UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA ARBA'IN DA UKU.
Sosai zuciyarta take bugawa a duk lokacin da Al'amarin Auranta da Dr.Erena ya zo mata filin tunaninta komai nata kwancewa yake yi komai nata take ji yana canzawa kamar ba nata ba.
Ta rasa ya zatayi ta rasa mai ya kamata tayi zuciyarta na zafi zuciyarta na raÉ—aÉ—i raÉ—adi mai girman gaske kudirin zuciyarta kawai take hangowa da ta dauka akan wannan azzalumin mutumin bata so abin da zai hadata dashi a inuwa daya sam-sam ko zaman da take yi a Company sa kawai tana yi ne don cinmma burinta amma ga yarda lamarin ya kasance har ya kai ga zancen aure a tsakaninsu.
Bata san wata irin rayuwa zatayi a gidansa ba bata san ya zata zauna ba zuciyarta na zafi tana shiga kunci duk lokacin da tunanin aurenta ya fado mata ba ta shirya masa ba ko da na kwana daya ne amma ba yarda za tayi tunda Hajiya Layla ta nuna kaunar ta akan lamarin kuma ta wannan hanyar ce kawai za su samu abin da suke so.
Sosai take mamakin yarda Hajiya Layla ta dauki lamarin da girma ta bada lokacinta da komai da ta san zai taimaka wajan tafiyar da komai yarda ya kamata.
"Areefa bawai ina son ki auri Dr.Erena bane a son raina a,a wallahi in da zan buÉ—e miki zuciyata ki ga bakinciki da takaicin da take yi akan wannan lamarin zaki ce naki ba komai bane amma na daure na mika zuciyata wani mataki na hakuri domin ganin ta yarje wannan lamarin ya kasance".
"Maama ban san ya zan koyi zama da makiyina ba ban san ya zan koyi zama da mutum kamar Dr.Erena ba daidai na sakan daya ne wai da sunan a idanuwa daya a matsayin mata da miji".
Wasu hawaye suka zubo mata a kunci masu dumi bata yi kokarin dauke su ba domin ko ta yi hakan ba daina zuba za suyi ba.
Hajiya Layla ce ta saka hannu ta dauke mata tana mai kwantar da ita kan cinyarta.
"Areefa ina so ki san wani abu guda san nan ki saka shi a zuciyarki auren Dr.Erena ba yana nufin kashe miki rayuwa bane auren Dr.Erena ba yana nufin numfashin ki ya daina wanzuwa bane a doron duniyar nan ki sani rayuwa ce zaki yi ta daukar fansa a gidansa wacce nake tsammani ita ce hanyar da tafi dacewa sannan ke dai ki zuba ido kiyi kallon komai zaki sha mamaki akwai ranar da zata zo da kan ki zaki zo kina bukatar al'amarin da yake wanzuwa a daidai wannan lokacin ba zan sanar dake komai yanzu ba amma duk ranar da komai ya tabbata zaki san komai".
Tashi tayi tana duban Hajiya Layla cike da mamakin furucinta sai faman juya idanu take yi tana rausayar da kai tana kokarin yin magana wayarta ta dauki Ring juyawa tayi ta dubi wayar a cikin jakarta dake yashe tun da ta dawo aiki yau gabadaya ta kasa sukuni ta kasa zaune ta kasa tsaye Hajiya Layla ce ta kai hannu ta dauki jakar ta fiddo da wayar ta mika mata ba musu ta ansa ganin mai kiran ya sanyata saurin dagawa don dama kamar ya san ta na cigiyarsa don sun kwana biyu ba su hadu ba gabadaya ta shiga wani irin yanayi na tashin hankali musamman yarda Dr.Erena ya sako ta gaba akan ta bashi dama ya turo domin neman aurenta.
Numfashi taja jin muryar Alhaji Abdulwahaaab ya ambaci sunanta.
"Areefa ina kika shige kwana biyu ne?".
Numfashi ta hadiye mai tauri kafin ta dubi Hajiya Layla.
