UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA.
BABI NA BIYAR
"Sannu da kokari Mariya, Allah ya yi miki Albarka".
Kamar daga sama ta jiyo sautin mahaifin nata ya na furta kalaman.
da sauri ta shiga goge fuskarta tana faman ajje numfashi da kyar sai da tayi kokarin samowa kanta natsuwa sannan ta taso tana mai dubansa tana faman sakin yaƙe kamar wacce aka cewa in bata yi ba ranta za a dauka.
"bari na fita naga yarda Allah zai yi damu".
ya sake magantuwa idanuwansa fes akanta yana faman gyaÉ—a kai cikin yanayi na tauyasawa dukkan nin su.
Sai da ta ajje numfashi mai rauni sannan ta nisa.
"Allah ya kiyaye hanya".
tana fadin haka ta shiga kokarin gyara wutar da ta hura domin ba ta son wata magana ta sake shiga tsakaninsu don kukanta a wuya yake in kuwa ta fiye magana komai zai iya faruwa.
tana jin ta kusan sa har ya fice sannan ta saki ajiyar zuciya cikin ta cikin hali na sanyi ta ja shi domin kowa wajan mahaifiyarta tunanunnuka birjin cikin ranta.
"Ahhhh ashe dai ba haihuwar guzuma akayi ba".
Goggo Marka da ke tsaye tun dazu tana kare musu kallo da yatsine yatsinan fuska ta fadi haka lokacin da Mariya ke kokarin shiga daki.
ba ta fahimci in da maganar ta dosa ba amma dai ta sakawa ranta cin fuska akayi mata gyaÉ—a kai kawai tayi ta kalleta na yan sakanni ta dauke kanta.
"munahika ni kike kallo haka, mara kunya 'yar masu baki hali kalle ni da kyau ba dai zagina zaki yi ba don wallahi kika zage sai na dake ki dukan shan gishiri".
da sauri ta fada cikin dakin don ba za iya jurar sauraron maganganun Goggo Marka ba ranta yayi matukar baci amma ba ta bari hakan yayi tasiri a fuskarta ba ta bar wa zuciyarta bakinta dauke da Sallama ta shiga dakin har yanzu Habeeba na nan yarda take can gefe kuma Nurses ringume da jariri dake ta faman rusar kuka tausayi da jiƙan duk ya gama jikin ta jingina tayi da bango ta na ajje numfashi idanuwanta kan mahaifiyarta abubuwa da yawa sunayi mata yawo akai amma ta rasa matsayar da za ta ajje tunaninta komai ya cakuɗe mata ya cinkushe mata ta kasa gane lamarin dake faruwa gabanta na faduwa sosai da sosai wanda ta hakikance akwai abin rashin natsuwa da yake shawagi cikin duniyarsu a yanzu.
Duban ta take yi cikin rashim abin yi komai ya kwance mata laɓɓanta sai rawa suke yi alamun ta na son cewa wani abu amma ta kasa hakan hawaye sai ambaliya sukeyi zuciyarta na tukuki ba abin da ke shawagi a kanta illa rayuwar da take ganin tana tunkaro su wacce ta hakikance ba tabbanci kayan kwanciyar hankali acikin ta sai wani nufi na Allah.
"gafaran ku dai masu jego".
Muryar Goggo Marka ta karaɗe cikin dakin ba wanda ya dubeta tsakaninsu har ta gama shan sharafin ta sannan ta kaea tsakar dakin ta samu waje ta ajje kugunta tana mai duban Habeeba wacce take rakuɓe waje guda ta juya wajan Nurses dake ta faman jijjiga jaririn ta shiga yashe baki kamar gaske.
"kai Masha Allah mikon min shi nagan shi".
ta fadi tana mai turawa Nurses hannunta da ta bata jaririn ba musu ta mika mata ita ma tana faman yashe baki amma ba kai zuci ba tunani ne ya ke mata shawagi cikin kai akan Goggo Marka don bata yi tsammanin akwai wata mace a gidan ba tunaninta kawai su Mariya ne gyaÉ—a kai tayi gami da ajje tunanin gefe ta shiga kokarin mikewa tana mai duban Habeeba .
