UKU-BALA'I 48

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS.
Cikin kwana biyun da tayi bayan haduwarta da Dr.Karami gabadaya ta gama rikiciwa ta rasa mai ke yi mata dadi a rayuwarta zuciyarta sai faman zillo take akan lamarin sa ta rasa ma me za tayi.
 A hankali take kokarin saita kanta da samo mafitan da take ganin ya dace da ita sosai take hana idanuwanta barci tana kai kukan ta wajan Allah domin ya zaba mata abin da yafi zama alheri a rayuwarta baki daya.
 Sosai zuciyarta ke matsewa sosai take jin nauyin da zuciyarta ke yi yana raguwa a hankali sosai take jin ya kamata ace izuwa wannan lokaci ta sarara wa kanta da rayuwarta sosai take jin lokaci yayi da ya kamata ta kawo karshen komai.
Amma ta yaya hakan zai kasance ta yaya hakan zai yuwu ba ta san ya za tayi ba sosai zuciyarta ta karkata zuwa ga Dr.Karami yawancin barci in tana yin sa duk shi take hangowa amma bata jin za ta iya aurensa.
Amma kuma bata san dalili ba in maganar aure tafi karkata ga Dr.Aqeel tana son Dr.Karami shima Dr.Aqeel tana jin son sa sosai a ranta ba kadan ba sai dai fili mai yawa Dr.Karami ya mamaye mata.
 Haka rayuwarta tayi ta tafiya har tsayin wata daya amma har lokacin bata yanke hukunci ba ta rasa wanda zata tunkaro ta fada masa halin da take ciki domin samun mafita tana tsoron sanar da Umma domin yanzu duk ta ja baya ta bata dama ita akaran kanta tayi abin da ya dace Baseera kuma har zuwa wannan lokaci taki yarda su hadu domin bata son ta zo mata da wani lamarin na daban bata so ta zaba mata abin da ba shi zuciyarta take so ba
Haka dai ta cigaba da dakon wannan lamarin har da karshe ta yanke zuwa gidan su Baseera domin ita kadai ce k'awa shakikiya da take ganin ya dace ta san matsalar kuma ta bata shawarar da take ganin ya dace.
Sanye take cikin daguwar riga mai kalar baki da ratsin ja kadan ta sanya jan gyale tayi rolling din shi a kanta sosai ya fito mata da kyanta duk da ba wata kwalliya ba ce ta a zo agani tayi amma tayi matukar kyau takalmi flat ta saka a kafarta sannan ta fito tsakar gida ta tadda Umma zaune ita da Mu'azzam duban su tayi su duka kafun tayi murmushi wanda iyakarsa fuska tausayin kanta da na Umma hadi da na kaninta kawai take ji tunowa da tayi da mahaifinta ko yana ina a halin yanzu Allah masani.
Numfashi ta ja mai tsayi har sai da Umma ta jiyo sautin sa juyowa tayi ta dube ta sosai.
 "Lafiyarki kalau kike wannan doguwar ajiyar zuciyar?".
Ta fadi tana kara duban jikinta.
GyaÉ—a kai tayi tana sake kokarin kakalo murmushi duk da kwallar da ke kawo mata farmaki a idanu.
 "Ba komai kawai dai...Uhmm yawwa Umma zani gidan su Baseera".
Kallon tuhuma Umma ta shiga yi mata na dan lokaci kafun ta gyaÉ—a kai.
 "Allah ya kiyaye hanya ki gaida mutan gidan amma karki dade fa kin ga yamma ta fara yi".
Ansawa tayi da 'to' sannan ta dubi Mu'azzam da yayi kuri yana dubanta dakune masa fuska tayi cikin tsokana.
 "Yah Mariya zan biki".
Ya fadi cikin sanyin murya zaro idanu tayi waje.
"Ni zaka bi caɓ! gaskiya a,a ba zan iya jigilar zuwa da kai ba ban son kaje gidan mutane kana yi musu rashin ji ka bar ni da jin kunya".
Ta fadi tana mai kama hanyar ficewa rau-rau yayi da idanu kamar zai yi kuka amma Umma ta hana shi ta shiga rarrashin sa.
Hafsat ce ta fito daga cikin daki fuskarta dauke da rashin walwala sai faman ya tsine fuska take yi kallo daya zakayi mata ka gane ramar da tayi ta É—ashe tayi fari sosai ga idanu duk sun zurma tayi firgai-firgai da ita.
Mariya dake koƙari ficewa ganin Hafsat ta fito ya sanyata tsayawa tana dubanta kafun ta dubi Umma cikin yanayi na tausayawa a hankali ta shiga motsa laɓɓanta.
"Uhmm Hafsa ya jikin naki...".
