UKU-BALA'I 54

UKU BALA'I
   NA.
    KAMALA MINNA
 
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
  BABI NA HAMSIN DA HUDU
Cikin hanzari ta fito daga cikin Toilet din jikinta daure da ta shawul kallo daya zaka yi mata ka hango tsantsan tashin hankalin da take ciki idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kamar wacce tayi KUKAN DOLE kai kawo kawai take yi gabadaya kanta ya gama kullewa ta rasa me ya kamata tayi a yanzu wanda ya dace a daidai wannan lokaci amma ta rasa gaɓadaya gaboɓin jikinta ji take yi kamar an lakaɗa mata duka ta ko ina.
Da hanzari ta isa bakin gadon dakin nata ta zauna tana mai da numfashi kamar wacce tayi gudun fanfalaki wayarta da ke yashe gefe guda ta janyo tana mai dubanta tana jujjuyawa har na tsayin dakiku kafun ta shiga latsata tana binciko lamba ta danna mata kira amma ina! Wayar akashe taji ta hakan ba karamin kara rikita mata kai yayi ba mikewa tayi da sauri ta nufi sif din dake dakin buɗewa tayi ta janyo doguwa riga baƙa ta zurawa jikinta gami da yin rolling da mayafin ta janyo flatshoes ta sanya key din motarta da ke kan Mirrow ta dauka tare da dauko wayarta sai da ta karewa dakin kallo kafun ta fice cikin hanzari zuciyarta na kara tsinkewa da tashin hankali mai girman gaske.
Cikin hanzari ta fice zuwa tsakar gidan motarta kirar 406 mai launi ruwan toka ta shiga tare da yi mata key bayan ta buɗe get din gidan ta fice ziciyarta na kara rikicewa ba abin da take jiyowa sai sautin muryar Areefa da yarda take kuka tana ihu akan ta zo ta taimake ta zata mutu bata san mai za tayi mata ba ba ta san abin da ya kamata tayi a daidai wannan lokacin ba tana tsoron Dr.Erena ya sake maimaita abin da ya zama shine sanadi a yanzu tana tsoron a sake komawa gidan jiya za tafi kowa bakinciki zata fi kowa takaici a duniyar nan domin komai ya faru da Areefa a yanzu da lokacin baya duk ita ce sila ta hanyarta komai ya ke tabbata.
Wasu hawaye ne ta ji sun sauko mata da sauri ta sanya hannu daya tana dauke su tana mai tuki jikinta a sanyaye zuciyarta ne ta shiga kai kawo tana so ta samo wanda zai taimaka mata da abin yi sosai kwanyarta take hayaki tana kokarin kamawa da wuta.
'Alhaji Abdulwahaab'
Sunan da ya zo mata kai kenan da sauri ta runtse idanunta kafun ta buɗe su tana jin wani irin yanayi a zuciyarta mai girma gaske da sauri ta gangara bakin titi tayi parking tana mai hada kanta da sitiyarin motar na dakiku sai faman sauke numfashi take kafun ta dago ta dubi wayarta lambarsa ta binciko jikinta har rawa yake yi ta danna masa kira gami da karawa a kunne cikin kankanin lokaci ta shiga ruri amma ba a daga ba har ta katse sai da tayi haka sau uku a na hudu Allah ya taimaka ya dauka wani irin ajiyar numfashi tayi mai karfi tana mai cewa.
 "Don Allah kana ina Alhaji Abdulwahaab akwai matsala fa sosai ina bukatar ka yanzu yanzun nan ko ina kake ina kan hanyar gidan Dr.Erena mu hadu acan".
Mamaki sosai ya cika shi jin abin da take fadi.
"Ban fahimce ki ba Hajiya Layla meke faruwa ne?".
Dafe kai tayi kafun ta sake nisawa.
 "Ba mu da lokaci don Allah ka zo yanzun nan akwai matsala ce".
numfashi ya sauke cikin wani yanayi.
 "Amma Hajiya Layla kin mata yanayin da muke ciki ne da Dr.Erena kin san za a samu matsala in har ya gane mu din ne muke tare da Areefa...".
 "Alhaji Abdulwahaab!".
Hajiya Layla ta kira shi tana mai katse shi zuciyarta na kara hargitsewa.
 "wannan lokacin ya dade da shafewa na manta dashi yarinyata nake bukata Abdulwahaab duk wani boye-boye ya kare tsakani na dashi zan fuskace shi komai zai faru zan tunkare shi sai dai duk abin da zai faru ya faru".
 "Hajiya Layla da kin yi hakuri man...".
Katse wayar tayi jin yana kokarin bata mata lokaci wani kuncin taji ya tokare mata wuya mai Alhaji Abdulwahaab yake nufi da nuna halin ko in kula akan wannan lamarin da ta sanar dashi anya kuwa ya san abin da yake yi anya kuwa ya ji abinda ta fada masa sosai dafe kai tayi na dan lokaci kafun tayi wa motar ki ta fizge ta da karfi zuciyarta cike da zullumi.
