UKU-BALA'I 07

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.



BABI NA BAKWAI.

Misalin karfe shidda da rabi suka isa cikin Asibiti bayan sun kwashi dirama ta kin karawa da Goggo Marka inda ta hau ta dire tace ba ta san zancen ba ba wanda ya isa ya koma da Habeeba Asibiti a karasa kashe ta mutane da yawa suka taru yarda kasan an kamo gobara ce ta kama gidan ba ka jin muryar kowa sai ta ta.
"kasan Allah ba za a je da ita Asibitin nan ba ka na kallon yarda kuka je da ita lafiya kalau amma daga dawowarku ko magana ba ta iyayi balle aji abin dake dawainiya da ita ka ga hakan na nuni da zuwa Asibiti ba shi da amfaninin komai illa a kai mace a kashe ta tun lokacin ta bai yi ba".
Tun da gari ya waye Mariya ke rusar kuka kamar ranta zai fice daga jikinta komai ya kwance mata musamman yarda ta ga Goggo Marka na nunawa a gareta da uwarta na halin-ko-in-kula sosai take jin bacin rai da takaici sosai taken jin komai na kwance mata na duniyarta rarrashi da ban baki ba wanda ba yi tsakanin Babanta da Goggo Marka ba amma saboda kin jini da rashin son gaskiya haka ta tunkuÉ—eta daga jikin ta ta na faman zazzaga ruwan BALA'I.
"ke dalla janye daga jiki ko na buge ki 'ya sai shegen makirci da munafurci duk kece ummul-aba'isin faruwar komai kuma wallahi zan ga yarda za a fidda Habeeba da ga gidan nan a mai da ita wajan wanda za suk kashe ta a banza a wofi".
A fusace Bello ya shiga dakin Goggo Marka in da ta janye Habeeba tun da safiya ta waye taji suna shirin mai da ita Asibiti zaune ya tadda ta jikinta sai faman mazariya yake idanuwanta na faman zubda hawaye fuskarta ta duk ta kumbure da sauri ya isa gareta jikin sa na rawa ya dago gabadaya kamar wata 'yar tsana ya yo waje da ita nan mutane suka rufa masa baya lura da sukayi Goggo Marka na kokarin hanawa daƙyar da soɗin goshi a ka fidda ita aka saka a Napep Mariya da Bello suka shiga mai Napep din ya ja aka bar Goggo Marka a nan tana ta faman zazzagawa ruwan bala'i ita ala'dole son Habeeba take yi ba ta so a kai ta inda za a kashe ta ba ta duk mutane kallon ta suke ba sun mai da ita wata mahaukaciya.
 Lokacin da suka isa Asibitin ba su tadda likita ba don a ranar bai zo aiki asibitin ba ya tafi can cikin garin Minna (General hospital) domin gudanar da wani aiyuka Nurses kawai suka samu kafin su amshe sai da suka gama yi musu tambayoyin ya akayi suka zo duniya sunyi matukar kuluwa musamman Mariya don ji take kamar ta shake wata figaggiyar Nurses mai zubin mociya ita ce kan gaba wajan jera musu tambayoyi sai da Bello ya shiga hada su da Allah da Annabi sannan suka amsi Habeeba cikin matsanancin halin da take ciki sun ba su gado sai da kuma abin da za ayi mata ne ya gagra domin tunda Nurses suka ba su gado suka je suyi zaman jiran likita har ya dawo sannan ya dubata su kam ba su san abin da za a suyi mata ba.
Mariya ce ta dubi mahaifinta bayan sun shafe sama da minti talatin ba wani canji tunda suka zo ko ta kan su ba a sake bi ba hakan ya kara shigan da su halin kaka ni kayi domin dai ga Habeeba nan akwance yarda take hakan take illa lokaci-lokaci tana figza.
"Baba nikam mai zai hana mu kaita wani asibitin tun da nan din likitan bayanan?".
ta fadi tana mai goge idaniwanta da suka gaji da zubar hawaye.
