UKU-BALA'I 34

UKU-BALA'I

NA

KAMALA MINNA

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA TALATIN DA HUDU.

A firgice ya farka daga barcin da yake yi mai dauke da wani RIKITACCEN AL'AMARI wanda ya kusan sanya zuciyarsa da kwanyarsa daina aiki na wucin gadi sosai ya firgita da mafarkin barcin da yake jin sa kamar a zahiran ce ne ya faru ba wai a badinance ba.
Da sauri ya zuro santala santalar kafafuwansa da hutu ya gama yi musu ƙawa a hankali ya sanya takalmarsa da suke bakin gadon ajje masu matukar kyau da burgewa kallo daya zakayi musu ka gane na zallar fata ce.
Mikewa yayi kan kafafuwansa jikinsa sanye da Boxer wanda ya kawo masa har gwuiwa sai singilet mai kalar ash-colour wanda tayi matukar kama jikinsa ta bayyanar da cikar halittarsa ta mazantaka yana da damatsa da budadden kirji sosai mai dauke da kwantaciyar suma mai santsi kugunsa kuwa ba shi da fadi sosai ya dan tsuke kadan.
A hankali ya dauko jallabiyarsa mai ruwan jinin kare dake rataye ya sanyawa jikinsa wanda hakan ya kara haskakashi matuka Toilet ya nufa ya wanke baki sannan ya watsa ruwa sosai kafin ya fito ya shirya cikin Suit baka sosai ya gyara sajensa gami da tararren gashin kansa gyararre in ka gani sai ka rantse Shampoo ya saka masa amma ko kadan haka sufarsa take baka sidik sai sheki da take yi sosai ya ke kula da ita wajan gyara kwantattacen sajensa shima haka fuskarsa ta fito fes da ita manyan idanuwansa da dogon hanci gami da bakinsan dan madaidaici sun yi matukar tasira wajan kara ƙawata fuskar tashi.
Cikin hanzari ya gama shirye shiryensa kafin ya dauke Berifcase dinsa da sauran karikitan sa ya fice daga cikin dakin ya kulle can harabar gidan ya nufa in da motarsa take park-space tun kafin ya isa gareta ya danna mata Remove ta saki wani dan sauti tare da dallo wasu kalolin haske masu kayatarwa isa yayi ya bude ya shige yayi mata key kafin ya danna Remove dan madaidai cin Get din gidan ya buÉ—e kansa da kansa ya cilla motar zuwa waje cikin yanayi na kwarewa a tuki yana ficewa Get din ya koma ya rufe kansa.
Gida ne dan madaidai na zaman mutum daya kirar gidan da ka ganshi zaka gane gine akayi sa na burgewa kuma na zaman yan gayu.
A hankali yake tuki yana jin yarda zuciyarsa da kwanyarsa suke kokari rakito masa lamarin da ya faru dashi a barcin sa da ya tashi a wayewar garin yau sosai ya ji zuciyarsa na kai kawo idanuwansa na buÉ—ewa suna wanzar masa da komai kamar yanzu komai ke faruwa runtse idanuwansa yayi yana mai daura hannunsa daya saman goshinsa a hankali yake furta.
"Yaa Allah what is wrong with me?".
Numfashi ya ja ya fesar kafin ya ware idanuwansa jin da yayi ana ta danna masa Horn sosai ya zaro idanuwansa waje ganin in da yake yayi mamaki sosai bai yi zaton ma wai tuki yake yi ba ya dauka yayi Parking domin ji da yayi akan sa a wata duniyar cikin sauri ya taka burki yana mai ambaton sunayen Allah kafun ya hada kansa da sitiyarin yana mai da numfashi.
"Yaa Allah wai shin me ke faruwa dani ne haka?".
Ya tambayi kansa tambayar da ya san ba wai yana da ansar ta ba ne komai yake ji a yau ya canza masa komai na duniya yana juya masa wani iri daban ba yarda ya sa ba ji ba zuciyarsa yake ji tana kai komo da wani lamari mai girman gaske wanda yake kokarin hana shi kwanciyar hankali da natsuwa.
