UKU-BALA'I 03



UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

BABI NA UKU

 Kuri likita yayi mata da idanu gabadaya hankalin sa da guntuwar natsuwar sa tana kan ta hannusa kuma yana mikawa nurses jaririn bayan ya yanke masa cibiya.

 Abubuwa ne suka shiga yi masa dirkar mikiya a kwakwalwa zuciyarsa na ta tunano masa wasu abubuwa da baya fatan ace sun faru da wannan baiwar Allah ajiyar numfashi yayi gami da saurin duban Nurses da suma hankalinsu na kanta ganin halin da take ciki na rai kwakwai mutu kwakwai.

 "maza kuje ku gyara jaririn sannan kuma ku dauko gado domin daukarta don na lura tayi matukar gajiya da galabaita".

Abin da likiti ya kokarta furtawa kenan cikin rashin tsammanin samun karfin daga laɓɓa har ya yi furuci gyaɗa kai yake yi yana gauraya kwayar idanuwansa cikin gurbin su laɓɓansa dake cikin bakin sa sai faman cizon su yake fuskarsa na kara bayyanar da rashin armashi da natsuwa.

 Mikewa yayi cikin rashin kumaji duk wani azancin sa yana jin yarda yake kokarin kufce masa daurewa kawai yake yi yana yaki da batun da kwakwalwarsa da zuciyarsa suke ta sanar dashi ba zai so haka ba, ba ya faman haka ta kasance gyaÉ—a kai ya cigaba da yi kamar yana magana da wani ya ma rasa abin da ya dace yayi tunaninsa gabadaya ya wargaje sai akan abu daya wanda yake tsammmanin ba É—a mai ido zai haifo ba.

Dawowar nurses ne ya dawo dashi daga duniyar fargaba da tsunduma ya shiga jan numfashi a hankali mai dauke da kayan tashin hankali
Ya dube su su duka yana mai kaÉ—a idanu yana mai yi musu nuni da ita nan suka shiga gyara mata jiki tamkar gawa haka suke sarrafa har suka kammala sannan suka daurata zaman gadon gami da gungurawa suka fice daga cikin dakin yana mai bin su da kallo numfashi ya ajje gami da jingina da jikin bango har zuwa lokacin zuciyarsa sai kokarin gasgata masa lamarin take wanda shi sam ba ya fatan hakan wuyar rigarsa ya gyara gami da jan jiki ya fice daga cikin dakin xan gefe ya hango Malam Bello tallabe da haba sai faman mazurai yake yi cikin yanayi na rashin kwanciyar hankali kallo sosai likita ke bin sa da shi zuciyarsa na dauko tausayinsa tana jingina masa ta kowani bangare na sassan jikinsa sannu a hankali ya fara kokarin jan jiki ya isa gareshi amma sam bai san ya iso ba har sai da ya daf kafadarsa wata irin zabura yayi mai dauke da ajje wani gwauron numfashi idanuwansa fes kan likiti jikinsa yana rawa ya riko hannunsa.

 "don Allah in har zaka yi furuci kayi wanda ba zai tafi da imanin zuciyata ba na rokeka".

 yanayin da yake sakin furucin da kyar yasan ya jikin likita kara sanyi ya shiga gyada masa kai.
 "ta haihu...".

shima ya fadi dakyar kamar wanda akayi wa dole idanuwansa na kan Malam Bello kamar yarda shi ma ya ke kallonsa zare hannunsa yayi saboda wani irin bugu da yaji ya kawo masa ziyara zuciya ya dubi Malam Bello.

 "ina zuwa zan maka magana in an kammala gyara mata jiki sai ka zo ka ganta da baby ko".

ya karashe cikin sakin murmushin yaƙe bai jira amsawar Malam Bello ba ya ja jiki da sauri ya nufi dakin hutu da aka kai Habeeba ya tura ya shiga har yanzu dai jiya-i-yau da sauri ya isa gareta yana duban nurses da sukayi carko-carko da alamun yanayin da suka ganta ya tafi da yar guntuwar jarumtarta su hannunta ya kamo bayan ya dan rankwafa zuwa gareta hannun ya shiga juyawa yana mai kai dayan hannun nasa izuwa wuyanta yana taba alamun nemon motsin numfashi cak! ya tsaya kamar wanda aka cewa in yayi kwankwarar motsi ba zai ji sautin saukar numfashin nata ba gyada kai yake yi cikin raguwar faduwar gaba jin saitin kirjinta yana harbawa alamun da rai a jikinta har zuwa wannan lokaci ajje numfashi yayi mai karfi kafin ya miki ya shiga binciken ta sosai tsayin wani lokaci bayan ya kammala ya umurci Nurses akan su dauko masa kayan karin jini cikin sauri suka fice gami da daukowa ruwa ya fara sak mata gami da yin wasu allurai a cikin ruwan sannan ya juya inda ya juyo jaririn na kuka inda aka kwantar dashi kallonsa yayi sosai ɗa namiji ne fari tas dashi kyankyawa mai kama da uwarsa.

