SHARHIN FIM ƊIN AVENGERS: AGE OF ULTRON
Avengers: Age of Ultron Fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2015 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Avengers wanda Stan Lee da Jack Kirby Suka rubuta a ƙarƙashin Kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne suka ɗauki nauyin shirya shi, yayin da Kamfanin Walt Disney Motion Pictures suka rarrabashi. Fim ɗin shi ne na biyun The Avengers (2012) kuma Fim na goma sha ɗaya daga cikin Fina Finan Duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU). Joss Whedon ne ya rubuta kuma ya bada umurnin Fim ɗin.
An fara Ɗaukar Fim ɗin ne a cikin watan Fabarairu 2014 a, yayin da sauran aikin ya ci gaba a tsakanin watan Maris da Agusta. Wuraren da aka ɗauki Fim ɗin sun haɗa da Shepperton Studios dake
Surrey, Italy, South Korea, Bangladesh , New York City, da sauran wasu wurare dake Ingila. An mayar da fim ɗin izuwa zubin 3D tun kafin a fitar da shi. Kasancewa an kashewa Fim ɗin kuɗi kimanin dala miliyan $365, hakan yasa ya zama Fim na biyu da aka fi kashewa kuɗi a Tarihin Fina Finan duniya baki ɗaya. An saki wannan Fim ne a ranar 13 ga watan Afrilu 2015 A Los Angeles, Sannan aka sake shi a duniya baki ɗaya a ranar 1 ga watan Mayu 2015 a zubin 3D da IMAX 3D.
Fim ɗin ya samu yabo sosai daga masana harkar Fina Finai sannan 'yan kallo ma ya burge su, bugu da ƙari, fim ɗin ya kawo maƙudan kuɗaɗe kimanin Dala Biliyan $1.4 a Kasuwancin Fina Finan duniya baki ɗaya, hakan yasa ya zama Fim na huɗu da yafi kowanne kawo kuɗi a 2015 kuma yafi kowanne kawo kuɗi a duniya.
Anyi na ukun sa mai suna Avengers: Infinity War a 2018, sannan ana sa ran fitar na huɗun sa a 2019.
LABARIN FIM ƊIN
Mayaƙan tawagar Avengers sun kai wani hari a Ƙasar Sokovia da ke gabashin Yurofiya domin ruguza wata mafakar jami'an Hydra wanda Baron Wolfgang Von Srucker Yake Jagoranta.
Wolfgang ashe yana ta sarrafa tsafin da ke cikin sandar tsafin Loki ne ta hanyar baiwa mutane ƙarfin da ke cikin ta. A nan ne tawagar Avengers ta ci karo da wasu 'yan biyu waɗanda suka samu irin wannan ƙarfin. Pietro Maximoff wanda ya samu ƙarfin gudu kamar tauraruwa mai Wutsiya, sai kuma ƙanwar sa Wanda Maximoff wacce take iya sarrafa tsafi yadda taga dama. Tawagar ta samu nasara akan Wolfgang inda Tony Stark ya ɗauke sandar tsafin Loki ɗin
Bayan sun koma gida ne sai Stark da Banner suka gano cewa wannan sandar tsafi tana da wani hankali na wucin gadi a cikin dutsen da ke jikinta. Saboda haka sai sukayi Shawarar su kammala haɗa wani saƙago da Stark ya fara haɗawa mai suna ULTRON da shi a asirce domin ya taimaka musu wajen yaƙi da 'yan ta'adda. Shi kuma Ultron sai yayi tunanin ya wanzu ne kawai domin ya ƙarar da' yan adam baki ɗaya a maimakon kare 'yan adam baki ɗaya da Stark ya ƙirƙireshi a kai.
Don haka sai nan take ya kashe saƙagon dake taimakon Stark wato J.A.R.V.I.S. Sannan ya kaiwa tawagar hari a Hedikwatar su, sannan ya fece da sandar tsafin Loki. Bayan nan sai kuma Ultron yayi amfani da ragowar kayan aikin Wolfgang a Sokovia ya inganta jikin sa, sannan kuma ya ƙirƙiro wasu ƙananan saƙagai irin nasa domin su taya shi aiki. Hakan fa bai ishe shi ba, sai kuma ya je ya ɗauko waɗannan 'yan biyun domin su zama mataimakan sa, su kuma dama suna jin haushin Stark saboda Kamfanin sa ne ya ƙera makamin da yayi sanadiyyar mutuwar iyayen su.
Daga nan kuma sai ya je wajen fitaccen ɗan harƙallar miyagun makamai Ulysses Klaue domin ya samu Sinadarin Vibranium wanda aka samo daga Wakanda. Tawagar suma sai suka kaiwa Ultron hari a can tare da muƙarraban sa. Sai dai Wanda ta yi amfani da ƙarfin tsafin ta wajen rikita su da hangen abubuwa iri daban daban sannan ta sa Hulk ya fita hayyacin sa ya kama yiwa jama'a ɓarna, da ƙyar Stark ya samu ya sumar da shi bayan yayi amfani da wata rigar ƙarfe ta musamman wanda ya Sana'anta saboda hakan
Ta'adin da Hulk yayi wa jama'a da kuma tsoron da Wanda ta dasa musu a zuciya ne yasa tawagar suka ɓoye a wani keɓaɓɓen gida na ɗan wani lokaci. Shi kuma Thor sai ya nemi taimakon Dakta Erik selvig dangane da munanan abubuwan da ya gani yayin da wanda ta rikita masa tunani. Shi kuma Nick Fury sai ya je maɓoyar tawagar ya ƙara musu ƙwarin guiwa kan yadda zasu samu nasara akan Ultron.