Tafiya mai 'yar tsayi yayi kafun ya isa Asibitin *Fortis Escorts Heart Institute* dake birnin Delhi a nan India da yake aiki a harabar yayi parking kamar yarda sauran yan uwansa likitoci sukayi ya jima kafin ya fito daga cikin motar don kuwa jin zuciyarsa yake tana kara narkewa da wannan lamarin da bai yi zaton lamarin har ya kai har haka ba ya jima yana binnewa a zuciyarsa ya jima yana dakon lamarin yana boye duk wata hanya da zata taso masa dashi ta hanashi kwanciyar hankali sosai yake danne zuciyarsa sosai yake hakurkurta da zuciyarsa akan lamarin da yake zaton ba zai taba kasancewa ba ko da kuwa ba azahiri bane ya raina lamarin rainuwa mai girman gaske amma a yanzu a wannan ranar a daidai wannan lokacin komai na shirin canza masa komai na shirin juye masa komai na shirin birkice masa ba tare da zato da tsammani ba.
A hankali yake takawa idanuwansa na bin sashi da sashi na cikin asibitin har ya isa babbar kofar da zata sa dashi da Reception din.
Kallo daya zakayi wa asibtin ka gane babba ne sosai domin akalla benensa zai kai hawa biyar zuwa shida cikin asibitin kuwa ko ina malale yake da tayal mai matukar daukar idanu da burgewa yanayin tsarin ma'aikatan dake zirga-zirga da kai komo kawai in ka kalla zaka gane ba karami asibiti bane lura da yanayin sa na kudi ne (Privet Hospital).
Haka Dr.Karami ya shiga taka kafafuwansa cikin asibitin ko wani bangare yabi sai ya daga masu hannu suma suna daga masa suna mai furta 'Morning' komai da yake cikin sauri yake yin sa saboda lura da yayi ya kusan makara sosai a haka har ya isa bangaren da Offices din sa yake da hanzari ya buÉ—e ya shiga yana mai yasar da Brifcase dinsa saman Table din tare da sauran hargitsen dake hannunsa danginsu waya da key.
Rufe idanuwansa yayi yana mai jan numfashi kafun ya isa kan kujerarsa yana mai cire Coat din saman suit dinsa yana mai rataye ta jikin kujerar zama yayi sosai yana mai jujjuyawa hannayensa saman kan sa jinsa yake yi a wani mataki na musamman wanda tunda lamarin yake faru dashi bai taba yi masa tsamari kamar na yau ba sosai yake jin zuciyarsa na ansawa kwanyarsa na rikicewa da lamarin da ya dauka ba mai sauki bane gareshi sosai yaji a daidai wannan lokacin ya na bukata komawa gida sosai yake jin zuciyarsa ta shiga azalzalarsa da ya tashi ya tafi sosai kwanyarsa ke tunano masa kasar sa.
Numfashi ya ja mai zafi yana fesar wa kafin ya mike tsaye cikin wani irin yanayi mai matukar razana zuciya da ruhi Table din dake gabansa ya kai wa bugu wanda sai da kayan da suke kai sukayi rawa sosai a hankali ya shiga safa da marwa cikin Office lokaci guda wani gumi yaji yana ke to masa wanda bai san ta ya ya hakan ya faru ba hannunsa ya dungule waje guda yana mai sakin wani numfashi mai zafi.
Kofar da yaji an taɓa ne ta sanya shi saurin juyawa ya fuskance ta idanuwansa a lokacin sun fara canzawa suna lumshewa kamar me jin barci.
"Dr.Vijay".
Ya fadi can kasar makoshinsa cikin halin damuwa.
Murmushi ya sakar masa yana mai karasowa inda yake tsaye hannu ya mika masa.
"Kayi latti yau zuwa na kusan uku ban samun ka abin ya bani mamaki ban san ka da haka ba ban san ka da latti a wajan aiki ba domin kai sam baka African Time kamar mu Why?".
