UKU-BALA'I 45

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA BIYAR.
Duban juna suke yi cikin tsanar da zuciyarsu take mika su akai ji suke yi kamar su shaki juna da kunci da takaicin da suke ji a tsakanin junansu sai faman huci suke yi kamar wasu mayunwatan zakuna.
Dr.Karami ya ja wani dogon tsaki kafun ya juya ya dubi kofar gidan su Mariya da wani irin yanayi mai girman gaske yana jin yarda zuciyarsa ke harba da sauri-sauri komai yake ji ya jagule masa gabadaya tunaninsa ya tsaya cak! Kwanyarsa sai kamawa take yi da wuta tana kokarin babbakewa numfashi yake ja yana jin yarda kirjinsa ke wata irin kartawa da tashin hankali mafi girma a filin duniyarsa juyawa yayi da idanuwansa da suka fara kaÉ—awa ya kalli Dr.Aqeel dake ta faman hura harci kamar zai ci babu.
"ka rubuta ka ajje bar ganin abotar da ke tsakanina da kai wallahi sai na shayar da kai ruwan mamaki a filin duniyar nan wallahi kayi kadan ka wulakanta ni a gaban wacce nake so har kake ikirarin ban isa ba to ka jira lokaci zai zo zaka ga yarda zan rabaka da wacce kake cewa kai kafi cancanta da ita".
Ya karashe yana nuna Dr.Karami da dan yatsa cikin tsananin bacin rai mara yankewa da sauri ya juya yana kokarin barin wajan amma jin Dr.Karami yayi gyarar murya mai sauti ya sanya shi juyowa murmushi ya gani dauke a fuskarsa mai ma'anoni masu yawa.
"karka manta da abotarmu domin ban sako ta a ciki ba amma tun da kace mu ajje komai a gefe to nima zan dauko makaman yaƙi na kuma za a buga ni da kai a ga wanda rana zata rigashi faduwa".
Kallon na raina wayon ka Dr.Aqeel yayi masa ya ja kwaɓa.
"Ok Hakan na da kyau ina tsumayenka".
Yana karasa fadin haka ya juya da sauri ya faÉ—a cikin motarsa ya fizgeta kamar wanda zai tashi sama.
Sosai tashin hankali ya bayya a fuskar Dr.Karami duk juriya da kai zuciya nesa da yake yi akan sabon halin da Dr.Aqeel ya kirkira ya dorawa kansa abin da bai taba zato ko tsammani ba bai taba kawowa kansa Dr.Aqeel zai iya katse ABOTA dake tsakaninsu ba ya sha mamaki sosai akan haka zuciyarsa ta jima tana ciwo akan hakan yayi hakuri ya kau da kai amma sai da ya sanya shi tsayawa ya dube shi har suka fara SA'INSA a tsakanin su.
Tun ranar da aka sallamo Mariya daga asibiti gabadaya ya ga ya rikice masa musamman da yaga Mariyar sam taki kula kowa a tsakanin su ko kallon banza ba su ishe ta ba amma shi ya danne zuciyarsa bai nuna komai ba sai shi ne zai dinga ajje masa bakaken maganganu ba tare da laifin sa ba domin shi dai bai ga abin da ya aikata masa ba har da zai din ga daukarsa a wani macuci har yake ikirarin haduwar su ba tayi kyau ba.
Jingina yayi da bayan motarsa yana harÉ—e hannayensa a kirji sosai ya runtse idanuwansa jin yarda zuciyarsa ke kartawa kamar zata yayyage komai yake ji yana zama kunci gareshi komai ya sauya masa sosai yake jin yarda so yake wahalar dashi bai san so haka yake ba bai san ana faÉ—awa har haka a cikin so ba bai taba tsammanin zai ganshi a DUNIYAR SO yana gararamba ba amma yau shi yake yawo a ciki kamar wani wanda bashi da mafadi ya fado duniyar nan.
Numfashi ya kuma ja kafun ya haÉ—e wani yawu mai tauri ya dubi kofar gidansu Mariya na ba dadi yau cikin satin sa na uku kenan yana zuwa amma Mariya taki kula shi ko fuskarta taki bari ya gani tun ranar da suka dawo da ita gida aike goma zai amma ba biyan bukatar ko daya daga ciki tashin hankalin sa na daduwa abun ya zame masa goma da ashirin ga lamarin Mariya ga wannan shi kuma yana masa hayaniya akai can kuma gida Hajiya ta saka shi gaba bai san me zai yi ba kansa kara kamawa da wuta yake yi ya kasa yin wani tunani ma na kirki ko zai samu mafita.