"ni bari na koma bakin aiki tunda Baaba ta iso ko".
ta fadi kamar mai son taji wata magana daga wajan Habeeba amma kamar a ajje dutse ko motsi sai Goggo Marka ce ta magantu.
"Ahhh ya haka kuma na dauka kece mai zaman wanka".
Cikin rashin fahimta Nurses ta shiga dubanta tana mai gyada kai tunaninta na dazu yana kokarin rugujewa akan Goggo Marka a tunaninta a gidan take zaune ashe ba haka bane barka ta zo yi gyaÉ—a kai ta sake yi sannan ta nisa.
"A,a bani ba ce ni ma'aikaciyar asibiti ce".
Kau da kai tayi ba tare da ta ce komai ba hakan da Nurse ta gani ya sanya ta isa kusa da Habeeba ta dafa kafadarta tana mai faman rausayar da kai tausayin ta sai kara tsargar mata yake tsayin mintina daya ta dauka sannan ta fara kokarin barin dakin bakin ta na yi musu fatan alheri.
Bayan fitar Nurses Goggo Marka ta numfasa tana mai duban Habeeba domin zuciyarta sai faman tsegumi take mata akan yanayin da ta ganta a ciki.
"na ganta cikin wani yanayi, me ke faruwa?".
ta fadi tana mai kallon Mariya itama Mariyar ita take kallo cikin rashin abin cewa numfashi take ajje a hankali zuciyarta na faman harbawa kamar zata faso kirji ta fito.
"dake fa nake kika yi mani banza, komai halin kurmantaka kuke ne yau ke da uwar taki".
"...uhmm nima ban sani ba".
Cikin ci da zuci ta furta haka tana faman jingine kanta da bangon dakin domin wani iri take ji duniyarta na yi mata sai shawagi kanta ke yi kamar wata waina cikin tadda.
"kamar ya baki sani ba, nifa munafurci ne bana so kin ji ko".
zuciyarta ta fara gajiya da lamarin Goggo Marka matuka. ji take yi muryarta nayi mata shawagi kamar zata tarwatsa mata kwanya cikin gajiya ta mike ta fice daga cikin dakin.
Hakan da Goggo Marka ta gani ya sanya ta sakin tsaki gami da kwaɓa.
"kin shiga uku da bakin halin ki".
ta juya tana kallon Habeeba sosai da sosai take kallon ta tana son gano wani abu dake boye amma har tagama hangenta bata hango komai ba sai halin shiri da ta tsinta wanda ta rasa dalilinsa gyaÉ—a kai tayi gami da ajje jaririn kusa da Habeeba ta mike tana gyara daurin zaninta sai da ta karewa dakin kallo sannan ta fice.
Mariya durkushe bakin murhu sai faman kokari take domin ganin ruwanda ta daura yayi zafi ko da bai tafasa ba ta san hakan yafi babu haka ta cigaba da gyara wutar har zuwa wani lokaci cikin Ikon Allah ruwan ya tausa sosai da sosai da sauri ta mike ta nufi dakin Goggo Marka gaban na bugu domin ta rigaya tasan da kyar ta samu komai a dadin rai a wajan ta.
"ruwan ya tafasa".
Dakyar ta furta hakan yanayi na rashin abin da za taji daga bakin Goggo Marka ilai kuwa magana ta caɓamata.
"ni meye nawa a ciki, na dauka tun da kika iya dafa ruwan wanka jego na ai za ki iya wankan ma".
maganar tayi mata kuna a rai amma ba nuna haka a zahiri ba sai ta shiga sakin murmushin yaƙe tana faman gyaɗa kai.