"kai dai kawai bari al'amarin duniyar nan ne yake neman sha mini kai wallahi akan maganar mutumin ka ne Dr.Erena".
Murmushi yayi mai sauti wanda har sai da Areefa taji sosai kafun yaja numfashi.
"kisan na kusan barin duniyar nan kuma ba wanda na daurawa sai Dr.Erena kisan an tare ni a hanya akayi min dukan tsiya har sai da na rasa kai na...".
"What! Me kake cewa Alhaji Abdulwahaab duka fa kace Yaa Allah!".
Ta fadi tana mikewa a razana lokaci guda ta ji kanta ya buga ta sanya hannu ta dafe shi sai numfashi take saki da sauri sauri kamar wacce tayi gudun ceton rai.
"kenan sai da yayi abin da yace zai yi ko wai shin me ke damun wannan mutumin ne na lura gabadaya shi cinnaka ne bai san na gida ba".
"Rabu dashi kin ji yanzu ya maganar ku ina kuka kwana akan batun auren naku don ya kamata ace kin ajje duk wata fargaba da tsoro a zuciyarki kin fuskance shi sosai ki yarda ki bashi hadin kai a yi aure nan wannan dama ce sosai a gareki da zaki cika burin ki gami da kudirinki".
"bana tunanin zuciyata zata aminci bana tunanin zan ita zama da shi bana tunanin burina da KUDIRINA za su tabbata in dai ta hanyar aure ne tsakanina da Dr.Eren...".
Fizge wayar taji anyi da sauri ta juya ganin Hajiya Layla taga fuskatar ta sauya da bacin rai ya tabbatar mata da bata so abin da take fadi ba.
"Alhaji Abdulwahaab".
Hajiya Layla ta fadi bayan ta daura wayar a kunnanta kafin ta nisa bayan ya ansa.
"Karka damu da duk abin da take ce maka Alhaji Abdulwahaab zuciyar Areefa ban san abin da ke damun ta ba amma ka bar komai a hannu na ni dai taimakon da nake so kayi mani a wannan tafiyar a yanzu ka neman min mutanan da za su kasance a mtsayin iyayen Areefa ina son cikin watan nan bikin nan ya tabbata...".
"Maama!!!"..
Areefa ta fadi tana zaro idanu waje kamar wacce ta ga mugun abu wani kallo Hajiya Layla tayi mata tana sauraron abin da Alhaji Abdulwahaab yake sanar da ita akan komai zai gudana ba matsala sauke wayar tayi ta cillar da ita kan kujera kafun ta dubi Areefa.
"ya kamata ki san wani abu guda daya lamarin nan fa sai ki ajje duk wata kiyayyer da kikewa Dr.Erena a gefe ke kin sani mutum ne dan duniya in har kika bada matsala wallahi tsaf zai kashe ki har ni da ma duk wanda ya san suna hada hannu damu don haka tun wuri ki san abin yi kuma ina so in kin fita aiki gobe ki sanar dashi kin aminci nan da sati guda ya turo".
Baki ta saki tana kallonta cikin mamaki da takaici a zuciyarta komai take ji yana canza mata duniyar taji tana juya mata da tashin hankali mai girma wani ciwo taji mai girma zuciyarta na kara shiga kiyayyar Dr.Erena na daÉ—uwa girgiza kai ta shiga yi kafun ta yi hanyar dakinta da gudu tana sakin wani numfashi mai wahalar gaske.
Wannan rana haka Areefa ta wuni cur! ba wani akayan farinciki har zuwa dare ko runtsawa ba tayi ba Hajiya Layla ta zo ta bata baki amma ina tashin hankalin da take ciki ya zarce a kwatantashi gabadaya a firgice take ba ta shirya ba bata da lokacin yin wannan aiki zuciyarta ba zata aminci ba.
Haka tayi ta saƙe-saƙe har zuwa wani lokaci kafun wani barawon barci yayi gaba da ita a nan zube tsakar daki.
