UKU-BALA'I 06



UKU BALA'I
 
 NA
KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.




BABI NA SHIDA

Da sauri ta dauke kanta daga barin kallonsa tana jin yarda sautin bugun kirjinta ke kara sauri cikin wani irin tashin hankali wanda sam ba tayi tsammani ba rintse idanu tayi iyakar karfin da taji a jikinta tana faman ambaton Allah komai nata take jin yana kwancewa komai take ji na duniyarta yana juya mata ji take kamar ba kan kafafunta take ba ji take kamar walagigi ake yi da ita jaririn da take daure a jikinta ji take kamar zai kwance ya fadi kasa da sauri cikin rashin abin yi ta kai hannunta zuwa saitin goyan ta rike sosai rikon da ko babban mutum akai wa shi sai yaji kamar za a dauke masa fata haka ta rike zanin goyan tana kara kankame jikinta waje daya ba abin da take jira sai hukuncin da take hangowa cikin idanun mahaifinta take zaton zai yanke akanta.

A sukwane ya iso gareta ba tare da yayi magana ba ya kama kokarin kwance goyon nata ba karamar faduwa gabanta ya kara yi ba har zuwa lokacin idanunta a runtse suke kawai jira take yi taji duka ko ta ina don tuni ta yanke tsammani akan yarda ta ga mahaifinta ya nuna a fuskarsa na matsanancin bacin rai.

 "Mariya me ke faruwa ne?".

Kamar daga sama ta juyo sautin muryar mahaifinta na fadin haka wata irin ajiyar zuciya ta saki gami da buɗe idanuwanta gabadaya ta sauke su akan sa tana mai faman gyada kai bakin ta na motsi.

 "Uhmm dama kawai shine...".

Da sauri ya daga mata hannu lura da yayi yanayinta ya nuna a firgice take sai faman kucincina maganar ta ta take yi.

"tambayarki nayi ba wai cewa nayi ki tsaya kwan gaba kwan baya ba".

ya fadi yana mai karasa kwance goyon da tayi ya rungume yaron wanda a wannan lokaci barci ya fara tafiya dashi ya shiga dubansu ita da Goggo Marka wacce ta zuba musu ido tana nazarin inda za ta kullo zanar makircin ta.

"Bello wai 'yar nan daga cewa bayi naje nayi wa uwarta wanka na fito nayi wa wannan yaron kawai ba da baya ashe ta kandami ruwan sanyi tayi daki ta zunduma shi a ciki ina daga bayani na ya saki kara hakan ya sanya ni fitowa a guje ko da na iso ya shaki ruwa har ya fara sheɗewa".

Marka ta fadi cikin yanayi na dagaske ne abin da ta fadi har da dauko fuskar tausayi ta azawa kanta.

Sosai yake duban Mariya yana karantar yanayin da take ciki yana kuma nazarin maganar Marka akanta yanayin da ya ga ta nuna alamun tsoro da firgici har da yar kwalla ya tabbatar masa ba tabbas a maganar amma saboda kar ya rikitowa kansa kwandon fitina sai ya dubi Mariya yana mai tsuke fuska.
 
 "me kikayi kenan mai yasa baki yi abin da ta ce miki ke yanzu har kin kai matakin da zata ce karkiyi kiyi sannan kuma ina ke ina yiwa jariri wanka sabon haihuwa kuma da ruwan sanyi ina kika taba ganinka haka...".

caraf! Marka ta dauka.

"yo hankali gareta ba gwanda ta nuna wa duniya uwarta ta haihuwa ba ga wadanda ba su taba zama a gwuiwa da sunan naƙuda ba".

ta fadi ita ala dole gaskiya take fadi da neman bin da zai harzuka Bello ya jibgi Mariya.

Riko hannunta yayi a tunzure ya jata kiiiii! Sukayi cikin dakin zuwa lokacin ta gama yarjewa kanta babanta dukanta zai yi nan da nan ta fara zubar hawaye tana faman bashi hakuri har suka isa cikin dakin ganin ba kowa aciki da sauri ya dubi Mariya.

 "ina Umman taki take?".

