UKU-BALA'I 42

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA BIYU.
Sunkoyawa yayi da zubar debo ruwa a gorarsa har ya nitsar da ita sosai yana kokarin dagowa yaji ta maƙale gabadaya taki daguwa hakan yayi matukar daure masa kai shiru yayi kamar mai tunani wani abu kafin ya sake dago gorar tasa amma ina! sai yaji kamar an kara daura mata gingimeman dutse.
"Ja'e zo ka taya ni gorata ta ki hidduwa daga ruwa".
Ja'e dake tsaye yana gabzar danyen Mangwaro ya juyo ya dube shi kafin yace.
"Ban fahimce ka ba me kake nufi?".
"Zo ka gani mana don Allah".
Ba tare da ya sake cewa komai ba ya tako zuwa wajen ya dube shi sannan ya dubi gorar da tayi kasa amma ga bakinta nan.
"Jayota mana kai ma sai kace wani sakakke ya za ayi gora ta makale a ruwa?".
Sake janyota yayi amma ina taki daguwa da karfin gaske ya fizgota gabadaya yayi baya ya zube a kasa gorar tayo waje sagale da ruwan rigar mutum hadi da kansa duk sunyo waje Ja'e dake tsaye bai san lokaci da ya kwala ihu ba ya ari na kare ya falle kamar wani zomo da yan farauta suka biyo shi Iro da ya baje cikin ciyayi mai taɓo ganin abin da Ja'e yayi ya tabbatar masa akwai abin da ya gani shima cikin tsorata da firgice ya k'urma da gudu shima ko tsayawa ganin abin da ke faruwa bai yi ba gudu ya shiga yi da yake irin siraran mutanan nan ne marasa jiki ga tsayi nan da nan ya kamo Ja'e da ke ta fama haki kamar wanda ya ɓalle daga lahira ya fado duniya.
Ba su tsaya tambayar juna ba suka sake arcewa gudu sukayi sosai har sai da suka fara hango bunkokin rugar su kafin su tsagaita suna mai da numfashi Ja'e ya sunkoya riƙe da kafafuwansa yana duban Iro da yake gabansa.
"Aradun Allah Iro lahira na hango".
Ya fadi yana mai waige-waige cikin tsananin firgici da razana Iro da yake can nesa dashi ya dube shi cikin rashin fahimta.
"Ban gane ba kaifa baka da hankali wa yace maka ana hango lahira daga nan duniya".
Nishi Ja'e ya saki na wahala kafin ya tashi tsaye sosai ya dubi bayansa sa'an nan yace.
"mutum ne fa kamar gawa na gani rike da Gorar...wai hala kai baka gani bane?".
Iro da yayi shiru yana sauraron Ja'e jin abin da yace ya sanya shi ware idanu waje.
"Aradu ban gani ba kawai biyo ka nayi don na tabbata abin da ka gani bala'i n...".
A guje suka sake kwasa suna zunduma ihu kamar wasu zararru sai faman tsalle-tsalle suke kawai don sun ji motsi abu cikin ciyayin da suke kusa da ita da wannan yanayin suka karasa cikin rugar ihun da suke ya firgita mutanan cikinta nan da nan kowa ya shiga kallon su ana tambayar dalili amma ba wanda yayi kokarin tsayawa balle ya basu ansar abin da ya jefa su cikin firgicin da suka samu kan su.
Da yake rugar ba mai girma bace kallo daya zakayi mata ka gane ZURI'A DAYA ce ta hadu a wajan don bunkokin na su tsilli tsilli suke a lissafe ba za su haura goma ba.
"Iro wai kalau kuke kuwa? Wannan wani irin wauta ne da girman ku da komai amma kuna wannan shiriritar".
Tsohon da suka gilma gindin wata bunka ya shiga fadin haka cikin yanayi na jin haushin abin da ya ga sunayi don mafiyawancin lokaci haka suke indai suka dawo kiwo sun dinga nuna yarintar su ke bayan kuma a shekaru ba wanda bai haura ashirin ba kuma ko wanne da matarsa ta aure.
Ba su bi ta kan sa ba sai da suka karasa shiga cikin jerin bunkokin da suke kafun kowa ya faÉ—a bunkarsa cikin halin firgici nan da nan matan da suke wajan su ma suka tashi suna kokarin kwasa da gudu amma tsohon nan ya hana su .