"Uhmm Goggo kenan ba wai nayi gaban kaina ba ne kawai gani nayi hakan ma rage wani aiki ne...Uhmm ni dai rokona ki taimaka kiyi mata wankan".
ta karashe cikin taushin murya mai cike da rarrashi.
dubanta take yi sosai tana jin maganganun da take fadi ta juyar da kallon ta zuwa ga Hafsatu dake yashe bisa gado tana faman kallon su.
"Amma dai...".
"...Don Allah Goggo ki taimaka".
Mariya tayi saurin tare ta tana mai hada hannayenta waje guda alamun roko idanuwanta tsaf! akan ta tana faman juya su kamar mai son fashewa da kuka.
Ba wanda ya tsake tsinkawa a tsakaninsu tsayin mitina uku sannan Goggo Marka ta mike ta fice daga cikin dakin Mariya na biye da ita har wajan murhun suka isa ta duba ruwan sai faman tafsa yake yi ta juya ta dubi Mariya.
"ni dai ba zan iya kwashe wannan tafasasshen ruwan ba tsakani har ga Allah don ba zan babbaka kaina ba".
GyaÉ—a kai Mariya tayi kafin tayi nishi.
"bari in kwashe ni zan iya".
Ta fadi cikin sanyin murya mai dauke da rawa sosai cikin karfin zuwa tayi wajan dakin Ummanta wani babban daro ta dauko wanda suke wanki dashi ta girke gindin murhun sannan ta bude tukunyar ta saka kofin da ta dauko ta shi ga kwashewa tana zubawa cikin dauro a hankali duk da ruwan na fallatsar mata a jiki amma hakan bai hana daurewa ba ta cigaba da abin da take yi sai da ta ga ta zuba sosai kwatankwancin yarda zata iya dauka sannan ta kinkima tayi hanyar bandakin su wandake zagaye da langa-langa ta ajje ta fito nan ta cigaba da kwashe ruwan a wani botiki tana kaiwa tana zubawa har sai da ta cika sannan ta tsagaita ta dubi Goggo Marka da ke tsaye tun dazu tana kallon abin da take yi.
"na kwashe".
"to yanzu ya za ayi kenan maganar ganyen wanka".
Shiru Mariya tayi shaf ta mance da ganyen wanka da ake amfani dashi ko dayake ba abin mamaki bane rashin sanin haka gareta tun da ba sanin yarda ake yi tayi ba gyaÉ—a kai tayi cikin rashin abin yi.
"Goggo kawai ayi mata ako da tsumma ne domin naji ana cewa nayi dashi tun da lokaci ya kure in za ayi mata na yamma sai a samo ganyen ko".
Yatsine fuska tayi gami da kau da kai.
"a ina kika taba jin anyi haka".
Cikin sauri ta amsa mata.
"a rediyo naji ana hira in mace ta haihu za ta iya wanka da tawul ba dole sai ganye ba".
sakin baki tayi tana kallon ta cikin mamaki.
"iyee Al'adun yahudawa kenan kike nufi za mu koma yi to ni dai ban san wannan falsafar taki ba ni dai A AL'ADATA ta hausa fulani da ganyen dogon yaro nasan ana wankan jego da wasu kuma dangin nau'ikan ganyayyaki domin akwai wani sirri da suke dauke dashi ni ban san wani ayi wankan jego da tsumma ko tawul ba...".
"Don Allah Goggo ki taimaka".
Mariya ta tare ta ganin tana kokarin cinye mata lokaci da suke dashi har ruwan wanka ya huce.
"ni fa ba zaki sakani yin al'adun yahudu ba in har ba za a samo ganyen wanka ba to ba dani ba".
tana gama fadin haka ta fara kokarin shigewa dakin ta da sauri Mariya ta shagabanta ta shigayi mata magiya da rantsuwar cewa in tayi mata wannan ba zata sake yi mata ba ba tare da ganye ba magiya sosai tayi mata sannan ta yarda.
