UKU-BALA'I 50

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA HAMSIN.
A hankali take duban Hajiya Layla gabanta na sake tsananta faduwa duban mutumin dake zaune gefe guda tayi sannan ta kalli dubun nan kudin da suke ajje cikin leda wani irin kartawa taji zuciyarta tayi da wani irin yanayi mai zafi da raɗaɗi ji take yi kamar ta hadiyi zuciya ta mace.
 Sosai ta ke jin komai na canza mata sosai take jin zuciyarta na sake yayyagewa da tashin hankali wanda bata yi tsammani zata kasa daukarshi ba tayi tunanin zuciyarta zata bata dama har ta ga kullewar wannan lamarin amma ina! ba zata iya ba da sauri ta fara ja da baya idanuwanta na rinewa da tashin hankali kafun ta juya da gudu tayi cikin dakinta.
Hajiya Layla da tun dazu take kallon Areefa zuciyarta na tausayinta ta sani tabbas dole Areefa taji ba dadi amma ba yarda zatayi dole wannan hanyar ta kasance mafita a gareshi su ita ce kawai take hango komai zai zama daidai bata tare da an samu matsala ba nisawa tayi sannan ta dube shi da fuska cikin damuwa.
 "Yanzu ya kukayi da su mutanan da suka zo neman Aure?".
Murmushi ya saki tare da gyara zama sosai yana fuskartarta kafun ya ja numfashi.
 "Ai Hajiya ba wata matsala duk yarda kika ce ayi haka akayi sati biyun nan dai masu zuwa za a daura auren kamar yarda kika bukata su ma ba su ja ba".
Murmushi tayi wanda iyakarsa laɓɓan bakin ta kafun ta janyo jakarta dake gefe ta zuge zip din kudi ta zaro ta mika masa kafun tace.
 "Ga wannan sai ku fara saye-saye wanda ka san gidan biki na bukata sannan duk wani abu zan turo muku dashi wanda zai tabbatar da cewa eh bikin na gaske ne".
Gyaɗa kai yayi yana ansar kudin goɗiya yashiga zabga mata kafun ya mike ya fice daga cikin gidan.
Sai lokacin Hajiya Layla ta samu tayi ajiyar zuciya mai karfi a hankali ta mike ta dauki ledar da kudin suke ciki zuciyarta na mikata wani mataki na tausayin Areefa a haka har ta isa cikin dakin ruf! da ciki ta hangeta ta hade fuskarta da filo a hankali ta taka ta isa gareta bakin gadon ta zauna bayan ta ajje kudin gefe guda.
Duban Areefa ta shiga yi wacce ta tabbatar taji shigowarta a hankali ta kai hannunta saitin bayan ta tana bubbugawa kadan-kadan kafun ta shiga cewa.
 "Areefa mai yasa zaki yi mani haka bayan kin min alkawarin ba zaki sake nuna wani damuwa kan lamarin nan ba karki manta ba wai nayi niyyar yin wannan abun bane don cutar dake a,a nayi ne don ƙwatar miki yancin ki wanda na tabbata in komai ya kammala ke akaran kanki zaki yi farin cikin haka".
A hankali Areefa ta dago tana zama idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir sai faman cizon laɓɓa take tana dakune fuska.
 "Farin ciki fa kika ce Maama kina tunanin a duniyar nan zan sake samun farinciki ne kina tunanin farincikin da ya guje mani zai sake dawowa gareni ne a filin rayuwar ta bana tsammanin haka zai kasance na sani rayuwata ba komai bane a duniyar nan bana tunanin a rayuwata farinciki zai wanzu...".
Numfashi taja da taji yana sarke mata wasu kwalla masu zafin gaske suka zubo mata saman kuncinta hannu ta saka ta dauke su kafun ta shiga girgiza kai.
 "Ban san ya zan fuskanci wannan rayuwar ba kawai ina yin ta ne ba wai don farinciki ko kwanciyar hankali ba dama can Allah ya halicce ni a haka zan kare rayuwa ta cikin kunci da takaici da rashin 'yanci na lura a duniyar nan in har baka da makusanci to kai ba ka da wata daraja ko kima da za a ganka da ita kai da banza duk daya ne....Maraya shima mutum ne kamar kowa yana da 'yanci a wajan ubangijinsa ko bai dashi a idon jama'ar duniya bani nayi wa kaina haka ba ba a son raina na zo a wannan yanayin ba amma saboda rashin 'yanci da sanin daraja ta aka lalata min rayuwata aka kashe mani duk wani hanyar da zan samu kwanciyar hankali da natsuwa Maami kina tunanin ko na auri Dr.Erena na fita akwai wanda zai aure ni a yarda nake ne?".
 Girgiza kai ta shiga yi kukanta na daduwa hawaye sai sintiri suke mata zuciyarta take ji ta matsewa da wani irin ciwo mai girman haske abun da ya faru da ita shekaru masu auki can baya take hangowa kamar yanzu komai yake faruwa runtse idanu tayi tana sanya hannayenta saman kirjinta da take jin yana barazanar tarwatsewa.
