UKU-BALA'I 49

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA TARA.
Sosai taji a jikinta kamar akwai abin da ke faruwa don haka ta dubi Baseera da taji ita ma tayi shiru tunda ta kira sunan Yah Tareeq dubanta tashiga yi ganin abin da take yi da idanu tana dakune fuska kamar wacce aka tursasa sai tayi abu ba tare da ta so ba.
  Haka kawai taji gabanta yana faɗuwa dago kanta tayi gabadaya ta sauke wajan Tareeq wanda yake ta faman biyawa Baseera karatu ta hanyar idanu da hannu ganin Mariya ta dago kai da sauri ya wayance yana faman cin magani.
 "wai shin me ya faru ne naji ihun ki?".
Ya fadi yana duban Baseera da tayi tsiru-tsiru gabanta na dokawa tsoronta daya kar Mariya ta gano abin da suke yi a tsakanin su akan ta ne susa keya tashiga yi kamar maras gaskiya tana faman yak'e.
  "Bakomai Yah Tareeq".
Ta fadi tana mai duban Mariya wacce ta komar da kanta kasa tana nazarin yanayinsu tabbas akwai wani abu a boye a tsakaninsu wanda zuciyarta ta tabbatar mata akan ta suke komai haka kawai ta sha jinin jikinta.
 "Uhmm Yah Tareeq..".
Da sauri ya juya har yana kokarin tuntube wajan fita nuni da Baseera tayi masa kamar Mariya ta gano su shi kuma abin da bai kauna kenan sam! Mariya ta gano halin da yake ciki a kanta.
Son ta yake yi amma ya rasa yarda zai yi ya fuskance ta ba yarda bai yi da Baseera tayi masa kamfe ba amma ta kekeshe kasa ta ki yarda ba abin da bata fada masa ba akan halin da Mariya take ciki amma ya ki amincewa giyar soyayya sai kwasar sa take yi amma ya kasa zuwa ya tunkari Mariyar.
  Wani murmushi Baseera ta saki lokacin da ta hango Tareeq na kokarin bugar bango da sauri ta kalle shi shima kallon ta yayi yana dakune fuskarsa sannan ya fice daga cikin dakin..
 "Mariya wai shin me ke faru ne naga duk jikin ki yayi sanyi haka".
 Baseera ta katse shirun da yayi wa dakin ado.
A hankali Mariya ta dago da kanta ta dubi Baseera cikin yanayi na tuhuma sai da ta sha jinin jikin ta ganin irin kallon da Mariya take yi mata.
Murmushi Mariya ta saki na yak'e kafun ta nutsu fuskarta na komawa yarda take a shigowarta alamun damuwa.
 "Sosai na kasa fahimtar komai, ban san ya zan fuskanci wannan lamarin ba".
Ta fadi tana mai tura laɓɓanta cikin bakinta fuskarta na kara bayyanar da tsantsanr damuwar da take ciki zuciyarta take ji tana kara matsewa da wani irin yanayi mai girman gaske haka kawai taji tana shakka akan ta fadiwa Baseera halin da take ciki a wannan lokacin.
 Numfashi taja mai tsayi kafun ta mike tsaye tana kai kawo cikin dakin na dan lokaci sannan ta tsaya cak! Ta juyo ta dubi Baseera da tayi shiru tana sauraron zuciyarta itama na ta fadan tsalle-tsalle da fargaban abin da take son kawowa Mariya din so take yi kawai fatanta ya tabbata Allah yasa maganar da Mariyar zata yi ya zo daidai da gaɓar da take so zata yi amfani da wannan damar domin samun abin da take bukata duk da zuciyarta na ta faman gargaɗinta ita akaran kanta jin wani iri take yi kan lamarin amma bata san ya za tayi ba.
 Mikewa tayi ita ma Baseera tana takawa zuwa inda Mariya take tsaye jikinta na kara karyewa sosai zuciyarta na bugawa cikin wani mataki na rashin tsammani.
Dafa kafadar ta tayi tana mai ajiyar zuciya.
 "Ban fahimce ki ba mai ke faruwa ne?".
Cewar Baseera cikin rashin abin cewa domin gabadaya ta shiga RUƊANI kawai jarumta ce take kokarin sanyawa kanta amma zuciyarta kamar zata faso tayo waje don fargaba.
 "So nake yi ki bani shawara Baseera na gaji da wannan Bala'in gwanda na san abin yi tun kafin zuciyata ta buga na mace a banza a wofi".
Zaro idanu tayi sosai jin abin da take cewa da sauri ta kamo hannunta ta saka cikin nata tana dankewa da wani irin yanayi.
 "A,a Mariya ki daina fadin haka wannan ba magana bace sam! komai da kika ga ya na faru dake ALKALAMIN ƘADDARAR ki ne a haka ki dauki komai a matsayin JARRABI a rayuwarki kar kiyi gangawar yanke hukunci ki bi komai a sannu karki ji zuciya ta kwashe ki ki zo kina dana sani".
