UKU BALA'I
NA
KAMALA MINNA
BABI NA HAMSIN DA DAYA.
Sosai Baffa ke kallon yanayin cikin takaici da tsananin mamaki abin da bai taba zato ko tsammani ko a mafarkinsa bai yi tsammanin zai sake tuna shuɗaɗɗen wannan lamarin ba amma bisa akasi wai yau Bello ne a gabansa shi ya tsinta shine har yayi masa magani kaico mutumin da ya tsana tsana mai ansa suna tsana a filin duniyar nan bai taba tsanar wani bawa kamar Bello ba amma wai yau shi ne a gidan sa yake zaune har yake tattalin sa yake kula masa da rayuwa ya ajje komai nashi ya bata lokacin sa mai tsayi wajan bautawa wanda ya tsana a filin duniyar nan kaico.
Wani irin maƙaki ne na takaici yake ji yana tunkodo masa zuciya ji yake yi ko wani sashi na zuciyarsa da ruhinsa suna shiga wani halin kunci mai tsanani.
Kai kawo kawai yake yi cikin dakin zuciyarsa na tunzurashi tana tuno masa da abin da ya faru sama da shekaru ashirin wanda ya ɗaɗe da binne wa ransa ba zai taba waiwaye ba amma yau rana daya ciwon da ke cin zuciyarsa ya tashi.
Runtse idanu yayi ji yake yi kamar ya kurma ihu don takaici da bakin ciki bai san ya zai yi ba bai san abin da zai yi wa Bello domin daukar fansa ba zuciyarsa ta shiga tunkodarsa akan ya dauki hukunci mai girma akansa wanda zai warkar masa da ciwon da ya haifarsa ba ma wannan ba 'yarsa yake tunawa 'yarsa mai biyayya a gareshi amma AKAN SO ta ajje duk wani girmamawa da biyayya da take masa ta shiga yiwa so biyayya ta rabu dashi ta rabu da kowa nata ta guje su duk akan so ya yafe ta tuni ya yafe ta cikin zuri'arsa ya sallamawa duniya ita amma yau daya yaji zuciyarsa na tuno masa da zaman da yayi da ita da kyautatawa da take masa.
Numfashi yaja mai karfi idanuwansa lokaci guda suka kawo kwalla komai ya faru dashi a filin duniyar nan Bello ne Sanadi ya raba shi da inda ya zauna zaman shekaru masu yawa ya rabashi da farin ciki ya raba shi da 'yarsa duk wani tashin hankali da kuncin rayuwa da suka shiga shine sila komai ya faru da su shine sila.
Dafe kan sa yayi zuciyarsa na kara rura wutar kiyayyar da yake yi masa ji yake yi kamar ya kashe shi abin da zuciyarsa take sanar dashi kenan amma yana gudun haka tunanin 'yarsa yake yau daya ya tuna da ita yau daya yana son ganinta bai san a wani hali take a yanzu ba bai sani ba ko tana raye a duniyar nan ko ta mutu duk bai sani ba ansar tana wajan Bello wanda shi kuma a duniyar ba wanda ya tsana ya sake gani kamar shi.
A hankali ya fara jan kafafuwansa da sukayi rauni sosai gabadaya jikinsa ya saki sosai tafiya yake yi yana bin kowa da kallo har lokacin da ya isa in da ya baro Bello zaune bayan ya gama fahimtar wanene shi tun daga nesa yake hangen sa yana jin yarda zuciyarsa ke kara narkewa da bakin ciki da Bello ya zama sila ji yake yi kamar yana isa ya dauke shi da mari.
A wajan Bello abin da yake ta nazari kenan akan Baffa sosai ya shiga tashin hankali sosai ya shiga cikin firgici da razana sosai yake hango yarda Baffa zai dauke shi da irin hukuncin da zai yi masa in ya gane shi wanene lokaci guda zuciyarsa ta karya ba wanda yake tausayi sai matarsa ya sani komai ya faru da ita shine sila AKAN SO komai ya faru a tsakanin su domin tayi wa so biyayya ta rabu da komawa nata tace sai shi sosai kalamanta suke masa yawo kai a can lokacin baya bayan iyayenta sun sallamata gareshi sunyafe ta gareshi...
"Bello kai kadai nake dashi a duniyar nan kai ne gata na kai ne komai nawa saboda so na rabu da kowa saboda so na rabu da komai nawa don Allah ka rikeni da amana karka sa nayi kuka A DALILIN ƊA NAMIJI ina tsoro...ina tsoron abin da zai je ya dawo Bello in har ka ci amanata ka tabbata ba zan taba yafe maka ba ni kaina ba zan yafewa kai na ba na roke ka".
