NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR.
💕 *_Ki Karba. ki Koya, Idan Kalma So Ta Amsu Yarda Ke Tabbatar Da Kauna._* 💕
-Usaini Danko.
A hankali take sauke jakar dake rataye a kafaÉ—arta cikin yanayi na sanyi jiki idanuwanta na kan kayan da ta gani zube tsakar dakin tana yawatawa idanuwanta akan su cikin yanayi na son sanin daga in da suka fito domin wani irin bugu taji gabanta yayi lokacin da idanuwanta suka sauka kan kayan.
Motsa laɓɓanta tayi da take jin suna cijewa kamar ba sa son ta motsa su.
"Umma wadannan kayan daga ina kuma?".
Ta fadi har zuwa lokacin idanuwanta na kan kayan ta dubi Mu'azzam da ya koma gefe ya tasa choculat gaba yana faman gabza.
"Uhmm!".
Ta sake fadi tana mai duban Umma da tayi tagumi fuskarta da yanayin damuwa dago idanu tayi ta dubi Mariya da gabanta ke ci gaba da bugawa kamar zuciyarta zata faso kirji ta fito.
"Uhmm baki hadu da Yayan naki bane?".
Cikin yanayi na rashin fahimta take duban Umma da son nuna bata sani ba gyaɗa kai tayi a hankali tana mai samun waje tana zama don ji take yi kamar kafafuwanta ba za su iya daukarta ba sosai yanayin ta ya canza lokaci guda ta shiga tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa gabanta take ji yana kara tsinkewa gaɓadaya tun da ta tashi yau take jin wani iri a jikinta kasala da rashin son magana duk su ne suka zama abokan hirarta ko da taje makaranta yau haka ta wuni sukuku Baseera ba yarda ba tayi ba akan ta fadi mata abin da ke damunta amma fir! ta nuna ita ba abin da ke damun ta kawai ba ta jindadin garin ne yau.
Lamarin yayi tsamari yanzu don sosai da sosai take jin faduwar gabanta na daÉ—uwa.
Wani numfashi Umma ta ja tana fesarwa kafun ta dubi Mariya da tayi sakato da baki tana dubanta alamun son karin bayani.
"Ban san mai kike nufi ba Umma. Wani Yayan nawa ne ya zo?".
Murmushi Umma ta saki mai dan zurfi don ta lura Mariya a dan ruÉ—e take kamar wani abu na damunta.
"Hashim mana".
'Yaa Allah'.
Mariya ta fadi tana mai kai hannayenta duk biyu tana dafe kanta idanuwanta lokaci guda suka dan kaÉ—a domin yanayin da take ciki ta kosa ta ji inda Umma ta dosa da zancen domin har yanzu a duhu kanta yake ta rasa gane in da lamarin ya dosa.
Duban kayan ta sake yi tana mai yarfe hannunta da ta cire daga baki kamar wacce ta taɓa wuta.
"Ban gane ba Umma waye haka?".
Wani irin kallon Mamaki Umma take bin ta dashi cikin yanayi na rashin zaton maganar Mariya din sosai take dubanta da yanayi na bata so abin da Mariyar tace ba numfashi ta ja kafun ta motsa laɓɓanta a raunane.
"Yaa Allah mai kike nufi Mariya ba dai har kin manta alheri ba ba dai zaki ce dani kin manta dashi a filin duniyar rayuwarki ba haba! mana yaushe har yaushe hakan zai faru ina! fada min shekaru nawa kuka dauka da rabuwarku dama akwai wannan rana Yaa Salma Haba mana Mariya karki saka zuciyata ta buga mana karki canza mana daga yarda na sanki".
Sosai rauni ya bayyana a muryar Umma bakin ta na rawa har ta dire furucin ta tana duban Mariya da wani irin yanayi mai dauke da daci sosai a zuciya fuskarta lokaci guda ta shiga sauyawa tana rinewa da wani irin abu mai girman gaske.