Ya jima tsaye a wajan kafun ya yanke hukuncin barin wajan domin ya tabbata ba fitowa za tayi ba shikuma ba iya shiga gidan zai yi ba domin kuwa gabadaya bai son su hadu da Umma kwata-kwata.
Yana kokarin shiga motarsa ya hango Mu'azzam ya fito da gudu yana waige da alamun biyo shi akayi da sauri ya dakata yana mai da kofar ya rufe kamar daga sama ya hangota ta tunkaro kofar fitowa tana ta faman kiran Mu'azzam amma ina sai kara wutar gudun sa yake yi wata irin mutuwar tsaye yayi ganinta ta canza sai yaga ta kara masa kyau da haske sai dai ta kara ramewa sosai harÉ—e hannayensa yayi a jikinsa kirjinsa da yake faman dokawa da sauri-sauri a daidai lokacin Mu'azzam ya iso gareshi ya kankame shi yana neman ya ceceshi amma shi ina fuskarsa da komai nasa na kan Mariya a daidai lokacin ita kuma ta dube she wata irin razana tayi kafun idanuwanta su yo waje sosai da sauri ta juya ta fada cikin gida cikin wani irin hali mai ciwo a zuciya.
Ya shafe lokaci kafun ya ja wani gwauron numfashi mai sauti ya durkusa ya dafa kafadar Mu'azzam yana kallon sa abin mamaki fuskar Mariya yake ganin tana yi masa gizo tana mai sakin tattausar murmushi a gareshi sai da Mu'azzam ya taba masa fuska sannan ya dawo hayyacinsa yana dubansa kafun ya ce dashi.
"Me kayi aka biyo ka da gudu haka hala rashin ji kayi ko?".
Juyawa yayi ya kalli kofar gidan kafun ya dubi Dr.Karami da ya kureshi da idanu.
"Yah Mariya ce ke kuka a daki shine na fadawa Umma kuma ta hanata kukan to shine don Umma ta shiga bandaki shine ta biyo ne don ina ce mata mai kukan banza".
Dariya Dr.Karami yayi amma cikin zuciyarsa ji yayi wani zafi na kawo masa farki sosai tashin hankalinsa na daduwa kalmar 'kuka' da yaji Mu'azzam ya ambata tana yi ita Mariyan sake daga kai yayi ya dubi kofar gidan yaji kamar ya mike ya fada cikin gidan ya lallashe ta.
"je kace ina kiranta".
Ya fadi yana dubansa cikin idanu shima Mu'azzam din dubansa yake kafun ya shiga girgiza kai.
"a,a dukana za tayi kuma ko an aika ta zo ba ta fitowa kullum".
"Me yasa?".
Ya fadi bugun kirjinsa na sauyawa da sauri-sauri
Girgiza kai yayi kafun ya sake kallon kofar gidan.
"nima ban sani ba kawai dai kullum a daki take zama ba ta fitowa ko Umma bata tayawa aiki".
Runtse idanunsa yayi jin wani abu ya tokare masa zuciya kafun ya sake fadin.
"Ba ta da lafiya ne".
"Tunda ta dawo daga asibiti shikenan ina ganin kila bata ji sauki bane".
Mikewa yayi ya saka hannu cikin aljihunsa ya zaro kudi masu auki ya mikawa Mu'azzam girgiza kai yayi alamun ba zai ansa ba sai da yayi dakyar sannan ya ansa.
"kace ina gaida Umma da Ita Mariyar kaji yi maza ka koma gida ba wanda zai dakeka".
Da gudu kuwa ya juya yayi gida shikuwa jin gina yayi da mota yana faman mai da numfashi sosai yake jin zuciyarsa wani iri jin halin da Mariya take ciki ji yake kamar ya kakkare mata damuwar ya dawo da ita kansa ya sani har da laifinsa wajan sanyata ko wani hali ta fada yana da kamasho in da ya san haka rayuwar zatayi musu inda ya san ALKALAMIN KADDARA haka zai rubuto musu wannan rayuwar da bai yi SAKE wajan bayyana mata yana son ta ba da ya furta mata tun lokacin da yake ganin bata cancanta ba ya san komai daren dadewa zata koyi son shi kuma zata ajje kalmar so da ya fadi mata tun lokacin baya har zuwa lokacin da za ta gane meye SO.
Da wannan kuncin zuciyar ya shiga motarsa ya bar kofar gidan kwanyarsa sai wuta take kokarin kamawa da ita gabadaya ya rasa me ke masa dadi a rayuwarsa dole ya san abin yi dole ya fuskarci wannan kalubalin dole ya nemi mafita a gareshi.