 Tafiya sosai tayi sannan ta isa unguwar da Dr.Erena yake nesa da gidan tayi parking zuciyarta ta na bugawa da sauri sauri bata san mai zata yi ba sosai take fargaba da tsoro a zuciyarta Areefa take so ta gani so take yi ta ga halin da take ciki runtse idanu tayi gami da kashe motar ta fito ta mai da kofar ta rufe a hankali ta shiga takawa zuciyarta na kara sautin bugu har ta isa bakin get din gidan lekawa ta shiga yi ko zata hango cikin gidan amma ba ta hango komai ba gefe ta ja kadan tana duban layin amma ba kowa sit kake ji kamar mutuwa ce ta gifta hakan ya dan kara tsorata ta amma cikin karfin hali da nuna rashin tsoro ta shiga kwankwasa Get a hankali idanuwanta na saitin karamar kofar zuciyarta na kara sautin bugun ta.
 "Waye a nan?".
Ta ji an fadi da sauri ta juya don jin muryar tayi kamar daga sama domin gabadaya a firgice take sai da ta saita kanta sannan ta lura ashe Maigadi ne wanda ya buɗe kofar a daidai wannan lokacin.
Yak'e ta shiga yi shikuwa sai faman gaisuwa yake watsa mata ganin Babbar mace ce mai suffar naira.
"Yawwa Alhaji na ciki kuwa?".
Ta fadi tana mai kokarin saita kanta sai da ya kare mata kallo don ya so gane rikicin da ke idanunta kafun ya gyaɗa kai alamun eh wani rugugin tashin hankali ne ya dirar mata a zuciya amma ta danne tana mai kara faɗaɗa yak'enta kafun ta numfasa.
 "Ok ni mahaifiyar matarsa ce Areefa".
Da sauri ya kara ladab yana mai bude mata kofar domin ta shiga sai da tayi addu'a kafun ta saka kafafuwanta cikin gidan tana takawa tana bin ko wani sashi da lungu na gidan tana kara tsorata da Dr.Erena irin dukiyar da ta ga an zuba a gidan ta fitar hankali ba ta lura da motar dake gabanta ba har ta kusan cin karo da ita san nan tayi baya da sauri motar tabi da kallo ganin yanayin da take da sauri ta zaro idanu waje ganin yarda motar tayi gilashin fitilun duk sun fashe mamaki ne ya cika ta da tsoro a zuciyarta tana tambayar mai ke faruwa Allah yasa ba Areefa ba ce tayi accident wani irin bugawa taji gabanta yayi da sauri ta yi cikin falon tana zuwa ta tadda shi a bude ba tare da fargabar komai ba ta fada ciki baje ta hango mutum tsakiyar falon sai faman murkususu yake yi idanuwansa a kankafe da sauri ta ja baya tana mai kiran Areefa da karfi gidan gabadaya ya dauka sautin muryarta.
Hancinta ta toshe jin irin warin dake tashi a tsakar falon gabadaya taji zuciyarta tana sama da kasa kamar zata yo waje rarraba idanu ta shiga yi tana faman kiran Areefa ganin ba alamunta hakan ya sanyata nufar cikin falon sosai tana buɗe daku har ta haye saman benan dakunan da ta gani ajere guda uku ta nufa tana kiran Areefa kamar wacce makoshinta zai yo waje.
Ita kuwa Areefa da take can kulle cikin daki kamar daga sama ta tsinkayo Muryar Hajiya Layla bata gasgata ba ta dauka kawai halin firgicin da take ciki ne take jiyo sautin kamar na ta amma kuma sai taji sautin na daduwa da sauri ta mike ta buɗe Toilet din kamar daga sama ta ji ana kwankwasa kofar dakin da take muryar Hajiya Layla na tashi da gudu ta fito har tana tuntuɓe ta nufi kofar ta buɗe da sauri Hajiya Layla ta gani a tsaye da sauri ta isa gareta ta rungume ta tana faman sakin ajiyar zuciya mai karfi idanuwanta sai zubda hawaye suke.
"Areefa me ke faruwa ne haka?".
Dago kanta tayi daga kafaɗarta ta dube da jajayen idanuwanta.
 "Maama Dr.Erena zai kashe ni ba zan iya zaman gidan nan ba wallahi na hakura ba zan iya zaman aure dashi ba don Allah ki fidda ni daga cikin gidan nan ji nake kamar numfashi zai katse".
Dubanta take yi sosai ta na hango rashin hayyaci a idanuwanta gami da firgice janta tayi cikin dakin gami da mai da kofar ta rufe bakin gado suka zauna Hajiya Layla tana dubanta kafun ta nisa lura da tayi ba abin da ya same ta.
 "Amma me ke faruwa dake haka duk na ganki a wannan matakin AREEFA?".
Runtse idanu tayi hawaye suka zubo.
 "Maama baki jin warin da nake ji ne?".
Ta fadi muryarta da rauni a ciki tana faman girgiza kai.
