BAYANI AKAN ZUMA (HONEY)

BAYANI DANGANE DA SIRRIN ZUMA


haƙiƙa ita zuma tana daga cikin manya-manya abubuwan da ake magani da su kuma itama kanta magani ce domin ya zo a cikin ALƘUR'ANI mai girma.

Inda Allah (S.W.T) yake cewa:

"Yana futowa daga cikinta (ita zuma) wani abun sha Wanda yake mai launuka daban-daban Haƙiƙa a cikinsa akwai waraka ga mutane.

Yana daga cikin kalar zuma

Farar Saƙa
Baƙar Saƙa
Da sauransu.

Kuma ko wacce tana da magani ta

Haka nan yazo a cikin hadisi Manzon Allah (S A W) yana cewa : na hore Ku da ababan waraka guda biyu (2) ZUMA DA ALKUR'ANI
(ibn majah da Hakim suka ruwaito )

Bayan haka an ruwaito cewa: wani mutum yazo wajan Manzon Allah (S.A.W) ya ce :
" yaa Manzon Allah nazo ne in gaya maka cewa dan uwana yana fama da ciwon ciki, sai Manzon Allah ya ce jeka ka shayar da shi zuma, sai ya Tafi ya shayar da shi zuma amma bai warke ba, sai ya koma wajen Manzon Allah (S.A.W) ya sake cewa jeka ka shayar da shi zuma, sai ya je ya shayar da shi, amma bai warke ba, sai ya komo wajen Manzon Allah sai Manzon Allah yace da shi hakika Allah yayi gaskiya cikin dan uwanka yayi karya, jeka ka sake shayardashi zuma, da yaje ya sake shayar dashi zuma sai ya warke.

Wannan hadisi yazo cikin bukhari da Muslim

Hakanan wannan yana daga cikin abun da ya kamata mu fa'idantu da shi cewa shi magani ba'a yi masa gaggawa, Ana so adinga mai-maitawa da haka har ubangiji ya kawo saukin cutar.

Hakanan yana daga cikin sirrin zuma zaka ga yawan cin magani Ana cewa hada shi da zuma farar saka.

        YARO

➽ yana daga sirrin zuma in an haifi yaro ya Kai kamar wata hudu (4) kullum a dinga diga masa a baki sau uku (3) a Rana saboda ta Kara masa wayo da basira da kaifin hadda in ya girma.

Sannan tana sa kashinsa ya Kara kwari.

        MAI JEGO

➜ yana daga sirrin zuma mace mai jego ta dinga shan zuma a kullum itama sau uku (3) a Rana , kafin ta haihu da bayan ta haihu saboda samun cikakkiyar lafiya da ita da yaronta.

        CIWON CIKI

 yana daga sirrin zuma idan mutum yana fama da yawan ciwon ciki mai daurewa, ya dinga karanta ayatul-kursiyyu kada (7) a cikin zuma yana sha a kullum in sha Allah zai rabu da shi.

      YAWAN KUKAN YARO

➜ yana daga sirrin zuma idan yaro yana yawan kukan banza na babu gaira babu dalili ko yawan kuka idan ya farka daga bacci sai a samu zuma mai kyau marar hadi a tofa BISMILLAH (9) a dinga bashi ya lasa insha Allah

  NUTSUWA KO HUTU

➜ yana daga sirrin zuma idan mutum yana so yasa mi natsuwa da Hutu da nishadi kyakkyawa a cikin kokon zuciyarsa ya dinga shan zuma tare da man habbatussauda da safe da kuma kafin yaya kwanta bacci.

      MACE MAI HAILA

➜ yana daga ainihin gudarin sirrin tatacciyar zuma ga mace mai haila da ta samu ta dinga samun ruwan zafi kofi daya (1) ta zuba zuma a ciki ta dinga sha zata ji banbanci.

           TASHIN ZUCIYA

➜ idan mutum zuciyarsa tana tashi da zarar yaji zata tashi, sai ya dibi zuma cikin cokali daya ya sha insha Allah .

           CIWON HANTA

yana daga sirrin zuma dan magance ciwon hanta, shi ciwon hanta yana da alamomi yawan kasala ko da yaushe yawan jin bacci da yawan amai da kuma yawan jin ciwo a kirji, sai a samu zuma da lemon tsami da man zaitun a hada guri daya a dinga diba Ana sha sau uku(3) a Rana insha Allah

      HAIHUWA CIKI SAUKI

➜ hakanan yana daga sirrin zuma a haihu cikin sauki , in Ana nakuda asha zuma kamar cokali goma sha biyu (12)

            WARIN BAKI

➜ yana daga sirrin zuma dan Hana warin baki kullum mutum yasha da safe bakinsa zai daina wari.

    FITSARIN KWANCE

➜ yana daga sirrin zuma fitsarin yara na kwance, sai kullum a dinga basu zuma sau biyu (2) a rana zasu daina insha Allah.

            CIWON

Haka nan yana daga sirrin zuma dan magance ciwon da ya Dade bai warke ba sai a dinga shan zuma Ana kuma shafawa a wajan ciwon.

NAUYI ABINCI

yana daga sirrin zuma sha bayan cin abinci.

Post a Comment (0)