Runtse idanu Mariya tayi tana jin zuciyarta na kara ya mutsewa da wani irin mataki tana mikata wani waje na daban buɗe idanunta tayi sosai kan Baseera wanda suka fara kaɗawa.
 "Hmm Baseera kenan kin fi kowa sanin halin da nake ciki kin fi kowa sanin Bala'o'in da na shiga dole na nemi mafita tun wuri".
 "Nasan da haka Mariya amma ki saurara ki yi tunani kafin ki yanke hukunci".
Sosai take dubanta karo na ba a dadi kallo ne wanda ya sanya Baseera shan jinin jikinta gani take yi kamar Mariya tuhumarta take bisa yanayin da ta lura yak'e ta shiga yi kafun Mariya ta kau da kai daga kallon da take mata ta ja wani numfashi mai tsayi tana tura laɓɓanta cikin baki tana cizawa.
 "Wa ya dace na zaɓa a cikin su wa kike ganin shine INGANTACCE wanda ya dace da rayuwata?".
  'An zo wajan'. Zuciyar Baseera ta fadi tana wani irin dogawa sosai zaka gane firgici a fuskarta idanuwanta a warwaje ta shiga motsa baki tana son yin magana amma ta rasa ta ina zata fara a hankali ta ja hannun Mariya suka koma bakin gadon suka zauna dukkaninsu sai faman ajiyar numfashi suke kamar wadanda suka yi aiki mai wahalar gaske suke zaman hutu.
 "Kin fasa canza wani saurayin ne daga cikin UKU BALA'In naki?".
Baseera ta fadi tana faman sakin murmushin yake gabanta sai dokawa yake so take yi ta dauko gaɓar da zata sanar da Mariya komai amma tana fargaba da tsoro akan abin da zai je ya dawo bata san ya Mariya zata dauki lamarin ba bata san ya zata kalle ta ba anya kuwa ba zata ce ta fiye SON ZUCIYA da son kanta ba? Gyaɗa kai tayi.
 "Duk mu ajje wannan maganar gefe Baseera na hakura da komai wallahi na mikawa Allah lamarina hukuncin sa kawai naƙe bukata a duk yarda ya zo zan anshe shi".
Jin abin da tace ya sanya Baseera dubanta sosai cikin sanya wa kai jarumta duk da dokawar da zuciyarta ke yi.
 "Nikam nake ganin kamar ki canza zai fi miki lura da yanayin rigimar da kike ciki a yanzu in har kika zabi daya a cikin su kina ganin za a samu maslaha a tsakani kuwa... ko da yake hakan da kike gani shima ya dace tunda ba dukkansu zaki aura ba dole in kika zabi daya dole sauran su yi hakuri tun dake ba MATAR MUTUM UKU bace matar mutum daya ce namiji ne MIJIN MACE HUDU ba ma daya ba".
 Tunda ta fara maganar take lura da ita sosai kamar akwai wani BOYAYYEN AL'AMARI da take boye mata haka kawai taji ba ta yarda da ita ba sosai take jin haka a jikinta.
 "Uhmm shikenan tom...ko daya ke ke ma kin kawo shawara amma kuma yanzu in nace zan nemi wani daban me kike tsammanin zai faru?".
Murmushi tayi sosai wanda iyakarsa laɓɓan bakinta.
 "Mazan ne ai ba wuya suke ba sai dai kice nagartarsu ce za ta yi wuya baki san wanda zai zo gareki ba akwai masuyi don Allah akwai kuma masu zuwa da wata manufa ta daban...".
Tayi shiru alamun maganar da take bata karasa ta ba numfashi ta ja kafun ta dubi Mariya tana kamo hannunta ta danke cikin nata.
 "Mariya dama akwai maganar da nake so muyi dake don Allah amma ina so ki dube ni da idon basira kiyi mani kyankyawar fahimta don Allah ba a son raina zaki ji komai ba amma na rasa yarda zan yi ne".
Gyaɗa kai Mariya ta shiga yi dama taji ajikinta akwai wani abu a boye.
 "Yah Tareeq ya jimawa yana kawo min maganarki tun Time din da ya dawo daga School kuka hadu shikenan yake ta faman zarya yana cewa dani wai...".
Gaban Mariya yankewa yayi ya fadi lokaci guda ta ji jikinta ya dau ƙyarma amma bata bari hakan yayi tasiri wajan bayyana ba illa murmushin da tayi kokarin daurawa a fuskarta tana karawa Baseera kwarin gwuiwar fadin abin da take son fadi din.
 "Son ki yake yi Mariya amma ni dai...".
