UKU-BALA'I 44

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA HUDU.
Sosai ta shiga tashin hankali cikin lokaci kankani ta rasa mai yake mata dadi a filin duniyar nan komai ya kara kwance mata tashin hankali ta ya kara hawa mataki mai girman gaske bata san me za tayi ba bata san mai ya kamata tayi ba lokaci tafiya yake komai kara kusantowa yake yi har zuwa wannan lokacin ta rasa mafitar da zata samu don cimma burin ta ba tare da auranta ya tabbata da Dr.Erena.
Numfashi take ja cikin sauri-sauri tana faman juyi saman faÉ—aÉ—É—en gadon ta wanda take jin sa kamar kan garwashin wuta take kwance komai na duniyar take ji yana yi mata k'iwa baya son ta da farinciki ko yaya ne.
Zuciyarta na ta hasaso mata cewa 'ta kashe shi ba tare da kowa ya sani ba' amma ta kasa tana tsoron haka ba kisa a tsarin daukar fansanta bata so ace wani abu ya gifta a tsakaninta da shi wanda zai sanya ta zama sanadin kashe shi tsoro take ji tsoron abin da zai je ya dawo tsoron yawan zunubansa da zai dawo kanta tana tsoron mutuwarta bata shirya ba ba zata iya ba.
'to ki kashe kanki tunda baki shirya auren dashi ba'.
Zuciyarta ta sake bata wani zaɓin na daban wanda yayi matukar girgizata lokaci guda ta shiga girgiza kai kamar wanda ya fada mata maganar a gabanta yake ba zuciyarta ba wasu hawaye ne masu dumi taji sun zubo mata sosai take jin kunci da matsi cikin zuciyarta sosai take jin zuciyarta na mikata wani mataki mai tashin hankali sosai take jin zuciyarta na buɗe wani wagegen ciwo mai girman gaske.
Runtse idanu tayi sosai tana jin yarda jijiyon kanta da na cikin idanuwanta ke wani irin murÉ—ewa da tashin hankali tana jin yarda wani irin raÉ—aÉ—i da zafi ke samun mazukunni cikin idanuwanta mikewa tayi daga kwance da take tana buÉ—e idanuwan nata hannaye bibbiyo ta zabga tagumi tana kallon yanayin DUHUN DARE da ya mamaye cikin dakin bata ganin komai ko jikinta bata iya hangowa sake runtse idanu tayi kafin ta sauke kafafuwanta a gefen gadon tana kai hannunta wajan fitilar dake girke gefen gadon kunnawa tayi haske ya wanzu sosai ta ko ina dakin ta shiga bi da kallo kafun ta mike saman kafafuwanta da take jin su kamar za su watsar da ita zuciyarta na ta karanto mata huÉ—ubobin da suke kara caza mata kwanya.
Maganganunta da Alhaji Abdulwahaab ne suke dawo mata a jiya da rana inda yake kara karfafa mata gwuiwa amma tana zillewa.
*****
"Ban san mai zan ce miki ba kuma Areefa da farko na dauko za ki zama jaruma mai dakakkiyar zuciya wajan cimma fata da burin da kike dashi a zuciyarki amma gabadaya duk wannan fatar da burin naki ya rugeje lokaci guda ban san mai yasa ba Areefa ban san mai yasa kike kaunar jinkiri a wannan lamarin ba dama ce sau daya take zuwa in kuwa ta kubuce da wuya WATA DAMAR ta sake zuwa".
Cire hannayenta tayi daga tagumi tana mai runtse idanu kafun ta buÉ—e su sosai tana dubansa zuciyarta na kara narkewa da lamarin Aurenta da Dr.Erena.
"ba wai na cire burin fata na bane akan Dr.Erena ba ba abin da ya canza...".
Ta fadi dakyar tana jan numfashi kafun ta dauki Glass Cup mai dauke da sanyayyan ruwa ta kai bakinta ta kurba ba wai don jin dadi ba a,a domin kuwa ji take yi kamar ta kurbi maÉ—aci a dandanon da harshenta ya bata runtse idanu tayi ta hadiye shi dakyar kafun ta buÉ—e tana dubansa shima idanuwansa na kanta.
"ina son fatana a kansa ya tabbata amma wannan lamarin da aka kawo min ne nake jin kamar zuciyata ba zata iya hakura ya tabbata ba".
Mikewa yayi kan kafafuwansa yana binta da wani irin kallo kafun yayi taku kadan ya goya hannayensa a bayansa.