Zabura yayi jin abinda tace domin tun dazu tunanin da yake tai kenan amma saboda rashin madafa shiyasa ba nemi hakan ba domin ko yace zai dauke zuwa wani asibitin ya san dole a bukaci kudi wanda shi ya tabbata ko wuka za a saka masa a makoshi bai maganin ko taro domin ko Napep din da suka hau bashi ya biya ba bai san ma wa ya ba mai Napep din kudinsa ba shi ya ga ya na sauke su ya ja abinsa yayi gaba zuwan su asibiti yayi ne kawai saboda rashin abin yi bai san yarda za su kasance ba in likita ya zo bai san me zai ce dashi ba.
"Don Allah Baba".
ta sake fadi ganin da tayi kamar bai yi amanna da maganar ta ta ba.
Gyada kai yayi yana mai sauke ganinsa ga Habeeba sannam ya juyo ya kalle ta.
"naji ki Mariya amma kuma...".
Sai yayi shiru yana kureta da idanunsa sa kafin ya sauke wami gumi da yaji ya keto masa lokaci guda.
Ita ma kallonsa take yi sosai da sosai cikin rashin fahimtar in da maganarsa ta dosa sai ta shiga gyaÉ—a kai.
"Mariya ba ni da hali, babu komai a gareni, komai ya kare".
Sosai take kallon yarda yarda yake maganar kamar mai son fashewa da kuka maganar yake saki kamar ana rike masa kuzarin harsheksa komai da yake fadi kawai fadi yakeyi cikin rashin abin yi zuciyarsa da ruhinsa a hargitse suke dalilin rashin in da zai sa gaba baya so ace ya nuna rashin jarumta a wannan lamarin ba ya so a ga gazawar so ya ya ne amma ba yarda zai yi sosai yake jin kunar zuciya da yarda yake jin wani makakin takaici da bakin ciki da suke tsarkewa waje guda cikin duniyar rayuwarsa cikin kankamin lokaci yana kallo yarda ƙaddara take kokarin buɗe masa sabon shafi na rashin dadi nisawa ya sake yi akaro na ba a dadi har izuwa lokacin.
 idanuwan Mariya na kansa tana kallon yarda komai ke sauya ga mahaifinta tana kallon yarda komai ke canza salo cikin rayuwarsa cikin kankanin lokaci ina ma ace tana da wata dama wacce zata yi amfani da ita domin taimakon rayuwarsu ina ma ina ma.
Haka tai ta saƙar zuci abubuwa da yawa take kudiri da buri cikin duniyar rayuwarta wadanda tayi kasafinsu cikin kankanin lokaci.
"na sani Baba amma rashin babu ba zai hana ku ki kai ta wajan da za a bata kulawa ba, kawai mu dauke mu kai ta wani asibitin duÆ™ da dai ba mu san yarda zata kasance ba, zaman namu hakan ba komai zai kara mana ba illa shiga wani ruÉ—anin".
Gyaɗa kai yayi ba tare da ya tanka ba domin ya rasa me ma zai ce sun jima cikin halin shiru kafin ya kokarta motsa laɓɓansa.
"mu kara hakuri, bari naje naji ko ya kusan isowa".
ya fadi yana mai kokarin mikewa cikin sanyin jiki ya fice daga cikin dakin.
Mariya ta bishi da kallo kallon tausayin su baki daya tana kallon yarda lokaci guda komai yake kokarin kara riccaɓe musu a duniyarsu tana kallon yarda rashin babu yake kokarin hana komai ya tafi yarda ya kamata a cikin duniyar su ta sani ba su dashi kuma ba in da za su je su samu ba su da wata kadara ta a zo a gani da za su saida tayi musu maganin abin da ke damun su sosai take jin tausayin kan su tana tuno irin rayuwar da suke ciki tun kafin wannan ƙaddara ta fara kokarin ruguzu musu cikin rayuwa ta sani babu tayi matukar taka rawa wajan wanzar da komai a duniyar rayuwarsu ta sani ba su dashi komai ma babu su dashi duk da hakan suna godewa Allah da ya ara musu numfashi cikin duniyar nan har suke rayuwa kala daban-daban.