Tsoro ne sosai ya bayyana a idanun Mariya lokaci guda idanuwanta su kayo waje sosai tana duban Umma da su yanayin da ta ganta a ciki da bacin rai yayi matukar daga mata hankali ba kadan ba da sauri ta mike kanta na wani irin dokawa kamar zai rabe biyu gaban Umma ta karasa ta durkusa kwalla suka cika mata idanu lokaci guda laɓɓanta suka shiga ƙarƙarwa kamar wacce ruwan sama yayi wa dan banzan duka.
"Don Allah Umma...".
"Ya isa haka mana Mariya".
Umma ta tare ta a zafafe tana mai daga mata hannu da wan irin yanayi mai bayyanar da bacin rai kafun ta ja numfashi mai zafi ta dubi Mariya wacce a lokacin hawayen su fara digo mata.
"Ban san haka ki ka koma ba, Ban san yaushe ki ka fara canza halayenki ba, Ban san mai yasa kike kokarin daukar hali na manta Alheri ba, sosai nayi mamaki sosai naji wani iri a raina ban yi tsammanin hakan ba ko A MAFARKINA".
Shiru tayi tana maida numfashi kafun ta dora da cewa,
"Nayi tunanin dama akwai abin da kikayi masa a lokacin baya kafun ya tafi na daÉ—e ina zargi haka banyi zaton samun haka ba a gareki Mariya Yaa Allah".
Rikicewa Mariya tayi lokaci guda kamar wata zautacciya tana duban Umma cikin yanayi na bayyanuwar tsoro a idanuwanta.
"Wallahi ban san wanene ba, ban san akan wa ki ke magana ba don Allah Umma kiyi hakuri ina nan a yarda kika san ni ban sauya halayena ba komai na nan a yarda kika sani na daga halayena na san ALHERI ban mantawa da wanda yayi mani shi".
"Bana tunanin haka, ba yarda za ayi ki ce mani baki manta da shi ba na yarda domin ga shi nan kin nuna na gani don haka...".
"Umma Please mana".
"Kin manta Dr.Karami ko Mariya kin manta mutumin da ya yi...".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Astagfurullah wa'atubu'ilai".
Abin da tayi saurin ambata kenan tana mikewa tsaye hannunta a goshin ta wani irin hajijiya take ji anayi da ita komai taji yana kwance mata a lokacin runtse idanu tayi komai taji ya na dawo mata a shekara daya da rabi da suka gaba komai take ji kamar yanzu yake wakana fatanta Allah yasa ba fushin nasa bane har yanzu ba ta san ya za tayi ba in bai yafe mata ba bata san wani hali zata shiga ba in bai yi mata afuwa ba.
'Yah Dr.Karami ya zo'.
Ta ambata da wani irin yanayi a zuciyarta wani irin bugu taji zuciyarta tayi a hankali ta sauke hannayenta tana dafe kirjinta da su Umma take duba kafun ta dubi kayan da suke jibge tsakar dakin Mu'azzam da ya gama shan sharafin sa da chocolut duk ya bata jikin sa ya tashi yana takawa a hankali kamar mai tsoron ya fadi saboda rashin kwarin tafiyar tasa.
"Da gaske Umma? Yaa Allah! Yana ina Umma don Allah yana ina fada min".
Yanayin da take magana da rawar jiki wani murmushi mai kauri yana samun mazauni a fuskarta zai tabbatar maka kamar ba a hayyacin ta take ba jin komai tayi a hargitse a daidai wannan lokacin.
Sosai Umma ta dube ta tana shirin gasgata yanayin da Mariya take nunawa na rashin sanin Dr.Karami ya zo da farko ta dauka rashin hankali zata nuna mata kamar ta mance dashi shiyasa gabadaya taji wani iri a ranta matuƙa domin kuwa a duniyar nan bai kamata ace Mariya ta mance Dr.Karami ba ko da kuwa shekara nawa zai yi ya dawo.
"Ya koma".