"tana bandaki don Allah Baba..".

tun kafin ta ajje maganar ta ta yayi wuf! ya ajje yaron ya fice daga cikin dakin da hanzari cikin kiɗima ya isa banɗakin tana yashe kamar yarda Marka ta barta ko motsi kirki ba tayi ta hade jikinta waje guda ta takure kamar wacce ake kokarin rabata da wani abu nata gabansa ne yayi wani irin mugun bugu har sai da yaji kamar kirjinsa zai buɗe da hanzari ya isa gareta ya na faman ajje numfashi mai karfi ya shiga ambaton sunanta amma ina! ba alamun zata motsa balle ya saka rai zata kalle shi jikinsa na ɓari ya shiga kokari gyara mata zanin da ke jikinta ya miƙar da ita tsaye ya haɗeta da jikinsa wani irin rawa yaji jikinta sosai da sosai.

 Gabadaya ya hadata da jikinsa wani irin tausayinta yaji yake tsaga duk wani sassan jikinsa lokaci guda yaji kwalla na kokarin zubo masa zuciyarsa sai faman zillo take yi tana faman hasasho masa abin da ba ya so ace ya tabbata domin in har hakan ya tabbata yana cikin matsala matuka gaya wanda sam ba zai samu murmushi ya cigaba da wanzuwa a fuskarsa ba.

 Cikin wannan yanayin na rashin tabbas da kwanciyar hankali ya isa da Habeeba cikin dakinta ya ajje Mariya dake can gefe sai faman kallo take bin su dashi gaɓadaya ta rasa gane kan wannan lamari zuciyarta sai wassafo mata abubuwa take wanda ba ta tsammanin na dadin rai ne niswa tayi wasu guntayen hawaye suka surnano mata ta sanya bayan hannunta ta dauke su gami da jan hanci.

  "Baba don Allah mu koma Asibiti".

Abinda ta kokarta fadi kenan cikin muryarta mai rawa da kuka a cikinta.

Ba tare da ya juyo ya dubeta ba ya cigaba da gyarawa Habeeba jikinta kamar ba zai yi magana ba domin bai san abin da zai ce bs ko da yayi niyyar yin magana a hankali yake sauke ajiyar zuciya bayan ya kammala gyara mata jiki ya kwantar da ita.
 
 juyowa yayi ya fuskanci Mariya sosai sannan ya dubi Yaron da ke kwance can gefe yana barci amma kuma hannunsa na cikin bakinda yana ta faman tsotsa kamar zai cinye shi da sauri ya kau da kai domin abubuwan tausayawa ne ya suka caki kirjinsa da sauri ya mai da duban sa ga Mariya.

 "nima ina tunanin haka Mariya domin kuwa wannan lamarin ya kamata ace an yi duba a kansa...".

  "wai don Allah ba za ka bar maganar asibitin nan bane Bello wai ina tunaninka ya tafi ne ya kamata ka zauna kayi amfani da MIZANIN HANKALI wajan nazarin wannan lamarin kai yanzu ba abin ka gujewa komawa asibiti bane ka duba ta kalau kuka dauki Habeeba zuwa Asibiti amma ka dubi yarsa ta ko tunda kuka dawo ko tarin ta ban ji ba balle na saka ran naji tana cewa wani abu kai ba abin ka tsorata bane da komawa asibiti in har ka na biyewa Maganar Mariya to tabbas zaka kashe matarka da kan ka domin ita yarinya ce ba ta san abin da ya dace da wanda bai dace ba kawai in haukar ta ta yanko mata zance haka zata faɗeshi ba tare da ta duba shi ba".

 "Amma Goggo...".

Da sauri ta daga masa hannu alamar dakatarwa sa'anan ta daura da cewa cikin yanayi na bacin rai.

  "Shawara na baka in har ka ga za ka iya nikam ka ga tafiya ta".

tana gama fadin haka ta fice daga cikin dakin zuciyarta sai faman sheka dariya take yi son ranta.

Shikuwa Bello tunda ta saka kai ta fice daga cikin dakin duk yaji komai ya jagule masa shiru yayi yama nazarin maganarta tun yana tsaye har ya koma zaune ya zabga uban tagumi komai yake ji ya kwance masa tufkar da yake yi sai faman warwarewa take yi komai ya kwance masa lokaci-lokaci yake ajje numfashi idanuwanta na kan Habeeba wacce ke takure waje guda ya rasa a ina zai ajje wannan lamarin nata ya rasa me ke damunta likita yace masa lafiya ta haihu amma ya za ayi ace kuma magana ta gagareta yi a karan kanta me haka ke nufi ya kamata ace anyi duba a wannan lamarin sake ajje numfashi yayi ya shi tambayar kan sa abubuwa wanda ko wuka a makoshi zai gani ba shi da amsoshin su

 sun jima cikin wannan yanayi har dare ya fara shigowa ka fara kiraye kiranyen Sallaha hakan ne ya fargar dasu daga duniyar tunanin da suka lulaƙa da sauei Bello ya mike yana mai duban Habeeba wanda idon ta yake ƙyar sama ko ƙiftawa ba tayi hakan ya dan fadar masa da gaba da sauri ya isa gareta ya dafata gami sa girgizawa sai yaga ta saki ajiya zuciya gami da lumshe idanuwanta wasu hawaye ne suka surnano mata a kunci hakan yay matukar sanya gabansa faduwa da sauri ya zauna kusa da ita yana kokarin tallabo ta.

