UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA TALATIN DA UKU
Huce mai zafi yake fesarwa kamar wani kumurci. tashi yayi tsaye daga kan kujerar dayake zaune yana bugun Table din dake gabansa idanuwansa sunyi jajir kamar wanda aka yiwa sirace da barkano.
"Alhaji Abdulwahaab na fada maka ka fice mani daga cikin Office in kuma ba haka zan yi maka abin da baka taba zato ba".
Ya fadi yana mai kara turbuÉ—e fuskarsa kamar zai cinye shi danye.
Murmushi Alhaji Abdulwahaab yake saki mai cike da bakin ciki da takaici wai yau har shine Dr.Erena zai dubi tsabar idanuwansa yana fada masa magana son ransa kamar wani wanda ya zo maula wajansa numfashi ya ja kafun ya dubi Dr.Erena sosai yana mai gyaÉ—a kai wani irin tukuki yake ji zuciyarsa nayi ba abin da yafi bata masa rai kamar yarda Dr.Erena ya zage yana keta masa rashin mutum bai taba tsammanin haka ba bai taba kawo wa kansa haka ba bai yi tunanin duk rashin mutuncin Dr.Erena zai iya yi masa.
"Dr.Erena ni...".
"I Say get out now i don wanna see you in my Office".
Dr.Erena ya fadi a zafafe yana kara so wa wajansa har yana tunkuÉ—ashi.
"Ka je kayi abin duk da zakayi kudi ne na cinye in akwai wanda ya isa ya kwatar maka ka turo shi tunda naga abin naka hauka ne har nawa ne kudin naka da zaka zo kana yi mani ihu kamar wani kare a cikin Compay".
Mamaki ne ya sake kume Alhaji Abdulwahaab jin zuciyarsa yake yi kamar zata faso kirji tayo waje gabadaya saboda tsabar tsananin bakin ciki dake nukurkusar sa hannunsa ya kai ya saukar da na Dr.Erena dake kafadarsa fuskarsa da wani murmushi kafin ya fara taka kafafuwansa a hankali har ya isa bakin kofar hannunsa saman Handle din ya juyo ya dubi Dr.Erena cikin wani irin kallon wanda shi kansa Dr.Erena sai da yaji wani iri a zuciyarsa amma bai bari hakan yayi tasiri a fuskarsa ba sai ma wata uwar harara da yake cilla masa.
A daidai lokacin da ya tura kofar domin fita ita kuma Areefa ta sanyo kai cikin Office din saura ka dan suyi gware dashi amma tayi saurin kauce wa don a tunanin ta Dr.Erena ne.
"Yaa Allah".
Ta furta tana duban Alhaji Abdulwahaab da wani irin yanayi mai kama da tuhuma kafin ta dubi Dr.Erena da yake faman cika yana batsewa kamar zai tarwatse ganin Areefa ya sanya shi ware idanuwansa sosai mamaki na kokarin ka kashe shi ganin Areefa yau a cikin Office din sa How Comes yace ya manta rabon da ya ganta ko sashin sa ta zo amma yau ita ce a bangaren sa abin mamaki lokaci guda jikin sa ya shiga rawa ya fara takowa izuwa gareta a daidai lokacin ta juya ta dubi Alhaji Abdulwahaab yanayin da ta ganshi a aciki ya tabbatar mata akwai abin dake faruwa bata karasa tsinkewa da lamarin ba sai da ta ga Alhaji Abdulwahaab ya kashe mata idanu daya hakan ya kara jefata cikin wani irin yanayi mai girman gaske na mamaki.
"Nace ka fice mani daga Office, ko sai na saka an fitar da kai a rashin mutunci ne?".
Dr.Erena ya sake fadi a zafafe ganin irin kallon da Areefa ke yi masa juyawa yayi ya dube ta yana faman sakin Murmushi kamar tsohon da aka bashi kyautar budurwa.
"Areefa ban yi zato ba...".
Hannu ta daga masa alamun bata so fuskarta a tsuke.
"Haba mana Dr.Erena me haka kayi wanda sam bai dace ba abokin ka ne fa wanda bai kamata ace irin haka ya faru a tsakaninku ba".
Ta fadi tana mai dubansa kafin ta dubi Alhaji Abdulwahaab wanda a daidai lokacin yake ficewa daga Cikin Office idanu ta kashe masa kafin ta juyo da kallon ta zuwa wajan Dr.Erena fuskarta da alamun damuwa.