"Mariye jurÉ—e don Allah karku biyewa shiriritar su Iro kun san dai halin su ba sai na fada muku ba indai daukar hakki ne sun iya shi wajan tayar da hankalin mutane".
Cak! Suka tsaya suna duban sa zuciyoyinsu na harbawa domin sun tsorata da yanayin da suka ga su iron.
"Amma Baffa kamar wannan yanayin da suka shigo dashi ya bambanta da sauran lokuta alamu ya nuna kamar akwai dai abin dake faruwa".
GyaÉ—a kai yayi yana murmushi kafun ya gyara tsayuwar malfarsa akai yana duban surukan nasa
"Nikam zan ga ranar da za ku daina daukar lamarin su Ja'e...".
Ihun da suka ji an kurma ne gabadayan su suka juya da sauri suna duban Bunkar Ja'e Asiya ce ta yo waje a guje kai ko dan kwali babu zani na kokarin kwance mata sai faman mazurai take gabadaya ta firgice.
JurÉ—e ce tayi sauri isa gareta tana rukota sosai a hannunta ganin yanayinta da firgici.
"Lafiyarki kuwa Asiya meke faruwa mai ya samu Ja'e?".
Jikinta na mazari ta shiga nuna bunkar kafun taja numfashi mai karfin gaske.
"wai gawa suka gano a bakin kogi".
Ta ida tana mai kokarin rike zanin jikinta dake kokarin subuce mata.
"Gawa!!!".
Su ka fadi su duka cikin yanayi na zaro idanuwa waje Baffa da ke tsaye tun dazu da sauri ya kwaÉ—awa Ja'e kira yana tunkarar bunkar cikin hanzari.
Ja'e dake makale cikin bunka sai faman mazurai yake yi jin muryar Baffa ya sanya shi takowa a hankali kamar wanda aka ce gawar tana biye dashi sai da ya leko kafun ya fito wani kallo Baffa yayi masa kafun ya dube shi sosai.
"Wai shin me ke faruwa ne naji matarka tace wai gawa kuka gano bakin kogi ya abin yake ne ina shi Iron yake?".
Cikin yanayi na firgici Ja'e ya hadiye numfashi mai tauri kafun ya dubi Baffan nashi.
"Aradun Allah Baffa Gawa ce Iro yaje debo ruwa a garo kawai sai ya ganta".
Cikin rashin fahimta Baffa ke duban sa kafun ya kwalawa Iro kira cikin hanzari ya fito shima yana faman mazurai har yafi Ja'e firgici ya tako ya iso matarsa na biye dashi sosai da sosai Baffa ke dubansa cikin yanayi na nazarinsa kafun yace.
"Ina jin ka me ya firgita ku?".
Rarraba idanu ya shiga yi kamar mai tsoron yayi magana gawar ta riko shi numfashi yake ja a hankali kafun ya dauke gumin da ya tsattsafo masa a goshi.
"Baffa gawa ce na gano bakin kogi naje debo ruwa to shine gorar tawa ta makale nayi-nayi ta fito amma takiya sai da nayi daƙyar sannan na jayo ta a nan ne sai ga gawar mutum ta biyo gorara".
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!".
Gabadaya suka dauki salallami suna duban Iro da yayi firgai-firgai kamar wanda suka karawa firgici Baffa yayi ajiyar numfashi mai kwari cikin rashin aminta da zancen domin shi dai ba ya ganin wannan lamarin zai tabbata tunda ba yarda za ayi ace a tsinci gawa a bakin kogi shi dai ya san tun da yake zaune a nan sama da shekaru ashirin kogin nan bai taba cin mutum ba balle yace gawar wani dan rugar tasa ce sake duban su yayi ganin har yanzu suna cikin firgici ya sanya shi nazarin son zuwa ya je ya gani domin tabbatarwa idanunsa abin da ke faruwa numfashi ya sake ajjewa kafun yace.
"Mu je na gano ni dai zuciyata ba ta gasgata maganar taku ba bana tunanin haka zata faruwa domin tunda nake ban taba ganin kogin nan yaci mutum ba amma dai..."