Ya fadi yana mai sauke idanuwansa sosai akan na Dr.Karami da yayi masa kuri kamar mai son fahimtar wani abu game dashi kafin ya kau da idanuwansa yana mai jan numfashi mai zafin gaske wanda yake ji har zuciyarsa tururinsa na kai masa yana haifar masa da wani irin yanayi a ƙasar ruhinsa.
Sosai Dr.Vijay ya lura da yanayin da yake ciki kamar akwai abin da ke damunsa bisa lakari da yayi da yarda idanuwansa da fuskarsa suka canza lokaci guda kamar ba nasa ba hannu ya kai ya dafa kafadarsa murya a tausashe.
"Dr.Karami something is wrong with you I think?".
Ya fadi yana mai kuresa da kallo.
"I don No but Dr.Vijay...".
Hannu ya daga masa kafun ya ja hannunsa su karasa wajan kujerun dake fuskartar juna guda biyu na tsakiyar Office din zaunar dashi yayi kafun shima ya zauna ya na mai dubansa sosai yanayin sa kawai yake karanta da yanayin Emotion din sa gami da Tension din sa da suka sauya sosai da sosai hannunsa ya kamo ya sarke a tsakanin nasa.
"Me ke damun ka Dr.Karami?".
Ya tambayeshi gami da kuresa da idanu.
Girgiza kai ya shiga yi kafin lokaci daya ya mike yana kwace hannunsa.
"I Need To Go Home Right Now".
Ya fadi yana mai dafe kansa da wani irin numfashi da yake fesar wa mai zafin gaske gabadaya ya rikice lokaci guda zuciyarsa yake ji ta azalzalsa ji yake yi kamar zata tarwatse jin komai yake yi na jikinsa kamar zai narke kawai gida yake so ya koma kasar sa yake bukatar ya gansa a ciki baya so ya kara ko da kwana daya ne ba ma kwana daya ba ko awa daya baya bukatar ace ya kara jin sa yake yi kamar in ya cigaba da zama zuciyarsa zata buga a ko wani lokaci zuciyarsa ta gaji matukar gajiyawa.
"What? Dr.Karami you need to go home? Akan wani dalili?!".
Mikewa yayi kan kafafuwansa yana dubansa cikin wani irin yanayi na mamaki da tu'ajibi kafin ya shiga nuna sa da hannu.
"Anya kalau kake kuwa da alamun akwai abin dake dawainiya da kai in ba haka ba ana cikin tsakiyar aiki rana daya kace zaka tafi Najeriya wannan ba zai taba yuwuwa ba Dr.Karami ka canza tunan...".
"Dr Vijay!".
Dr.Karami ya fadi muryarsa da sauti sosai idanuwansa izuwa lokacin sun kaÉ—a matuka duban sa yake yi cikin wani irin yanayi kafun ya narkar da muryar.
"I Need Help Please ka taimaka min ina son naje gida a yau din nan ba zan iya cigaba da zama ba domin kuwa sosai da sosai nake ji a jikina kamar akwai abin da ke kokarin faruwa dani zuciya taba kaji...".
Ya fadi yana mai kamo hannunsa yana kaiwa saitin kirjin nasa yana mai lumshe idanunsa.
Ware idanu Dr.Vijay yayi sosai jin yarda bugun zuciyarsa yake sauri a ko wani lokaci yana kara sauri kamar wanda yayi matsananci gudu.
"...ina so a yau din nan na bar Delhi Dr.Vijay ina so ka saman min jirgi da zai dauke ni ya fita dani daga wannan kasar cikin mintina".
Yanayin da yake maganar a hargitse kamar wanda ya kamu da hauka ya sanya Dr.Vijay saurin rikesa yana mai bubbuga bayansa a hankali kafin ya fara magana cikin sanyin murya.
"Cool Down mana aboki na fada min meya same ka mai yasa kake so ka bar wajan aikin ka a irin wannan lokacin da ake matukar bukatar ka ya kamata ka zauna kayi tunanin kafin ka zartar da hukunc...".
"Dr.Vijay Please mana".