Wata harara da ta maka mata shi ya sanyata saurin tsuke bakinta tana kau da kai zuciyarta take ji tana wani iri tuni ta fahimta har zuwa wannan lokacin ba abin da ya canza a Hafsat duk rashin lafiyar da take fama da ita kamar zata mutu amma bai sanya komai ya canza ba duban Umma tayi itama Umma ita take kallo mai cike da 'Allah ya kara' ta maka mata harara da sauri ta ja jiki zuciyarta na kunci.
 "Munafukar banza sau nawa zance miki ki daina shiga lamarina ina ruwanki da rashin lafiya ta".
Furucin Hafsat kenan ta fadi da kyar kamar wacce akayi wa dole Mariya bata bi ta kanta ba illa karasa fita daga gidan cikin sauri da tayi.
*****
A hankali take tafiya zuciyarta ta mika ta can wani waje na daban kawai tafiya take ba tare da ta kula da inda take jefa kafa ba cikin wannan yanayin har ta isa bakin titi ta tsayar da mai Napep tana kokarin shiga wata bakar mota kirar 406 ta zo gilmawa ta gabanta kamar ance ta dago kai ta dubi motar wani irin faduwar gaba taji ya ziyarce ta da sauri ta runtse ido ta bude lokaci guda.
Shi din ne ba wani ba har ta mance yaushe rabon da ta ganni a idanuwanta tun lokacin da suka kusan kashe ta sai kuma ranar da ya zo wajan Hafsat abin yayi matukar bata mamaki yarda Huzaif ya kasance mai FUSKA BIYU a gareta yana bibiyarta yana ikirarin yana sonta sannan kuma yana son 'yar uwarta sosai taji lokaci guda ya fice mata a rai wani haushi da takaicin sa ya tsirga mata a rai domin ganin rainin wayo yake musu a tsakaninsu ya mai da su kamar wasu ball ya buga wannan ya buga wannan. 'Mtss.
Ta ja dogon tsaki dago kai tayi ta dubi mai Napep wanda shima ita yake kallo haushi ya sake turnuke ta ganin irin kallon da yake yi mata kamar ya ga wata bakuwar halitta.
"Tafi abin ka na fasa".
Ta fadi cikin haushi da takaici a rayuwarta ta ki jinin kallo shi kuwa kamar wani maye gabadaya ya juyo yana dubanta a hankali ta fara takawa tana barin wajan tana ji yana kiranta amma ko ta kansa ba ta sake bi ba.
Da sauri ta tari wani Napep din ta dane tana hango waccan sai faman dubanta yake yi har suka zo suka giftashi suna hada idanu ta galla masa harara gami da jan tsaki.
Tafiya sukayi sosai daidai wajan wani Mall ta hango motar Huzaif anyi Parking dinta daga dan gefe ta hango shi shida wata mace ya rike mata hannu sun tunkari cikin wajan zaro idanu waje tayi zuciyarta na harbawa da sauri-sauri kamar zata fallo daga cikin zuciyarta rintse idanu tayi zuciyarta na matsewa da wani irin bakin ciki tana tattama akan Huzaif anya kuwa son da yace yana yi mata na gaskiya ne an ya son gaske yake yi mata?
Girgiza kai ta shiga yi da sauri-sauri zuciyarta na mikata can baya lokacin da suka fara haduwa da yanayin da ya nuna mata ta tabbataa akwai alamar tambaya akansa bata san abin da ya shigar mata kai ba har ta yarda dashi bata san me yasa har ta saki da Huzaif ba sosai take ganin wautarta sai yanzu ta hango kuskuren da tayi har ta bashi fili a zuciyarta yake abin da ya ga dama aciki.
bata san sun wuce wajan ba sai da suka kai daidai wata hawa taji anyi sama da ita sannan tayi firgigin ta dawo hayyacinta ta shiga ware idanu gani tayi har sun shigo layin su Baseera wata irin ajiyar zuciya tayi mai karfi kafun ta runtse idanunta da wani irin yanayi a zuciyarta ta sanar da mai Napep daidai in da zai sauke ta.
Tana sauka ta bashi kudin sa ta dauki hanya domin karasawa gidan a bakin Get ta tsaya ta kwankwasa mai gadi ne ya leko ganin wacece ya saki murmushi ita ma murmushi tayi masa tana gaishe shi ya buÉ—e mata ta shiga a hankali take tafiya tana tunkarar kofar da zata shigar da ita cikin babbar falon haka kawai taji zuciyarta na kunci tana kuma bugawa cikin sauri-sauri a haka har ta isa bakin kofar ta rike Handle din haka kawai ta ji wata kasala da gajiya ta saukar mata sakin Handle din tayi ta dan ja baya tana ajjiyar numfashi tana mai lumshe idanu kamar mai jin barci a hankali ta sake kamawa idanuwarta a rufe ta tura gami da yin sallama muryar Mami da taji ta ansata ya sanya shiga ciki.