"Ban san haka wasu in suka gani ai sai su yi muku dariya".
Wani gundumeman tsaki ya ja gami da kau da kansa.
"Bar ni kawai Areefa raina min hankali zai yi ni kuma a rayuwa ta abin da bana so kenan komin kusanci na da kai in har kace zakayi mani akuyanci to wallahi ba zan kyale ka".
Sosai ta gano in da lamarin ya dosa amma cikin basarwa da kin ba wa zancen muhimmanci ta dube shi.
"Good and Fine ina son mutum haka mai ra'ayi irin naka na rashin son daukar raini".
Ai ji yayi kamar ta cilla shi a gidan aljanna haka ya shiga yashe baki kamar wani bugun shaho da sauri ya dube ta cikin rawar jiki yana yi mata nuna da ta zo ta zauna a hankali ta fara taka kafafuwanta idanuwanta na kansa kallon sa take yi da wani irin kiyayya mai girman gaske dubansa take yi da wani irin haushi da takaici zuciyarta take ji tana wani irin kartawa kamar zata faso kirjinta ta fito saboda tsabar tsanar sa da take ji a duk wani sashi na zuciyarta.
'Ni yake so wai da aure'
Ta ji wani sashi na zuciyarta na fadin haka ji tayi kamar ta daura hannu aka ta kurma ihu don bakin ciki amma ina bata so ta bata shirinta ba ta so ta bata salon da Hajiya Layla ta karanta mata tayi amfani dashi bata so ta samu wata É“araka daga wannan KUDIRIN nata da take kokarin cin masa.
Isa tayi cikin takunta wanda yake kara fizgar Dr.Erena yana jefashi cikin wani irin hali na matsanancin son ta sosai ya firgice cikin lokaci kalilan sai kai kawo yake yi yama rasa abin da ya dace yayi sai kai kawo yake yi yana dube-dube sannan ya juya ya janyo kujera kamar zai zauna sai kuma ya fasa ya shiga sakar mata murmushi ita kan ta sai da taji wani iri na daban da yanayin da yake nuna wa amma zuciyarta wani irin kunci take jefa ta a duk lokacin da ta kalle shi ji take yi kamar ta tashi ta shake shi ya mutu kowa ya huta sai dai wani sashi yana gargadin ta da wannan kudirin nata na kisa wanda sam bai dace ace tana sanyo shi a lissafin ta ba.
"ka zauna mana gabadaya duk ka wani rikice sai kace wanda aka kama da satar butar masallaci".
Sai a lokacin ya tsaya da kai kawon da yake yi ya janyo daya daga cikin kujerun dake girke a gaban Table din ya zauna yana fuskantar ta.
"Nayi mamaki matuka da ganin ki Areefa na dauka har yanzu ba a yafe mani gingimeman laifin da nayo ba".
"wa yace kayi laifi?".
Ta tare shi tana mai sakin wani yake da BAI KAI ZUCI BA.
"Uhmm dole nace haka mana Areefa yaushe rabon da ki tsaya ki saurare ni yaushe rabon da ko alfarmar kallon arzuki na samu a gareki muna Company daya amma har ki shigo ki gama abin da zaki yi ba ki dubana da kallon arzuki in ma nayi miki magana sai ki nemi dizga ni don kawai na nuna ina son ki ban san laifin da nayi har ya kai haka ba ban san me nayi miki da kika tsanani har haka".
Runtse idanu tayi jin ya ambaci kalmar 'ina son ki' wani takaici da makakin bakin ciki taji sun taho sun tsaya mata a zuciya wani abu mai nauyin gaske taji ya zo saitin kirjinta ya zauna numfashin ta taji yana sama da kasa kamar zai katse.
Sosai taji ba za ta iya cigaba da zama cikin Office din nan ba sosai take ba za iya kara ko da minti guda bane tare da Dr.Erena komai zai iya faruwa sosai zuciyarta ke tururi sosai take ji kwanyarta na juya wa.