Wani hawaye ne suka gangararo masa lokacin da ya tuno kalamanta tana zubda hawaye cikin tsananin firgici da yanke tsammani komai na rayuwa sai BIYAYYAR SO da take tsammanin tayi kuma take tsammanin zata samu kulawa akan wanda tayi wa so din.
Saukar hucin da yaji ne akan sa ya sanya shi saurin dawowa hayyacin sa yana waigawa Baffa ya gani fuskarsa ta haɗe kamar bakin hadari idanuwansa sun kaɗa sun yi jajir sai faman hirji yake yi kamar wanda zai ci babu shi kan sa Bello ya tsorata da yanayin da ya gan shi a ciki.
Zuciyarsa ce ta shiga bugawa da sauri-sauri kamar zata faso kirjinsa ta fito saboda tsananin firgita ba abin da yake hangowa cikin idanun Baffa sai kiyayya da rashin so kallon da yake yi masa na tsana da takaicin ganin sa sosai yake tuno waye Baffa sosai yake tuno irin DAMBARWAR da suka kwasa a tsakaninsu akan ya rabu masa da 'ya har fada Baffa ya ja shi suyi ya sha jibgarsa ya sha yi masa rotse da sanda amma duk wannan bai saka ya guje 'yar sa ba sosai yake hango irin ikirarin da Baffa yayi a ranar da ya sallama Habeeba gareashi a ranar da aka daura mata aure a ranar da suka kwashe komai na su suka bar garin.
"Ba zan taba yafe maka ba Bello ka cuce ni ka dasa min ciwo a zuciya mai girman gaske amma ka sani wallahi wallahi kaji na rantse zan sallama maka Habeeba ka je ka aure ta amma ka tabbata babu ni babu ku har abada bana kaunar na sake haduwa da daya daga cikin ku".
Runtse Idanu Bello yayi jin zantukan Baffa suna maimaita kan su a cikin kwanyarsa tsoro na kara ziyartarsa sosai a zuciya ya sani Baffa ba zai taba kyaleshi ba ya sani dole ya dau hukunci akan sa tun da yau ALKALAMIN ƘADDARA ya hada su har suka zauna waje daya a lokaci mai tsayi wanda shi a akaran kansa ba zai iya cewa ga adadin lokacin da ya kwashe a tare da su ba.
Kawai ji yayi tum akasa da sauri ya waigo Baffa ya gani ya fadi yana faman numfarfashi kamar wanda rai ke kokarin fita daga jikinsa zaro idanu yayi sosai cikin tsananin firgici ya isa gareshi yana kokarin tallabo shi amma duk da halin da Baffa yake ciki bai hana shi kokarin janye jiki daga gareshi ba hakan ya kara rikita Bello sakin baki yayi yana kallonsa gabansa na tsananta bugawa.
A daidai lokacin su Iro suka dawo daga kiwo ganin abin da ke faruwa da gudu suka iso suna kiran sunan Baffa Ja'e ya rungumo shi yana mai duban Bello da hawaye suka balle masa suna ta kwarara kamar wani karamin yaro.
"Na...ts.a..na she bana...son...ganinsa".
Cikin sarkewar muryar Bafffa yake fadin haka da sauri suka shiga duban sa domin ba su gane in da ya dosa ba ba su gane mai yake nufi da kalmar da yake fadi ba sosai suka rikice suka shiga kokarin daukarsa domin kai shi daki amma idanuwansa na kan Bello da yayi kasa ke yana kallon ikon Allah iya tashin hankali ya shiga a wannan lokaci zuciyarsa sai faman zillo take tsoro yake yi kar ya zama ajalin Baffa don ya lura yanayinsa ya tabbatar ya gane ko shi waye da sauri ya mike ya bi bayan su daidai bunkar da suka shigar da Baffa ya tsaya tsoron shiga yake don bai san abin da zai faru ba ya sani Baffa ya tsane shi in da ya san ko shi waye tun farko ba zai dube shi har ya taimaka masa ba.
A cikin Bunkar kuwa kokarin taimakawa Baffa sukayi har ya fara dawowa hayyacin sa sai faman magana yake saki wanda su dukkansu ba su gane abin da yake nufi ba idanuwansa sun kara kaɗewa sosai.
"Bana son na sake hade idanuna dashi bana kaunarsa na tsane shi ku fitar min dashi daga cikin zuri'a annoba ne shi bala'i ne komai da ya faru dani shine sila shi ne ya dasa min ciwo mai girma a zuciya shi ya raba ni da farinciki na a dalilin sa na rasa matata a ta dalilinsa ne komai nawa ya kasance da kunci a cikinsa".
Magana yake yi idanuwansa na kawo hawaye suna zuba sosai su Ja'e suka firgita da ganin tsohon na su cikin wannan yanayin abin da ba su taba gani ba kenan tsayin rayuwarsu kukan mahaifin su lokaci guda suma zuciyoyinsu suka karye kwalla ta cika masu idanu Iro ne yayi kokarin duban Baffa a dan firgice.
