UKU-BALA'I 46

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA SHIDA.
Zuciyarta zafi take sosai kwanyarta sai kokarin kamawa da wuta take yi ta rasa komai nata mai armashi ta rasa duniyar guntun farin cikinta dake rayuwarta sosai take cikin yanayin kunci zuciyarta sai faman yayyagewa take yi da girman tashin hankalin da take ciki kuka ya daina samun gurbi a idanuwanta HAWAYEN ZUCIYA su ma kan su sun dai samun gurbin zuba komai ya kafe komai ya daina samun numfashi mai kwari daga gareta ba ta san ya zata kwatanta wannan lamarin ba bata san ya zata dauke shi ba bata san mai yasa duniyarta take kokarin yamutsewa ba koma tace ta ya mutse ALKALAMIN KADDARA yayi rubutu mai tsauri akanta bata yi tsammanin rayuwarta zata kare a haka ba farin ciki babu shima kwanciyar hankali babu komai da komai babu kawai dai...
Wani irin kartawa zuciyarta tayi da hanzari ta mike daga kwancen da take tana sanya hannayenta duk biyu tana dafewa idanuwanta a runtse kamar wacce ake sokawa karfe mai tsanani jar wuta a jikinsa numfashi take da kyar tana jin kirjinta na kara tsananta bugawa mikewa tayi kan kafafuwanta tana faman cizon laɓɓa kamar zata fizge su daga mazauninsu.
Kai kawo ta shiga yi cikin dakin a hankali tana duban su Umma da suke barcinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da matsala ba sosai take tausayin kanta sosai take ganin kamar ita kadai ce a filin duniyar nan take cikin tashin hankali gani take kamar ita kadai ne so yake bugawa yadda ransa ke so kamar wata ball bata san ya zata dauki AL'AMARIN SO ba a filin rayuwarta bata san ya zata kwatanta bala'in da fada ba A DALILIN SO ba tana shakka akan cewa so yana da dadi gaskiya ba za ta amince da haka ba so guba ne ba komai ba.
Haka tai ta safa da marwa a tsakar dakin har zuwa wani lokaci mai tsayi cikin DUHUN DARE ba tare da ko yaya ne barci ya so kama ta ba in aka ce ma barci zai zo wajan ta zata karya ta domin kuwa ita a karan kanta ta manta yaushe rabonta da yin barci mai ansa suna barci...
"Ke Mariya wai lafiyarki kalau kuwa?".
Kamar daga sama taji muryar Umma a dan razane ta juya ta dube ta zaune ta hangi Umma ta kafeta da idanu kafun ta cigaba da fadin.
"Ke yanzu fisabilillahi kina ganin haka ya dace miki Mariya kina zaton wannan abin da kike yi shi ne zai zame miki mafita a filin duniyarki bana zaton haka wannan damuwar da kike shiga ba karamar matsala zata jefa ki ba ke ko fada ba zakiyi wa kanki ba yaushe ki ka farfaÉ—o daga ciwo wa yayi zaton ma za ki sake WATA RAYUWA a duniyar nan".
Rausayar da kai tashiga yi cikin rashin abin cewa ta sani duk maganganun da Umma take fadi akanta gaskiya ne amma ita bata san ya zata koyi duk wannan abubuwan ba zuciyarta sosai da sosai take zafi sosai take cikin tashin hankali wanda ba ta san ya zata kwatanta shi ba.
"Zo ki zauna muyi magana".
Cewar Umma cikin Muryar rarrashi da tausayin 'yar tata a hankali Mariya ta ja jiki ta isa kusa da ita ta zauna kafun ta dago ido ta dubi Umma jikinta ya shiga rawa kamar wata mai jin sanyi.
"Umma ina cikin bala'i ban san ya zan kwatanta shi ba bana zaton na shigo duniyar nan a nasara bana tunanin akwai wata rayuwa da zan yi har karshen numfashi na bayan wannan...".
Sosai tausayin ta ya kara rikita zuciyar Umma nan da nan ƙwalla suka tarun mata a ido bata bari Mariya ta gani ba domin kuwa ita ta san halin da take ciki akan duk matsalolinta amma bata nuna mata ba ta son abin da zai kara dagula mata lissafi dakatar da ita tayi.
"ki daina fadin haka Mariya na sha fada miki duk abin da ki ke ganin yana faruwa da baya dama tun fil'azal ALKALAMIN KADDARA ya zana masa haka a KUDINSA don haka Mariya ke daina cewa ke ce kika fi kowa rashin rabo a duniyar nan ke taki matsalar kika sani in da zaki ga na wani zaki sha mamaki zaki ce ke ba komai bane ya same ki godiya zakiyi wa Allah duk wannan abubuwan suna cikin KUDIN JARABAWARKI...".