 Barin wajan yayi, ya yi hanyar fita waje. A bakin kofa ya tadda Malam Bello tsaye ya na jiran fitowarsu, da hanzari ya isa gareshi dauke da fuskar murna sai faman tallar hakoransa yake yi kamar wanda aka baiwa sabuwar amarya amma in ka lura sosai zaka tabbatar da murmushin na yaÆ™e ne cikin kokarin dauko jarumta ya dorawa kansa ya isa gareshi shima da ya hango shi cikin hanzari ya baza masa idanu yana takowa a hankali kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki lura da yayi fuskar likita da murmushi sai faduwar gabarda take wa kirjinsa bugun kato ta fara saurarawa yashiga ajje numfashihar suka iso ga juna suna shakar numfashi Malam Bello ya sake ajje numfashi yana mai gyara zaman hular kansa ya shiga jiki na É“ari ya dubeshi.

 "likita ka ja min rai wallahi, don Allah sanar dani halin da ake ciki, ko na samu raguwar bugun katon da zuciyata ke yi".

 ya fadi yana kara kusanto shi kamar zai shige jikinsa idanuwansa fes akan sa.

zuciyar likita tayi matukar cilla cikin wani hali na ta rarrabi na rashin tabbas akan lamarin da yaji duniyar tunaninsa na shawagi dashi a ciki ya rasa mazaunan hankalisa sun ka sa zaman kalau ya tabbata zuciyarsa bata yi masa adalci ba in har ta dauko mata banzan tunanin nan wanda in har ya gasgatashi komai zai iya faruwa wani yake ya kinkimo ya daurawa fuskarsa tare da dafa kafadar Malam Bello.

 "ta haihu lafiya an samu É—a namiji ina tayaka murna...".

Sautin ihun da ya dauki cikin asibitin gabadaya shi ya daskarar da duk wani motsi na mutanan cikinsa ya tafi da furucin su likita da yayi mutuwar tsaye idanuwansa fes akan na malam Bello wanda shi ma kallo daya zakayi masa ka tabbatar zuciyarsa ta shiga halin tsoro matuka da ihun da ya karaÉ—e cikin asibitin da saurilikita ya juya ya yi dakin da Habeeba take ba wai don ya na da yakinin daga dakin ihun ya fito ba kawai zuciyarsa ce ta ja linzamin hankalinsa izuwa dakin ilai kuwa yana kokarin shiga suka ci karo da Nurses cikin yanayi na firgici da razana bakin ta na rawa ta shiga nuna masa cikin dakin da hannuamma sam ta kasa kokarin fadin wani abu da zai zarewa likita yarjewa kansa Habeeba ce tayi wannan ihun da hanzari ya fada cikin dakin malam Bello dake bin su a baya shima a daidai lokacin ya fado ciki.

 Zaune take taÉ—e jikinta waje daya hannayenta cikin kunnuwanta sai faman zabga ihu take yi jikin ta na faman kyarma kamar wacce akayi wa tsinannan duka. kan ta su kayi gabadayan su malam Bello yana isa ya zauna kusa da ita yana mai kokarin janye hannayenta daga kunnuwanta yana mai dago habatar idanuwanta ya gani sun kaÉ—a sunyi jajir sai hawaye da suke kwaranyowa gabansa yayi mugun faduwa ganin irin halinda take ciki na rashin hayyaci juya wa yayi da sauri ya dubi likita bakin sa na rawa shima likitan idanuwansa na kanta domin abin da yake tsoro ne ya faru domin kuma ko tantama ba yayi ta samu matsala akan ta gau da kai yayi daga kallon da Malam Bello ke yi masa ya isa kusa da Habeeba ya kira sunanta amma ba ta amsa ba domin bata san ma yanayi ba sam! duban Malam Bello yayi cikin murya mai dauke da rauni.