Can kuma a Seoul, Ultron ya matsawa abokiyar tawagar Avengers wato Dr. Helen Cho Domin tayi amfani da na'urar ta wajen Samar masa da wani sabon cikakken jiki mafi inganci. Yayinda Ultron yake ƙoƙarin ɗaura kansa a wannan sabon gangar jiki ne sai wanda ta samu damar karanta zuciyar sa, a nan ne fa ta gano shirin sa na son ganin ya hallaka gaba ɗayan mutanen duniya don haka sai ita da yayanta suka juya masa baya.
Daga nan sai Rogers, Romanoff da Barton suka tunkari Ultron suka ƙwace gangar jikin, sai dai sunyi rashin sa'a domin ya kama Romanoff ya tafi da ita. Rikici kuma sai ya sake ɓallewa a tsakanin tawagar bayan Tony Stark ya ɗaura J.A.R.V.I.S. a kan wannan sabon jiki. Ashe Jarvis ba mutuwa yayi ba, ya ɓoyewa Ultron ne. Ana cikin hakane Thor yazo ya taimaka wajen kunna gangar jikin, tare da yi musu bayanin cewa wannan dutse da ke goshin gangar jikin ɗaya ne daga cikin duwatsun al'ajabi shida da ake da su, kuma su ne duwatsun da suka fi kowanne ƙarfin tsafi a duniya kuma ya gansu a cikin hangen nesan da yayi.
Daga nan sai " Vision " tare da waɗannan 'yan biyu suka raka tawagar Avengers zuwa Sokovia inda Ultron yayi amfani da ragowar Sinadarin Vibranium ɗin da ya siyo wajen samar da wata Muguwar na'ura wacce zata iya ɗaga ilahirin Ƙasar sama tun daga ƙasa ta kifar da ita kowa ya mutu. Banner ya samu damar ceto Romanoff wacce ta farkar da Hulk domin yin wannan yaƙi. Tawagar avengers sunyi baƙin gumurzu a tsakanin su da Ultron Yayinda Nick Fury, Maria Hill, James Rhodes da kuma wasu Jami'an S.H.I.E.L.D. Suka zo a wani babban jirgi suka kwashe mutanen Ƙasar. Ana cikin hakane Pietro ya mutu a lokacin da ya kare Clint Barton daga harsasai, jin haushin haka ne yasa wanda ta bar inda aka ajiye ta domin ta ruguza jikin Ultron, wannan ya baiwa ɗaya daga cikin saƙagan Ultron damar kunna wannan Mummunar Na'ura. Nan take birnin ya fara ɓuɓɓugowa gaba ɗaya amma sai Stark da Thor suka haɗa ƙarfi suka tarwatsa komai.
Bayan ƙura ta lafa ne sai Hulk ya gudu a wani jirgin sama saboda baya son ya cutar da Romanoff idan ya ci gaba da kasancewa tare da ita, shi kuma vision sai ya Fuskanci Ultron ya tarwatsa shi. Bayan nan sai tawagar ta kafa sabon wurin zama inda Nick Fury Maria Hill da Rhodes zasu dinga kulawa da shi, thor kuma ya koma Asgard domin ya ƙara bincike dangane da Al'amuran da suka jawo faruwar waɗannan yaƙe-yaƙe. Shi kuma Clint Barton Sai yayi ritaya, Yayinda Steve Rogers da Romanoff su kuma suke koyar da sabbin Membobin tawagar wato Wanda, Sam Wilson, Rhodes da Kuma vision.
A wata fitowa ta ƙarshe, an nuno Thanos wanda ransa ya ɓaci da rashin nasarar da karnukan farautarsa suke haifar masa, inda yasa wata safar hannun Ƙarfe kuma ya sha alwashin samo duwatsun al'ajabin dukkan su da kansa.
JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA
* Robert Downey Jr. - Tony Stark / Iron Man
* Chris Hemsworth - Thor
* Mark Ruffalo - Bruce Banner / Hulk
* Chris Evans G Steve Rogers / Captain America
* Scarlett Johansson - Natasha Romanoff / Black Widow :
* Jeremy Renner - Clint Barton / Hawkeye:
* Don Cheadle - James "Rhodey" Rhodes / War Machine
* Aron Taylor-Johnson - Pietro Maximoff / Quicksilver
* Elizabeth Olsen - Wanda Maximoff / Scarlet Witch
* Paul Bettany - J.A.R.V.I.S. / Vision
* Cobie Smulders - Maria Hill
* Anthony Mackie - Sam Wilson / Falcon
* Hayley Atwell - Peggy Carter
* Stellan Skarsgård as Erik Selvig
* James Spader - Ultron
* Samuel L. Jackson - Nick Fury
* Thomas Kretschmann - Baron Wolfgang von Strucker
* Henry Goodman - Dr. List
* Linda Cardellini - Laura Barton
* Claudia Kim - Helen Cho
Andy Serkis - Ulysses Klaue
* Julie Delpy - as Madame B.
* Kerry Condon - F.R.I.D.A.Y
* Josh Brolin - Thanos
<••••••••••••••••••••••••••••>
Hãïmâñ Khãñ Řăééş <••••••••••••••••••••••••••••>
08185819176
Twitter: @HaimanRaees
Instagram: Haimanraees
Infohaiman999@gmail.com