  "Sannu Habeeba me ke samun ki, fada mani don Allah".

yana magana bakin sa na rawa amma ita ba alamun za ta yi masa wata magana illa kafeshi da ido da tayi.

 "kiyi magana mana sanar dani abin da ke damun ki".

numfashi idanuwa tayi lokaci guda jikinta yayi wani irin fizga shi kansa Bello sai da jikinsa yayi rawa da sauri ya zabura yana mai faman jinjigata yana ambaton sunanta amma ba ta yi magana kuma ba ta buɗe idanunwata illa kirjinta dake bugawa kadan-kadan da sauri ya duba in da Mariya ke zaune amma bai ganta ba sam bai lura da ita kusa dashi tsaye ba idanuwanta na faman zubar hawaye

 "sai da nace a mai data Asibiti amma a kace ai magana ta akwai yarinta a cikinta wanda ni A KARAN KAINA na san maganata tana sahun da za ajerata a maganganun da za ayi amfani da su domin ceto Ummata".

Sosai yake dubanta yana kallon yarda hawaye ke safah da marwah akan fuskarta tausayinta yaji yana tsargar masa ko ina na jikinta yana ganin rashin dacewa da kuma kin yarda da yayi da maganar 'yarsa wacce ta cancani ace an dubata kuma an daurata a mizanin hankali amma bai yi haka ba har sai da ta budi maki ta nuna alamun kin yarda da kayi da ita.

  "Mariya ban ki ta taki ba amma ai abin lura nan shine kina jin abinda Goggo Marka ta fadi kan wannan lamarin kin ga ai bai dace ace anyi gangawar mai da ita Asibiti ba domin tun acan ya kamata ace sun sanar damu abinda ke faruwa amma suka ce damu ba komai".

tun da ya fara magana take dubansa cikin wani irin yanayi da yarda furucin nasa ke sauka wanda ta tabbata ba a son ran sa yake yin sa ba kawai FIN KARFI ake nuna masa wanda haka sam ba zai haifar musu da ɗa mai idanu ba.

nisawa tayi hawaye na kara samun mazauni a fuskar ta.

 "ceton rai daban yake a wajan dangin rai ko wani hali kake ciki in har kana da damar ceton wami rai ko ba makusancin ka ba zaka iya don Allah baba na rokeka mu mai da Umma Asibiti".

 "kiyi hakuri sa kukan haka nan za a mai da ita".

Girgiza kai kawai take yi domin ba ta ga alamun Eh da gaske za ayi hakan ba kawai magana ce akayi ta wacce sam ba alamun za ayi ta a aikace jinjina kai ta shiga yi tana faman sauke numfashi a hankali cikin jan jiki ta fice daga cikin dakin domin ta tabbata in har ta cigaba da tsayuwa cikin dakin komai zai iya faruwa da ita ba za ta iya cigaba da ganin mahaifiyarta cikin wannan hali ba.

Tana fita waje ta hango Goggo Marka zaune kofar dakinta sao faman kai lomar abincin takeyi bakinta wanda ta tabbata daga gidansu Hafsatu aka kawo mata shi ko kuma taje da kanta ta amso da sauri ta kau da kanta domin bata ga amfanin kallon nata ba illa ya kara mata wani takaicin a zucci.

  "wai har yanzun Habeeba ba tayi maganar ba?".

Kamar daga sama ta tsinkayo muryar Goggo Marka tana tambayarta wani haushi ne ya zo mata wuya domin ita dai ba ta ga amfanin wannan tambayar ba ya za ayi kana cikin gida tare da mutum amma kuma kake tambayar ya yake kai da ya kamata ace sai sai wani ya tambayeka gyada kai tayi kamar ba zata tanka ba amma sai kuma ta fara kokarin motsa baki domin amsa mata 'ta ce mi' ta ji wani bangare na zuciyarta tace da ita haka sai tayi gum da bakinta tashiga tsayuwa a kofar dakin domin ita dai ba ta san abin yi ba akan wannan lamarin da ta rasa dame zata fassara shi cikin duniyar rayuwarta

  "ai wuya makarantar kare ce duk wanda ya ki ji ba ya ki gani ba nidai iyakata ido kuma fadan da yafi karfin ka dadin kallo gareshi".

