*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
FATALWAR SINU 01
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
A Short Story
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
*ѕtσrч/wríttєn ɮʏ✍🏻:*
👉🏻© *_Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
Ina mai fara wannan rattabe nawa da sunan ubangijin Kaji da Zabbi, Tsira da abinci ga shugaban talikai. Wannan rattabe yana ɗumi ne dangane da lamarin da ya auku gareni. Da fatan zaku ji daɗin sa. Nagode.
A yayin da dubun dubatar jama'a suke murnar shagalin ƙaramar Sallah, ni kuwa Haiman cike nake taf da taraddadin abinda ya same ni tamkar randar da aka cika ta da ruwa. Hausawa kan ce ƙaddara ta riga fata, Haƙiƙa wannan haka yake domin kuwa duk iya Addu'o'i da fatan alkhairi da mutane suka yi ta antayo min bai hanani fige kazar Wahalar da na yanko wa kaina ba. Amma nasan duk wannan ba abinda ya shafe ku ba ne, don haka bari in antaya ku zuwa ga labarin kai tsaye.
Da fari dai ya kamata ku sani cewa, tun ana jibi sallah nayi wata kasassaɓa ta hanyar bayyana Ra'ayina dangane da irin kyautar da nafi so a Suburbuɗo min Matuƙar dai so ake a burge ni, inda na Zana abubuwa uku a matsayin waɗanda nafi so. Waɗannan abubuwa kuwa su ne Alƙalami, Littafi da kuma turare. Kasancewar Mai duka ya haɗa ni da abokai da ƙawaye nagari, da yawan su sun antayo min kyautukan abubuwan da na ambata a baya, wasu ma tun daga birnin Dabo suka antayo min nasu, wasu kuma daga ta Dikko, kai har ma da mutanen birnin Zaman-fara.
A taƙaice dai, na samu sunƙi-sunƙin wagagen littatafai tare da zabga-zabgan Alƙalumma gami da ribɗa-ribɗan kwalebanin kayan ƙamshi. Shin ƴan uwa, yanzu anan Feesabilillah ina da laifi? To amma bari kuji yadda ƴar wannan maganar ta zama Makekiyar gaske.
A washe garin Sallah ne, ina zaune a Ɗaki na da ke ƙofar gida (kun san har yanzu ban shiga daga ciki ba), sai naji an rafka sallama, bayan na amsa sai na yaye labule na leƙa domin in ga ko wanene. Kwatsam! Sai naga wani yaro tsaye da akwati ɗan ƙarami a kansa. Ko da ganin wannan yaro sai na tambaye shi lafiya? Sai yace aiko shi akayi wai ya kawowa uncle Jamilu wannan akwatin, na tambaye shi wa ya aiko shi sai ya ce min wani mutum ne, ina mutumin yake? Wai ya fece amma yace in duba cikin akwatin zan taras da dukkan bayanan da na ke buƙata. Tun a sannan na ji nifa ban yarda da wannan lamari ba, to amma da yake ina da rabon shan duka, sai na Amshi wannan akwati na shige Ɗaki, har da yiwa wannan yaro tukuici kuwa.
Bayan na koma cikin Ɗakina, sai na samu Kujera na Kame sannan na sheƙe duk kayan da ke kan ɗan teburina. Daga nan sai na jawo wannan ɗan akwati na buɗe shi domin in kashe ƙwarƙwatar da ke ido na. Ko da na buɗe wannan akwati, kwaram sai nayi arba da wani wagegen littafi mai kama da littafin Tarihin duniya. A jikin littafin kuma, an liƙa wata ƙaramar takarda wacce take ɗauke da wani rubutu a jikinta. Ban yi wata-wata ba wajen yakito wannan takarda domin ganin abinda ke rubuce a jikinta.