"Sauki fa kika ce Umma?"..
Mariya ta fadi da wani irin yanayi mai karya zuciyar mai sauraronta kafun ta ja numfashi tana tura laɓɓanta cikin baki.
"bana tunanin haka bana zaton akwai wanda ya kai ni rashin nasara a filin duniyar nan...".
Da sauri Umma ta rufe mata baki muryarta na karyewa kamar mai son fashewa da kuka.
"A,a Mariya ki daina yawan batun nan zaki iya yin saɓo Allah zai yi fushi dake ki dinga tunanin bayanki ki dinga tuna wanda ya fiki Mariya akwai wanda yafi ki da yawa su zaki duba domin ki tabbatar da cewa ke rayuwarki ma a haka akwai farin ciki shin kina tunani kuwa akan wanda suke faɗowa duniyar ba tare da komai ba ba uwa ba uba ba dangi shin bakya tunanin irin rayuwar da suke yi shin kina tunanin in suka shiga matsala akwai wanda yake rarrashin su ke ki godewa Allah kina da masu duba ki har su ji ƙan ki Mariya rayuwar nan da kike gani ba wai farin ciki bane a cikinta ba wani nishadi a cikinta duk wanda kika ji yace duniyar nan akwai dadi to ki tabbatar auren sa duniyar tayi ki sani duniyar nan ba wai zama ake yi na dindindin ba komai dake faruwa jarabawa ce akwai ranar da komai zai sauya kuma zai canza...".
"zuwa yaushe Umma zuwa yaushe kike tunanin rayuwa zata sauya bana tunanin haka bana tunanin rayuwa zata sake buÉ—e mana wani shafi bacin wannan ki duba tun da na ta so rayuwa take juya mana baya rashin gata rashin Uba rashin kwanciyar hankali komai ma Umma babu a rayuwar mu ta yaya kike zaton zan yi farin ciki?".
Maganar take yi cikin rashin hayyaci muryarta na kara buÉ—ewa bakinta sai rawa yake yi Umma kallonta kawai take yi tana faman gyaÉ—a kai hawaye sai bin kumatunta suke yi bata san ya zata kwatanta wannan al'amarin ba ita gabadaya komai ya kwance mata komai ya kara dagule mata numfashi ta ja mai karfe kafun ta hadiye wani yawu mai tauri ta sake duban Mariya bayan ta dauke hawayen da suke faman zubo mata gabanta yana todakawa so take yi tayi magana amma tana tsoron yarda komai zai watse in batayi wasa ba amma ana ta tunanin ita ce kawai hanyar mafita a garesu.
"Mariya mai zai hana ki zabi daya a cikin su tun da abin da ya kasance haka duk wannan kai ruwa ranar da ake yi bana tunanin zaki iya zama matar su su duka mace bata auren namiji sama da daya maza ne suke da wannan damar ta aure mace sama da daya kokari zakiyi ki baiwa zuciyarki juriya da hakuri ki runtse idanu ki zabi daya a cikin su".
Galala Mariya tayi da baki tana kallon Umma da wani irin yanayi gabanta na tsananta bugawa kafun wata dariya ta kwace mata kamar wata sabuwar kamu sosai take duban Umma wasu hawaye na zubo mata da take jin su kamar garwashin wuta suna saukar mata a fuska laɓɓanta ta ciza sosai har sai da taji zafi ya ziyarce ta kafun ta sake su.
"Zabi kuma Umma? bana tunanin cikin UKU BALA'I zan iya daukarwa kai na daya gaskiya bana tunanin a filin duniyar nan ko zan rasa mai so na zan iya daukar wani a cikin su bana son su su dukan na hakura da su domin kuwa komai ya faru dani a dalilin su ne duk wata bakar rayuwa da wahalar ta da na shiga a dalilin su ne ba su da tausayi ba su da imani sam a zuciyarsu suna son kan su da yawa in da suna jin tausayina wallahi ba za su yi mani haka ba Umma WASU MAZAN san kan su kwai suka sani da burinsu da suke fatan cimmawa akan abinda suke so ba ruwan su da abin da zai faru in dai ba akan su ba ne".
"A,a Mariya ki daina fadin haka duk ba mafita bane mafitar kenan ki zabi daya a cikin su dolen su ne su kyale ki tun da ba dukan su zaki hada ki aura ba miji daya a ka sani mace na aura a al'adance haka a addinance".