********
Tana zaune ta na aikin Cake wanda ya zama yanzu ita ce take yinsa Mariya ta zama abin da ta zama sosai lamarin na Mariya ke sha mata kai ta rasa mai ke damun 'yarta ta yau kusan wata guda kenan tun da aka sallamota daga asibita ta rasa gane kanta kullum cikin kuka take kullum cikin damuwa bata da aikin yi sai kuka abin na taba mata zuciya tayi faɗan tayi rarrashin amma bata sauya zani ba har ta zurawa sarautar Allah ido ta sani suna cikin yanayi na rayuwa duk yarda ta zo musu dole su anshe ta duk wani abun dake faruwa dasu na dadi da rashin sa ALKALAMIN ƘADDARAR su ce a haka ba yarda za suyi...
Tunanin ta ya katse lokaci guda da hanzari ta dawo hayyacinta jin an kwaso da gudu anyo waje gabanta ya yanke ya fadi daga idanuwanta tayi cikin fargaba da tsoro duk a tunaninta Mariya ce amma sai taga akasin haka Hafsat ce ta fito da gudu daga dakin Goggo Marka ta zube tana ta faman amai da kakari kamar wacce zata amayar da 'yan hanjin cikin ta amai take yi wanda ba komai a cikinsa sai ruwa da majina sosai ta rike cikinta tana faman nishi tana murkususu kamar wacce akayiwa dukan shan gishiri.
Da sauri Umma ta zare hannunta cikin kwabin da take yi ta dauraye hannayenta ta mike kan kafafuwan ta da sauri ta karasa inda Hafsat take wacce ta gama galabaita rikota tayi tana mata sannu gabadaya jikinta ya saki sai faman nishi take yi kamar wacce rai ke kokarin ficewa daga jikinta sosai Umma ta tauyasa mata ganin irin halin da take ciki lokaci guda duk ta zurma kamar wacce take amai da guda.
Ruwa ta debo ta bata ta dauraye bakinta sannan ta wanke mata fuska ta taimaka mata ta mike ta raka ta daki ta kwantar kafun ta dubeta ganin ba kowa a dakin.
"Dama baki da lafiya ne ina Goggo din take?".
Banza tayi da ita jin yarda cikinta da kasar mararta ke kartawa da wani irin azababben ciwo kamar yan hanjinta zasu zazzage sai faman juyi take tana cizon laɓɓanta idanuwanta a runtse sosai zuciyar Umma ta karyewa da yanayin da ta ganta a ciki sai faman sannu take mata jin ta kasa bata ansar tambayar da tayi mata sai da ta jima a tsaye ganin Hafsat ta lafa da murkususun ya sanyata juyawa tana kokarin fita har ta daga labule sai ga Goggo Marka ta sanyo kai ita da sauri ta ja baya Goggo Marka ta shiga dubanta da wani irin yanayi na tuhuma kafun ta leka cikin dakin ta hango Hafsat a kwance sake dubanta tayi.
"Lafiya me ya shigo dake dakina".
Ta fadi cikin tsawa tsawa da nuna bacin rai
"A,a Hafsat naga ta fito tana ta kalaya amai shine na taimaka mata ban san bata da lafiya ba".
"Ba ta lafiya fa ? Kika ce injiwa ya fada miki lafiyarta kalau sai dai in wani abu taci yake tayar mata da zuciya har ya kaita ga amai"..
Yanayin da take maganar kawai zaka kalla ka gane bata da gaskiya da sauri ta shigo dakin har tana bangaje Umma kayan da suke hannunta gabadaya suka watse Umma tabi kayan da kallo lokaci guda gabanta ya yanke ya fadi ganin kulin maganguna har su mataccen ƙadangare da sauri ta ja da baya ita ma Goggo Marka kayan tabi da kallo kafun ta dubi Umma a dan tsora ce ta shiga tattare kayan tana cewa.
"to ki fita mana ko kin tsaya kina kare min kallo ko da kwai wani abu ne?".
Tana magana jikin ta na rawa da sauri Umma ta fice daga cikin dakin gabanta na kara tsananta faduwa sai sunayen Allah take kira sosai zuciyarta ta shiga zargin abin da tagani fata take yi Allah yasa hakan kar ya tabbata kar dai ace wani abun Goggo Marka take aikatawa domin sosai ta ji a jikinta akwai wani abu a boye dangane da abin da ta gani a yanzu ta jima tsaye a kofar dakinta tana tunani kafun ta isa wajan aikin da take yi gabadaya taji ya kuma sure mata kwasar kayan tayi ta fada cikin dakinta...
  *_Kamala Minna_*😘😘😘
Post a Comment (0)