HUKUNCIN AUREN MACE DA CIKI :
https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN
*TAMBAYA*❓
Assalamu alekum dafatan muntashi lafiya amin, donAllah Inada tambaya kamarhaka wato mutum ne yakeneman aure sai shedan yashiga tsakanin su da ita yarinyan harta samu ciki kuma aka dauramusu aure bayan aure da wata 5 da sati 2 saita haihu to yaya auren su yake kama ya shi ko abinda aka haifa take? nagode dafatan malamai zasu taimaka su amsamun tambaya ta wassalam.
*AMSA*👇
Wa alaikumus salam.
In dai sun tabbata sunyi zina, Kuma sun tabbata cewa alokacin da aka daura auren ma Matar tana da ciki, to ai babu auren ma. Domin kuwa ita mai ciki hukuncinta kamar na masu Iddah ne. Wato Kamar yadda ya haramta adaura auren Matar dake cikin iddah, to hakanan ita ma Mai juna-biyun bai halatta a daura mata aure ba, har sai bayan ta haife abinda ke cikin nata.
Gaskiya auren ma babu shi. Shi kuwa abinda ta haifa tunda 'dan zina ne bashi da wata alaqah da wannan mutumin. Babu gado atsakaninsu koda shi mutumin ya amince cewa shi yayi mata cikin.
Ya zama wajibi Malamai su tashi tsaye wajen warware irin wadannan matsalolin domin kuma suna yawan faruwa acikin al'ummah. Mutane sun san cewa 'Yarsu tana da juna biyu, amma a haka zasu 'daura mata aure, taje ta haihu agidan wanda yayi mata cikin. Kuma suci gaba da zama amatsayin Miji da Mata, alhali kuma wannan ba aure bane. Zaman sa'bon Allah ne. Allah ya sawwake.
Amma idan aka daura aure atsakanin Ma'aurata, sai Matar ta haihu bayan watanni shida da daura auren, to wannan 'dan na mijinta ne. Sai dai in akwai Shaidar da ta tabbatar da cewa ba agidansa ta samu wannan cikin ba.
WALLAHU A'ALAM.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: ▽_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*