Hannu ta sanya ta dauke hawayem da suke ta faman zubo mata ba tare da ta hannusu ba ta sani lokacin su ne yayi suna da damar zuba yarda suke so duk da dai ta san zubar na su ba wani abu ne da zai taimaka wajan hana wanzuwar komai ba.
duban Ummanta take yi tana faman gyada kai tana kallon yarda Ummanta ta sauya lokaci guda tana kallon yarda Ummanta komai na ta ya sauya wanda za ta iya cewa ba ta da bambanci da GAWA DA RAI eh mana gawa da rai duk mutumin da zai rasa bakin magana ko wani abin yi yana zaune waje guda shi kansa bai san waye shi ba bai san me ke damun sa ba zai iya fadar matsalar sa ba ai ko za a iya kiransa da haka din.
"nima za ki iya buÉ—e baki Umma ki fadi abin da ke damun ki, ina ma ace zaki iya kwatanta mani abin da ki ke ji a jikin ki da kuma abin da ya assasa rashin maganarki".
Sosai taji kuka na taho mata hakan ya sanyata saurin yin shiru gami da rufe bakinta da tafukan hannayenta sai faman girgiza kai take yi kukan na kara kokarin sautin bayyana mikewa tayi ta isa gareta cikin hanzari ta kankameta sosai kamar zata koma ciki kuka take yi sosai mai cike da rauni da karayar zucci kuka take yi mai matukar bai wa mai sauraro tausayi da jin kai kuka ne take yi kamar ranta zai fita.
"Umma bana so haka ta kasance a gareki bana so ki kasance cikin rayuwa a haka bana so na ganki a haka har iyakar numfashi a duniyar nan. Ina son ganin ki kamar yarda kike a da koma fiye da haka don Allah Umma don Allah na rokeki".
Tun da ya tun karo dakin yake jin sautin kukanta kukan da ya sanyi jikinsa sanyi ya samya zuciyarsa cikin wani irin yanayi lokaci guda tausayi gami da jikan 'Æ´ar da matarsa gabadaya sun gama galabaitar dashi lokaci guda a duniyar rayuwarsa sosai yake jin zuciyarsa na kuna sosai yake jin kirjin sa na bugawa a dukkan wani karan sautin kukan Mariya in yaji. Wai shin ya zai yi ne, me ya kamata yayi ne?.
Tsayin dakiku ya shafe a wajan kafin ya fara jan jiki domin isa cikin dakin sosai yake jin faduwar gabansa na daduwa sosai yake jin ko ina na jikinsa na canza sautin rayuwa sosai da sosai yake jn wani yanayi na rashin dadi na ywo da shi a sama a gajiye ya isa cikin dakin yanayin da yaga Mariya rungume da Ummanta yanayin da yake kallon kwayar idonta ta canza gabadaya izuwa ja fuskarta ta fara canzawa ita kanta da sauri ya isa gareta cikin tashin hankali a idanuwansa.
"Mariya!".
ya ambataci sunan cikin wani irin sauti mai dauke da rauni da amon sauti.
"don Allah Baba don Allah na rokeka".
abin da ta ke fadi kenan cikin sautin kuka ta yo kasa gabadaya ta dafa kafafuwansa sosai yake jin zafin hawayenta dake zuba akan fatar kafarsa sosai yake jin tausayinta.
"na rokeka ka taimaka...".
"Mariyaaa".
ya sake fadi cikin sauti sosai.
Hannu ya saka ya dagota gbadayanta ya hadata da jikinta ya shiga bubbugawa a hankali cikin sigar rarrashi.