Ware ido tayi tana duban Umma.
"Yaa Hayyu Yaa Kayyum! me yasa yayi mani haka Umma mai yasa ya tafi ba tare da ya tsaya mun ga juna ba shin ya mace shekara da muka dauka har da rabi ba tare da mun sanya juna a idanu ba bai kamata yayi min haka ba haba! Umma mai yasa ba ki ce yaje makaranta ba ko kuma ya jirani na dawo".
Muryarta tayi rauni kamar mai son fashewa da kuka a hankali ta fara kokarin zubewa kasa domin jin komai take yi yana sauyawa komai take jin ya narkewa na jikin ta kafafuwanta take jin su kamar ba za su iya daukar gangar jikinta ba.
'Ban san laifi na ya kai har haka ba, ban san abin da na aikata yayi tsamari haka ba, ya kamata ace ka tausaya min kayi mani uzuri akan abin da ban san na aikata ba haba mana! haba mana!'.
Zuciyarta ta shiga fadin kalamai kamar mai shirin zaucewa sosai take jin wani irin zafi na tururi suna wanzuwa a zuciyarta da kasan ruhinta.
Ba ta san ya zata fassara yarda take jin wannan lamarin ba bata san ya zata fassara yarda take jin akan yanayin da Dr.karami ke nuna mata ba sosai zuciyarta da dukkan jikinta ke shiga tashin hankali mara yankewa.
Cikin yanayi na rashin fahimta Umma ke dubanta fuska na bayyanar da tausayin da take ji akan 'yarta ta ta sani dole ta ji ba dadi ta jima da lura da yanayin Mariya akan Dr.Karami shakuwa ce mai girman gaske Allah ya halitta a tsakaninsu wacce rabuwarta take da matuƙar hatsari a junansu musamman Mariya da ta zurfafa lamarin ta bashi matsayi mai girman gaske a filin zuciyarta.
"Assalamu alaikum! Wai ana sallama da Mariya".
Kamar daga sama suka jiyo amon muryar yaro daga tsakar gida.
Umma ta dubi Mariya ita ma ita take kallo.
"Waye?".
Umma ta fadi da sanyin murya har lokacin idanuwanta na kan Mariya da tayi fakare tana zazzare ido fata take yi Allah yasa Dr.Karami ne.
"Wani ne a cikin mota".
Zabura Mariya tayi ba tare da wani jinkiri ba ta sa kai za tayi waje.
"Mariya!".
Umma ta fadi da sauti tana mai tsayar da ita Cak! ta tsaya jikin ta sai faman rawa yake yi kamar wacce aka kaÉ—awa gangi.
"Ban so abin da kikeyi haba mana Mariya sai kace wata karamar yarinya ko wacce bata da kamun kai meye haka yanzu ke da wannnan yanayin zaki fita shin kin san ko waye yake kiran ki kin san yarda zaki taddashi ba kya tsoron kallon da zai miki na rashin kamun kai ban yarda ba don haka dawo".
Ji tayi kamar ta daura hannu aka ta rusa ihu don takaici da haushi hana ta fita da akayi domin zuciyarta sai tsalle take yi tana sanar da ita ta fita shine ya zo nemanta.
Jiki a sanyaye hawaye na kokarin zuba mata ta samu gefe ta zauna tana wasa da hannayenta.
"Ke haka zaki girma ko da rawar kai ana yabon ki sallah alwala zata gagari ki wannan wacce irin wauta ce sai kace ba 'ya mace ba ki ke irin wannan haukar to ba zan lamunta ba kin ji ko tun wuri ki daina hakan tun kafun ya zame miki jiki ai kewar mutum ba hauka bane...ba ma wannan ba yanzu dake ki barin jiki zuwa ganinsa ki na da tabbacin shine".
Kasa takara yi da kai tana girgizawa zuciyarta na kara matsewa a filin kirjinta so take yi kawai ta ganta a wajan nan.
"Maza tashi ki wanke wannan fuskar taki".