Sai yayi shiru yana nazarin wani abu kafun ya sake dubansu yana mai cewa su je amma cikin su ba wanda ya motsa sai mazurai suke da mamaki yake kallon su ganin ba wanda ya motsa balle yace dashi wani abu.
"Magana nake yi daku fa cewa nayi muje ku nuna min ko?".
Nan ma ba wanda ya motsa sai dakuna fuska suke yi kamar za su fashe da kuka kamar wanda ba mazaje ba sosai Baffa ke mamakin halayensu na tsoro tun da yake haihuwa bai taba haihuwa 'ya'ya maza masu bakin tsoro kamar su ba ko don suna tsakiyar mata ne oho! shi wani lokacin abin mamaki yake bashi sannan kuma ya bashi takaici musamman in yayi lakari da har iyali suka ajje amma yarinta bata bar su ba.
Tsuke fuska yayi cikin yanayi na rashin wasa muryarsa da sauti mai nuna bacin rai ya shiga nuna su da hannu.
"ku wuce muje tun kafin ranku ya baci bana son sakarci kun ji ko".
duban juna sukayi kafin su ja jiki su fara tafiya wannan ya tura wannan wannan ma ya tura dan uwansa Baffa ya shiga bunkansa ya dauko sanda sannan ya sauya riga ya fito ya dubi surukan nasa dake tsaye cirko-cirko sannan ya juya ya tafi tun da suka fito daga sashin su yawancin matayen rugar suke bin su da kallo don sun tabbata ba lafiya tun da suka ga Baffa da kan sa.
Tafiya suke yi kamar wanda ba sa son zuwa Baffa na biye da su da sun tsaya sai ya daka musu tsawa cikin wannan yanayin suka tunkari kogin zuciyoyinsu suka fara lugudan bugu suka fara tirjiya kamar dabbar da ba ta son zuwa inda za a kaita ganin da Baffa yayi ba su da niyyar karasawa sai ya raɓa su ya wuce yana mai watsa musu kallon na raina muku wayo.
Tun daga nesa Baffa ya fara tsinkewa da lamarin hango abu da yayi bakin kogin ruwa sai wuce yake yi ta wajan amma ba alamun motsi bakinsa dauke da addu'o'in neman tsari ya tun kari wajan zuciyarsa na harbawa amma haka ya dake ya isa wajan ba karamin razana yayi ba sosai ganin mutum zube a kasa rabin sa a waje rabinsa a ruwa turkewa yayi daga nesa yayi nazarinsa sosai ya tabbatar da cewa 'eh' gawa ce dagaske domin ganin yarda fuskar ta kumbure sosai ba ma ka iya gane halintarsa ta asali da hanzari Baffa ya isa har zuwa lokacin zuciyarsa da bakinsa ba su daina karanto addu'o'i ba ya tsorata sosai tsoron da ya kusan sanya zuciyarsa firgici har ya fara shakkan zuwa wajan gawar domin bai san abin da ya faru da wannan mutumin ba bai san mai ya kashe shi ba sannan yana tsoron abin da zai je ya komo musamman a halin rayuwar da ake ciki na yanzu baka san hawa ba baka san sauka ba fada TARKO da zai kashe maka rayuwa shi kuwa ba zai so haka ba baya fatan rayuwarsa ta kare da tashin hankali wanda zai hana zuri'arsa samun nutsuwa suma sosai zuciyarsa take karanto masa shafi-shafi na matsalolin da zai iya fadawa amma duk da hakan zuciyar tasa ba tayi tasiri ba domin wani bangare na cikin ta yana kwadaita masa ribar TAIMAKO a rayuwa numfashi yaja mai karfi kafin ya hadiye wani yawu mai tauri ya juya ya dubi su Iro da suka kara yin nesa dashi suna hangensa daga nesa murmushi yayi duk da halin da yake ciki bai taba ganin matsorotar maza irin su ba.