A hankali ta mike kan kafafuwan ta tana jin yarda kanta ke sarawa da wata irin tsana ta Dr.Erena bata zaton zata iya juri zuwa gareshi bata zaton zuciyarta za ta barta tayi abin da ya dace sosai take jin ina ma ace ta kashe shi shine kawai hanya guda da take zaton samun nasararta a akansa amma ina hakan sam bai dace ba bai dace ace zuwa wannan lokacin ace ta kashe shi ba ba ita kadai ke bukatar Dr.Erena ba ba ita kadai bane a filin duniyar nan take son daukar fansa akan sa mutane da yawa wanda ba ta san a dadin su ba suna BURI da KUDIRI mai girman gaske akansa sai dai rashin WATA DAMA da ba su samu ba amma gata ita ta samu amma tana kokarin ruguza komai.
"Areefa ya dai ba dai tafiya zakiyi ba?".
Muryar Dr.Erena ta doki kunniwanta ba ta san ma ta fara tafiya ba sai da taji amonsa sanna ta dawo hayyacinta har ta kai bakin kofa da sauri ta juya ta dube shi fuskarta da wani irin murmushi wanda ita a karan kanta ba ta san ma tayi ba sam! ba tare da tace dashi komai ba ta buÉ—e kofar ta fita.
Fitar ta ke da wuya Dr.Erena ya mike cikin hanzari fuskarsa na kara haÉ—ewa waje guda wayarsa ya janyo ya shiga danna kira yana mai kaita saitin kunnuwansa sai faman numfashi yake ja.
"Bobby".
Ya fadi da wata irin murya kafun ya dora da fadin.
"Ina son ganin ku anjima a gida".
Daga nan bai sake cewa komai ba ya sauke wayar yana mai sakin wani murmushi na mugunta yana murza gashin gemunsa.
"Alhaji Abdulwahaab".
Ya furta yana mai hade hannayensa waje guda yana lankwasawa.
******
"Meye amfanin haka da kayi Alhaji Abdulwahaab baka tsoron Dr.Erena ya turo a kashe ka don karka kawo masa tsaiko cikin lamarin sa kai fa da kanka ka fadi mani ko waye ya zo masa da rainin hankali ko yana kokarin tona masa asiri kashe shi yake yi amma kai kayi gangancin tunkaransa akan wani dalilin?".
Areefa ta fadi tana mai duban Alhaji Abdulwahaab da takaicin duniya ya ishe shi sai faman huci yake yi kamar wanda zai hadiyi zuciya ya mutu.
Mikewa yayi tsaye ya shiga kai kawo sai faman kai wa iska naushi yake yi kamar da ita cikin wanda suka bata masa rai juyawa yayi ya dubi Areefa ita ma idanuwanta na kansa hannun ta rike da Glass Cup a hankali take kurbar lemon da yake ciki.
"Areefa ya kamata ki san wani abu wannan abin da ki ga nayi masa so nake yi na kara tunatar dashi cewar ina nan fa ban matan abin da ke tsakaninmu ba don na lura sam ya mance wani abu da ya shiga tsakanina dashi ba wai nayi bane don neman hakki akan sa a,a nasan ma ba samu zan yi ba nayi hakan ne don ya sani ina nan kuma komai daren dadewa sai ya bani hakki ba zai ci bulus ba".
"Wannan ba magana bace Alhaji Abdulwahaab".
Areefa ta katse shi da fadin haka kafun ta dora da cewa.
"Ko Shakka bana yi yanzu haka nasan yana nan ya na kokarin bin hanyar da zai kawar da kai a filin duniyar nan kar kayi tunanin ABOTA da ta ratsa tsakaninku zatayi wani tasiri a gareshi na rantse maka da Allah yarda da lura da Dr.Erena duk da dai kafi ni saninsa amma ina da zaton ko kaninsa ne zai kawo masa wasa zai iyayi masa komai Dr.Erena MUGUN ABOKI ne a gareka domin kuwa ba ya bukatar ace ka samu cigaba yarda yake yi maka yana nuni da cewa da ma can abin ka yake so".
Runtse idanu yayi yana kai komo zuciyarsa yake ji tana zafi bai taba zaton Dr.Erena zai masa haka ba bai taba zaton ko da a mafarki ne haka zata faru ba.
"Shikenan Areefa amma don Allah ya kamata ace zuwa yanzu kin san komai game dashi lokaci tafiya yake yi a ko wani lokaci zai iya gano ke wacece tsoron abin da zai je ya dawo bana so ayi BIYU BABU ba wan ba kanin karatun dan kama".