*****
A sanyaye take shiryawa gabadaya jikinta ya mutu sosai take jin zuciyarta na mikata wani mataki mai girma gaske yana haifar mata da wasu lamaruka masu girma a zuciyarta numfashi take dak'yar ji take yi kamar wacce ake toshewa hanci da baki.
Turo kofar da akayi ne ya sanyata hanzarin mikewa Hajiya Layla ce ta tokare bakin kofar tana binta da kallo kafun ta kau da kai.
"Kisan karfe nawa yanzu kuwa Areefa? Wai mai yasa bakya jin magana ne Areefa ya kamata kiyi hanzarin shiryawa ki tafi aikin nan rashin zuwa aikin nan zai iya canza tunanin mutumin nan ta inda baki taba zato ba wallahi ke da kanki kwanaki kike bani labarin abinda wata ta zo tana gaya masa akan ki na cewa ba don Allah kike aiki a Company din sa ba akwai KUDIRI da kike dashi a zuciyarki ba ki tunanin wannan tunanin ya fara tasiri a zuciyarsa bakya tunanin in bakya nan ta sake zuwa ta sanar dashi har akai matakin da zai yarda yanzu ya dace ace kina nan nan dashi ya gane eh da gaske auran sa zakiyi sannan karki sake ya gano ko yar karamar hanyar da za ta bashi dama ne ya fahimci wani abu wallahi in baki iya kama barawo ba to tsaf! barawo zai ka maki Dr.Erena da kike gani ba karamin kwallon shege bane...ko dayake ba sai na fada miki ba ke kan ki kin san waye".
Tana gama fadin haka ta juya da hanzari ta bar dakin ta bar Areefa tsaye tana kokarin sanya dankunne cak! ta tsaya tana jin maganganun Hajiya Layla nayi mata yawo akai tunanin faruwar wani abu daban da yarda zata kasance ya dire mata a zuciya tabbas ta sani dole wani abu ya faru in har tayi sake musamman yanayin da Mufeeda take kokarin sanya Dr.Erena ya so ta ta sani ko wani hali kuma komai zata iyayi don cin ma burinta.
Cikin hanzari ta karasa saka dankunne ta saka takalmi kafun ta kara gyara fuskarta sosai da sosai ta dauki jakarta bayan ta duba kanta a MADUBI sa'annan ta fice daga cikin dakin bata samu kowa a falon ba hakan ya tabbatar mata Hajiya Layla na daki bata yi yinkurin zuwa gareta ba illa saurin ficewa da tayi.
Tana shiga motarta ta fizgeta sosai tana zabga guda gabadaya kwanyarta ta mikata cikin wani yanayi a yanzu da take hango Mufeeda tare da Dr.Erena tana karantar dashi komai akan Areefa gabanta taji ya tsinke duk da dai ta tabbata Mufeeda ba za ta sake dawowa wajansa ba sannan kuma shima yana nuna rashin so akanta sosai.
Da wannan tunanin ta isa Company din sai da ta tsaya bakin Get tayi kokarin saita numfashin ta kafun ta karasa ciki tayi Parking nan ma sai da ta dau mintina tana karewa motocin da suke zube a wajan kallo kafun ta dire a ta Dr.Erena wani numfashi ta ja mai tauri kafin ta buɗe motar ta fito a hankali ta shiga takawa kamar mai tausayin kasa har ta kai bakin kofar da zata shigar da ita cikin Reception din bayan sun gaisa da Security tana kokarin sanya kai ciki sai ga Dr Erena shima ya sanya kai zai fito saura kadan su yi gware da sauri taja da baya tana mai da numfashinta da take ji yana fizga runtse idanu tayi kafin ta buɗe su lokaci guda ta dube shi wanda shima gabadaya ya shagala da kallonta sai faman zabga murmushi yake yi sosai ta ji gabanta na bugawa kafun tayi kokarin kirkiro yaƙen dole tayi masa tana kokarin raɓashi ta wuce amma yarda ya tsare kofar ya sanya dole yin maganar da bata so yi ba.
"Barka da safiya Sir".