 "yi mata magana sanar da ita kai wanene".

da mamaki ya shiga duban likita jin abin da ya ce dashi gabadaya ya ji kansa na juyawa wasu lamura na tashin hankali yaji sun kawo masa hari ba shi ya mike yana nuna likita da hannu.

 "ban gane zancen naka ba sam, taimaka kayi mani fashin baki, ta ya ya zaka ce na sanar da ita wanene ni, bayan nasan kuma mun san junanmu ba bakin fuskoki bane mu a tsakani don Allah likita ka fahimtar dani abin dake faruwa".

Ya karashe yana mutsuttsuka wuyar rigarsa yana mai cizon laɓɓansa ransa sai faman daci da fargaba yake yi domin yarda ya lura da canjin likita ya tabbata akwai matsala a tsakanin rayuwa matarsa kukan da jaririn ya saki ne ya sanya shi saurin juya inda ya juyo kukan da sauri ya kara kusa da gadon da jaririn yake kwance sai faman wuntsil-wuntsil yake yi da kafafuwansa hannunsa cikin bakinsa da alamu yinwa yake ji bai san halin da duniyar ta sa ta zo masa dashi ba hannu ya saka yadauki jaririn wanda yake nannaɗe ido ya zuba sa sosai yana ƙare masa kallo zuciyaraa da kasar ruhinsa sai hasaso masa abubuwa suke yi ma bambanta so da kaunar ɗan nasa yaji sun tsargar masa a jiki da jinin dake gudana ta ko ina a gareshi.

Hannu ya saka ya dauko jaririn kafin ya juya na kallon likitan.

 "kace mani wani abu don Allah ko na samu saukin kunar rai da na zucci".

Idanuwa duk suka zuba masa ganin yarda yake magana cikin yanayi na wahalallan yanayi da rashin hayyaci.

Likita ya shiga gyaÉ—a kai kamar kadangare kafin ya nisa.

 "ban san ya zan fara yi maka bayani ba amma dai zan ce maka ka yarda da Æ™addara ko wacce iri ce ta fado rayuwarka".

"ƘADDARA".

malam Bello ya furta kalmar cikin jan numfashi da fada ruÉ—ani.
Ya shiga nazarin kalmar shi dai ana sa tunani ya san abin da ake nufi da ƙaddara akwai kaddara mai kayan farin ciki akwai kuma akasinta shi dai a yanzu ya san kaddarar sa ba mai dadi ba ce.

"likita kayi min bayani yarda zan fahimta zuciya ta na cikin bala'i".

Ya fadi yana mai dauke gumin dake karyo masa kamar wanda ya fito daga surace hannunsa daya kuma jariri ne sai faman wuntsil-wuntsil yake yi yana tsotsar hannunsa alamun yunwa yake ji.

"...Uhmm nace ya kamata ka nemo wacce zata kula da ita na dan lokaci kafin komai ya zama daidai".

Likita ne ya fadi haka cikin rashin abin cewa.

Kallon sa yake yi, kallo na tuhuma mai cike da son karin bayani akan komai, kallon sa yake yi na rashin yarda da yanayin da ya gan sa a ciki, kallon sa yake yi cikin bugun zuci da ruhi. idanuwansa ya shiga juyawa akan ko wani dayan su cikin yanayi na kara tsoro da fargaba gani yake yi kamar Habeeba mutuwa zatayi in da a kwance take zai iya cewa mutuwa tayi amma suke boye masa amma zaune take cikin wani irin yanayi wanda shi kan sa bai san a matsayar da zai ajje shi ba.

Nisawa yayi gami da juyawa ya ajje jaririn kafin ya dubi likita.

"bana tsammani zuciyata zata yarda da kai da sauran ma'aikatan ka, na lura kana boye min wani abu da yake boye, likita in kayi min haka ba ka yi mani adalci ba sam, kuma ba zan yafe maka ba".

Magana yake yi wanda da ka kalle shi zaka tabbatar ba isasshen hayyaci a gareshi.

GyaÉ—a kai likita yake yi tausayin sa na kara narkar masa da zuciya cikin jan jiki ya isa gareshi ya dafa kafadar sa.

"kayi hakuri kayi abin da nace".

"bani da wannan natsuwar, ka taimaka".