Wani murmushi ta saki kafun ta juya idanuwanta.
"Alhaji Abdulwahaab".
Ta fadi cikin wani irin yanayi tana mikewa kan kafafuwanta da wani irin ƙarfi da take ji yana taso mata tun daga zuciya da rushi ajiya Cup din dake hannunta tayi kafin ta dauki jakarta dake kan Table din da suke zaune a hankali ta fara taku kamar ba zata ce dashi komai ba juyawa tayi a hankali har zuwa lokacin da murmushi a fuskarta da BAI KAI ZUCI BA amma yana tattare da abubuwa masu yawa.
"Yanzu za a fara Alhaji Abdulwahaab ka shirya zaman kallo".
Ta fadi tana mai kashe masa idanu kafin ta juya ta cigaba da tafiyarta cikin sassarfa.
Hannu ya daga ya jinjina mata yana hango gaskiya a batunta yana hango kudiri da buri da ta dauka akan Dre.Erena abin da yake so kenan dama kuma tsaf ya shirya duk yanayi sai ya ga yarda wasan nan zai kare kamar yarda ta fada amma kuma dole ya ja baya da Dr.Erena kamar yarda Areefa ta fadi ya san dole ya farauce shi a ko wani yanayi zai iya yi masa bazata.
*******
Kai kawo kawai take yi cikin tsakiyar falon gabadaya kanta ya gama kullewa tunaninta take ji ya cak! ya daina tafiya yarda ya kamata numfashi take ja a hankali tana dukan hannunta da dayan idanuwanta sun kaÉ—a sun yi jajir kallo daya zakayi mata ka gane tana cikin damuwa matsananciya da tarin KALUBALE.
Sosai take ji a ranta lokaci yayi sosai take jin komai na dawo mata kamar yarda ya faru a shekarun bayan komai zuwa mata yake yi komai kallon sa take yi a yanzu yake faruwa ba TUNA BAYA bane runtse idanuwanta tayi zuciyarta da wani raÉ—aÉ—i da zugi ga wani bugu da take yi kamar zata faso kirji ta yo waje.
Zubewa tayi kan kujera ta mai jan numfashi wasu kwalla suka cika mata idanuwa hannun bibbiyu ta dafe kanta da take ji yana barazanar tarwatsewa.
"Yaa Allah".
Ta furta cikin wani irin yanayi matsananci duniyar take ji tayi mata zafi da kunci komai take ji babu dadi a hankali ta kuma mikewa hannayenta goye a bayanta ta cigaba da safa da marwa so take yi ta tunano abin da ya dace tayi so take yi zuciyarta ta kawo mata wata satar ansa da za tayi mata amfani so take yi kwanyarta ta binciko mata wani abu mai girman gaske da ya dace ace shi ya kamata tayi.
Motsin kofar da taji ne ya sanyata saurin juyawa Areefa ce ta gani tana kokarin shigowa cak! ta tsayar da idanuwanta akan ta sosai take jin komai na sake dawowa mata kamar yanzu ya faru wani tunani taji ya zo mata a bazata runtse idanu tayi tana mai sake buÉ—e su akan Areefa gabatan taji yayi wani irin dokawa da abu mai girma.
'Anya kuwa?'
Ta fadi a can cikin ranta tana mai girgiza kai a daidai lokacin Areefa ta iso gareta tana mai dubanta.
"Ya dai Maama ko jikin ne?".
Ta fadi tana mai yawatawa da idanuwanta akanta.
Girgiza ka tayi alamun babu komai hannunta ta riko tana mai sarkewa cikin nata da wani irin yanayi mai girman gaske da sauri Areefa ta bude idanuwanta tana kallon cikin yanayi na alamun son sanin wani abu murmushi tayi mata kafun ta jata suka zauna waje daya suna fuskartar juna zuciyar Areefa sai kai kawo take yi so take yi ta san abin da ke faruwa domin ta hakiƙance yanayin da take ganin Hajiya Layla a ciki ya tabbatar mata akwai matsala bata saba ganinta cikin wannan yanayin ba duk da boyewar da take yi na abin dake damunta amma ita a jikinta taji kamar akwai wani abu mara dadi dake shirin faruwa.