"ko RIGAR SILIKI haka ta ganki ta barki Areefa ana taroki ta nan kina watse wa ta can ban san mai yasa ba...ko da yake shikenan amma ki sani auren ki da Dr.Erena shi ne mafita kuma ita ce hanyar da zaki bi domin cimma burinki kamar yarda Hajiya Layla ta fadi bana tunanin zata cutar dake ko da cikin rashin sani ne ki sani baki da wata a duniyar nan ita ce uwarki da ubanki baki da mai kaunarki kamar ita ba zata taba yin abin da zai taba miki rayuwa ba kuma kema kin san haka don haka ya kamata ke ma ki yaki ce duk wani k'i da zuciyarki take nuna miki ki koya mata hakuri da juriya".
*****
Wani huci ta saki tana mai cusa hannayenta cikin gashin kanta zuciyarta taji tana sauya bugu da sauri-sauri a hankali ta zube kan gadon tana kwanciya gami da runtse idanu so take yi ta koyi hakuri da juriya domin ganin tabbatar wannan lamarin amma ta kasa amma ya zame mata dole ya zame mata tilas! Ta koyi jarumta da juriya a zuciyarta domin ganin komai ya tabbata yarda ya kamata tayi alkawarin yin abinda Maama take so a gareta da wannan tunanin barci barawo yayi awon gaba da ita ba ta farka ba sai wajan shidda da rabi shima Maama ce taji ta shiru ta shigo dakin sai da kare mata kallo cikin yanayin tausayawa domin daga ganin kwanciyar barcin bata yi shi tadadin rai ba kuma ba da wuri ba a hankali ta zauna kusa da ita ta shiga shafa mata goshi a hankali Areefa ta buÉ—e idanuwanta mai cike da barci ganin Maama ya sanya ta kara buÉ—e tana ya mutse fuska cikin muryar barci tace.
"Maama!".
Murmushi tayi mata kafun tace.
"bakiyi barci da wuri ba ko Areefa kin sakawa kanki damuwa ko?".
Girgiza kai tayi kafun ta mike zaune tana mai duban agogo ganin karfe bakwai saura ta ware idanu da sauri.
"Yaa Allah har lokaci ya tafi haka".
Tana kokarin mikewa Maama ta rike mata hannu ta koma ta zauna tana kallonta cikin rashin fahimta numfashi ta ka kafun tace.
"Ba zan takura ki ba Areefa domim bana son abin da zai sanya ki a damuwa amma bari zan fada miki dalilina nayin haka din yanzu na san zakiyi amanna da batuna da nake jajircewa domin ya tabbata...".
da sauri Areefa ta kai hannunta bakin Maama tana rufe fuskarta da wani irin yanayi.
"kiyi hakuri Maama komai ya wuce na yarda komai ya tafi yarda da kike so zan baki hadin kai daga wannan lokaci bari ki gani daga yanzu ma".
Ta mike da hanzari ta fada toilet wanka ta sallo kafun ta zo ta tsantsara kwalliya ta sanya riga da siket ta saka wanda suka dan kamata kadan takalmi mai tsini ta saka gami da dauko wata gold-bag mai shegen kyau ta daura glass no respect sosai ta fito kyanta yakara bayyana kamar ba wani abu da ke dawainiya da ita sai murmushi take zabgawa Maama ita kuwa baki ta saki tana kallon ikon Allah kafun ta mike kan kafafuwanta ta riko Areefa ta rungumeta sosai da sosai sannan ta sake ba tare da tace mata komai ba sosai take dubanta bayan ta raba jikinta da nata amma hannunsu a tsarke.
"My Preety Areefa".
Murmushi Areefa tayi kafin ta sake duban agogo bakwai daidai da sauri ta zare hannunta tayiwa Maama sallama ta fice daga cikin dakin.
Motarta ta dauka kirar Benz kalar Ash sai kyalli take yi domin tayi alkawarim yau zata baiwa Dr.Erena mamaki zata nuna masa kulawa ta musamman wanda sai ya raina kansa motar shine ya bata ita amma bata taba amfani da ita ba sai yau domin dai ta nuna eh tana son sa din amma da alkawari tayi bazata taba amfani da wani abu daga dukiyar da yake mata kyauta a ciki ba.