 "Tun ranar da na zo gidan nan nake jin wannan warin har izuwa yau kuma wallahi daga jikinsa ne warin nan ke fitowa da farko nayi zaton wani mushe ne a cikin gidan amma ban gani ba sai jiya da muka hadu dashi a falo nake jin warin na fitowa daga jikinsa zuciya ta dinga tashi".
Kure ta tayi da idanu kafun ta saki murmushi wanda ya jefa Areefa a wani mataki na mamaki.
 "Mai ya same shi na ganshi baje a falo yana faman murkususu".
Zaro idanu Areefa tayi gami da mikewa.
 "Wallahi ban sani ba ni dai dazu naji faduwar abu gami da ihu to a tsora ce nake ban fita ba".
Mikewa tayi ita ma ta ja hannunta suƙa fito ganin sun nufi falon hakan ya sanya Areefa turjewa tana duban Hajiya Layla.
 "Maama..".
Daga mata hannu tayi gami da nuna mata alamun tayi shiru ba ta sake magana ba ta bi bayanta gabanta na bugawa ga warin da take ji yana karuwa sosai hannu ta saka ta rufe hancinta har suka isa falon zaune suka hango shi ya jingina da kujera sai gumi yake yi kamar wanda aka watsa wa ruwa hannayensa duk biyun dafe da kai sakin Areefa tayi ta isa gareshi tana mai yi masa wani irin matsayacin kallo kafun ta saki wani murmushi wanda shi kuma a daidai lokacin ya dago kansa ya sauke a saitin ta.
Kallo yake binta dashi na alamun na sanki sosai yake maimaita kallon nasa akanta zuciyarsa da kwanyarsa suna kwaso masa abubuwa da suka shuɗe na shekaru masu yawa runtse idanu yayi ya buɗe su bakin sa ya shiga motsawa a hankali yana mai runtse idanuwansa shi kadai ya san wahalar da yake ciki.
 "Hajiya Lay...".
"A kul! din ka karka sake kar ka so ma ambatar sunana da wannan bakin naka".
Ta nuna shi da yatsa kafun cigaba da fadin.
 "Ashe ka gane ni ai na dauka ka mance fuskata a duniyar rayuwarka".
Sosai yake cikin tu'aji da daurewar kai tashi yayi sosai daga jikin kujerar ya juya ya dubi inda Areefa take tsaye kallon ta yayi kafun ya juyo ya dubi Hajiya Layla.
 "Me ya kawo ki gidaɓaa me kika zo yi ba na ce miki karki sake na sake haduwa da ko mai kamar ki bane".
Ya fadi yana mai cizon labbansa idanuwansa na kara kaɗawa sosai kwaɓe baki tayi kafin ta nuna shi da yatsa.
 "Dr.Erena kenan kana tunanin zan bar rayuwarka ne ai duk wanda ya dama dani to wallahi tare zamu shanye na san zakayi mamakin ganina a gidan ka ko?".
Ta fadi tana mai murmusawa.
Mamaki ne ya sake cika shi tare da firgice mai girma domin shi dai ya mance da wata Hajiya Layla a duniyarsa tun da kuwa ya ganta a yanzu akwai wani abu tattare da ita.
 "Dr.Erena Attajirar duniya".
Ta fadi tana barkewa da dariya wanda sosai ta kaɗa cikinsa amma ya ki nunawa ya shiga kokarin tashi amma ya kasa rikewa yaji bayansa yayi ji yake yi kamar ana doka masa guduma.
 "kar fa ka damu kan ka ba wani abu bane Malam Nata'ala ne ya bani sako in ba ka ai na san ba zaka mance sunan ba ko?".
Ta fadi cikin yanayi na izgilanci.
 'Malam Nata'ala'.
Can kasar makoshi yana tunanin inda ya san sunan kwanyarsa ne ta fara shawagi da sunan amma har ta gama bai canko ba illa idanu da ya zubawa Hajiya Layla da take ta faman sakin murmushi.
 "nayi mamaki da naga komai naka ya fara sauyawa wai yau kai ne da yin aure da alamun dai komai dake faruwa kwanyarka bata daukar sa da alamun kuma tarihi zai maimaita kan sa".
Duban Areefa tayi kafun ta dubi Dr.Erena da yaje ta faman cizon laɓbansa kamar zai cizge su daga jikinsa.
 "wannan ita ce matar taka?".
Ta fadi cikin yanayi na rainin hankali a hankali ta taka ta isa wajan da Areefa take tsaye ta dafa mata kafaɗa kafun ta sake ta dawo ta zauna cikin daya daga kujerun falon tana dora kafa daya kan daya gami da duban Dr.Erena da kan sa ya shiga wani mataki na rashin aiki komai yake ji yana cinkoshe masa ya kasa tuna komai a daidai wannan lokacin.
 *Afuwan naji na shiru kwana biyu kusan yanayin garin sai a slow yau fari gobe baki haka rayuwar take dafatan ba kuyi fushi ba😎😎 ina tare da ku ina irin mugin kaunarku din nan*👏👏👏
 *Kamala Minna*😘😘

Post a Comment (0)