Ya fadi yana mai katse shi cikin yanayi na bukata sosai da gajiya da maganar da yake yi masa.
"Dr.Karami".
Dr.Vijay ya fadi yana mai sakin sa yana mai duban idanuwansa.
"...Kasan dai yau ba zaka samu jirgin ba ko duk jiragen dake tashi ba wanda zai yi wajan kasarka ko don haka ya zama dole kayi hakuri zuwa gobe...".
"Ba zan iya ba Dr.Vijay ba zan iya sake ko da awa ba ne akasar nan kawai ka taimaka min ko babu jirgin da zai tashi yau to ni kaje kayi mani Boking na jirgin gabadaya zan iya daukarsa ko nawa ne kuwa zan biya".
Ware idanu yayi sosai jin abin da Dr.Karami yake fadi kamar wanda bai da hankali.
"What? Dr.Karami jirgin ne zaka dauka zuwa kasarku...Ina hakan ba zai taba yuwuwa ba kasan kuwa ko zaka samu nawa zaka kashe...".
"Wannan ba damuwa ta bace kawai kayi mani abin da nace maka in zakayi".
"Gaskiya da matsala ba zan iya ba domin ko nace zan iya nayi maka karya".
"Shikenan Nagode".
Dr.Karami ya fadi rai bace yana mai zubewa kan kujera cikin tsananin bacin rai hannayensa duka saman kansa da yake ji yana barazanar tarwatsewa zuciyarsa yake ji tana yi masa zafi da raÉ—aÉ—i ji yake yi kamar ya farka kirjinsa ya zaro ta ya ajje ta waje.
Dr.Vijay da yayi fakare yana dubansa gabadaya yaji lokaci guda ya bashi tausayi duk da dai bai san abin da ya saka abokin nashi cikin wannan halin ba amma ya tabbata abin ba mai sauki bane sosai ya lura dashi ya fice daga hayyacin sa sosai.
A hankali ya fara takawa har iyasa gareshi kafadarsa ya dafa yana mai bubbuga masa baya a hankali.
"Kayi Hakuri don Allah duk da dai ban san abin da ke damunka ba amma na tabbata ba mai sauki bane amma kayi hakuri zuwa gobe please nayi maka alkawari jirgin farko da kai zai daga...".
Hannu ya daga masa cikin wani irin yanayi.
"Please ka rabu dani kawai tun da ba zaka yi mani abin da na bukata ba ni ma ai ba nakasasshe bane zan iya da kai na".
Da hanzari ya mike yana faman huci har lokaci hannunsa na kansa key din motarsa ya dauka yana kokarin fita Dr.Vijay yayi saurin rikesa sosai runtse idanu Dr.Karami yayi kafun ya buÉ—e su da wani irin yanayi na bacin rai a cikin su.
"Please sake mani hannu Dr.Vijay tun da nace kayi mani kace ba zaka yi ba ban ga dalilin da zai sanya ni kuma ka hanani yi ba wanda kuma bai zai taba yuwuwa bane".
"Ban san ka da gardama ba, ban saba ganin ka cikin wannan halin ba, ban san ka da zafin zuciya har haka ba, Dr.Karami karka canza yanayin da nake kallon ka dashi na mutumin kirki mai hakuri da kai zuciya nesa karka canza kallon da nake maka a matsayin mai TAWAKKALI akan duk abin da ya same ka kaifa musulmi ne ya kamata ace kana rungumar ko wani irin yanayi ka samu kan ka aciki ya kamata ace kana danne zuciyarka akan duk abin da zata bijiro maka dashi wannan tashin hankalin da ka saka kan ka a ciki bana tunanin shine maganin abin da yake damun ka ya kamata ka sassauta ka mai da komai ba komai ba sannan kayi tunanin abin da ya dace duk abin da hakuri bai bayar ba bana tunanin rashin sa zai bayar".