Ita kanta Hajiya Layla hawaye take yi ji take yi kamar yanzu ta tsinci Areefa cikin wannan mawuyacin halin janyo Areefa tayi jikinta ta shiga rarrashin ta hakan ya kara tsananta kuka Areefa sai da tayi mai isarta ba tare da Hajiya Layla ta hana ta ba domin ta san dole taji rashin jindadi dole taji kunci da bakinciki ba 'ya macen da zata so aci zarafin ta haka ba 'ya macen da za ta samu kwanciyar hankali a irin wannan halin.
 "kiyi hakuri Areefa kiyi hakuri komai zai wuce ba wai zaki yi wannan auren don ke kadai ba ne Areefa duba zaki yi da halin wannan mutumin in har aka barshi a doran duniyar nan Allah kadai ya san iya yarda zai tsaya da cutar da mutane hanyar daya ce shi ne ki aure shi na tabbata ke sai kin yi mamaki abin da zai faru ba dai shi yace yana son ki ba to wallahi tallahi ya janyo wa kansa duk wani kunci duniya da bala'i da yake saka mutane sai ya ji yarda ake jin sa ni dai kawai ki bani lokaci ki ajje komai a gefe sannan ki cigaba da addu'a da izinin Allah sai munyi nasara akan sa".
Dago jajayen idanuwanta tayi tana mai ajiyar numfashi zuciyarta sai faman kartawa take yi.
 "Shikenan Maama komai ya wuce zan yi yarda kike so".
Murmushin dole Hajiya Layla ta saki tana sake rungume Areefa tana jin yarda zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri hakan ya kara mata jin tausayin Areefa dole ta kwatar mata yanci ta dole ta nunawa Dr.Erena a duniyar nan ba komai yake tabbata ba musamman zalunci da cin amana sai ta nuna masa komai da yake yi akwai karshen sa kuma sai ta tabbatar masa MARAYA shima mutum ne kamar kowa yana da daraja da kima.
****
Kallo daya zaka yi mata ka gane irin ramar da ta zabga cikin yan kwanaki gabaya ta kasa kwantar da hankalin kullum cikin tunani da damuwa take akan abin da zai je ya dawo tsakaninta da Dr.Erena sosai take fargaba da tsoro sosai take jin wani irin yanayi a jikinta komai take ji yana sauya mata ji take yi kamar ba ita ba ba ta san ya wannan lamarin zai kasance ba bata san mai yasa Hajiya Layla take son bikin nan ya tabbata ba taki fada mata dalilinta tace ba yanzu ba hakan na kara sanyata cikin damuwa.
A hankali take tuki zuciyarta na ta faman safa da marwa har ta isa kofar gida tayi parking sannan ta fito hannunta rike da manyan ledoji da alamun sayayya tayi haka kawai take ji yau gabanta na faduwa ta rasa dalili ko da yake ba zata ce ta rasa dalili ba in ta danganta da lamarin nan lamarin dake kokarin faruwa da ita tana cikin wannan tunanin ta ji wayarta ta fara Ring runtse idanu tayi kafun ta dubi fuskar wayar dake hannunta ganin mai kiran ya sanyata jan dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta sai da tayi kamar ba zata dauka ba amma tuno maganar Hajiya Layla da take cewa karta sake ta nuna hanyar daya da zai fuskanci wani abu ta nuna masa kulawa sosai musamman a daidai irin wannan lokaci da bikin ya gabato saura mako daya.
A hankali ta kai wayar kunnnan bayan yayi kira na biyar bata daga ba numfashi ta ja ba tare da ta ce dashi kala ba shi kuwa acan nashi bangaren jin ta daga wayar ya sanya shi sakin ajiyar zuciya tare da murmushi.
 "Amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida".
Abin da ya fadi kenan cike da tsokana yana faman dariya ita kuwa Areefa ji tayi kamar ta kurma ihu don bakin ciki da takaici haka kawai taji wani kululun wani abu mai girman gaske ya tokare mata zuciya numfashi ma na kokarin gagararta ja runtse idanu tayi tana jin yarda kanta ke sarawa kamar zai rabe gida biyu a hankali ta ciji laɓɓanta kamar zata bula su kafun ta sake jan numfashi mai tafe da makakin takaici da bakin ciki.
 "Uhmm aiko wannan maganar taka ba gaskiya bane domin in har na kashe d'an mai gida ba abin da zai hana ba a hukuntan ni ba wannan falsafar taka sam bata yi ba".
Ta fadi da nuna kulawa amma a filin zuciyarta da fuskarta wani kunci ne yake kokarin kashe ta.
Wata mahaukaciyar dariya ya saki mai sauti kamar zai tarwatsa mata kunne da sauri ta zare wayar tana mai sakin numfashi kallon wayar take yi a wani irin yanayi ji take yi kamar ta rotsata da kasa ko ta samu natsuwa ko yaya take a zuciyarta.