A hankali ta shiga motsa laɓɓanta idanuwanta akan Hajiya Layla da sai faman yak'e take yi kamar wacce akayi wa dole zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi na tashin hankali tsoro take ji tsoro mai girman gaske tana son tayi wa Areefa magana amma zuciyarta na gargadinta akan haka bata san ya zata dauki lamarin ba bata san ya zata fuskata ba tsoronta daya lamari ya maimaita kansa bata son haka bata son abin da zai sake dawowa a matsayin WAIWAYE sosai ta sani Areefa zata tashi hankalinta ita kuwa a filin duniyar nan abin da ta tsana kuma take gudunsa kamar shiga damuwar Areefa bata so ace ta sanadinta wani abu ya same ta so take yi ace har karshen rayuwarta ta dauwamar da Areefa cikin farinciki da muradan jin dadi amma Ta ya ya hakan zata kasance?.
'Bata sani ba'.
Zuciyarta ta fadi duban Areefa tayi akaro na ba a dadi wacce gabadaya ta gama shiga yanayi lokaci guda jikinta yayi sanyi sosai.
"Maama wai meke faruwa ne don Allah sosai naji gabana na faduwa fa don Allah fada min".
Ta fadi tana mai kara matse hannunta a na Hajiya Layla.
"Ban san ya zance miki ba, ban san ta ya ya zan fuskance ki ba, sosai nake jin rashin jindadi sosai zuciyata ke bugawa ina tsoron abin da zai je ya dawo, ba na son ace ta sanadina kin sake fadawa halin damuwa bana so nayi miki Waiwaye...".
"Maama!!!".
Areefa ta fadi da sauti mai girma a muryarta kafun ta sake motsa laɓɓanta kamar zata yi kuka.
"Don Allah mene ne? Ki fada min zuciyata sosai take bugawa Allah taba ki ji".
Ta karashe tana mai dago hannun Hajiya Layla tana kaiwa saitin inda take zaton zuciya na ajje.
"Areefa wani abu nake so na tambaye ki guda daya kwal! Amma kuma ban san yarda zaki dauki lamarin ba ban san da wacce fuska zaki anshe ni ba...".
"Kawai ki fadi koma mene ne zan dauke shi a yarda ya zo mani nayi miki alkawari".
Ta fadi da murmushi na kara karfin gwuiwa ga Hajiya Layla don ta lura da ita sosai yanayin ta ya sauya kamar da tsoro akan abin da take so tambayar ta akai.
"Zaki iya tuna ranar da muka dauko ki daga gidan marayu?".
Yanayin da take furta kalmomin da yarda bugun zuciyarta ke sauyawa ya sanya Areefa kureta da idanuwa kanta taji lokaci guda ya ansa wata kara mai girman gaske kirjinta yayi wani irin dokawa kamar zuciyarta zata faso kirji ta fito a hankali ta ji duniyar na juya mata idanuwanta lokaci guda suka shiga lumshewa da wani irin tashin hankali mai girma wani CIWON RAI mai tsanani zafi da zugi taji ya ta so mata komai taji yana dawo mata kamar yanzu yake faruwa gabadaya numfashin ta ya dauke lokaci guda ta zube jikin Hajiya Layla ganin haka da ita kuma tayi ya sanyata kwala kara mai sautin sai da falon ya ansa gabadaya cikin tsananin firgici da razana tashiga girgizata tana ambatar sunanta amma ina Areefa tayi nisa cikin wata duniya mai cike da kwazazzaben tashin hankali da sanya zuciya ciwo.
Da gudu ta mike ta isa wajan Firjin dake girke cikin falon ta buɗe gorar ruwan EVA ta sungoma tana mai balle murfin tana isowa gareta ta tuntule mata akai aiko wani numfashi mai karfi ta ja har tana sarkewa da sauri Hajiya Layla ta durkushe idanuwanta na zubda hawaye masu zafi jikin ta ba abin da yake yi sai rawa laɓɓanta na kaɗawa.
"kiyi Hakuri Areefa ban so haka ba, abin da nake gudu kenan shiyasa na ki tambayar ki ban son abin da zai jefa rayuwarki a wani yanayi ban son na sake fama miki ciwon da ya jima a zuciyarki...".
Cikin wani irin yanayi Areefa ta daga mata hannu.
"Bakomai Maama wallahi ba komai karki damu tambaye ni abin da kike bukata na san ba wai zaki tambayeni bane don cutar dani".