Sai da ya kwashe mintina masu dan dama kafun ya karasa wajan gawar ya durkusa yana karewa fuskar kallo mai cike da suma kallo daya yayi masa ya gane babban mutum ne zuciyarsa yaji ta bugu lokacin da fuskar mutum tayi masa gizo da wata fuska da ya taba sani duk da dai ya manta a ina ya san ta amma fuskar tana yi masa kamanceciniya a hankali ya sanya hannu yana jayo shi daga cikin ruwan gabansa na cigaba da bugawa sosai gefen kogin ya ajje shi yana kare masa kallo zuciyarsa na ta nazarinsa kafun ya mike cikin yanayi na JARUMTA ya dubi su Iro da suka kara matsawa can nesa tun lokacin da suka ga ya fara kokarin fiddo da gawar da hannu yayi musu alamu su zo amma ba wanda ya motsa ganin in ya biye musu ba abin da zai yi hakan ya sanyashi takawa ya isa garesu.
"kuje ku taho mani da amalanken shanu yanzun nan ina jiran ku".
Duban sa sukayi cin rashin fahimta kafun Iro ya motsa laɓɓansa a dan tsora ce.
"Baffa Amma...".
Hannu ya daga masa cikin alamun yayi shiru.
"kuyi abin da nace muku kawai bana son jin komai".
Yanayin da yayi maganar rai bace ya sanya su jan jiki suka bar wajan da sauri domin yin abin da ya umurce su.
Nan ya tsaya yayi shiru abubuwa da yawa suna masa yawo akai zuciyarsa sai kai komo take yi akan lamarin nan sosai da sosai abin ya daure masa kai bai san yarda zai kwatanta lamarin ba bai san ya zai dauke shi a zuciyarsa ba sosai yake jin wani iri a jikinsa abin da bai taba faruwa dashi ba tun da yake a rugar nan tashi sama da shekaru ashirin kenan amma abun ya zo masa kamar almara numfashi yaja kafun ya É—aga kai ya dubi gawar daga inda take kwance mamaki al'ajabi duk sun baibaye zuciyarsa.
Bai san me duniyar nan take so ta zama ba, bai san ya zamanin nan yake so ya zama ba, bai san me al'ummar nan ta wannan karnin suke so su zama ba, sosai yake tsoron duniyar nan a wannan zamanin sosai al'ummar cikinta suke firgita shi komai ya sauya tashin hankali an mai dashi kamar abin ado kisan kai abu mai sauki a yanzu kamar ran kiyashi zuciyarsa kuka take yi sosai in ya tuna al'ummar nan yarda suka É“ace a wannan zamani zai iya yuwuwa wannan bawan Allah kashe shi akayi ba tare da laifin sa ba kila yana da iyali a yanzu haka Allah kadai ya san matakin da suka kai na tashin hankali haka rayuwarsu zata dauwama kullum zuciyarsu na kuka tana kunci na rashin tabbacin inda yake...
Karar amalanken da yaji ne ya katse masa dogon tunanin da ya faÉ—a da sauri ya juya ya dube su sannan ya nisa.
"Meye yasa kuke abu ne kamar ba masu hankali ba, mai yasa kuke abu ne kamar ba 'ya'yan musulmai ba, mai yasa kuke abu ne kamar ba masu imani ba, mai yasa kuke abu kamar ba masu tausayi ba, mai yasa kuke gudun dan'uwan ku, ban san dalili ba? ko shakka bana yi duk da dai ban san waye wannan mutumin ba amma na tabbata yana da alaka da addinin musulunci ko ba ku da dangantakar komai da za ku iya taimakonsa dashi ya kamata ku dubi dangantakar addinin da kuka hada dashi shin ba kwa tunanin irin wannan lamarin ya faru da ku ko wani naku shin ba kwa tunanin ku faÉ—a halin rayuwa irin haka shin za ku so a bar ku cikin irin wannan mawuyacin halin ko wani dan uwa naku ya kamata ku sani duk zuciyar da bata taimako sannan bata tausayi to bata cika mai imani ba ya kamata ku sani shi wannan bawan ba shi ya saka kansa cikin wannan halin ba ina mai gargadin ku ku fidda tsoro a zuciyarku ku ajje komai na sakarci ku dauki hankali da natsuwa ku daurawa kan ku fisabillalahi yanzu in aka bar wannan mutumin a haka me kuke tsammanin zai faru dashi a amtsayin na matacce amma ba ayi masa suttura ba dabbobi ne da tsintsaye za su zo fa suna cin namansa wanda ba haka aka so ba ku kan ku na sani nan da dan wani lokaci in dai yana nan wajan wallahi ba za ku iya zuwa ba a yanzun ma kuna tsoronsa a haka ina ga kuma suffarsa ta fara canzawa ya kamata ku canza rayuwarku ku da zuciyoyinku tun wuri!".
