FATALWAR SINU 02


*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              FATALWAR SINU 02
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              A Short Story
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
   
                      ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
         *ѕtσrч/wríttєn ɮʏ✍🏻:*
👉🏻© *_Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹

Haka dai wannan iska tayi ta gudu da ni kamar zamu bar duniya har sai da na manta iya lokacin da ta ɗauka tana wannan gudu dani. Bayan mun daɗe a cikin wannan yanayi, sai can na jini Tim! Na faɗo kan wani abu mai kama da tarin raugar gyaɗa wanda ina kyautata zaton laushin sa ne kawai ya hana ƙasusuwana karyewa tare da yin rugu-rugu. Kasancewar na galaɓaita ainun, ban ma fahimci cewa wannan Igiyar da ta ɗaure ni ta kwance ni da kanta ba balle in lura da inda nake, hakanan dai na langaɓe ina numfashi sama-sama sai kace tsohon karen da cuta ta kwantar da shi.

Ina nan kwance ina tunanin ta yaya akayi har wannan al'amari ya faru da ni? Yaya daga buɗa littafi kawai shikenan waƙi'a irin wannan zata antayo kaina? Ban kai ga gama wannan tunani ba sai naji wata murya na cewa: "Barka da zuwa Hãïmâñ, lake-lale marhabin da makafcin zamani, aminci ya kaiwa tsafin gidan mu, Haƙiƙa na tabbatar da cewa zaka zo, kuma gashi kazo ɗin. Hahah! Tsabar galaɓaitar da nayi, tare da rashin ƙwarin jikina suka sa na kasa furta komai kuma na kasa Waigawa inda wannan murya ke fitowa domin inga ko wanene, kuma na kasa furta komai. Ko da mai maganar yaji shiru, sai naji yace: "a'a, ya naji yayi shiru kuma, Ko dai ya mutu ne? Bari mu gani". Ko da yazo nan a zancen sa sai naji wata irin iska mai sanyi tana shiga cikin Jikina, ba'a daɗe da yin haka ba sai naji duk gajiyar da ke jikina ta gushe, wahalar da na sha ta kau, sannan wani gagarumin Ƙarfi ya shige ni tamkar nayi baccin awa goma na tashi nayi wanka kuma na ci abinci. Ko da naji wannan canji a jikina, sai nayi zumbur na miƙe tare da Waigawa inda wannan murya take fitowa domin ganin kowanene.

Tooooofah! Mai zan gani haka? Ba kowa na gani ba face Kwarkwar sinu zaune cikin sigar Kafcen sa na fim ɗin Racha (Hatsabibi). Kujerar da yake zaune a kanta kyakkyawa ce ba laifi, Singiletin da ke wuyar sa kuma Koriya ce, Yayinda ya ɗaura wani farin zane a ƙugunsa ya kuma ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗaura a kan ɗayan. A hannunsa na dama kuma kwalbar barasa ce wacce a daidai wannan lokaci yayi rabin ta, ko da muka haɗa ido sai yayi min wani azzalumin murmushi.

Tsananin mamakin ganina tare da shi a wannan wuri kuma a daidai wannan lokaci yasa yasa na wangame baki kawai ina kallon sa. Bayan mun an samu ɗan lokaci muna kallon juna ba tare da ɗayan mu ya ce da ɗayan komai ba. Sai ya ce da ni: "zauna mana". Kafin in ƙyafta ido sai ga kujera ta bayyana a gabana alhalin da can babu ita. Har na yunƙura da nufin in zauna sai na lura cewa ashe duk allurai ne soke a jikin kujerar, zama kawai suke jira in yi su tsire ni, don haka sai na ƙi zama. Ko da yaga haka, sai ya ɓarke da dariya kamar sabon hauka, yayi ta yi har ya gaji, daga baya kuma sai ya murtuke fuska kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa. A daidai lokacin da ya ɗaure fuskar ne kuma kayan jikinsa suka canja launi izuwa ƙananan kaya. Daga nan sai ya miƙe tsaye ya nufo inda nake yana kaɗa kai cikin murmushin antakaranci kamar dai yadda ya dinga yi a cikin shirin Nayaak (masheƙi). Ko da yazo dab da ni sai ya buɗe baki da nufin yin magana. Ai kuwa nan take naji wani wari, ɗoyi gami da hamami sun Durfafo ni, ba shiri na kau da kaina daga saitin inda yake don naga warin na neman yin barazana wa lafiya ta.