Juya yayi ya dube shi yana mai sakin ajiyar zuciya kafin ya ja jiki ya isa kan kujera ya zauna yana mai runtse idanuwansa gabadaya hakan da Dr.Vijaya ya gani ya tabbatar masa Dr.Karami ya fara saukowa don haka ya isa gareshi yana bashi baki da tausasa zuciya a hankali zuciayarsa ta fara rage zukin da take yi masa da rikicin da kwanyarsa take masa don ya tabbatar maganar Dr.Vijay gaskiya ne shi a karan kansa ya sani duk haukar da yake yi nacewa zai bar Delhi a yau ya san hakan ba yuwuwa zai yi ba domin kuwa ya san ba jirgin a yau sai dai zuwa gobe din.
Sun jima Dr.Vijay na bashi baki kafin ya hakura zuwa goben amma yarda yake jin zuciyar tashi kamar ba zata iya barinsa ya kai goben ba duk da hakurin da ya jona mata.
A ranar dai haka ya wuni ba tare da tabuka komai ba illa kai kawo da yake tayi a cikin Office din har zuwa lokacin tashin sa yayi a lokacin ma sai da Dr.Vijay ya sake dawowa ya din ga bashi baki har gida ya rakashe ya tabbatar da ya hakuri din sannan ya barshi sukayi sallama.
Ko da dare yayi kasa barci yayi domin gani yake yi kamar in ya kwanta din zai makara ko da dai Dr.Vijay yace zai yi masa komai kafin gobe din har da su Viza duk zai samar masa amma duk da hakan hankalin sa bai kwanta ba haka ya dinga safa da marwa da ya kwanta sai ya tashi yashiga zarya a daki daga daki zuwa falo lokaci-lokaci yana duban Agogo sam! ya kasa tsayawa waje daya kamar wanda yake fama da basir zaman ma ya gagareshi a tsaye ya dinga gangaÉ—i da yaji yana kokarin fin karfin sa sai yayi Toilet ya wanko fuskarsa ya dawo haka ya dinga yi har zuwa lokacin da barci barawo gwanin iya sata yayi awan gaba dashi bayan ya zauna a kan hannun kujera bai san lokacin da ya tuntsure a cikinta ba.
Misalin karfe hudu ya farka a firgice kamar wanda aka shekawa ruwa da sauri ya dubi Agogon falon ganin karfe hudu da yan mintina ya sanya shi ware idanu ya na mikewa cikin hanzari yayi hanyar Toilet da gudu kamar wanda gudawa take kokarin kufce masa bai dau tsawon wani lokaci ba ya fito ya shirya cikin kananun kaya da sukayi matukar amsarsa ya gyara sumar kansa da sajen fuskarsa, fuskarsa tasa tayi fayau sai idanuwansa da suka dan kumbura na rashin isasshen barci da bai yi ba karamar jaka ya dauka ya zuba abin da yake bukata na tarkacen sa kaya ko kala daya bai dauka ba bayan na jikin sa.
Wayarsa ya dauka ya danna wa Dr.Vijay kira a daidai lokaci agogo ya buga karfe biyar minti kamar uku aka dauka kafin ya dau wayar don har ya fara rawar jiki jin an ansa shi ya sanshi saurin yin magana baki na rawa.
"Morning Dr.Vijay ni fa na gama shirina ga ni nan zuwa...".
Zabura Dr.Vijay yayi daga kwancen da yake idanuwa a warwaje.
"Ka shirya kace? kai kam kalau kake karfe nawa yanzu ka sani? don Allah Malam ka koma ka kwanta don nasan da alamun ko barci bakayi ba jirgin fa ma sai biyun rana zai tashi".
Wata ashariya Dr.Karami ya dauko ya sauke.
Sai da Dr.Vijay ya tsorata duk da dai bai san abin da yace ba amma ya tabbatar abun ba mai kyau bane.
Cikin bacin rai Dr.Karami ya dora da cewa.
"Ban son wulakanci kaji ko ta ya ya zaka ka ma min jirgin rana nida nake so na tashi da safiyar nan ban so rana ta fito ta tadda ni a kasar nan".
Dariya sosai Dr.Vijay yayi kafin yace.
"Wai anya ba Amarya aka ce an baka ba kake wannan rawar jikin ni abin naka ne naga ba sauki...".