Shiru sukayi suna jin abinda Baffa ke fadi lokaci guda jikkunansu sukayi sanyi zuciyoyinsu suka mika su wani mataki na daban wanda ba su san suna dashi ba sosai suka ji wani yanayi mai girma ya dalsu a zuciyoyin su tsoro da fargaba ya shige su sosai dangane da maganganun Baffa sai faman rauyasa kai suke bai ce da su komai ba ya fara kokarin karkata akalan amalaken yana kora shanayen ganin haka ya sanya su sauri zuwa suka anshe shi duban su yayi kafun ya kau da kai sosai yaji dadi a zuciyarsa ganin maganganunsa sun yi tasiri a garesu a hankali ya fara takawa suna biye dashi har suka isa wajan gawar hannu ya saka yana kokarin daukarsa duk da a zuciyarsa yana ji ba zai iya shi kadai ba amma bai so yayi musu magana so yake yi ya ga halin da suke ciki sannan da yanayin da suka shiga a game da maganar tasa bai gama tunaninsa ba yaji su a kusa dashi a tsaye suna faman bin gawar da kallo sannan suna bin shi shima da kallo kafun su saka hannu duk da zuciyoyinsu suna harbawa amma duk da hakan sai da suka raruma jarumta suka sakawa kansu suka taimaka suka saka gawar a amalanken kafun suka hawan suka fara kokarin kaɗa shanun amma ya tsayen dasu isa yayi wajan wata bishiyar dogon yaro ya sanya hannu ya katso reshe mai girma da yake bishiyar ba tsayi gareta ba sosai kuma shi dama mai tsayi ne zuwa yayi ya lullube gawar dashi kafun ya hau su ja su tafi zuciyar sa cike da tausayi da jin ƙai ga wannan gawar abubuwa sosai yaji suna yawo akansa da zuciyarsa.
A wannan yanayin suka shiga cikin rugar duk aka shiga bin su da kallo cike da yanayi na dan firgici a daidai saitin bunkarsa suka tsaya su Mariye duk sun fito daga bunkokin su sun yi tsarko-tsarko sai faman mazurai suke yi kamar wanda za ace musu kes! su kwasa da gudu.
"Taimaka mu shigar dashi daga ciki ko".
Ya fadi yana duban Iro da yake duban Baffa tun dazu yana son sanin abin da za ayi sun dauko gawa sun kawo gida bai san kuma abin da za ayi yanzu ba numfashi ya ja kafun ya dubi Ja'e sannan suka kama ba tare da sun buÉ—e gawar ba suka tattara har ganyen suka yi cikin Bunkar dashi ajje shi sukayi kan tabarmar dake shimfiÉ—e a tsakar bunkar duk suka saki ajiyar numfashi kafun Iro ya sake numfasawa a karo na biyu.
"Baffa yanzu me za ayi masa to?".
Murmushi yayi kafun ya shafa kasumbar fuskarsa wacce ta fara zama fara fat!.
"Kokari zamu yi mu yi masa suttura mu kai shiga gidan sa na gaskiya shi kadai ne gatar da za muyi masa".
GyaÉ—a kai sukayi dukkannin su suna masu sakin ajiyar numfashi mai girman gaske.
"Amma Baffa kana ganin haka ya dace ba fa mu san shi ba, ba mu san daga ina yake ba kana ganin in muka yi haka ba wata matsalar?".
"Ja'e kenan yanzu ya kake so muyi in ba mu yi masa gatar kai shi gidansa ba in muka ce sai mun binciko wanene kasan lokacin da zamu dauka ba fa RAI gareshi ba, ba ma wannan ba yanzu in muka ce sai mun binciko yan uwansa ta ina zamu fara ba da wani haske ko tsani da za mu bi ya kai mu matakin da muke so lalube kawai muke a duhu hanya daya ce kawai muyi masaa suttura duk da dai ba mu san alkiblar da yake ba amma a zuciyata nayi amanna musulmi ne".
Da mamaki suka dube shi.
"Baffa kai ma dai da wata magana kake ai da ka kalli wannan zaka gane musulmi ne duk da dai ba a fuska ake rubutawa ba amma yanayin suffar mutum ma Allah na nuna yanayin sa da kuma zaton da za ayi masa na alkiblar da yake kalla".