Ta fadi ba tare da ta dube shi ba bai ansa taba kuma da alamun bashi da niyyar ansa ta din sosai ta matsu ta bar wajan yarda take jin kafafuwanta na wani iri lauyewa kamar za su zubda ita a kasa sai da ya gama shan sharafin kallonta sannan ya kau da kai ya na mike mata wani abu dake hannunsa.
"in kin shiga ki karasa min dashi cikin Office".
Ya fadi ba alamun wasa sosai take kallonsa da abun da yake mika mata lamarin ya shiga tsingular mata zuciya wanda take kallo a matsayin raini eh mana raini ta yaya za ace mutumin ya fito da abu daga ciki sannan kuma ita da zata shiga yanzu ya bukaci ta mai da masa mai yasa ya fito dashi bata san abin da yake hawa kan Dr.Erena ba a yan kwanakin nan yana shige mata sosai ita kuma bata son haka ansa tayi sannan ta wuce ciki binta yayi da kallo yana sakin murmushi harda taÉ—É—ar baki kamar namijin da ya shekara hamsin gidan yari ya fito ya ga mace kafun ya juya da sauri ya isa wajan motarsa ya bude abu ya dauko sannan ya rufe ya kama hanyar kowama cikin reception din.
Ita kuwa Areefa tana shiga bangarenta ta isa ta ajje jakar da sauran tarkacenta kafun ta dubi abinda Dr.Erena ya bata ta shiga juya shi ba wani abu bane na azo a gani kawai neman shiga rayuwarta ne da hanzari tayi hanyar benan cikin sauri don bata so ya zo ya tadda ita a ciki don tasan kadan daga aikin sa ne.
Tana hawa wajan Office dinsa ta tadda sakatariyarsa ko ta kanta bata bi ba ta karasa ta shiga Office din can wajan Table ta isa ta ajje masaa kafun ta juya tana karewa Office din kallo tana yatsine fuska sa'anna ta ja kafafuwan ta tana kokarin fita mutum ta gani tsaye bakin kofar harÉ—e da hannaye a kirjisa wani irin dokawa taji gabanta yayi kafun ta daure fuska tamau!
"Ina zuwa ko".
Ta fadi cikin rashin son kawo mata wasa murmushi yayi kafun ya tako kamar zai shige mata jiki hakan ya sanya ta saurin ja da baya.
"Areefa ban san me zan miki ba kuma nayi iri bakin kokarina don ki bani dama amma kin kiya ban san dalili ba?".
Ya fadi yana mai kare mata kallo kafun ya dora da cewa.
"Ina so a yanzu ayi komai ya wuce don wallahi ba zaki fice daga Office din nan ba sai kin fada mini matsayata a gareki".
Wani irin dokawa zuciyarta tayi amma bata bari hakan yayi tasiri a fuskarta ba kau da kai tayi.
"Areefa ya kamata ki ce dani wani abu ki baiwa zuciyata dama ta so ki ta kauna ce ki ta daÉ—e tana daukon son ki amma ke kin ki yarjewa dagaske nake ba da wasa ko yau ki ka ce na fito akan zancen aure wallahi ko awa daya ba za a kara ba".
Yaa fadi kamar wani karamin yaro sosai maganganunsa suka taba mata zuciya amma sai ta nuna halin ko in kula sai ma kokarin raɓashi ta wuce take yi amma yaki bata dama sun jima haka kafun ta yanke hukunci da taga yafi cancanata wanda take ganin illa ce mai girma gareta numfashi taja kafin ta saita kanta sosai ta dube shi.
"Dr.Erena ni ban ki ta taka ba..ko da yake kawai abin da za ayi mu bari nan da sati daya lokacin na sanar a gida sai ka turo".
Ta fadi ba a son ranta ba tana jin yarda zuciyarta ke yayyagewa da tashin hankali sosai taji jikinta na ansa bakon lamari mai girma da sauri ta rabashi ta wuce ganin ya saki baki yana kallonta kamar wani butum butumi.
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