Goggo Marka ta sake fadi tana mai kai loman abinci bakinta takaici ya kume Mariya ji take kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu da wannan jirwayen gami da shaguɓe da ake antayo mata duban Goggo Marka tayi tana mai faman kada kai ba shiri ta juya ta koma cikin daki abu dai gashi nan ya zame mata goma da ashirin ta rasa ma ina zata dosa da wannan lamarin.

Haka suka rayu cikin wannan dare tsayin lokaci ko wanne zuciyarsa sam ba kayan jin dadi cikinta komai yayi musu kunci abubuwa maras dadi sai faman wuntsulowa suke yi cikin rayuwarsu cikin lokaci kankani ƙaddara ta juya akalar rayuwarsu zuwa wani fikire wanda ba su taba tsammani ba za su kai gareshi.

A daran Mariya tayi kuma matsananci domin kuwa yanayin da ta ga mahaifiyarta a ciki gabadaya susuta ta, ta rasa mai ke yi mata dadi cikin rayuwa bala'in take gani ya na tunkaro mata wanda take tsammani komai na rayuwarta zai iya raguzama mata shi duk wani kudiri da buri da ta daukar wa kanta cikin duniyar rayuwarta ta fara hango rashin tabbatuwarsa tana hango wata bahaguwar ƙaddara na kokarin tafiya da komai nata na jindadi tana kallon yarda ƙaddara ke kokarin sauya mata akalar yarintar ta wanda ta rasa hanyar da za tabi domin dawo da komai a cikin wannan dare.

Nishi take yi kamar mai kokarin haifo ɗa ta direshi a duniyar nan wani abu ne taji yana tokare mata kirji duk sa'ilin da ta ji Ummanta na fizga kamar wacce aka jonawa wuyar wuta take fizgarta.

 "Baba kun ki kamar uzuri ne wallahi uzuri na yana da matukar amfani lokaci tafiya yake yi kuma ba waiwayo mu zai yi ba na rokeka da mu nemi abin yi".


Magana take yi muryarta na kokarin bayyanar da kukan da take boyewa a zucci laɓɓanta sai faman rawa sukeyi ba ta jin tausayin kanta kamar yarda take tausayin dangin rai din nan gudawa biyo domin yalwar kwanciyar hankalinsu shi ne nata.

 "Mariya nayi kuskure da na sani tun waccan lokaci na dauki maganarki...".

Da sauri ta mike jikinta na rawa sosai ta isa gareshi.

 "wallahi yanzun ma lokaci bai kure ba na rantse maka da Allah Baba ka taimaka ka tashi mu tafi mu ceton ran da yake da abubuwan taimakawa sosai a rayuwarmu".

Ido sosai ya zuba mata yarda yake ganin tausayi da jin kai cikin idanuwan Mariya hakan ya kara narkar masa da zuciya cikin tausayinta yana kallon rashin hayyaci yarda yake da wainiya da ita amma karfin zuciya kawai da ikon Allah ke bata kwarin aiwatar da komai in ba don haka ba komai zai iya faruwa da ita.

 "mu bari gari ya waye Mariya dare yayi sosai".

Sosai Mariya ta kureshi da idanuwanta jikinta lokaci guda ya saki ta zube a kasa kamar wani kayan wanki da aka yasar hannu biyu duk ta daura bisa kanta kamar mai shirin kurma ihu amma hakan ya gagara safiyar da taji ya ambata yafi komai kawo mata tashin hankali cikin rayuwarta a wannan Daren ga take yi kamar KAFIN SAFIYA komai zai iya faruwa kundin ƙaddararta zai iya buɗe mata wani shafin wanda bata tsammani zata iya karance shi balle kuma ace hadda za tayi duban su ta shiga yi duk su biyun idanuwanta na faman hargitsewa kamar wacce ya tuntuli barasa ta kai ma karo hannu ta sauke daga saman kanta ganin ihun yaki zuwa ta kurma shi ta gumi ta zuba hannu bibbiyu sai walanniya take yi da idanuwanta.

Post a Comment (0)