DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 01

DARUSSAN RAYUWA DAGA JARUMI SHAH RUKH KHAN 

Kashi Na É—aya 01

Fitowa Ta ÆŠaya 01

Daga Haiman Khan Raees 

Bismillahir Rahmanir Raheem. 

Barkan Mu da Warhaka. 

   Jarumi Shah Rukh Khan yana É—aya daga cikin Manya-manyan Jaruman Fina Finan Ƙasar India. Na san cewa wannan Jarumi baya buÆ™atar a bayyana ko shi wanene a harkar Fina-Finan India 🇮🇳, domin kuwa duniya ta riga ta san da wanzuwar sa. Babu wani waje da ake kallon fim ko da a cikin rijiya ne da sunan wannan bawan Allaah bai je ba, to amma ba wannan ne abin mamakin ba, hatta ma waÉ—anda basu san da wanzuwar kallace-kallacen Fina-Finai ba ma sun san shi a hoto ko kuma labari. Misali, an kai wani mataki da a nan arewacin Nijeriya da zarar ka faÉ—i wata kalma ta soyayya ko kuma ka aikata wani gagarumin abu da ya danganci soyayya, nan take sai kaji ana cewa 'hmm su sharukhan baban soyayya, uhm kaji su sharukhan da dai abubuwa Makamantan haka masu Alamta cewa jarumin ya samu isa zuwa wajen waÉ—annan mutane. Wannan kuma har wa yau alama ce da ke nuna tsantsar suna da kuma shahara da wannan bawan Allaah yayi a duniya. 

To a Zahirin gaskiya babu wani mutum da za'a ce gashi ya shahara a duniya face sai ka samu wasu darussa da za'a iya koya daga gare shi, Darussan nan kuwa suna iya zama na kirki ne wanda za'a É—abi'antu da su ko kuma akasin haka. Wannan dalili yasa na yanke Shawarar tsakuro mana wasu daga cikin kyawawan Darussan da suka zagaye rayuwar wannan Jarumi tun daga rayuwar sa ta kansa da kuma Fina Finan sa domin su zame mana ababen lura saboda rayuwar yau da kullum. Sai dai kuma fa, mai karatu ya kamata ya sani cewa ba wai na kawo waÉ—annan darussa bane don in wanke jarumin daga wasu kurakurai da yake aikatawa ko kuma in nuna shi yafi wani bane, abinda na sani shi ne, shima yana laifi kamar yadda kowa ke yi kuma yafi wani wani abun shima wani ya fishi wani abun. Sannan ina fata wannan muÆ™ala Tawa ta zamo amsa ga masu tambaya dangane da Jarumi Shah Rukh Khan. 

Na Kasa wannan Muƙala Tawa izuwa gida huɗu. Ga su Kamar haka:
 1. Darussa daga Rayuwar Sa kai Tsaye. 
 2. Darussa daga Fina Finan sa kai tsaye. 
 3. Darussa daga Kalaman sa kai tsaye. 
 4. Darussa daga kalaman Fina Finan sa. 

Don haka yanzu zamu fara bayani ne akan kashi na ÆŠaya: ga kaÉ—an daga cikin Darussan da zamu iya koya daga rayuwar Jarumin Kai tsaye. 

1. MARAICI BA HUJJA BACE TA RAGONCI: 

Mai Yiwuwa mai karatu ya kasance baÆ™o ne a harkar Tarihin jarumai, mai yiwuwa kuma ba baÆ™o bane. To idan har ba baÆ™o bane, nasan kana da Masaniya akan wannan. Idan kuma kai baÆ™o ne to yau ka sani. Mahaifan Jarumi Shah Rukh Khan duk sun mutu tun kafin ya zama wani abu a duniya, amma hakan bai karya masa zuciya ba, bai sa ya langaÉ“e ya É—ora hannu a kai yana Wayyo Wayyo Jama'a ku zo ku taimaka min na shiga uku ba. Hasali ma hakan Æ™ara masa Æ™warin gwuiwa yayi wajen ganin ya cimma burin sa a rayuwa. 