"Shiru Mariya kiyi shiru, komai zai zo karshe, likitan ya dawo yanzu...yanzu haka yace zai zo kiyi shiru".
kawai magana yake yi cikin yanayi na karfin zuciya da ya ruhi sosai yake ajje numfashi ga duk wata kalma in ya furta ta.
A hankali ta dago manyan idanuwanta wanda suka canza kala tana mai kallon sa sosai tana son gasgata abin da take ji yana amsa amo a kunnuwanta da kwakwalwarta sosai take jin saukar kowa kalma da yake furtawa ba tare da tace komai ba ta zare jikinta daga nasa tana ja da baya a hankali sosai tayi nisa dashi har ta kai bakin kofar ta kwasa da gudu tayi waje.
kallo kofar da ta fita yake yi zuciyar cike da fargbar in da ta dosa da sauri ya fara kokarin barin dakin amma sai ya tsaya cak! Motsin da yaji da sauri ya juya Habeeba ce ke kara takure kanta waje daya sosai yake kallon yanayin da ya ga tana yiwa jikinta kamar wacce ake kokarin zarewa wani abu dunkulewa take yi waje guda har sai da ta jingina da bangon dake kusa da gadon da take gyada kai yake yi ya rasa dalili ya rasa me hakan ke nufi ya rasa in da zai saka lamarin ya gano ME KE FARUWA? sosai ya rasa komai na tunanin sa lokaci guda sosai yake jin tausayinta na kara samun gurbi a zuciyarsa kau da kai yayi saboda in har ya cigaba da kallon ta hawayensa za su iya zuba bayan HAWAYEN ZUCIYA da yake ta faman dambe da su amma sun ki tsaya.
da hanzari ya doshi kofar ficewa daga cikin dakin tafiya yake yi cikin ikon Rabbi! sosai yake jin komai na canza ji yake yi ina komai zai fice daga jikin Habeeba ya dawo masa ina ma inama.
da wannan zancen zucci ya isa harabar asibitin ya shiga rarraba idanu domin hango Mariya amma ba alamun ko da mai kama da ita ne bai hanga ba da sauri ya fara nufar kofar Get din domin fita waje cak! ya tsaya muryarta da ta keto cikin iska ta kawo wa kunnuwansa duka nan ya shiga waige waige domin canko inda ya ji sautin muryarta ta mai dauke tausayi sosai har ma da kuka a cikinta.
Idanuwansa ne sukayo waje gabadaya gaban sa yayi wani irin bugu sosai har sai da ya kai hannunsa saitin kirjinsa Mariya ya hango ta na biye da likita kamar wacce za ta kifa domin roko da take yi da hannayenta duk biyu idanuwanta na fidda hawaye sosai shi kuwa likitan sai faman tafiya yakeyi kamar bai wata halitta mai daraja na biye dashi ba sosai yayi kunnan uwar shegu da ita rintse idanuwansa yayi ji yake yi wannan lamari kamar ba gaske ba jin komai yake yi kamar a mafarki.
"Yaa Rabbi!!".
ya furta yana mai dafe kansa sosai ji yake yi yana juya masa 'yar sa ta cikinsa take bin wani yana yarfata yana wulakantawa 'yarsa gudan jininsa kaico ba ya fata hakan ya tabbata ba ya kaunar haka ko a mafarki a halinsa su kasance a haka baya fatan rashin babunsa ya sanya ahalinsa cikin wannan irin hali na kaskaci da wulakantawa a hankali yake kokarin bude idanuwansa yana rokon Allah kar ya sake ganin wannan kaskancin.
Girgiza kai ya shiga yi lokacin da ya buÉ—e idanuwansa ba tare da yayi arba da mugun ganin da yayi dazu ba da sauri jikinsa na É“ari ya koma cikin asibitin dakin da Habeeba take ya dosa yana jin kunar rai sosai bakin ciki takaici duk sun samu mazauni cikin ransa.