Ficewa sukayi gabadayan su waje suka tadda matan rugar da tsirarin maza sun yi dandazo suna jiran fitowar su Baffa kallon su kawai yayi lokacin da ya fito ya san za ayi haka dama dole su ne mi ba'asi ta yarda suka ga an shigo da mutum wanda suka tabbatar ba kalau ba kuma suka ga sabon abu da ba a tabayi a rugar ba.
Cikin son fitar da su daga kokwanto nan Baffa ya shiga sanar da su abin dake faruwa ba karamar razana da tsoro suka nuna ba musamman matan masu tausayi wasu har da hawaye nan dai ya ja mazajen cikin su gefe duk da yawancin sauran sun fita kiwo ba sa nan musamman manyan 'ya'yan Baffa.
Nan dai suka ba shi goyan bayan akan shawarar da ya yanke nan cikin kankanin lokaci ka shiga kokarin suttur tashi Baffa da kan sa ya shiga yi masa wanka cikin wannan yanayin wani al'amari ya so daurewa Baffa kai koma yace ya daure masa ya sanya shi tsayawa akan abun da yake yi domin ya lura cikin gawar na dan motsawa kadan-kadan alamun numfashi da farko bai yarda ba ya dauka juyawar da yake yi masa na wakan yake motsa cikin nashi amma sai yaga akasin haka da sauri ya mai da komai gefe ya ajje yana kallon sarautar Allah.
Abu kamar wasa cikin hukuncin Allah sai ga motsin ya cigaba dayi har hannyensa sun fara motsawa nan da nan Baffa ya fita ya kira su Ja'e ya nuna musu abin da ke faruwa sosai suka nuna tu'ajibinsu.
"Baffa ko dai yana da rai ne bai mutu ba?".
Cewar Ja'e.
"Akwai alamun ran a jikin sa kasan mi yanzun kamata yayi mu taimaka masa tunda alamun ya nuna da ransa".
Cikin hanzari Ja'e ya mike yana duban Baffa.
"Bari na kira Malam Jaura Mai Magani Baffa".
Ba tare da ya jira ansar su ba ya fice jikinsa na É“ari dama ya matsu ya bar dakin domin gani yake kamar FATALWA ce ba wai sahihin mutum bane ya farko.
Ya jima kafin ya dawo tare da Malam Jauro din irin mutanan nan ne masu maganin gargaji na kauye kafaɗarsa rataye da jaka ta fata kallo daya zakayi masa kasan ya tsufa sosai fuskarsa duk ta tattare abin ka da bafulatanin mutum ba kauri sai tsawo ga wani gemu da ya ajje yayi masa tsiri a haɓa yayi fari tas! dashi.
Taimkon gangawa ya fara yi masa magani ya hada na sauyoyi ya murtsuke su kafun ya tsiyayi ruwan ya baiwa Baffa ya dura masa duk da izuwa wannan lokacin jikin nasa ya daina motsi hannu Baffa na k'yarma ya kai maganin saitin bakin sa yana mai furta Addu'ar neman dacewa ya shiga dura masa amma hakoran sunki buɗewa sai zubewa maganin yake yi a jikinsa ajjewa yayi gefe kafun ya sanya hannu ya buɗe bakin sosai wanda ya kunbure sosai jini duk ya taru masa laɓɓan nasa sun canza kala sunyi bakinkirin alamun mataccen jini a hankali yake dura masa wani na zubewa wani na wuce har ya gama ya mikewa Malam Jauro kokwan yana mai ajiyar numfashi kusan awa guda ana abu daya amma ko motsi bai sake yi ba amma Malam Jauro ya tabbatar musu da cewa yana da rai in Allah ya yarda zai tashi nan ya basu magunguna wanda za a dunga shafa masa da wanda za a dinga bashi na tsawon lokacin da zai farka domin ba karamar jika yayi ba jikinsa duk a kunbure yake ta ko ina sosai da sosai rigar jikinsa Baffa yayi kokarin cewa wacce gabadaya ta gama rine da jini.