Ba musu ta mike tayi waje ji take yi kamar ta zura da gudu amma tana tsoron bacin ran Ummanta don haka tana wanke fuskar ta dawo ta zauna tana ajje numfashi kadan-kadan.
"ki goge fuskarki ki tashi ki tafi".
Umma ta fadi da Umarni a zuciyarta cikin yanayi na daure fuska sosai. Ba musu mafiya tasa ta goge fuskarta har tana muttsuƙa ɗan basilin kafun ta mike bayan ta zare kayan makarantar dake jikinta ta saka doguwar jallabiya da hijab sannan ta sa kai ta fice.
A hankali take taku tana jin gabanta na dokawa duk takun daya sai taji ya karu sosai a haka har ta isa soro nan ta ja burki ta tsaya tana mai da numfashi a hankali ta shiga kokarin daidaita kanta.
Motarsa dake girke gefe guda take sauke idanuwanta akanta sabuwa ce fil! sai daukar idanu take yi kamar yanzu aka gama ƙerata bakin glass din ta mai duhu wanda ya boye sirrin komai na cikin motar sosai taji gaban ya doka lokacin da ta fara takawa cikin sanyi jiki zuwa wajan motar ba abin da take ambata a zuciyar sai sunayen Allah.
"Yaa Rabb!".
Ta furta lokacin da wani kamshi mai karfi ya daki hancinta har sai da ta kusan dauke numfashi gabanta yayi wani irin bugu ta shiga ware idanu cikin yanayi na tsoro a fuskarta hannayenta biyu ta saka ta dafe goshinta da take ji kamar zai fice gefe daya wani irin abu ne taji zuciyarta ta buge ta dashi da bata yi tsammani ba dago idanunta tayi ta na saukewa akan motar a daidai lokacin shi kuma ya buÉ—e murfin yana zuru kafafuwansa masu dauke da wani haÉ—aÉ—É—en takalmi sau ciki mai kalar baki sai daukar idanu yake yi.
Gabanta ya cigaba da dokawa tana kara ware idanu so take yi ta karyata zuciyar da idanuwanta da suke kokarin wanzar mata da abin da ba tayi zato ba ko kadan a daidai wannan lokacin ba ta fada abin dake shirin faruwa a yanzu ya faru ba haka take so ba bashi tayi KUDIRI ta gani ba a daidai wannan lokacin.
"Dr.Aqeel".
Ta fadi da wani irin yanayi mai zurfi a zuciyarta da gangar jikinta numfashi take kokawa dashi da yake kokarin yanke mata tashin hankalin ta take jin ya karu ba kadan ba ba ta shirya ba bata shirya karbar wani tashin hankalin ba bayan wanda take ciki mai yasa zai mata haka mai yasa zai katse mata hanzarin ta mai yasa ya zo a daidai irin wannan lokacin da bai dace sam dashi ba mai yasa?.
A hankali ya gama fitowa yana mikewa kan kafafuwansa idanuwansa na kan Mariya dake tsaye kamar wacce aka dasa kwankwarar motsi ba tayi illa numfashinta da yake fita da sauri-sauri fuskarta a haɗe kamar hadarin dake shirin zubda ruwa a hakan kuma take yaƙe wanda yafi kuka ciwo.
Murmushi a fuskarsa mai girma duk da glass din da ya mannawa idanuwansa hakan bai hana ta hango tsakar idanun nasa ba kau da kai tayi da sauri tana jin yarda zuciyarta ke bugawa cikin wani irin yanayi mai girma in ba ta manta ba rabon ta dashi yau kusan wata shidda kenan tun wani zuwa da yayi da wani lamari mai girma da ta kasa fahimtarsa tun daga lokacin ya dauke kafarsa da zuwa gidan su da sunan ya bata lokaci tayi tunani akan lamarin da ya zo mata dashi Alal-hakika ta mance da wanzuwansa duk da dai tana jin sa a ranta amma abin da ya zo mata dashi tuni ta ajje shi gefe domin ita a tunanin haukar ta ba zai dawo ba tsokanar ta yake yi a sigar wasa amma ganinsa a yanzu ya dawo mata da komai tsoronta daya ya tuhumeta bata san mai zata ce dashi ba bata san ma ya za tayi da maganar ba domin ko a MIZANIN HANKALIn ta da ta daura bata ga komai ba.