"Ka ga don Allah Malam karka bata min rai kuma ka taso kawai ka zo ka dauke ni ko kuma na fito yanzu ka ganni a gidan ka".
"Allah ya baka hakuri bani 30Mins yanzu zaka ganni".
Sauke wayar yayi yana faman tsuki jakarsa ya dauka ya fito falo duk ya kashe kayan wuta da suke jone kafin ya fito ya kulle kofar fallon sannan ya yi wa motarsa securty-Key ya samu waje ya zauna a harabar gidan yarda kasan wanda aka koro sosai ya ƙagu duk bayan mintina biyu sai ya dannawa Dr.Vijay kira tun yana dauka har ya daina hakan ya kara tunzura Dr.Karami daga karshe ma da yakira Dr.Vijay sai yaji wayar akashe hakan yayi matukar kular dashi da hanzari ya mike yana kokarin buɗe motarsa yaji Horn wata irin ajiyar zuciya ya saki kafin ya figi jakarsa yayi waje cikin hanzari Dr.Vijay ya hango yayi parking yana kokarin fitowa daga cikin motar sai da galla masa harara kafin ya jingina da motar ya harɗe hannayensa a kirji yana faman dubansa fuskarsa a tsuke a haka Dr.Karami ya kulle gidan ya karaso wajansa.
"Wai ma na tambayeka duk wannan É“arin jikin da kake yi ka nemi izini daga wajan aiki ne jiya".
Wani irin duba yayi masa kafin ya isa ya buÉ—e motar ya cillar jakarsa ciki ya juyo ya dube shi.
"Ban yi ba kai yau sai kayi mani ko?".
Ya fadi yana faman murmushin yake.
"Ai wallahi baka isa ba in ka ga na rakaka Airport to wallahi muje ka nemi izini ne".
"Yaa Allah wai shin me yasa kake son takura mani ne har haka mai yasa kake son bata min rai ne?".
"Ni ban bata maka rai nayi ba gaskiya ce na fada maka".
"Ni gaskiya at this Time ba zan iya zuwa ba sai dai ka taimaka in kaje ka nema min".
GyaÉ—a kai yayi kafun ya juya ya shige cikin motarta kafun shima Dr.Karami ya shige yana faman lallashin Dr.Vijay akan ya taimaka in yaje Asibiti ya neman masa izini gami da tafiyar da zai yi shi dai Dr.Vijay bai ce masa komai ba haka ya figi motar suka dauki hanya domin zuwa Airport.
Cikin mintina da ba su haura ashirin ba suka isa Airport jirgin karfe bakwai Dr.Karami zai hau domin keta hazo zuwa kasar sa Najeriya.
Dr.Vija sai iya shege yake masa wai bai yarda dashi ba anya rawar jikin da yake yi ba amarya aka bashi ba ya matsu yaje ya kanta.
Shi dai yaƙe kawai yake yi masa domin dai a daidai wannan lokaci. ya matsu ya ga jirkin su ya tashi ya sauka a kasarsa.
 Bakwai da minti biyar jirginsu Dr.Karami ya daga zuwa najeriya.
********
Ya mutsa fuska tayi tana mikewa kan kafafuwanta duk ta hada gumi a goshi hannunta face-face da kwabin fulawar Cake duban Umma tayi kamar za tayi kuka domin kuwa gabadaya take jin jikinta yayi sanyi da nauyi kamar wacce aka doddokewa kafadu lokaci-lokaci tana jin gabanta na faduwa wanda ta rasa dalilin haka tun da garin Allah ya waye a yau take jin ta a haka kwabin Cake din sai dakyar take yin sa jin Umma tace bazata yi mata ba ta gaji da son jikin da take yi sai kace mai laulayi.
"Don Allah Umma ki karasa min wallahi ba dadi nake ji ba a jikina".
Wani kallo ta watsa mata kafun ta dubi kwabin Cake din.