Mariya da kanta ta shiga dakinsu ta riko Ummanta domin ita Goggo ta ce sam ba zata taba jikinta ba haka da kyar da gumi ta fiddo ta daga cikin dakin sai faman nishi take yi domin gabadaya jikin Ummanta a sake yake ba abin da take yi sai yarda akayi da ita a haka har ta isa bandakin da ita kan wani dandamalin dutse dake tsakar bandakin da suke zama kan sa suna wanka.
Ficewa tayi ta ba su waje ta koma can kofar dakin su ta zauna tare da zabga tagumi abubuwa sai mata shawagi suke mara dadi da armashi kamar wacce aka tsikara ta mike da sauri tayi cikin daki can in da jaririn ke kwance ta isa ta dauke shi gami da rungumeshi tana jin wani irin a zuciyarta tausayin sa take ji da yanayin da ya samu duniyar aciki ta tabbata yarda take rayuwa haka in shi ma ya tashi zai yi sai dai ba za ta so haka ba za ta so ace rayuwarsa ta fice daban da tata da take yi zata so ace bai fuskanci wani matsi ko ukuba ta rayuwa ba za ta so ace ya tashi cikin kwanciyar hankali da muradan farinciki cikin duniyarsa sai dai ba tabbacin haka zata kasance sai wani iko na Allah domin za ta iya cewa yanzu shigo ya ga rayuwar duniyarsa tun daga fadowarsa ya fara ganin rikicin duniya.
Nisawa tayi gami da mai dashi ta kwantar ta fice daga cikin dakin wani karamin bahon wanka ta dauko ta zubo ruwan zafi ta sirka yarda take tunanin ba zai cutar dashi ba ko ya haifar mata da wata matsala dakin ta koma ta ajje ruwan sannan ta dauko shi zuciyar ta na faman buguwa tana tsoron abin da zai je ya dawo domin har kasar ruhinta tsoro ne fal ta yarda zatayi wa jariri wanka abin da bata san ya ake yi ba amma dai zata gwada ta gani domin ba zata iya barin kanin nata cikin wannan yanayi ba an haifeshi kusan a wanni amma ko ruwa vai gani ba.
Tsunbulashi tayi cikin ruwan cikin yanayi na faduwar gaba aiko sai ya saki kuka lokaci guda da sauri ta zare shi jikin ta na faman kyarma ta shiga kallonsa idanuwansa bude sai faman lumshe su yake yi kamar mai jin barci sake saka shi tayi sai dai a wannan karon bai yi kukan ba illa ajiyar zuciya da yayi hakan da ta gani ya bata kwarin gwuiwa fara wanke masa jiki a hankali haka ta cigaba da yi ko sabulu babu sai da ta wanke masa jiki sosai da sosai har sai da taji ruwan ya fara sanyi sannan ta zare shi daga ciki cikin kayanta ta dauko wani zani mai dama-dama ta sakashi aciki ta nannade.
Kiran ta taji Goggo Marka nayi da sauri ta mike rike da jinjirin ta yi waje tsaye ta tadda ita tayi jage jage da ruwa.
"ki je ki fito da ita".
nar-nar tayi da ido kamar mai son fashewa da kuka.
"don Allah Goggo ki taimaka ki fito da ita wallahi ban zan iya ba dazu da kyar na samu na fito da ita kuma kin ga yaro ne a hannu na yanzu na gama masa wank...".
ai ba ta dire zancen nata ba taji ta dauki sallallami tana tafa hannu kamar wacce ta ga mugun abu.
"Mariya wanka fa kika ce ke yanzu har kin san yarda za kiyi wa jariri wanka".
nan da nan jikin ta ya fara rawa hawaye suka fara sankoma mata dama abin da take gudu kenan abin da take tsoron faruwarsa kenan Allah yasa ba wani abu ne zai same shi ba Allah ba ganganci tayi ba cikin rawar baki ta fara magana.
"Wallahi Allah ban yi...".
cak! ta tsaya da zancen ta ganin Mahaifinta tsaye bakin kofa yana kallon ta nan da nan faduwar gabanta ya karu musamman da taga ya kafe da idanuwansa