Zaune suke ita da Tareeq ya mike sosai kan kujera waya a hannunsa sai faman latsata yake yi Mami da ta ganta ta saki Murmushi kamar ko yaushi da sauri ta isa gareta ta durkusa ta na gaishe ta ansawa tayi kafun ta dube ta sosai.
"Ya jikin naki Mariya da fatan dai komai Normal ba abin da ke damun ki kuma?".
GyaÉ—a kai tayi ganin Tareeq ya juyo da sauri yana dubanta suna hada idanu tayi kasa da kai shi kuwa har zuwa lokacin idanuwansa na kanta ajikinta take jin haka ana kallonta wani tunani ne ya fado mata kar Mami tace bata kyauta mata ba dago kai tayi a hankali ta dube shi.
"Ina yini Yah Tareeq".
Ta furta murya can kasar makoshi tana rawa bai ansa ta ba illah duban sosai da ya sake yi mata jin da yayi ance bata da lafiya kafun ya numfasa ya ansata ba yabo ba fallasa tare da yi mata ya jiki.
Haka kawai taji wani iri yanayin da ya ansa mata cikin izza da nuna rashin baiwa gaisuwar tata muhimmanci ji tayi zuciyarta wani iri duban Umma tayi tana faman yake.
"Umma Baseera na ciki kuwa?".
"Eh tana ciki yanzun nan ta tashi daga nan wai barci zata yi".
Murmushi Mariya tayi tana mikewa kan kafafuwanta duk sai taji wani iri ganin yarda yake kallonta gabadaya taji kafafuwanta suna harÉ—ewa kamar zata zube a kasa sauri ta kara don kar tayi abin kunya agaban wanda bai san ya kula mutane ba in an kula shi mtss ta ja tsaki ta dane sama abin ta har ta kai matakin sauka sannan ta juyawa da kanta kasa aiko sai idanuwansu suka sarke zaro idanu tayi sosai ganin har zuwa wannan lokacin yana kallon ta wani murmushi taga yayi na gefe kumatu tare da lumshe idanu da sauri ta kau da kai tana jin zuciyarta na bugawa cikin hanzari ta bar wajan.
Tana isa kofar dakin Baseera ta tsaya cak! tana mai da numfashi me Tareeq yake nufi da ita mai yasa yake yi mata haka me hakan ke nufi wannan kallon na meye yake yi mata ta lura dashi in dai ta zo gidan nan ta same shi gaban Umma ya dinga sha mata kamshi kenan amma in bata nan sai ya dinga jifanta da wani kallo dake faÉ—ar mata da gaba ta rasa me yasa haka.
'me ya shafe ki dashi'
zuciyarta ta fadi mata da sauri ta daga kafunta alamun 'babu' ta tura dakin ta shiga ruf! ciki ta same ta waya a hannunta sai faman danne-danne take a waya da sauri ta karasa ba tare da Baseerar ta sani ba ta zaune gefenta tare da sanya dan yatsar ta daya ta ta sosa mata tsakiyar tafin kafarta wata irin razana da ihu Baseera tayi tana mai komawa can gefe ta cillar da wayar saman gado idanuwa a warwaje jikinta sai k'yarma yake yi Mariya ta kwashe da dariya kafun ta ce.
"Ke banza ni ce fa matsoraciya kawai".
Wata uwar harara Baseera ta cilla mata kafun ta ja wani numfashi mai nuna alamun ta firgita sosai.
"Allah ya isa wallahi ke kam an yi muguwa ai wannan sai kiyi ajalin mutum da tsoratarwa wallahi".
Ta fadi tana mai sankowa daga gadon tana isowa gareta ta zauna kallon sosai tayi mata kafun tayi murmushi.
"Baby din nan fa kyau kike karawa wallahi kamar wata sabuwar amarya meye sirrin ne ko dai...".
Sai kuma tayi shiru tana kyalkyalar dariya dubanta Mariya tayi cikin muryar mai rauni.
 "Magana na zo muyi don Allah Baseera ki bani shawara".
Sosai Baseera ta shiga dubanta ganin yarda fuskarta ta nuna alamun damuwa gyaÉ—a kai ta shiga yi tana kokarin yin magana suka ji an turo kofa gabadayan su suka juya suka Fuskanci kofar Mariya ce ta zaro idanu kafun ta kau da kanta gefe.
"Yah Tareeq".
Cewar Baseera tana duban sa murmushi ya saki yana duban Mariya kafun ya dubi Baseera ya kashe mata ido daya dakune fuska tayi tana mai girgiza kai ba tare da ta bari Mariya ta ganta ba.
  *_Kamala Minna_*😘😘😘
Post a Comment (0)