Idanu ya zuba masa sosai kamar wanda ya ga bakuwar fuska, bai san mai zai ce masa, ko ma ya samu abin cewa ba tabbacin zai iya kamar sa domin yasa dole abin da yake faruwa ya fado cikin abin da zai ce dashi.

"kai nake jira likita kace min ta haihu kayan farinciki kenan amma kuma naji kana kokarin dauko min kayan da za su ruÉ—ani cikin wannan lokaci, na lura akwai abin dake kokarin faruwa, koma nace ya faru amma ka ki ka sanar dani".

zuciyarsa ce ta fada masa da ya kawai fada masa domin ta san koman daren dadewa dole abin da ke boye ya fito fili.

Kallon Habeeba yayi wacce take takure waje daya kamar wacce ake kokarin cire mata wani abu daga jiki ta hada gwuiwa da kai sai sakin numfashi take yi kadan-kadai

"Uhmm...".

Sai kuma yayi shiru yana duban Malam Bello ya ma rasa da mai zai fara wani tunani ya fado masa zuciya lokaci guda da sauri ya dubi Nurses ya ba su Umarni cikin yanayi na amfani da ido a take suka gane abin da yake nufi da sauri suka fice daga cikin dakin.

Malam Bello ya dubi Likita izuwa lokaci. Zargi da kokwanto akan sa ya fara samun mazauni sosai a zuciyarsa.

"ina ga kawai gida zaka ku tafi da ita tunda ta haihu lafiya...sai dai in ko wata matsalar ta faru sai ka dawo da ita".

Tunda ya fara magana Malam Bello ke yi masa wani irin kallo mai dauke da TUHUMA hakan ya sanya jikin sa sanyi domin ya lura sam bai abince da batun sa ba.

Juyawa yayi da sauri ya fice daga cikin dakin ya barshi tsaye shanye da baki hannunsa ruke da É—an jaririn da izuwa lokacin ya fara kuka mai sauti sosai.

kallon Habeeba yayi har yanzu dai tana nan yarda take isa yayi gareta yana mai zama kusa da ita.

"HABEEBA".

ya kira sunanta cikin wata irin murya mai taushi.

ba ta dago ba, balle ya saka ran zata dago idanuwanta har ta sauke su akan sa, ko motsi ba ta yi ba, illa sautin ajje numfashi da take yi.

Sake kiran sunan nata yayi a karo na biyu nan ma bata dago ba balle kuma ya sa ran zatayi magana.

Tsayin lokaci suka dauka cikin haka shikuwa jaririn sai zunduma ihu yake yi sai faman jijjigashi yake yi amma ba alamun zai daina kukan mikewa yayi tsaye yana zarya cikin dakin yana duban Habeeba gabansa na kara tsinkewa da lamarin nata musamman da ya ga duk kukan da jaririn yake yi ko motsi bata yi ba.

Nurses ne suka shigo ba tare da sunyi masa magana ba suka kama hannun Habeeba suka fice da ita yana mai bin su da kallo kamar wani sauna abubuwa da yawa sun daure masa kai ya rasa a ciki wanne ya kamata ace yayi tunani akai da ya dauko zaren tufka tunanin nasa sai ya warware haka ya cigaba da zarya domin rashin abin yi kusan mintina biyar yana cikin wannan yanayi sai ga likita ya shigo yana duban sa.

"An kammala komai ka zo ku tafi don Allah ka kula da ita sosai domin ba karfin jiki gareta ba haihuwar ta bata wahala matuka kai kan ka sheda ne don haka a kula mun yi mata duk wani bincike da ya kamata, zamu hadaka da ma'aikaciyarmu daya domin akwai abin da muke bukata ta kula dashi".

tunda ya fara magana yake gyaÉ—a kai cikin amincewa amma ba har zuci ba kawai rashin abin yi yayi ya bige da amsa maganar da ba yarda yayi da ita ba.

Duk halin da yake ciki Likita na lura da shi haka ya ja shi suka fice daga daki har zuwa inda motar da aka saka Habeeba tana zaune a takure kallo kawai ya bita da shi yana gyaÉ—a kai cikin rashin taka maimai in da zai ajje tunanin da yake yi akan ta.

gaban motar ya shiga rungume da jaririn can baya kuma Habeeba ce da Nurses zaune gefen ta sai direban da zai ja su.

Sosai da sosai likita ke tausayin su a zuciyarsa sai faman gyaÉ—a kai yake yi har ya ga tashin su suka bar harabar asibitin...
Post a Comment (0)