2. IDAN BA ZASU IYA TAFA MAKA BA, TAFA WA KANKA:

 Jarumi Shah Rukh Khan yana É—aya daga cikin É—aiÉ—aikun Jaruman da basu da uwa a gindin murhu a Masana'antar Fina-Finai ta Bollywood, kuma mafi Shahara daga cikin su. Yayin da ya shigo harkar bai san kowa ba kuma babu wanda ya san shi, amma haka ya dage har Allaah Ya kawo shi matakin da yake a yau. Rashin wani wanda zai masa alfarma a harkar bai hanashi jajircewa wajen ganin ya cimma muradin sa ba. 

3. NACI DAMBEN KUTURU: 

Kowa yasan cewa Jarumi Shah Rukh Khan bai kai irin su Hrithik Roshan iya rawa ba, amma hakan bai hana shi dagewa wajen ganin ya taka iya rawar da zai iya a cikin Fina Finan sa ba. Bai kai irin su Salman Khan iya faÉ—a ba, amma hakan bai hana shi jajircewa wajen ganin ya kafta ba. Shin ko kun san Jarumi Shah Rukh baccin da yake samun damar yi a yini bai wuce awa huÉ—u zuwa shida ba? Sauran duk yana tafiyar da su ne wajen baiwa aikin sa muhimmanci? 

4. JAHILCI BA HUJJA BA CE:

 Jarumi Shah Rukh Khan yana É—aya daga cikin jarumai waÉ—anda suka fi sauran tarin ilimi a cikin Masana'antar Fina Finan India. Duk da cewa iyayen sa Talakawa ne, hakan bai hana su dagewa wajen ganin sun bashi ilimin da ya dace ba. Hakanan bayan rasuwar su ma, ya dage har sai da ya kammala karatun sa a Fannin tsimi da tanadi watau economics. Baya ga haka, jarumin ya kasance mai yawan karance-karance wanda hakan ya sa ya zama gwani wajen iya tsara zance da kuma saita kalamai. Bugu da Æ™ari kuma, a halin yanzu jarumin yana da Digirorin girmamawa guda huÉ—u wanda ya samu daga Jami'o'i Mabanbanta a faÉ—in duniya. Kenan hakan na nuna mana cewa, lallai ne ko me zaka yi in har ka zama ma ilimi, lallai ne al'amura za su zo maka da sauÆ™i kuma cikin lumana. 

5. BIN NA GABA BIN ALLAAH:

 Jarumi Shah Rukh Khan ya kasance mutum mai MatuÆ™ar biyayya ga na gaba da shi, hakan yasa jama'a da dama suke son shi fiye da wasu Jaruman. Yana girmama na gaba da shi kuma yana mutunta su sosai. Haka kuma yana mutunta na Æ™asa da shi. 

6. MUTUM BABU MUTUM IN BAI DA MATA: 

Kamar yadda wani mawaƙin Hausa yake cewa "Gida babu gida in babu mata, mutum babu mutum in bai da mata". Tabbas wannan magana haka take, domin kuwa Jarumin ya fahimci Muhimmancin mace a rayuwar sa kuma yayi aure tun da sauran Ƙuruciyar sa. Hakanan kuma matar Jarumi Shah Rukh Khan watau Gauri Chibber Khan ta bashi gudunmuwa sosai a rayuwar sa. Duk da kasancewar sa mutum mai tsoron mata, hakan bai hana shi girmama su ba. Duk duniya ta aminta da cewa yana ɗaya daga cikin Jarumai mafiya kyawawan Ɗabi'u da kuma ɗa'a ga mata. A shekarun da suka gabata ne ma ya fitar da wani tsari na duk fim ɗin sa da zai fitar, to lallai a fara saka sunan Jarumar da zasu fito tare a cikin Fim ɗin kafin Nasa saboda girmamawa.

Zan Ci Gaba In Shaa Allaah. 
<••••••••••••••••••••••••••••>
  Hãïmâñ Khãñ Řăééş_* <••••••••••••••••••••••••••••>
 08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
 Instagram: Haimanraees 
 Infohaiman999@gmail.com


Post a Comment (0)