Da wannan tunanin ta fice daga gidan nasu ta dau hanyar Company din zuciyarta sai faman zillo take yi mata gani take yi abun kamar a MAFARKI ba gaske ba a haka har ta isa Company din tans yin Parking taji ana kokarin buÉ—e murfin hakan ya daure mata kai da sauri ta dubi glass din ganin wanda yake tsaye ya sanyata ware idanu da mamaki kafun taja guntun tsaki can kasar makoshinta sannan ta buÉ—e murfin tana kokarin sako kafa waje ya tokare a bakin kofar ya daura hannunsa saman murfin dayan hannun nasa rike da key yana faman kaÉ—awa sai murmushi yake zabgawa kamar tsohon da ya samu kyauta yar sha bakwai a bagas ko dayake a bangaren Dr.Erena yadda yake jin son Areefa a zuciyarsa gani yake yi ta fi ko wacce mace dake numfashi a doron duniyar nan so yake yi mata mai ansa suna so zai iya sadaukar da komai domin yaga ya mallake ta ko da kuwa zai rasa komai na shi na duniyar nan son Areefa ya rigaya ya gama tafiya da imaninsa sosai ya zautu akan sonta numfashi ya ja idanuwansa na kara lumshewa da wani irin yanayi da yake jin zuciyarsa na kara jefashi a ciki akan Areefa.
"Kin makara yau da nayi tunanin ba zaki zo ba har zan bi sahu".
Gaban tane ta ji ya yanke ya fadi jin da tayi yace zai bi sahu ita dai a iyakar zamanta dashi bai taba zuwa gidan su kuma bata taba jin yace ya sani ba yayi nacin ta kai shi amma ta kiya wani yawu ta haÉ—iye mai tauri kafun ta dube shi da murmushin yake a fuskarta.
"to da kake cewa zaka bi sahu ina zaka kai da baka san gidan mu ba".
Daga kafaÉ—a yayi yana mai kara juya idanuwansa akanta.
"wai shin me kika mai dani ne kin dauka son da zan miki zai zauna a raina haka ba tare da na san gidanku domin zuwa kai ziyara ba to ko jiya naje gidan ku lokacin kina nan wajan aiki ba tare da kin sani ba".
Wani irin dokawa taji gabanta yayi da tashin hankali runtse idanu tayi lokaci guda kanta taji yana sarawa shikenan asirinta ya tonu ta gama yawo in har Dr.Erena ya ga Hajiya Layla ta tabbata kashinta ya bushe zuciyarta ta shiga kara mata kwarin gwuiwa akan cewa 'ke kin fiye karaya da yawa ki bari ki ji wani gida yaje mana kuma inda yaje gidanku ai da hajiya Layla ta fada miki tun jiya din'.
Wani numfashi taja gami da buÉ—e idanu tana mai kakalo murmushin dole don bata son ya gane halin da ta fada aiko tana daga idanuwanta ta dube shi wani kallo taga yana yi mata kamar na tuhuma.
"Uhmm ban yarda ba ai in da kaje da an fada min".
Murmushi yayi yana kara gyara tsayuwarsa kafun ya nuna ta da hannu kamar zai lakace mata hanci.
"Bosso Lowcost gida mai lamba 112 gidan Alhaji Saifullahi Suraj".
Wata irin ajiyar zuciya tayi lokaci guda jin sunan da ya fadi tabbas ta gane sunan da ya ambata gidan da za su zama iyayenta ne da Alhaji Abdulwahaab ya zo ya sanar da Hajiya Layla ajiya tabbas tayi mamakin amma da ya san gidan cikin nuna mamaki ta dube tana kara fara'arta.
"Amma nayi mamakin yarda akayi ka sani fa".
"Abu mai sauki ne a gareni kin ga tashi mu shiga daga ciki nan yayi hanya da yawa bana so a zo wuce wa ana kalle min kenan wannan hadaddiyar kwalliyar da kikayi mani domin na tabbata don ni akayi mata kuma zan saye ta da farashi mai tsada ke dai meke mu shiga daga ciki".
Mamaki sosai ya kama Areefa ganin yarda yake rawar jiki ba tare da nuna isa da izzar nan tashi ba da yake da ita kamar bashi ba ko da yake kadan daga makircinsa ne zai iya fiye da haka don ganin ya cimma burinsa akan abin da yake so a hankali ta zuro kafafuwanta ta mike bayan ya matsa ta dauko jakarta tana kokarin dauko wayarta taji ya anshe jakar da sauri ta dago ta dube shi ba tare da tace dashi komai ba tana kokarin mai da kofar motar ta rufe nan ma da sauri ya sanya hannu ya rike yana mai sakar mata tattausar murmushi yana girgiza kai matsawa tayi sannan ya rufe kofar kafun yayi mata nuni da hannu su tafi amma ta kiya ta mika masa hannu ya bata jakarta da ya rike kamar wata uwargijiya da bawanta sai da tayi da gaske tana nuna rashin amincewarta sannan ya bata suka jera don cewa yayi bata isa ta taka ita kadai ba ba yarda ta iya haka suka jera din kamar wasu mata da miji shi kuwa sai rawar jiki yake yana faman yashe baki yana zuba surutu.
  *_Kamala Minna_*😘😘😘
Post a Comment (0)