IMANI DA ƘADDARA

━━━━•✿✍🏼✿•━━━━
IMANI DA 'KADDARA
━━━━•✿✍🏼✿•━━━━

Imani da 'kaddara alkhairinsa da sharrinsa rukuni ne cikin rukunan imani, kuma imanin musulmi ba ya cika har sai ya san cewa abin da ya sameshi bai kasance zai kuskure masa ba, haka abin da ya kuskure masa dama bai kasance zai sameshi ba,
Allah Madaukaki yace:

"إِنَّا كُلَّ شَيْءٍ خَلَقْنَاهُ بِقَدَرٍ"

"Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri."[Al-Qamar:49]

Kuma yace:
"وَخَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ فَقَدَّرَهُ تَقْدِيرًا"

"Sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa." [Alfurqan:2]

"K'addara na nufin:Tsarin da Allah ya tsara halittu a kansa, gwargwadon yanda iliminSa ya gabata kuma hikimarSa ta hukunta. Wannan tsari na 'Kaddara ya samo asali ne daga sifar Allah ta "K'udura", wato ikonSa da kasancewarSa Mai cikakken iko ne a kan komai da komai, kuma mai cikakkiyar damar aikata duk abin da ya ga damar aikatawa ne"(Littafin Arkanul Iman).

A cikin wannan rukuni na Imani, wato imani da k'addara alkhairinsa da sharrinsa akwai lada mai yawa da sakamako mai girma ga wanda yayi imani cikakkiyar imani, yayi hakuri, ya yi tawakkali ya fawwalawa Ubangiji lamarinsa.

MARTABOBIN IMANI DA K'ADDARA

Imani da 'Kaddara alkhairinsa da sharrinsa ba ya cika har sai mutum ya tabbatar da wasu abubuwa guda hudu:

1- ILIMI
Imani cewa lallai Allah ya san kowane abu, a dunkule, da kuma a d'aid'aikunsa. Allah Madaukaki yace:

"أَلَمْ تَعْلَمْ أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۗ إِنَّ ذَٰلِكَ فِي كِتَابٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ"

"Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne."[Al-Hajj:70]

Kuma yace:

"وَعِندَهُ مَفَاتِحُ الْغَيْبِ لَا يَعْلَمُهَا إِلَّا هُوَ ۚ وَيَعْلَمُ مَا فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ ۚ وَمَا تَسْقُطُ مِن وَرَقَةٍ إِلَّا يَعْلَمُهَا وَلَا حَبَّةٍ فِي ظُلُمَاتِ الْأَرْضِ وَلَا رَطْبٍ وَلَا يَابِسٍ إِلَّا فِي كِتَابٍ مُّبِينٍ "

"Kuma a wurinSa mabũdan gaibi suke, babu wanda yake sanin su fãce Shi, kuma Yanã sanin abin da ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganye ba ya fãɗuwa, fãce Yã san shi, kuma bãbu wata ƙwãya a cikin duffan ƙasã, kuma babu ɗanye, kuma babu ƙẽƙasasshe, fãce yanã a cikin wani Littãfi mai bayyanãwa."[Al-An'aam:59]

2-RUBUTU
Imani cewa lallai Allah ya rubuta k'addaran kowane abu, har zuwa tashin Alk'iyama.
Allah Madaukaki yace:

"مَّا فَرَّطْنَا فِي الْكِتَابِ مِن شَيْءٍ..."

"Ba Mu yi sakacin barin kõme ba a cikin Littãfi..."[Al-An'aam:38]

3-NUFI
Imani cewa, dukkan abin da Allah ya nufa, shi yake kasancewa, abin da bai nufa ba kuma ba ya kasancewa, sannan kuma lallai bawa yana da nufi, amma tana a k'arkashin nufin Allah ne, ko yayi nufi toh kuma sai Allah ya nufata. Allah Madaukaki yace:

"وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ"

"Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda."[At-Takweer:29]

4-HALITTA
Imani cewa, lallai dukkan halittu, bawa dashi da ayyukansa dukansu halitta ne..
Allah yace:

"اللَّهُ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ ۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ وَكِيلٌ".

"Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme." [Az-Zumar:62]

Kuma yace:

"وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ"

"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?"[As-Saffaat:96].

Mai waqe ya kawo wadannan martabobi gabaki dayansu cikin baiti yace:

علم كتابة مولانا مشيئته وخلقة وهو إيجاد وتكوين

Ma'ana

Ilimi, da rubutun Majibincinmu (Allah), da nufinSa da halittarSa, wanda shine samarwa da kasantarwa.
Post a Comment (0)