakiya da jirgin S.H.I.E.L.D. Ya jefawa Sansanin. A nan ne kuma suka gano cewa Pierce shi ne jagoran Hydra a cikin ƙungiyar S.H.I.E.L.D. Rogers da Romanoff sai suka nemi taimakon wani tsohon sojan sama mai suna Sam Wilson , tare da rigar tashin sa. Bayan sun gano cewa Jami'in S.H.I.E.L.D. Jasper Sitwell shima ɗan Hydra ne, sai suka tilasta shi yi musu bayani. A nan ne ya bayyana musu cewa wannan shiri na INSIGHT an tsara shi ne da nufin ya kashe duk wani mutum da ake tunanin zai iya zama haɗari wa duniya a nan gaba, kuma hakan zai faru ne da zarar an baiwa na'urar da ke tauraron ɗan adam umurni domin cike take da bindigu. 

Kwatsam sai Winter Soldier ya kawo ma su Rogers hari inda nan take ya kashe Sitwell. A nan ne Rogers ya fahimci cewa Winter Soldier fa ba kowa bane face abokin sa Bucky Barnes Wanda Kowa yayi tunanin ya mutu. Ashe bai mutu ba, hydra ne suka ɗauke shi suka juyar masa da tunani. Daga nan sai Maria Hill ta ɗauke su izuwa wani keɓantaccen gida inda suka yi ido biyu da Fury, ashe bai mutu ba, kawai dai yayi basaja ne. A nan ne Fury ya bayyana musu shirin sa na daƙile shirin INSIGHT ta hanyar canja wasu Na'urori guntaye da ke jikin jiragen. 

Bayan Membobin Ƙungiyar tsaro ta duniya gaba ɗaya sun taru, sai Rogers yayi wata Sanarwa dangane da halin da ake ciki tare da yunƙurin hydra na son ganin bayan dubunnan Jama'a, Romanoff, wacce ita kuma ta yi ɓadda bami a matsayin ɗaya daga cikin Membobin Ƙungiyar sai ta ƙwace Makamin Pierce, a nan ne Fury ya shigo ya tilastawa Pierce ya buɗe tuƙullumar bayanan Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. domin Romanoff ta samu damar watsawa duniya MUHIMMAN bayanai dangane da shirin Hydra. Bayan wata ƴar Fafatawa, sai Fury ya kashe Pierce. 

A can gefe kuma, Rogers da Wilson sun samu damar canja waɗannan Guntayen Na'urori na Jirage biyu, sai dai Winter Soldier ya Lalatawa Wilson rigar tashin sa, sannan suka fafata da Rogers a kan na ukun. Da ƙyar dai Rogers ya samu ya canja wannan na'urar jirgi na uku wanda hakan ya baiwa Maria Hill damar sanya jiragen su harbe kansu maimakon su harbe mutane. 

 Daga nan sai Rogers yaƙi yaƙar Winter Soldier bisa tunanin yin hakan zai bashi damar riskar abokin sa. Yayin da waɗannan Jirage suka rikito akan wanda Su Rogers suke ciki, sai suka faɗa wani kogi. Daga nan sai Winter Soldier ya Ciro Rogers daga Kogin a sume, sannan ya shige daji. 


Ganin cewa Ƙungiyar S.H.I.E.L.D. tana cikin damuwa Romanoff sai ta bayyana a gaban Kwamitin Sanatoci domin gabatar da jawabi, yayin da shi kuma Fury ya tafi Gabashin Yuropiya domin gano tare da tarwatsa sauran Sansanonin Hydra. Rogers da Wilson kuma sai suka bazama neman Winter Soldier yayin da shi kuma Rumlow, wanda ɗan Hydra ne yake jinya a asibiti sakamako munanan raunuka da ya sa. 

A wata fitowa ta ƙarshe, an nuna Baron Wolfgang von Strucker a wani ɗakin gwaje-gwaje na Hydra Yayinda malaman kimiyya suke karantar wata sandar tsafi, ga kuma wasu mutum biyu nan da aka yiwa aiki, ɗaya yana da ƙarfin gudu ne kamar walƙiya, Yayinda ɗayar kuma take iya sarrafa tsafi daga Zuciyar ta. 

An kuma nuno Barnes Yayinda ya je gaban wani hoto da aka Manna domin tunawa da shi. 


JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA 


* Chris Evans - Steve Rogers / Captain America

* Scarlett Johansson - Natasha Romanoff / Black Widow

* Sebastian Stan - Bucky Barnes / Winter Soldier

* Anthony Mackie - Sam Wilson / Falcon

* Cobie Smulders - Maria Hill 

* Frank Grillo - Brock Rumlow

* Emily VanCamp - Sharon Carter / Agent 13

* Hayley Atwell - Peggy Carter 

* Robert Redford - Alexander Pierce

* Samuel L. Jackson - Nick Fury

* Toby Jones - Arnim Zola 

 * Maximiliano Hernández - Jasper Sitwell

* Garry Shandling - Senator Stern 

* Georges St-Pierre - Georges Batroc

* Callan Mulvey - Jack Rollins



<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...
Post a Comment (0)