Ko da na duba jikin wannan takardar, sai naga an yi rubutu kamar haka: "Zuwa ga Hãïmâñ, ga kyautar Jinjina nan gareka daga shugaban Makafta wato M.S Narayana". Ko da na karanta wannan rubutu sai nayi murmushi, domin a wancan lokacin nayi tunanin ɗaya daga cikin abokaina ne ya kafto min wani Kafce domin ya sani Nishaɗi, sai dai kamar yadda zaku ji a nan gaba, nayi babban kuskure. Daga nan sai na zaro wannan wagegen littafi tare da wangame shi. Abinda na fara arba da shi bayan na buɗe wannan littafi shi ne rubutun harshen telugu, ni kuma wannan tafiyar tanar ba wani gane shi nake yi ba, don haka sai nayi tunanin lallai kowanene wannan makafcin, tabbas yayi ƙoƙari Matuƙa gaya, (ba zan yi mamaki ba idan aka ce min Muby Ontop ne).
Tun da ba iya karanta yaren nayi ba, kawai sai na antaya shafi na gaba. Wannan Karon kuma sai naga Hoton Jarumi M. S. Narayana a jiki, watau Kwarkwar Sinu kenan. Sa'ilin da naga haka, sai na fara tantamar Anya ma kuwa wannan saƙon ni aka aikowa da shi? Anya ba kuskure aka yi ba? Ko dai yaron nan ɓatan kai yayi ne? Na dai daure na ci gaba da buɗe shafukan wannan littafi. Sai dai wani abin mamaki, duk shafin da na antayo sai in ga Hoton Sinu, wasu hotunan tun yana makaranta ne, wasu hotunan tun yana saurayi, wasu Hotunan shi da iyalan sa ne, wasu da abokan aikin sa ne wasu kuma a yayin gudanar da kafcen Shirye-shiryen sa ne. Haka dai na ci gaba da kallon waɗannan Hotuna har na zo kan Hoton gawarsa Yayinda aka fito da gawar sa bayan ya sheƙe.
Ko da nazo kan wannan hoto, sai na tsaya cak na kasa yin gaba balle baya, zuciyata kuma sai ta hau dukan shida-shida Yayinda idanuwana suka tsaya car a kan Hoton basa ko ƙiftawa. Ba komai ne ya jawo faruwar wannan al'amari ba kuwa face ganin kaina da nayi a jikin wannan hoto. Na san cewa ku kanku zaku yi mamakin jin wannan batu, amma ko rabi na baku kai ba. Gani nayi gani nan tsaye cikin tawagar masu raka gawar tasa a daidai lokacin da aka kafta wannan hoto. Nan fa na ƙurawa wannan hoto ido ƙuriiii... Ina mamakin faruwar wannan al'amari, domin ko da yake na san cewa ana samun mutane da dama suyi kama da junan su, abin da mamaki ace akwai mai kama da ni a Ƙasar Indiya har ma ace ya bayyana a jikin hoto irin wannan. Bayan na daɗe ina kallon wannan hoto tare da ƙoƙarin ganin cewa na gano ko ni ne ko bani bane ba tare da nayi nasara ba, sai na kai hannuna na taɓa wannan hoto wai ni a tunanina hakan zai sa in fahimci ko akwai tarayya tsakanina da wannan mutumi da ke jikin wannan hoto.
Hannuna na sauka a kan wannan hoto, sai naji kamar daga sama an ɓarke da wata irin Mummunar dariyar mugunta, kafin in tantance ko daga ina ne wannan dariya take fitowa, kawai sai gani nayi wasu ƙananan Igiyoyi sun fito daga cikin wannan littafi sun ɗaure ni tamu, har sai da ta kai ga bana iya motsa ko ɗan yatsa na. Kwatsam! Kuma sai ga wata iska mai Ƙarfi ta biyo bayan waɗannan Igiyoyi tana kaɗawa da ƙarfin gaske, nan take ta Jani da ƙarfin tsiya ta dunƙule ni har sai da na koma ɗan ƙarami tamkar Ant-man sannan ta antaya da ni cikin wannan littafi. Duk Ihu, magiya da kururuwar neman taimako da nayi ta antayawa sun tashi a banza domin kuwa babu wanda ya ko jiyo ni balle ya kawo min ɗauki.
Zan Ci Gaba In Shaa Allaah
<••••••••••••••••••••••••••••>
Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com