Sosai Babba ya tsorata lokacin da ya gama cire masa rigar dak'yar wacce sai da ya yage ta ba dai ya fidda ita ta wuya ba saboda mannewa da tayi da ciwon dake jikin nasa hannunsa na dama da ya kumbura ya suntume Baffa ya kurawa ido sosai yana nazarin sa kafin wani lokaci ya gane harbi akayi wanda ya same shi a hannun nan ya shiga kwaɓa wani magani wanda Malam Jauro ya bashi ya shafe masa wajan dashi kafun dukkannin su su fice daga cikin dakin zuciyoyinsu cike da fargaba da yanayin da suka gan maras lafiyar a cikin in ba don Malam Jauro yace akwai numfashi ba ba su yarda ba musamman Ja'e da Iro wanda sukayi zaton kawai dama can a mace yake ganewa ne ba suyi ba suke ganin kamar motsi yake yi duk da wani ɓari na zuciyoyin su na sanar da su da sauran numfashin sa.
******
"Anya Baffa wanna mutumin zai tashi kuwa?".
Cewa Ja'e dake faman gasa masa jiki da tafasheshen ruwan magani wanda izuwa wannan lokacin jikin nasa ya sabe sannan kuma numfashin sa na fita a hankali.
Baffa wanda ya kure shi da ido tun dazu yana kallonsa yau kwana biyu kenan zuciyarsa na damuwa da lamarin mara lafiyar nan da ya tsinta sosai ya damu sosai yake son ya ga ya tashi kan kafadun sa yana so ya san ko waye shi yana son ya san wani abu game dashi sosai yake ji a zuciyarsa wani lamari mai girma yana tattare da shi zuciyarsa da idanunwansa suna nazarin fuskarsa wanda har zuwa wannan lokaci bata dawo daidai ba ko idanun nasa bai iya buÉ—ewa.
Numfashi ya ja kafun ya dube Ja'e.
"zan so ace ya tashi kan kafafuwan sa sosai nake bukatar haka ina so ya dawo duniyar nan ya cigaba da rayuwa sosai nake ji a jiki akwai wani al'amari da zai faru a game da wannan mutumin ko da dai ban san sa ba amma ina ji a jikina akwai wani abu a boye".
Shiru yayi yana duban Baffa jin abin da yake cewa wai akwai wani abu da yake zaton zai faru anya kuwa meye zai sanya kansa damuwa akan mutumin da bai san shi ba bai san daga ina yake ba...
Motsin shigowa haÉ—e da sallama da akayi ya tsinke musu zaren tunanin da suke yi Asiya ce ta shigo hannunta dauke da kwarya cike da damammiyar salala mai dauke da hadin magani a ciki durkusawa tayi har kasa.
"Sannu Baffa gashi an gama".
Ta fadi tana mai ajjewa gefe guda tana mikewa kan kafafuwanta bayan ta karewa mara lafiya kallo zuciyarta da tausayi sosai a ciki sannan ta fice tana mai dauke kwallar da suka kawo idanuwanta hari.
"Baffa!"
Ja'e ya fadi da sautin murya yana mai zaro idanuwa waje cikin yanayi na firgici da sauri Baffa ya dube shi kafun ya sauke idanuwansa kan maras lafiyar jini ne ke fitowa ta bakin sa bakikkirin kirjisa sai faman harbawa yake yi cikin sauri-sauri ko ina na jikinsa sai motsawa yake yi kamar wanda aka jonawa wayar nepa da hanzari Baffa ya mike ya isa wajansa yana dafeshi cikin yanayin fargaba ganin jinin sai bulbulowa yake yi yaki dainawa.
"Maza Ja'e maza tashi ka kirawo Malam Jauro yi hanzari".
Tun kafun ya rufe baki Ja'e ya fice daga gudu cikin kankanin lokaci suka iso a tare Malam Jauro na kallon abin dake faruwa bai wani damu ba ya dubi Baffa.
"Ba wata matsala bace buguwar da yayi ne jini ya tarun masa shine yake amayar dashi hakan ma duk cikin samun sauki ne".
"Haba Malam Jauro ya zaka ce haka ka ga mutum na aman jini amma kace ba komai anya kuwa".
"Ni na fada maka ai in ka lura da jinin ai ba lafiyayye bane ya rigaya ya lalace ko ya tsaya masa a jiki ba abin da zai haifar masa sai wata matsalar cutar ka kwantar da hankalin ka in Allah ya yarda zai farko kuma cikin sauki".