Cikin wannan yanayi ya isa dakin tun a bakin kofa ya ja birki yayi turus! idanuwansa sosai sukayo waje likita yake gani da Mariya tsaye kan Habeeba jikin Mariya sai rawa yake yi sosai da sosai takaicin sa ya kara daduwa lokacin da ya lura da irin kallon da likitan ke wa Habeeba hannunsa a harÉ—e.
*"eclampsia".*
Abin ya likitan ya fadi kenan ya na faman gyada kai yana kyaɓe fuska kamar wanda ya ga wani abun ki.
Mariya da sauri ta dubeshi lokacin da taji yayi magana sosai take kallonsa kamar mai son karin bayani bata fuskanci abin da yace ba bata gane me yake nufi da kalmar da ya furta.
Nisawa tayi tana kara kureshi da ido shi kuwa sai faman jinjiga kai yake yi har zuwa wannan lokacin hannunsa na harÉ—e a kirjin sa.
laɓɓanta ta motsa alamun son yin magana.
"Uhmm...".
Sai kuma tayi shiru ganin irin kallon da ya cilla mata.
"ai kin ji abin da na ce ko?".
ya fadi gami da daga mata girarsa.
Da sauri ta shiga gyada kai alamun a,a ba ta fahimci mai yace ba amma sai ya nuna ko a jikinsa domin shi ana nashi bahagon tunanin nuni tayi masa ta fahimta daga kafada yayi gami da juyawa domin ficewa daga cikin dakin.
"Likita!".
Mariya ta fadi cikin sauti mai dauke da rauni sosai kafin ta dora da cewa.
"Taimako don Allah na rokeka".
ta karashe tana mai hada hannayenta waje guda alamun roko idanuwanta cike da kwalla.
Sosai yake kallonta bayan ya tsaya jin ta kirasa idanuwansa manya jajaye ya sauke akanta yana faman gyada kai kafin ya saki nishi kofofin hancin sa duk suka buÉ—e gabadaya kamar wanda ya gaji da gudu fuskar nan tasa bakinkirin sai faman yatsine ta yake yi gami da tabe bakinsa mai kama da jikankiyar ganda.
"Me ki ke so nayi miki yanzu?".
ya fadi ya na shafar runbuÉ—eÉ—an cikinsa mai kama da cikin yan tagwaye wata tara.
Rausayar da kai tayi kwallar da take makalewa suka zobo a kuncinta.
"Taimako don Allah...".
"Taimako fa kika ce, nikam wani irin taimako zan yi miki a yanzu?".
Sosai taji gabanta ya buga jin irin kalamansa da kuma nuna halin-ko-in-kula da ya nuna akan ta da kuma maganarta hawaye taji sun sake balle mata ta rasa mai kuma ya dace tayi lallami da ban bakin ta duk sun kare iyakar roko dai ta nema a wajan sa amma duk hakan bai saka ya jikanta ba ko ya ya ne sai kace mara imani da tausai a ran sa gyada kai ta sake yi tana dubanda har da wani murmushi ta saki wanda ita kanta ba ta san daga ina ya fito ba bata san amfanin yin sa ba illa wani kullin abu da taji ya tokare mata zuciya da ruhi.
"Uhmma ban san mai zan ce da kai ba kuma amma... Uhmma taimako dai nake nema".
ta karasa tana mai sake kai hannu bakinta domin wani irin kuka ne taji yana tasowa tun daga ruhi da zuciyarta yana kokarin samun masaukin a laɓɓanta da sauri ta kallo da kai daga kallonsa sosai take jin haushi a zuciyarta haushi akan likitan da bashi da tausai ko ya ya ne a zuciyarsa ba imani.
Kallon ta yake yi da irin halin da take ciki sosai yake jin wani abu a ransa amma sai ya kau dashi da sauri gami da jan tsaki ya juya cikin sassarfa yana kokarin barin cikin dakin.