Ganin abinda nayi yasa ya sake fashewa da dariya sannan yace: "Watau baka son warin barasa, amma ka iya yamaɗiɗi da ni kan cewa ni mashayinta ne ko a zahiri, ko ba haka ba? Lallai ka cika Maras kunya, Tir da kai! Ko da naji wanna kalami sai raina ya ɓaci, amma saboda ban san me ke faruwa ba sai na danne zuciyata ban nuna mishi ba. Maganar farko da ta fito daga baki na ita ce: "Waye kai?". Ko da yaji wannan tambaya, sai naga yayi tsalle ya koma gefe tare da riƙe baki wai shi yayi alamar mamaki, sannan yace: "ai iyye! To in baka sani ba ka sani, ni ne nan Mailavarapu Surya Narayana, watau Kwarkwar sinu kamar yadda ku Ƴan fassare-fassaren nan kuka liƙa min". Yayin da yazo nan a zancen sa, sai naga ya sake murtuke fuska yana harara na.

Ni kuwa wannan bayani da yayi ba ƙaramin mamaki ya bani ba, na sake duban shi da kyau naga dai tabbas shi ɗin ne, sai nace da shi: "To amma ba ka mutu ba? Ya kuma aka yi ka ci gaba da rayuwa?" ko da yaji waɗannan tambayoyi nawa sai ya ƙara ƙyalƙyalewa da dariya sannan yace: "Ai fatalwa ta ce kake gani yanzu, kasancewa ta ɗaya daga cikin Mabiya ubangiji Rama da kuma kasancewata ɗaya daga cikin mutanen da aka fi zolaya a duniya, shi ne Ubangiji Rama ya bani damar dawowa duniya a matsayin fatalwa bayan mutuwa ta domin in rama abinda aka yi min wanda kai da ire-iren ka kuke sahun gaba wajen aikatawa! Na daɗe ina kafawa masu zolayata tarko suna shallakewa ba tare da na tarka ko ɗaya ba, sai fa kai yau. Don haka ya zama dole in gana maka azaba mai raɗaɗi don hakan ya zama sharar fage na taron Ɗaukar fansata da zan yi. Mamaki da taraddadin abinda ka iya biyo bayan wannan batu nasa ne suka sa nayi shiru na kasa cewa komai. Can dai sai na yanke Shawarar jan shi da labari ko wataƙila hakan yasa ya bayyana min wasu al'amuran, don haka sai nace: "Eermm... Kaga Kwarkwar ɗan Dakata kaji... Ai iyye! Watau ni kake kira da Kwarkwar ko? Lallai ka cika maras kunya yaron nan! Sinu ne ya katse ni da wannan jawabi nasa ta hanyar daka min tsawa. Cikin rawar baki nace "Erm... To Sinu ka ɗan saurare ni... Kai! Kada ka raina min wayau, sunan ba Sinu bane Srinu ne, kuma kada ka sake kirana da wannan sunan ka kira ni da sunana na asali watau Mailavarapu Surya Narayana! " To Mailavarapu Surya Narayana... Erm.. Ina ganin kamar an samu saɓanin fahimta ne, ina so ka sani cewa ni ba kowa bane a harkar fassara, domin ayyukan da aka yi dani basu da yawa, hasali ma ni aikin shirin ka ɗaya zan iya tunawa nayi. Bugu da ƙari ni ban ga ta yadda za'a yi ace wannan abu ya zafafe ka ba da har zaka dawo duniya a matsayin fatalwa kace zaka ɗauki fansa. Laifin me masu fassara suka yi maka? Hasali ma dai, shin wai wannan Karon ne aka fara fassara ne? In gaskiya ne me yasa waɗancan basu zafafe ka ba sai wannan?


Zan Ci Gaba In Shaa Allaah.



<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees
 Instagram: Haimanraees
 Infohaiman999@gmail.com
Post a Comment (0)