Wata irin mikewa tayi gami da fizge hannunta idanuwanta a warwaje ta shiga duban Baseera da tayi mutuwar tsaye kallonta take yi cikin wani irin yanayi bata taba tsammanin maganar da zata yi mata ba kenan bata taba kawo hakan akan taba sosai taji wani iri sosai take jin ta wani mataki wanda ba ta san ya zata kwance kanta ba 'So kuma Yah Tareeq din yake so na?'. ta shiga fadin haka a zuciyarta tana faman girgiza kai idanuwanta na kara rinewa zuwa ja bakin ta na rawa take duban Baseera wacce ita gabadaya a rikice take dama ta san za ayi haka sosai ta san Mariya ba zata dauki wannan lamarin ba domin kuwa an shata ta warke ita kanta ba zata goyi bayan hakan ba duk da dai dan uwa ne kuma za ta so ace Yah Tareeq ya auri Mariya sosai take ganin dacewar haka amma ina! ba damar hakan.
 A hankali ta shiga ja da baya ta girgiza kai cikin tsananin tashin hankali.
 "Kiyi Hakuri Baseera don Allah ki yi hakuri ki fahimce ni zuciyata... zuciyata ba zata iya bada wani GURBIN SO ba ta rigaya ta gama so ta rigaya ta gama illatuwa AKAN SO ko nace miki zan sake so to nayi miki karya kiyi hakuri ba zan iya ba".
Tana gama fadin haka tayi hanyar ficewa da sauri kanta take ji yana wani irin sarawa gabadaya taji duniyar na juya mata a haka har ta sauka Allah ya taimake ta ba kowa a falon cikin hanzari ta fice daga cikin gidan baki daya ta dauki hanya sai faman zancen zuci take yi kamar waya zararriya.
Ita kuwa Baseera hada kai tayi da gwuiwa tana jin yarda zuciyarta take zafi sosai bata so yin wannan maganar ba dama can abin da zai faruwa take guda bata son abin da zai bata kawancensu akan Yah Tareeq ba yarda bata yi dashi ba amma yaki yarda yanzu ya zama dole ta fada masa gaskiya duk da yana dan'uwanta ba za ta so abin da zai cutar da Mariya duk da itama tana kwadayin yayan nata ya auri Mariya amma lokaci ya kure ba damar yin haka din.
 *****
Tafiya kawai take tana saka kafarta duk inda ta sauka ba ta tsaya neman abin hawa ba domin bata da wannan natsuwar Allah ya taimaketa har ta isa unguwarta.
Kallo daya zakayi mata ka gane bata cikin natsuwar sam! Cikin wannan yanayin ta iso layin su har zuwa wannan lokacin bata dawo hayyacin ta ba kamar daga sama taji ta bangaji abu mai girma hakan ya sanyata yin baya luuuu tana kokarin faduwa runtse idanu tayi sosai tana jiran jin ta a kasa amma sai akasin haka rikota taji anyi sosai an dagota wani irin Shock taji jikinta ya dauka ya mikawa kwanyarta da zuciyarta lokaci guda suka tsaya cak! da aiki.
 A hankali ta shiga kokarin buɗe idanuwanta zuciyarta na dawowa hayyacinta tana bugawa fargabarta daya Allah yasa ba wani ta buge ba zai hukunta ta...
Bata gama tunanin ba ta ji gabanta ya yanke ya fadi lokacin da idanuwanta suka buɗe akan fuskarsa kallon shi ta shiga yi shima kallonta yake yi da tattausar murmushi a fuskarsa gabadaya taji ta a wani irin yanayi jikinta sai ansa wani bakon al'amari yake yi bata yi kokarin kwace kanta ba domin ji tayi gabobin ta gabadaya kamar sun daina aiki motsi ma ta kasa yi.
Runtse idanu tayi sannan ta buɗe izuwa lokacin ta fara gano komai dake faruwa da sauri ta kwace kanta daga gareshi tana ja da baya idanuwanta har zuwa lokacin ba su bar cikin nasa ba sai faman ajiyar numfashi take yi mai girman gaske.
 Sosai ya fita shiga cikin yanayi mai girman gaske zuciyarsa yake ji tana dokawa da wani irin yanayi zuciyar na kara buɗewa sosai idanuwansa suna dauko masa wasu abubuwa masu muhimmanci daga idanuwanta suna sauke wa akan sa.
A jiyar zuciya yayi murmushi na kufce masa a fuska kafun ya kau da kai zuciyarsa na kara saurin bugu ita kam gabadaya ta gama tafiya wani mataki da sauri ta fara daga kafafuwanta da take ji suna kokarin lauyewa su zubda ita kasa a haka har ta zo gilma shi.
"MARIYA!".
Ya fadi da sauti tsayawa tayi cak! zuciyarta na bugawa kafun ta dubeshi na yan sakanni sannan ta ja jiki ta bar wajan cikin hanzari domin bazata iya tsayuwa ba ta tabbata in tajima a haka sai dai a tsince ta zube a kasa tana jin zuciyarta na kara buɗewa da lamarin Dr.Karami bata san mai yasa haka ba sosai take jin GURBIN SON da ta bashi a zuciyarta yana kara buɗewa yana kara fadi yana saukar da wasu lamuraka masu taushi a cikin zuciyar ta ta...
 *_KAMALA MINNA_*😘😘😘
Post a Comment (0)