Wani murmushi mai ciwo ta saki.
"Bana tunanin zan iya daukar daya daga cikin su...nifa Umma na dawo daga rakiyar su a rayuwa ta ba zan sake kokarin faÉ—awa matsalar rayuwa A DALILIN ÆŠA NAMIJI ba an yi na farko ba za a sake yin na biyu ba na gwanmace in zauna haka ba aure har na karashe rayuwa ta...".
"Ya isa haka Mariya nace miki ya isa haka abin naki yana neman zama rashin hankali kuma kina nuna nufin don wannan abin ya faru dake shikenan kuma kin yanke rahama a rayuwarki kenan butulci zaki yi wa Allah to tun wuri ki san abin yi domin ba zan lamunci wannan shirman naki ba".
Tana gama fadin haka ta koma ta kwanta hakan ba karamin tashin hankali ya saka Mariya ba duban Umma take yi da mamaki zuciyarta sai faman bugawa take yi sosai take jin wani iri maganganun Umma sai tsananta sauti suke yi a cikin kanta runtse idanu tayi tana daura hannayenta saman kirji tana jin yarda yake bugawa cikin wani irin yanayi sake buÉ—e idanu tayi ta kalli Umma wacce tayi shiru ta san ba barci take yi ba sosai ta lura ranta ya dan sosu kin amincewa da tayi da maganar ta gyaÉ—a kai tayi kafun ta zabga tagumi hannun bibbiyu.
******
Tunda Baseera ta shigo take kallonta da wani irin yanayi na tausayawa ganin yarda Mariya ta fige ta kanjame kamar wata mai amai da gudawa ko da yake irin wannan bala'in da take ciki komai ma zata iya zama numfashi ta ja tana zama bakin katifar da Mariya take zaune tayi mata kuri da idanu sai faman yake take yi wanda sam bai mata kyau ba.
"Kin gama fushin da ni kenan kin ga dama kin zo".
Cewar Mariya tana hararar Baseera da jikinta ya gama yin sanyi da Al'amarin Mariya sai faman gyaɗa kai take yi zuciyarta na tsananta bugu kafun tayi kokarin kirkiro yaƙe ita ma ta yi mata.
"Ban san me yasa har yanzu Baseera ki ka kasa daidai ta komai ba dama fa a hannun ki take amma kin kasa amfani da ita duk wannan abun dake faruwa ke ce kike da mafita amma kin ki amfani da ita ban san me yasa ba?".
Ta karashe tana janyo hannun Mariya ta damke a nata nan da nan sai ga hawaye a idanuwansu su duka numfashi suke saki a hankali Mariya sosai take jin wani iri a zuciyarta ana cewa tana da mafita a hannu amma ita ta ka sa gane a ina mafitar take a gareta komai ta kasa tunani akan sa kwanyarta a tsaye take cak! tana babbakewa bata da wani kuzari ko jarumtar yin wani tunani.
"ki yi kokari don Allah ki samarwa kanki farin ciki da kwanciyar hankali har da muma mu sa mu don Allah".
Baki ta shiga motsawa tana kokarin yin magana amma ta kasa sai da ta runtse idanu kafin ta buɗe su da ƙyar ta daga laɓɓanta.
"Ban san me zan yi ba Mariya sosai na kasa yin komai bana so wani abu ya sake hadani da su Umma tace wai zabi na gareni har da mafita kamar yarda ke ma kika ce amma na kasa tuna haka bana tunanin haka zai yuwu".
"Mariya ke ki da wannan damar sai dai kin kasa amfani da ita ya kama ta ace kin fidda daya daga cikin su ina tunanin haka shi ne kawai mafita a garek...".
Da sauri ta fizge hannunta tana ja da baya kamar wacce aka doÉ—anawa garwashin wuta duban Baseera take yi cikin wani irin yanayi idanuwanta sun kara kaÉ—awa sun yi jajir sai faman hirji take yi tana jan numfashi yana kokarin kwace mata kai ta ke girgizawa a hankali tana mai runtse idanunta kafun ta kai hannunta daidai kirjinta ta dafe da karfin tsiya.
"Ba zan iya ba Baseera bana son su na tsane su".
"Zaki iya Mariya za ki iya ki na son su baki tsane su ba ni na san haka daurewa zaki yi don Allah".
Bude idanunta tayi da sauri tana duban Baseera kafun lokaci guda ta kifa kanta kan katifar tana faman nishi dakyar kamar wacce aka shake a makoshi....
  *_KAMALA MINNA_*😘😘
Post a Comment (0)