"Mariya".
Ya fadi yana kara ƙawata fuskarsa da murmushi sanye yake da Suit light Blue wanda tayi matukar amsar jikinsa sosai hannu rike da hula mai kama da malfa baka haka takalmin kafarsa baki ne sai kyallin sabuntaka yake yi.
Tun daga kafafuwansa ta fara kallonsa har izuwa kirjinsa sosai shigar tasa ta burgeta ba kadan ba sai dai turaren da ya fesa ne yake hawa mata kai sosai ji takeyi kamar zata yi amai.
"Dama kai ne?".
Ta fadi tana mai tura laɓɓanta gabadaya cikin bakinta cikin wani irin yanayi na karfin hali.
Dubanta yayi cikin mamaki da kuma tuhuma yana sauke glass din idonsa sosai yake kallonta yana karantar yanayin da yake ganin ta a ciki sosai ya fuskanta kamar da matsala a tattare da ita lakari da yanayin da yarda ta nuna na rashin hayyaci a tattare da ita kuma ga idanunta da fuskarta a haÉ—e kamar hadari.
"Ba kiyi tsammani ba ko?".
Ya fadi yana daga mata gira da murmushi a fuskarsa kafun ya sake cewa,
"Akwai wanda kikayi tsammanin gani kenan ba ni ba?".
Ya sake jeho mata tambayar da ta sanya cikinta kaÉ—awa domin gabadaya a tsora ce take.
"Uhmm!?".
Ya sake fadi yana mai jingina da jikin motarsa bayan ya rufe.
Shiru ya gifta a tsakaninsu ba wanda ya sake cewa komai Dr.Aqeel dubanta yake yana jiran cewarta yana harÉ—e hannayensa a kirjinsa
Ita kuwa gabadaya ba ma ta san ya take ba komai nata a kwance yake laɓɓanta sai motsawa suke yi alamun ta na son cewa wani abu amma ta gagara idanunwanta har zuwa lokacin a kasa suke.
"Dr.Karami ya zo ko?".
Da sauri ta dago kai tana dubansa jin abin da yace idanunwanta take yawatawa a nasa wani abubuwa ne masu matukar girma take gani suna fitowa suna doso ta daga idanuwansa da sauri ta janye idanunta tana faman kokawa da numfashin ta da ke kokarin kufce mata.
"Uhmm nima yanzu na dawo makaranta Umma ke fada min amma ba mu hadu dashi ba".
Ta karashe tana yarfe hannaye kamar wacce ta taba wuta.
Sosai ya fuskanci ruÉ—anin da take ciki sosai ya gane in da yanayin da tashi ya dosa wato Dr.Karami tayi tunanin ya kira ta shi yasa ta fito cikin yanayi na hanzari amma ganin sa da tayi ya sanya komai nata kwancewa.
"Shi kika son gani ko Mariya, Dr.Karami kika so ki gani bani ba, na sani domin na gane hakan a tattare dake".
Sosai yaji wani irin abu mai girma ya tokare masa zuciya. Ya fuskanci Mariya hankalinta da natsuwarta suna tare da Dr.Karami tun da yake zuwa bai ta ganin rawar jiki ko wani É—oki ba a game da ita amma yanzu ya gane in da tafi wayo sai dai kuma ba zai yarda da hakan ba.
"Mariya!".
Ya fadi da wata irin murya mai girma da zurfi da abubuwa masu yawa a ciki.