 "Ai ke ta daban ce ko a cikin matayen ko kin kashe ba wanda ya isa ya hukunta ki".
Ta jiyo sautin muryarsa na fadin haka runtse idanu tayi a zuciyarta tana mai cewa 'kenan ce masa akayi kowama mara imani ne a duniyar sa kaico'.
Amma a fili mai da wayar tayi kunnnanta tana murmushin da yafi yak'e ciwo.
 "Uhmm ka ji ka da wani batu lokacin da zaka kira jami'an tsaro suyi ram dani ai duk wannan batun mantawa zakayi dashi".
 "Wai kina zaton ba zan iya bane Areefa?".
Ya fadi cikin iyakar gaskiyarsa bata yi mamaki ba don ta san kadan daga aikin sa ne dakune fuska tayi kafun tace dashi.
 "Ina zuwa gida zan shiga yanzu kaji sai an jima".
Tana fadin haka ta kashe wayarta tana jin yana magana amma taki kula shi tsaki ta ja kafun ta rangwadar da kai cikin yanayi na fidda tsammani zuciyarta na kara tsanar halin Dr.Erena tsoro take yi akan abin da zai je ya dawo.
Da wannan tunanin ta karasa cikin gida zuciyar cike da yarda al'amarin nan zai kasance.
 Haka rayuwar tayi ta tafiya zuciyarta Areefa na kara rikicewa da al'amarin Dr.Erena don ta ga dai da gaske yake an kawo lefe da komai da komai ranar daurin aure kawai ake ji izuwa lokacin gabadaya ta gama fidda tsammani Hajiya Layla ce take ta faman tausarta tana bata baki amma ina lokuta da yawa zama take yi ta ci kukanta har ta koshi ba abin da ta tsana kamar wai ita ce zata auri Dr.Erena mutumin da ya bata mata rayuwa yayi mata illa ya hana ta duk wani farin ciki ya wulakanta ta wai shine a matsayinta kaicon wannan rayuwa kaicon wannan rana da ta zo a gareta mutumin da ta tsana tsana mai tsanani a rayuwarta shine za su hada inuwa daya a haka ta cigaba da dakon kiyayyar Dr.Erena har zuwa ranar da Aure ya tabbata akan su bayan an yi shagulgula wanda hankali ba zai dauka ba an kashe kudi bidi'o'i ba kalar da ba ayi ba Areefa tayi kuka kuka mai ansa suna kuka a ranar ta so Allah ya dauki ranta ta so ta mutu da ganin wannan BAKAR RANA a rayuwarta kunci da bakin ciki a ranar ya kara daduwa a gareta haka ta wuni cur tun da aka ce an daura auren wani zazzafar zazzabi ya saukar mata ta shiga rawar sanyi kamar wacce aka saka cikin firji aka fiddo ta numfashin ta sai sauri-sauri yake yi ita kanta Hajiya Layla sai da ta firgita da yanayin da ta ga Areefa a ciki a wannan halin haka ta dauke ba tare da sanin kowa ba ta kaita asibiti nan aka ba su gado sai da ta sha ledar ruwa biyu tare da allurai sannan bayan jikin ya lafa suka dawo gida Hajiya Layla ta yi kuka ita kanta sannan ta shiga bata baki akan cewa tayi hakuri ba abin da zai faru da ita da izinin Allah Dr.Erena ba zai taba nasara akan su ba sosai ta bata baki har zuwa dare lokacin da za a kai amarya motoci kuwa ba a maganar su jerin gwano sukayi da kyar da suɗin goshi sannan Areefa ta yarda aka fiddo da ita daga cikin gidan bayan Hajiya Layla ta bar gidan domin cewa tayi ba zata iya tsayawa ba tana tsoron abin da zai faru tausayin Areefa zai iya hana ta cimma burinta.
 Tunda aka saka Areefa cikin motarta da sauran mutane da Hajiya Layla ta dauki hanyar su yan kai Amarya shikenan ta tsagaita da kuka zuciyarta na dauko mata wani tunani tana kawo mata tsanar Dr.Erena da kiyayyarsa na kara hauhauwa a zuciyarta abin da take gudu shi take jin zuciyarta na kokarin bata damar aikatawa sosai ta aminta da wannan shawara lokaci guda duk wani fargaba da tsoro suka fice mata har lokacin da suka isa katafaren kerarren gidan da za a sakata wanda ya gama haduwa tsayawa fasalta shi ma kauyanci ne babu abin da babu a cikin sa sai babu din sai dai ga Areefa duk wannan bai yi mata ba tana jin yan kai amarya na zuzutawa da koɗawa da cewa tayi goshi ta samu aljanar duniya amma ita a wajanta ko gidan yari yafi mata da wannan bakin gidan...
*_KAMALA MINNA_*😘😘😘

Post a Comment (0)