"Ai ke zan ga ranar da zaki daina son jikin nan naki wallahi kina mace amma ke gabadaya kamar wata mage ai ko mage ba zata nuna miki son jiki ba yarda ki kasan ruwa haka kike kuma ki karasa kwabin ki don ba yi maki zan yi ba ga dai yamma dai nan ta sako kai in kika bari har aka kira magrib wallahi ba zan tayaki aikin daren nan naki ba barci na zanyi".
Marere ce fuska tayi kamar zata fashe da kuka.
"Haba don Allah Umma daure ki karasa min...".
"Yaa Allah wai Mariya na tambayeki haka in kika yi aure zaki je kina wa mijin ki wannan SANGARTAR aiko tun wuri ki sauya don ba a san mace da nawa ba duk mace mai nawa sai kin same da kazanta da rashin sanin yarda zata kula da gidan auren ta".
"Naji Umma don Allah tausaya min Allah bana jin dadin jikina ne gabadaya yau din nan...".
"Sannu. ba rashin jin dadi ba kece General Hospital karewarta".
Umma ta fadi tana kokarin mikewa a daidai lokacin Mu'azzam yashigo da gudu ba in da ya dosa sai wajan kwabin Cake din ganin haka da Mariya ta yi ya sanyata saurin hanzarin cafko shi tana matse masa kunne.
"Sannu Biri sarkin barna wai kai don Allah Mu'azzam baka gani dai ka kyale sai ka bata ko to wallahi zan dinga dukan ka bar ganin Umma na goyan maka baya".
Turo baki yayi gaba kamar zai fashe da kuka Umma da ke tsaye ta shiga yi musu dariya.
"Yo cewa fa kikayi kin gaji ba sai ki barshi ya karasa miki ba ai sha yanzu magani yanzu ne Auta ba shi da jinkiri in dai wajan aiki ne yanzun nan zai yi sa yaro ba kiwa kenan".
Ware idanu Mariya tayi gami da tura baki gaba kamar zata rushe da kuka ta dubi Mu'azzam da yake kici-kicin kwace kansa ta tallake masa keya.
"Kai Umma wannan yaron naki ke kike goya masa baya kullum in zan yi kwabi sai ya nemi bata min bayan kuma in nayi duk shi yake cinye 'yar ribar".
"Kan ki ake ji miko min kwabin na karasa miki don na lura in na biye miki wannan kwabin sai ya dauko lalacewa".
Ai sai ta saki dariya da hanzari ta saki Mu'azzam ta dauki kwabin ta mikawa Umma da sauri ta shiga wake hannayenta cikin kwanon dake girke da ruwa a ciki.
Doguwar rikace a jikinta sai kallabi da ta daura kan ta dashi fuskarta fayau ba alamun kwalliya amma hakan bai hana sirrin kyanta fitowa sosai da sosai doguwar rigar ta anshe ta ta dan kamata kadan daga kugunta wanda yake cike sosai daga cikinta kuwa a matse yake kamar wacce bata cin abinci kirjinta ya cika sosai har yana kokarin rinjayarta saboda rashin ƙiɓarta doguwa ce amma ba can sosai ba jikinta kiran coca-cola ne.
A hankali ta warware dan kwalin kanta bayan ta matse daga kusa da Umma tufkanken gashin kanta ya baje sosai wanda yake ta faman sheki da daukar idanu a hankali ta shiga tattare shi a daidai lokacin wani kamshi mai dadin shaka ta ji ya doki hancinta da sauri ta ware idanu gami da kara buÉ—e hancin nata don sosai kamshin ya tafi da imaninta a daidai lokacin kuma wata murya wacce ta kusan narkar da Mariya kasa tayi Sallama wanda ya sanya gaban Mariya dokawa cikin wani irin yanayi mai razanarwa sumar tsaye tayi a daidai lokacin da ta daga fararen idanuwanta manya ta sauke su akan saitin mutumin dake tsaye cak! A kofar fuskarsa da wani irin yanayi idanuwansa dauke da wani kallon da ya sanya numfashinta kusan daukewa....

*_KAMALA MINNA_*😘😘😘
Post a Comment (0)