UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA.
BABI NA HUDU
Kamar wacce aka watso haka ta fado cikin gidan, kallo daya za kayi mata kayi tunani rainon dawanau ce gabadaya yana yin jikinta ba shi da maraba da wacce aka durbuɗe cikin jar kasa ana cakudawa har sai da aka ga ta canza launi aka sake ta.
"Ahayye Yaro Ahayye Yaro,
A ƙyawu wata tafi wata a taku koni nafi".
Waƙar da take ta faman yi kenan da tayi tafiya daya biyu za ta tsaya tana girgiza kugu gami da tafa hannu a haka har ta isa kofar daya daga cikin dakunan gidan ba sallama ta bankaɗe labule ta faɗa.
Goggo Marka dake zaune tana faman ƙadin zare zumbur tayi tana shirin arcewa don ba karamar tsoro taji ba wani irin kallo ta watsa mata bayan ta ga wacece.
"ke kam an yi 'yar wofi wallahi ai wannan sai ki tsinkar min da gaba".
turo baki tayi gama tana mai galla mata harara.
"Uhmm nikam Goggo ki daina ce mani 'yar wofi".
"ke dalla jaye ki bani waje yar banzar 'ya mara hankali".
"nikam ba 'yar banza bace".
ta fadi tana mai yatsine fuska.
Juyawa tayi zata fice daga cikin dakin da sauri Goggo Marka ta dakatar da ita ta hanyar cewa,
"haba 'yar gidana ba ma haka dake, ina kuma zaki je?".
ko sauraron ta bata yi ba ta kara azama wajan ficewa daga cikin dakin da sauri ta mike ta riko hannunsa cikin karya murya.
"haba hafsatutuna yar gidan Mati da Abulle jikanyar Goggo Marka yar gaban goshin Danliti kar kiyi fushi mana".
Da alamun kirarin da akayi mata ya yi mata dadi shagwaɓe fuska tayi.
"Nikam in har kina zagina zan bar zuwan gidan ki ke kenan kullum zagin mutum".
"yi hakuri na daina, yo ai kece da turawa mutum haushi ba ki iya abin hankali ba amma dai yi hakuri zo mu zauna in ji abin da ke faruwa".
ba musu ta koma cikin dakin ta zauna ta shiga jayo kayan kaɗin Goggo Marka tana kokarin batawa da sauri ta buge mata hannu.
"nifa tsiya ta dake kenan ba kya gani ki kyale sai kin taba".
harara ta galla mata.
"kwarankwatsi zan daina zuwa gidan ki ke abu kadan sai ki daki mutum ko ki zage shi".
Hafsatu jikan Goggo Marka ce ba ta ji sosai da sosai rashin jinta ya wuce inda kake tsammani kullum cikin kawo wa uwarta korafi ake yi duka kuwa kullum cikin shan sa take amma ba abin da yake sauya zani ba wanda bai santa ba cikin kauyen nan iyaye da yawa ba sa son suka ga 'ya'yansu da ita domin rashin jin ta da kangarewrta sau da dama in tayi laifi bata zaman gida domin tasan halin uwarta jibgarta take yi kamar Allah ne ya aiko ta shiyasa da tayi laifi sai ta kwaso jiki tayo gidan Goggi Marka wacce ita ce bata ganin laifinta ko fada ta tsokano in dai ta zo wajan ta sai dai ta balbale wanda ta tona da masifa da zagi a wajan Goggo Marka ta samu daurin gindi take tsula tsiyar ta yarda take so sai dai kuma wani abu dake faruwa tsakaninsu duk son da Goggo Marka take yi mata bai hana a dinga jin kan su ba kullum in har ta zo gidan ba ta barin sa ba suyi fada ba Goggo Marka bata da hakuri sam kamar zawo ita kuma Hafsatu ba ta ji kamar 'yar Allah bani.
Mikewa Hafsatu tayi tana kokarin ficewa daga cikin dakin da sauri ta ce da ita.
"ina kuma za ki je?".
Cikin rashin baiwa maganarta muhimmanci tace.