"Baffa wai me ke faruwa ne me ya same ka kuma waye kake cewa ka tsana?".
Runtse idanu Baffa yayi zuciyarsa na zafi kafun ya buɗe su yana duban su daya bayan daya yana faman ajiyar zuciya.
"Mutumin da na taimakawa mutumin dana bata lokaci na ina jigilar ganin yana dawo mutum mutumin da na shafe tsayin lokaci ina jinya mutumin da duk na wahala akan shi ashe ban sani ba mikiyi nane ashe ban sani ba annoba ne annobar da ta lalata komai nawa ta hanani farinciki tana hanani kwanciyar hankali ta raba ni da masauki dana kwashe shekaru ni da zuri'ata amma a ta dalilinsa na bar komai na dawo nan da zauna".
Duban junansu sukayi kafun su sake duban Baffa cikin rashin fahimtar maganganunsa murmushi mai ciwo ya saki kafun ya dauke hawayen da suka zubo masa nan ya shiga ba su labarin komai dake faruwa wanda ba su sani ba don lokaci ba su wuce shekara biyu ba.
Mamaki sosai ya cika su lokacin da ya gama ba su labari duban sa suka shiga yi cike da mamaki da al'ajabin lamarin domin duk wannan lamarin ba su san dashi ba Ja'e ya kokarta duban Baffa cikin yanayi na tausayi.
"Amma Baffa kana ganin wannan matakin daka dauka shi ne daidai?".
Wani irin duba Baffa yayi masa kafun yaja numfashi.
"Me kake nufi Ja'e? Kana nufin hakan da nayi ba daidai bane ko me?".
Girgiza kai ya shiga yi cikin kunar zuci sosai yake jin takaicin lamarin da kuma haushin Bello.
"Ba wai nace baka kyauta bane amma kana tunanin abin da kayi wa Yayah Habeeba daidai...".
"Dakata min Ja'e me kake son sanar dani kana nufin ban yi mata adalci ba ko me kasan Allah ko ita ce 'YA DAYA TAK! dana haife zan iya rabuwa da ita tunda har ta fifita wani a kai na balle kuma ina da wasu 'ya'ya mahaifiyarku da sunan Habeeba ta mutu a bakinta tun lokacin da muka baro inda muka ta so shikenan ta rasa kwanciyar hankalinta har zuwa lokacin da ta rasu ta yaya kake zaton zan yafe ko zan dauki lamarin da sauki".
Ya karashe cikin zafin rai da tsananin fushi mikewa yayi cikin hanzari yayi waje Bello na tsaye kikam tun dazu zuciyarsa da kwanyarsa duk sun tsaya cak! da aiki ya rasa mai ke yi masa dadi saukar duka yaji da sanda a tsakar kai hakan yayi matukar firgita shi Baffa ya hango sai faman Hirji yake yi bai ankara ba ji dumin jini na sauko masa zuwa fuska duban Baffa yake yi cikin wani irin yanayi yana hango kiyayyar da yake yi masa a karo na biyu yana daga sandar yana kokarin sauke masa da sauri Ja'e ya rike wanda ya fito a daidai lokacin ya shiga duban Baffa yana duban Bello dake tsaye jini duk ya wanke masa fuska lokaci guda.
Wani irin duba Baffa yayi masa kafun ya fizge sandar yana nuna Bello da ita.
"Tun wuri ka fice mani daga cikin ruga tun kafin nayi ajalinka na fada maka dama duk ranar da muka sake haduwa da juna sai na yi ajalin ka don haka tun kafin na kashe ka na mai da kai in da na tsinto ka ka san in da dare yayi maka".
Sake duban Baffa yayi zuciyarsa na zafi da raɗaɗi a hankali ya shiga takowa yana iso wa gareshi da sauri Baffa ya daga sandar jira kawai yake ya iso ya dauke masa a jikinsa sai faman ɓari yake yi kamar wanda ya sha dukan ruwa su Iro kam lamarin ya fara shallake tunanin su ba su taba zaton haka Baffa yake ba ba su taba zaton yana da zuciya haka ba tunda suke dashi ba su taba ganin ya aikata makamancin wannan halin ba gani suke yi kamar a mafarki ba gaske ba.
"Na tsane ka karka sake ka iso inda nake wallahi zan yi ajalinka".
Duk ikirarin da Baffa yake yi bai hana Bello isowa gareshi ba haka shima Baffa yana isowa ya sauke masa sandar a tsakar kansa wanda tayi sanadiyar zubewarsa kasa warwas sumamme da gudu su Ja'e sukayi kansa shi kuwa Baffa jikinsa ɓari kawai yake yi gaɓadaya ya shiga wani yanayi na rashin hayyaci.