Ita kanta wani yanayi taji da salon da ya kira sunan nata komai taji ya zama kamar ruwa na jikinta yana narkewa zuciyarta ta yi wani irin zillo da wani abu mai girman gaske wanda ta jima tana a jiyarsa a zuciyarta a tsakaninta da Dr.Aqeel wanda har izuwa wannan lokaci bata san menene ba.
Sosai ya gyara tsayuwarsa don ji yake yi kamar zai tiku da kasa kansa yake ji yana sara masa da wani irin yanayi mai zafi bai san haka zata faru ba da bai bata lokacin sa ba da ya san haka zata kasance da ya mika bukatarsa tun wuri sosai da sosai zuciyarsa ta jima tana gargaÉ—in sa akan yayi abin da ya dace amma yayi ragwanci shi a tunanin sa ya raina yanayin Mariya bai san ba a nan lamarin yake ba yana cikin filin zuciya domin ita zuciya ba ruwanta da kankanta ko girma in ta nuna so da kulawa a abu to tabbas hakan ne.
Nisawa ya yi kafun ya furzar da wani huci mai zafi.
"Mariya wai shin mai ke damun ki ne ko dai ni din ne ba kya bukatar gani a filin rayuwarki?".
Ya fadi da wani irin yanayi mai zafi da nuna bacin rai hakan ya sanya Mariya saurin dagowa tana dubansa lokaci guda wani haske mai kama da kibiya ya fito daga idanuwansa ya sauka a nata.
'Yaa Rabb!'.
Ta furta jin yarda zuciyarta ke amsawa da wani irin yanayi mai girman gaske.
Girgiza kai ta shiga yi alamun ba haka bane.
"haka ne ma na gashi nan kin nuna min tun da na zo gabadaya na ga sauyawarki komai naki ya canza kamar bakya maraba dani ko na lura bani kika yi tsammanin gani ba nayi miki shigar sauri ".
"Kayi Hakuri Dr.Aqeel".
Ta fadi da rauni a muryarta kamar zata saki kuka laɓɓanta take motsawa alamun ta na so ta sake cewa wani abu amma zuciyarta taki bata dama.
"Ba maganar bada hakuri bane Mariya so nake yi ki buÉ—e baki sannan ki dube ni muyi magana so nake yi komai ya kasance a wannan lokaci so nake yi duk wani SIRRIN DAKE RAINA ki ji shi a yau so nake yi komai da yake cikin zuciya ki ji shi da kunnuwanki so nake yi ki bani dama na shigo rayuwarki mu kasance a INUWA DAYA".
A razane ta dago kai tana dubansa gabanta na daÉ—a faduwa ji take yi komai na duniyarta a lokacin yana wurgi da ita ta ko wani fanni ba ta san mai Dr.Aqeel yake kokarin dauko mata ya jeho mata a filin duniyar rayuwarta ba bata san wani irin tashin hankali bane yake kokarin jeho mata.
Tsoron ta ya karu sosai ta shiga gyaÉ—a kai wasu kwalla ne taji su na taruwa a idanuwanta wanda bata san dalilin su ba sosai zuciyarta take matsewa da zancen Dr.Aqeel wanda ba ta san yarda zata fassara yarda suke kasancewa a zuciyarta ba.
"Mai zai hana ki karba Mariya sannan ki koya kuma tun da nasan baki iya ba baki taba yi ba wannan shi First time dinki a cikin wannan lamarin ya kamata ki bani dama da yarda na tabbatar miki na san zaki karba kuma ki koya a lokacin da kika bani hadin kan ki na bayyana miki SIRRIN DAKE RAINA".
Zuciyarta taji ta yi wani irin harbawa gabadaya ta dago mata kirji sama hannu tasa ta dafe kirjin nata ji take yi kamar ta kurma ihu ko ta samu sa'ida amma ina ba za ta iya yin haka ba bata san mai ALKALAMIN ƘADDARARTA ke kokarin dauko mata ba da ya jona ta da Dr.Aqeel da wannan lamarin mai girman gaske.
"Ban san me kake nufi ba, ban san ina zancen ka ya saka gaba ba don Allah Dr.Aqeel...".