Ajiyar zuciya Baffa yayi mai girma kafun ya koma gefe yana sharce gumin dake ta faman tsantsafo masa a goshi.
Jini sosai ya zubar kafun wani lokaci ya lafa nan Malam Jauro yayi masa yan daburansa kafun ya dura masa wani magani da ya ciro daga jakar sa sannan ya bukaci wani abu mai dan dumi mai ruwa-ruwa domin ya bashi nan take Baffa ya mika salalar da Asiya ta kawo sai da ya kare mata kallo kafun ya dubi Baffa.
"Dama ba a bashi ba tun dazu da nace".
"Yanzu aka gama ina kokarin bashi sai ga wannan lamarin ya afku"
Ba tare da ya sake magana ba ya shiga dura masa salalar a hankali cikin ikon Allah ya buÉ—e baki ya mikawa cikinsa sakon abincin da yaji yana saukar masa amma duk da hakan idanuwansa a runtse suke ba su buÉ—e ba sai da ya sha sosai sannan Malam Jauro ya dubi Baffa.
"In Allah ya yarda komai zai zo da sauki tun da hakan ta kasance yanzu dai ku bar shi zuwa wani lokaci muga yarda Allah zai yi".
Gyaɗa kai sukayi suna yi masa godiya kafun ya mike ya sabi jaƙarsa ya fice daga bunkar.
Haka su Baffa suka cigaba da jinyarsa a hankali yana samun lafiya jikinsa na komawa daidai sai dai magana ce ba ya iyayi sam! sannan idanuwansa sun buɗe sai dai mutane ma dishi-dishi yake gani a haka har sati guda ya shuɗe Baffa bai gajiya da taimaka masa ba shan maganinsa cin abinci har makewayi shi yake taimaka masa ya kai sa da kan sa daidai da rana daya bai gajiya ba da kansa yake za gayawa dashi cikin rugar domin motsa jiki shi ya zame masa DAN JAGORA lokaci lokaci yana tambayarsa waye shi? Amma ba ya bashi ansa sai dai idanuwansa suyi ta zubda hawaye yayi ta kokarin yin magana amma ba dama sai dai yayi ta jan numfashi a haka har suka saba da Baffa sosai da sosai mutanan gidan ma haka rugar gabadaya ba wanda bai san DAN MAKAHO ba sunan da suke kiransa dashi kenan ko DAN KURMA a haka ake ganewa amma ba sa fadi gaban Baffa domin fada yake yi sosai ya nuna bacin ran shi akan haka domin komai ya samu bawa na dadi da akasin sa DAGA ALLAH NE kuma tun fil'azal ALKALAMIN ƘADDARAR bawa ya rubuta hakan sai ta faru dashi a duniyarsa.
Shakuwa sosai Baffa yayi dashi domin a zuciyarsa yana jin wani bakon yanayi game dashi lokaci lokaci yake jin gabansa na faduwa wanda ya rasa dalili musamman in yana kallon fuskarsa sai ta dinga yi masa gizo da wanda ya taba sani amma ya rasa tunanin da zai kara masa haske akan fuskar cikin wannan hali suka shafe wata guda izuwa lokacin idanuwansa sun buÉ—e sosai yana ganin kowa da kowa ranar da ya fara ganin fuskar Baffa ba karamin yanayi na fargaba ya shiga ba zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri-sauri lokaci guda ya firgice sai mazurai yake yi ji yake kamar ya kwashi kafafuwarsa ya zura da gudu ko kuma ya nutse cikin kasa jikinsa sai É“ari yake yi Baffa dake gefensa yana ta faman bashi labarai sam bai lura da abin dake faruwa ba motsin mikewa da yaji yayi ne ya sanyashi dubansa ganin yanayi da yake ciki ya sanya shi mikewa ya riko masa hannu.
"Lafiya me ke damunka?".
Baffa ya fadi yana mai dunduba jikinsa kafun ya sauke idanuwansa a saitin nasa hakan ya
kara fadar masa da gaba shi kansa Baffa ji yayi gabansa ya yanke ya fadi lokaci guda...
  *_KAMALA MINNA_*😘😘😘
Post a Comment (0)