"aƙwai zafi yasin dakin ki sosai ba zan iya zama ba, bari na zauna waje".
ba ta tsaya jin abin da zata ce da ita ba, ta bankaɗe labulan ta fice nan kofar dakin ta samu kujera yar tsugunno ta zauna ta shiga sakin yan waƙoƙin ta na shirme a zaunan ma rawa take yi.
Mariya dake kunshe cikin daki cikin wani irin yanayi na rashin tsammani komai na rayuwa domin ta gama yankewa kanta ta rabu da uwarta kenan tunanin ta sai wansafo mata abin da yake wakana da uwarta yake yi aceqar ai ta jima da matuwa gawarta kawai za a kawo gida lokaci-lokaci hawaye da suka zama abokan zamanta a wannan lokaci sai faman zubowa suke amma ko ta kan su ba ta bi don ta tabbata ko dauke su tayi ba abin da zai ragu daga tashin hankali da take ciki saboda komai na duniyarta ya kwance mata.
juyi take yi lokaci lokaci abubuqa sai faman kara yawa suke na tunanin zuci masu tayar hankali.
kamar wacce aka tsikara haka ta mike zumbur cikin taimakon jarumtar zuci jiki kuma a sake ta miki sai faman tangaɗi take yi kamar wacce ta baje aka idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kamar wacce akayi wa surace da barkonon tsohuwa sannu a hankali ta fara jan kafar ta har zuwa kofar dakin ta dage labulan ta fito ba ta lura da Hafsatu dake zaune ba can gefe guda ta shiga kokarin yin waje motsinta ne ya sanya Hafsatu dagowa daga abin da take yi ganin Mariya ya sanyata jan jaki domin ba shiri suke yi ba sam! Jininsu bai haduba.
sarai ta ji tsakin da aka ja amma ba ta tsaya daga tafiyar da take yi ba domin tashin hankalin da take ciki ya zarce ta tsaya neman ba'asi ko da bugun ta kuwa akayi a daidai soron gidan su ta tsinkayi tsayuwar Napep cikin wani irin karfi da bata san tana dashi ba ta kwasa yi waje a guje adaidai lokacin Mai Napep din ya tsaya turus! tayi ta tsaya ba tare da ta isa wajan da suke ba idanuwanta kuriii kan na mahaifiyarta abubuwa ne suka shiga yi mata shawagi akai gani take kamar ba gaske ba gani take kamar mafarki ne yake kokarin yaudararta.
ba ta san lokacin da Malam bello ya fito ba har ya biya mai Napep kudin sa Ya dubi Nurses.
"zaki kamo ta ku fito ko sai na taimaka muku".
"barshi kawai shiga da jaririn cikin gida tukunna".
Habeeba ya kalla har yanzu tana nan yarda take ba abun abin da ya canza domin tunda suka taho maganar duniya yayi mata amma ko tari bai ji tayi ba girgiza kai yayi gami da daukar hanyar cikin gidan Mariya da tajima cikin tunani ba ta san lokacin da ya iso ba ya dafa kafaɗarta firgigit tayi tana mai baza idanuwa kamar wacce zata arce kallon mahaifinta tayi da abin da ke hannunsa kanta taji yana juyawa gani takeyi kamar ba gaske gani take yi lamarin kamar ba faruwa yayi sai da taji ya ambaci sunanta tare da girgizata sannan ta tabbatar da abin da take zargi ta shiga duban jaririn ta na kallon mahaifinta murmudhi take ajjewa wanda bata san ya akayi ta samu damar yin sa ga ruwan hawaye sai kwaranyo mata suke.
Shima murmushin yayi mata wanda shi da ka kalle nashi bai kai zuci ba iyakarsa fatar baki.
"jeki ga Umman taki can".
ba ta tsaya tanka masa ba tayi hanzarin barin wajansa ta nufi Napep in da ta hangi Nurse na kokarin fito da ita shi kuma ya fada cikin gidan.
tun kafin ta isa gabanta ya yi wani irin bugu lokaci guda taji wani irin yanayi ya ziyarce ta zuciyarta na sanar da ita an samu matsala, matsala babba.
da sauri ta isa gaban Nurse tana kallon ta cikin wani irin yanayi kamar mai son karin bayani kallon Ummanta tayi wacce ta zama tamkar rakumi da akala ba wani kuzari sam! a gareta sai yarda Nurse tayi da ita.