Ta fadi da hawaye a idanuwanta zuciyarta na wani irin motsawa da ciwo mai tsananin gaske laɓɓanta take tura cikin bakinta tana cizawa komai taji ya sauya mata jikinta take ji yana narkewa kamar ruwa.
Duban Hajiya Layla tayi wacce gabadaya ta gama rikicewa da tashin hankali ganin halin da Areefa ta shiga jikinta sai faman kaÉ—awa yake yi ta janyota jiki tana rungumewa.
"Kiyi Hakuri Areefa...".
"Ya isa haka Maama don Allah".
Shiru tayi jin abin da ta fadi dubanta take yi cikin wani irin yanayi na tausayawa zuciyarta na kara narkewa da kauna da tausayin Areefa.
"Shikenan na bari".
Hajiya Layla ta fadi da murmushin yake a fuskarta Kafun ta riko hannun Areefa sosai tana kwanta da kanta a kafadarta.
"Abu daya nake so ki fama min in har zaki iya tunawa Areefa kuma in har ba za ki kuma shiga yanayin nan da kika shiga yanzu ba kiyi man alkawari".
GyaÉ—a kai tayi da murmushi a fuskarta tana mai kara kwantar da kanta a kafadar Hajiya Layla.
"NAYI ALKAWARI".
Shiru ne ya ratsa falon na yan mintina ba wanda ya sake magana a cikin su sai ajiyar zuciya kawai a hankali Hajiya Layla take shafar kan Areefa tana son yin magana amma zuciyarta na tsoratar da ita akan yin maganar domin bata san abin da zai faruwa ba sai dai kuma bata da zaɓi dole sai tayi tambayar domin ita kadai ce hanyar da take hango mafita a gareta da ita kan ta Areefa din.
"Bayan fita ta daga cikin Motar Dr.Erena shin gidan sa kuka tafi ko kun biya wani waje daban ne?".
Tsoro sosai ya bayyana a fuskarta lokacin da take maganar tana jin yarda jikin Areefa ya dauki rawa lokaci guda tana kankameta ajikinta sosai taji wani irin yanayi wanda bata san ya zata misaltashi ba game da Areefa lokaci guda taji gabanta ya yanke ya fadi da tashin hankali.
"Areefa".
Ta kirata muryarta na rawa.
"Na'am Maama".
Ta ansa ta da son nuna ba komai amma yarda take ji a zuciyarta da ruhin ta kamar an dauko KASKO WUTA an juye mata haka take jin kirjin ta na wani azabar zafi runtse idanu tayi kafun ta motsa baki.
"Ba gidansa muka je ba wani daji muka nausa sosai ya kaini wani gida wanda shi kadai ne a wannan lokacin...".
Da hanzari Hajiya Layla ta dagata tana dubanta bakinta har rawa yake yi.
"Kenan ba gidan sa ya kai ki ba ko to gidan da kike ce kun je din waye a cikinsa?".
Runtse idanu ta sake yi idanuwanta na kawo kwalla.
"Haba mana Areefa karki yi kuka kin yi mani alkawari".
Hannu ta saka ta dauke hawayenta kafun ta shiga bata labrin abin da ya faru shekaru masu dama da suka shuÉ—e.
Kuka sosai Hajiya Layla take yi zuciyarta da ruhinta na zafi sosai ta rungumi Areefa ita ma da take kuka a hankali ta mike fuskata da murmushi mai tsananin ciwo.
"Shikenan Areefa ina so duk runtsi duk wuya karki sake daidai da rana daya Dr.Erena ya san nan gidan sannan ko yace yana so ya gana da iyayenki kice masa zakiyi shawara ki zo ki same ni don nasan nan da dan lokaci ya bukaci son ganin iyayenki domin neman auren ki auren da nake so ayi sa...".
"Maama".
"Shiru Areefa kiyi abin da nace kawai".
Daga nan ba wanda ya sake magana a cikin su Hajiya Layla sai safa da marwa take yi a tsakar dakin ita kuwa Areefa kwance tayi luf! tana jin yarda tsana da kiyayyar Dr.Erena ke kara samun masauki a filin zuciyarta KUDIRI tayi tare da Alkawari duk runtse sai taga bayan sa a filin duniyar nan..
*_KAMALA MINNA_*😘😘