A bakin kofa ya ci karo dashi tsaye fuskarsa a tamke kamar bai taba wani abu wai shi murmushi ba sosai yake kallon likatan ciin yanayi haushi da takaicin abin da yayi wa 'yarsa sosai yake ji kamar ya shako wuyarsa ya hada da bango domin ban ga amfanin sa ba, ba irin wadannan mutanen ake so cikin aikin likitanci ba, ba irin wadannan mutanan ake so a wajan taimako da jin kai gami da tausai ba.
Haka ya cigaba da kallonda har ya rabashi ya wuce ba tare da ya tanka masa ba illa wani irin mugun kallon tsana da yake bin sa dashi ransa a matukar bace ya juyo yana duban Mariya wacce take tsaye waje daya kamar wacce aka dasa sai faman sharar kwalla take yi.
"Me ki kayi kenan Mariya, ina amfanin haka wa yace miki irin wadannan mutanan ake neman taimako wa wajansu?".
rintse idanu tayi wani É—aci take ji tun daga kasar ruhinta har zuwa zuciyar.
"na rasa ya za nayi ne, komai ya kwance mani na dauƙa duk mutane iri daya ne a duniyarnan in kaje neman taimako za suyi maka".
ta karashe tana mai tura laɓɓanta cikin baki gabadaya tana cizawa sosai take jin haushin kanta duk da karancin shekarun ta amma hakan bai hanata jin daci a ranta ba akan abin da bakin mutumin nan mai kama da gwanki ya yi mata ta tsane shi tsana mai tsana ni a rayuwarta ko fuskarsa bata muradin sake gani.
"in jiwa ya fada miki mutane iri daya ne? A halinta ne suke iri daya amma a DABI'A da hali suna da bambanci sosai da sosai".
Sosai take jin kalaman mahaifinta na shiga cikin kunnuwanta tana fahimtarsu daya bayan daya tana gasgatawa.
'na tsane shi bana son sake ganin sa, ko A MAFARKINA'
abin da ta ambata kenan cikin kunar rai a zuciyarta tana mai faman dauke hawayen fuskarta
"ina kika ganshi har kike kokarin shiga wani yanayi na rashin jindadi rai".
gyada kai tayi kamar ba zata amsa masa ba can kuma ta nisa.
"na dauka shine likitan da ake jira shiyasa naje na sameshi da kaina domin ganin da nayi lokaci tafiya yake yi".
ta karashe tana mai yamutse fuska gami da yarfar da hannu.
Sosai ya fuskanci in da ta dosa tunaninta shine likitan da aka ce zai zo ya duba Ummanta.
"ni ban ma san shi ba ko da na kawo Ummanki ba shi bane ya dubata wani daban ne...".
Sallamar Dr.Aqeel ne ya sanyashi saurin jinkirta zancen sa ya mai da idanuwansa gareshi ita ma Mariya duban mutumin da yashigo takeyi wanda lokaci guda tayi amanna shine likitan da Babanta ke magana.
"Sannunku ko, ya mai jikin?".
abin da Dr.Aqeel kenan yake fada fuskarsa na bayyanar da yanayin jimami da sauri ya isa ga Habeeba sosai da sosai yake dubata tsayin wani lokaci kafin ya saki ajiyar zuciya ya dubi Bello da Mariya cikin fuskar tausai
"Uhmm...".
Abin da yayi kenan cikin cizon laɓɓa yana mai sake duban su.
da sauri Mariya ta isa gareshi.
"Uhmm Likita don Allah...".
"karki damu na san halin da kuke ciki dukkan ku kuyi hakuri dole ku shiga damuwa da tashin hankali musamman lamari irin wannan wanda ba ku san ina ya dosa ba eclampsia take fama dashi".
Sosai kalmar da ya furta tashiga yi musu yawo akai cikin rashin fahimtar kalmar wacce lokaci guda Mariya ta gano irin wanda waccan bakin mugun ne ya fadi dazu amma kuma ba ta san me nene ba bata san mai kalmar ke nufi ba?.
Post a Comment (0)