"NA SHIGA UKU!".
Mariya ta fadi gami da riko Ummanta kallonta sosai Nurse tai jin abin da ta fadi girigaza kai tyi cikin yanayi na tausayi a haka suka rungumi Umma sukayi cikin gida da ita wacce a wannan lokacin sam bata san a ina take ba duniya ce ko lahira haka suka isa cikin gidan a lokacin Malam Bello ya fito daga cikin dakin ya na musu nuni da dakin ta ciki suka shigar da ita
Duk abin da ake yi Hafsatu tana nan zaune shanye da baki mamaki ne ya cika ta sosai ganin an shigo da Habeeba ya sanya ta saurin mikewa ta fada dakin Goggo Marka tana kiran ta.
"Goggo zo ki ga Umman Mariya ta haihu".
dubanta ta shiga yi da mamaki don ita sam ta mance da cewa Habeeba na nakuɗa har sun ta fi asibiti cikin hanzari ta mike tana duban Hafsatu cikin murya kasa-kasa.
" wa ya ce miki ta haihu?".
"yanzu naga sun shigo Malam rike da jinjiniya sai kuma wata mata ringome da Umman Mariya...".
kuri tayi mata da idanu kamar mai son gano wani abu ita ma Hafsatun kallon ta tashiga yi cikin rashin abin yi
kwankwasa kofar da akayi ne duk ya sanya su zabura Goggo Marka ta kalli kofarta jin muryar Malam Bello wani takaici ya turnuke ta ba shiri ta saki hannun Hafsatu kamar bata san abin da ke faruwa ba ta bankaɗe labulan tana kokarin tura ashar harara ta saki gami da jan guntun tsaki juyar da kan ta tayi cikin dakin cikin kunkuni.
"gaskiya na shiha hakki wallahi, sai azo ai ta dannawa mutum sallama duk a firgita shi sai mutum yayu zaton mutuwa ce ta kawo farmaki".
kasa-kasa tayi maganar amma sarai ya ji abin da take cewa ransa kuma ya sosi da maganar sai dai ya ki nuna hakan a fuska illa girgiza kai da yayi ya shiga kokarin yin magana.
"kiyi hakuri Goggo, dama zuwa nayi na sanar dake Habeeba ta haih...".
dariyar da Hafsatu ta saki ne ya sanya shi kasa karasa maganar sa domin bai yi zaton tana cikin dakin ba sam!
ita ma Goggo Murmushi ta shiga saki, sai ka rantse na farinciki ne amma ina! ba haka bane duban sa tayi tun daga sama har kasa baki a kwaɓe.
"Ikon Allah. ashe shiyasa na ga sai faman ɓarin jiki ka ke yi kamar wanda ya ga sabuwar Amarya".
Gyaɗa kai ya shiga yi jin maganganun da take fadi ya tabbata ba har zuci ba kawai magana ce a fakaice take dankara masa.
"Uhmm shi ne dama na zo na sanar dake...".
bai dire ba, tayi saurin caɓewa.
"Gaskiya kam!".
Ta sauke guntuwar maganarta ta da dubansa tana mai sakar masa yaƙe.
Shiru yayi yana ganin ikon Allah ran sa yayi matukar ɓaci musamman da ya lura dariyar da Hafsatu ke yi ta gayya ce da raini ita kuma Goggo ta hanashi sauke maganar da ya dauko nisawa yayi cikin haushi.
"ba wani babba don Allah Goggi ki zo ki yi wani abu".
"...haka fa na manta ashe watan tashin asuba na da wankar jego ya kama Hafsatu zo muje zaman mursu".
ta fadi tana mai duban Hafsatu da take ta faman dariya
Baki ciki iyaka Malam Bello ya shaka ji yake kamar ya fada cikin dakin ya shago Hafsatu ya jibga ko ya rage jin haushi amma ba damar haka don ya tabbata in har ya dake ta yau sai kowa ya ji a gari ga abin da yayi cikin rashin abin yi ya juya ya bar kofar dakin yana mai cizon laɓɓa.