"Haba mana Mariya me yasa zaki fadi haka mai yasa kike kokarin dauko abin da kika san ba zan taba yarda dashi ba na sani kin ji ni sa rai kuma kin fahimta kawai karba ne ba zaki yi ba saboda baki yarda dani ba".
"Yaa Allah! haba mana Dr.Aqeel mai yasa kake fadin haka mai yasa kake kokarin kasa fahimta ta da ganga bayan kuma kasan ba haka lamarin yake ba".
Sosai yaji jikinsa yayi sanyi da maganganun Mariya dubanta yake yi da wani irin yanayi mai girma a zuciyarsa kafun ya nisa.
"Mariya mai zai hana mu fahimci junamu mu bai wa zuciyoyinmu damar fahimtar tsakanin su hakan ne kadai zai sanya lamarin da muke fuskanta ya zo mana da sauki a filin duniyar nan ta mu".
"Ta ya ya kake zaton haka zai kasance bayan kasan ni ba kowan kowa bace a duniyar nan".
"Ba abin da nake so naji daga gareki ba kenan Mariya ki daina kauce hanya yakamata ki tsaya a mataki daya wanda zai kawo mana mafita a tsakaninmu".
Shiru tayi tana tunanin abin da za ta ce dashi zuciyarta ta rabu gida biyu hankalinta ya karkata izuwa wajan Dr.Karami shi take bukatar gani shi take bukatar sanyawa a idanunta a wannan lokaci tafi bukatar dashi da kowa so take yi su gamu da juna ba ta san wani matsayi ya ajje ta ba bata san ko har yanzu ya na fushi da ita ba zuciyarta ta na sanar da ita har yanzu yana nan kan bakarsa tun da har ya iya zuwa bai neme ta ba kuma ya san inda zai same ta amma yayi birisda ita dan hakan tana cikin TSAKA MAI WUYA domin ta lura da Umma ita kanta ta nuna bacin ranta nunawa da tayi bata gane Dr.Karami ba to ina ga kuma ta san halin da suke ciki a tsakaninsu na bacin rai da ta sanya shi.
So take yi ta gujewa tashin hankalin da Dr.Aqeel ke kokarin turata a ciki domin kuwa zuciyarta gabadaya ta hargitse kwanyarta sai tururi take yi.
"Ki bani lokaci mana a lokacin da ke cikin rayuwarki na sani zaki fahimce ni nan gaba kadan".
GÆ´aÉ—a kai take yi cikin rashin abin cewa bata san abin da zata ce dashi ba ta sani Dr.Aqeel yayi mata HALACCI bai kamata ta watsa masa kasa a ido ba bai kamata ta mance ALHERI da yayi mata ba a filin duniyar rayuwarta ba ma ita kadai ba har da iyayenta sai dai zuciyarta ba ta san matsayar da zata ajje shi ba bata san a wani matsayi yake ba a cikinta.
"Shikenan".
Ta fadi da wani irin nauyi mai girma a zuciyarta domin ita dai ba ta san mai zata ce dashi ba bata so ta fadi abin da zai sanya shi bacin rai ko ya tafi da fushin ta a zuciyarsa bata so ayi na biyu kamar Dr.Karami.
Gyaɗa kai kawai yayi yana mai sakin yaƙe sosai ya fuskanta Mariya na bukatar lokaci sosai take matakin koyon komai da yake nuna mata zai yi kokarin don ganar da ita komai yarda ya kamata ba ya so yayi sake a cikin wannan lamarin.
"Sai anjima ki gaida su Umma".
Ya fadi da murya mai sauti wanda tayi matukar tasiri a zuciyar Mariya ta saukar mata da kasala.
Tana kallon shi ya shiga motarsa ya bar layin tana bin sa da kallo har ya bacewa ganin ta kafun ta ja raunannan jikin ta ta koma cikin gida zuciya cike da rikici mai yawan gaske...
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