Isar sa cikin dakin ya tadda Nurse ta gyara ko ita da taimakon Mariya wacce natsuwarta rabi da kwata ba ta tare da ita tana ga Ummanta wacce take girke waje guda ba Uhmm ba uhm-uhmm.
"ya kamata ace anyi wani abu izuwa wannan lokaci".
Cikin rashin fahimta ya dubi Nurse yaka faman gyaɗa kai.
"kamar me kenan?".
ya fadi cikin raunin murya da rashin abin yi domin ya tabbata kayan bukata ake nema wanda ya tabbata ba shi da karfin yin su don ko wuka za a daura masa a makoshi baya magani kudin da za ace za ayi bukatu na azo a gani.
"ya kamata ace izuwa yanzu an yiwa jiririn nan wanka itama.uwar kanta ta gyara jikin ta sannan kuma da abubuwan da za ta sanyawa cikinta".
tun da ta dora zancenta yake faman binta da kallo yana gyaɗa kai cikin rashin abin yi ita kan ta Mariya kallon Nurse take yi domin abin da taji tana fadi to ta tabbata mahaifinta bai da wannan halin a yanzu haka ita sheda ce.
kamar wacce aka tsikara ta mike tayi tsakar gida gindin murhu ita isa ta janyo guntayen itace da karare ta hada ta tada wuta ganin wutar ta kama ta mike da sauri ta dauko katuwar tukunya wacce rabon da ta ga wuta anjima daurayeta tayi taje ta daura kan murhun sannan ta shiga debo ruwa tana zubawa a hankali har ta cika ta fam ta sanya murfi ta rufe tana mai sakin ajiyar zuciya tana bin tukunyar da kallo abubuwa da yawa suna yi mata yawo cikin kwakwalwa tausayin iyayenta sai kara raunata ta yake yi ji take yi kamar ta fice domin samo abin bukata sai dai tana tunanin in ta fita ina zata je wajan wa zata ba ta sani ba ita ba namiji bane balle taje tayi aikin karfi domin sabun abin taimakawa iyaye ita 'ya mace ce kuma rauni gareta tana tsoron abin da zai kawo wa rayuwarta farmaki hawaye suka zubo mata hannu ta saka ta dauke su ta sake duban murhun wutar taga tana kokarin mutuwa da sauri ta durkushe tana hurawa da baki amma kamar kara kashe wutar take da sauri ta mike ta nemo wani yagalgalallan mahuci ta shiga fifitawa amma ina ba alamun wuta zata ci domin itacen yayi karanci sosai da sosai da sauru ta mike tayi waje yaye-yaye na ledoji da duk abin da ta san zai ci wuta tayo ta dawo ta shiga cusawa cikin murhun hayaki ya turnuke sosai nan da nan ta shiga tari idanuwanta suka kara rinewa zuwa jajaye suna zubda hawaye amma hakan bai hana ta kokarin tayar da wutar ba dakyar da gumin goshi wutar ta tashi bayan ta gama sharafin ta na hayaki ganin wuta ta kama ganga-ganga ya sanya yin zaman dirshan a wajan ta zabga tagumi tana kallon ikon Allah.
Abubuwa take tunawa marasa dadi a rayuwar nan tun da ta fadi duniya ta tsinci iyayenta cikin wannan hali na rashin dadi tana bukatar fidda su daga cikin ƘANGIN RAYUWA sai dai ta rasa ta ina zata fara tana so ta samowa iyayenta YANCI amma ta rasa mai ya dace tayi ita yarinya ce amma kuma ta fara fuskantar matsalar rayuwa tun kafin ta kai haka in ana haddace matsalolin rayuwa ya kamata ace ta haddace su akana ta rasa tana ina zata fara kokarin tunkaran rayuwar nan domin samo wa iyayenta farin ciki