UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA HAMSIN DA SHIDA.
Tsaye yake jikin motarsa ya harɗe hannayensa saman kirji idanuwansa sunyi mici-mici alamun bacin rai duban ta yayi a karo na ba adadi ya na jan tsaki kamar harshensa zai tsinke.
"Baki da hankali Hafsat na lura kan ki rawa yake yi dakikanci da jahilci su ne suke karanta miki karatun hauka kika zo kina sauke mani to ba zan dauka ba don na rantse da Allah na fiki tashanci duk akuyancin ki".
Ya fadi yana mai kara tsuke fuska Hafsat dake tsaye sai faman jinjiga take yi kamar wacce ake kaɗawa gangi duban sa tayi sosai cikin takaici da rashin abin yi.
"Huzaif haka ma zaka ce dani ga mari ga tsinka jaka to wallahi ba ka isa ba kayi kadan an gaya maka zan dauki rainin wayon ka ne duk wani ihukan banza da zakayi mani wallahi ba za suyi tasiri akai na ba".
Tun daga kasa ya fara kallon ta yana yatsine fuska kamar wanda ya ga sabon kashi sai da yayi mata kallon tsaf! Sannan ya tsartar da yawu ya juya yana kokarin buɗe motarsa ya shi gami da fadin.
"In da na san wannan haukar zakiyi mani da kika kira ni wallahi ba abin da zai kawo ke na rantse da Allah da ga yau zamu raba jaha don ba zaki dauko kamayamaya ki jona min ba ina zaune kalau ki jaza min salalar tsiya an gaya miki ban san halin da kike ciki bane ban san abin da kike yi bane wato gani karkatacciyar kuka mai dadin hawa ko to kin yi kadan Huzaif daban yake ba irin mazajen da za ki wanke tas! bane".
Ganin da tayi yana kokarin faɗawa cikin motarsa da sauri ta zabura ta isa gareshi gami da rike murfin motar da ya buɗe kallon ta yayi ido cikin idanu itama kallon shi take yi kafun ta kau da kai.
"Kasan Allah Huzaif yarda muka dama tare da kai wallahi sai mun shanye shi a filin duniyar nan ba wani na miji da nake hulda dashi sama da kai kaima kasan haka amma saboda tsabar ka raina mani wayo shine zaka nuna min halin-ko-in-kula gaskiya da sake".
Kallon ta yake yi sosai cikin tsana da takaici wai har wannan kucakar yarinyar ce za ta dubi tsabar idanunsa tana masa rashin kunya shi kam! bai san tsautsayin da ya hadashi da wannan mahaukaciyar yarinyar ba har sukayi tarayya bai san ina tunaninsa ya shiga ba bai san ina hankalinsa da lissafin sa suka fada ba har hakan ta faru a gareshi.
Daga hannu yayi kamar zai kwaɗa mata mari da sauri ta ja da baya tana mazurai hakan da ya gani ya bashi daman faɗawa cikin motar da sauri yana kokarin rufewa ita kuma tayi hanzarin riko murfin saura kadan ya datse mata hannu kallonsa take idanuwanta sun kada sunyi jajir kwalla sai surnano mata suke yi kau da kai tayi cikin raunanniyar murya.
"Huzaif bai kamata kayi mani haka ba kai kan ka ka sani ba ni da wani wanda muke hulda dashi sai kai amma na ga kana kokarin baɗa min kasa a ido kana kokarin bari na da masifa da bala'i ya kamata kayi tunani mana...".
Wata tsawa ya daka mata gami da zaro idanuwansa waje da sauri ta saki murfin motar ta ja baya fitowa yayi gabadaya yana nuna ta da yatsa bakin sa sai rawa yake yi kamar wanda zai ci babu.
"Karki sake karki soma don wallahi in har kikayi kokarin laƙa mani wannnan abin kin ji na rantse danginku gabadaya sai na daure su har igiya tayi rara don ba zan dauki Nosense things din nan ba".
Kallon sa take yi cike da mamaki maganganunsa ne suke mata yawo a kwanya ji take yi jiri na kwasarta kamar zata watse a kasa runtse idanu tayi don ba ta gasgata wai Huzaif bane ya daka mata tsawa har yake fada mata wadannan kalamai ina ba zai taba yuwuwa bane.
Buɗe idanuwanta tayi sosai akan sa tana dubansa.
"Kasan Allah Huzaif baka isa ba"..
Ta fadi tana takowa gareshi wuyar rigarsa ta cafka ta rike gam! ta shiga zazzaga masa rashin mutuncin tana faman firirita da girgije-girgije takaici ya kule shi bai san lokacin da ya dauketa da wani wawan mari ba wanda ya sanyata sakin kara ta runtse idanu wasu taurari ta ga su na yi mata yawo a saman kai gabadaya ji tayi duniyar na juya mata buɗe idanunta tayi hannayenta dafe da kunci kallonsa take yi da wani irin yanayin wanda bata taba zaton zata samu kanta a cikin ba wai Huzaifa ne ya mareta ina mafarki ne wannan ba gaskiya ba zata so ta farka daga wannan dogon malalacin barcin da take yi laɓɓanta ta tura cikin baki gabadaya cizawa tayi jin zafi ya sanyata tabbatar da cewa eh da gaske ne komai ke faruwa.
Juyawa tayi tana duban layin nasu mutanan da suke kai kawo ta hango suna kallonsu hakan yayi matukar bata mata rai ba ta san lokacin da ita ma ta fidda hannu ta zabga masa mari ba tana faman huci kamar wata kububuwa idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kwallar da take makale da ita ta sake zubowa.
Shikam! A bazata yaji marin hakan ba karamin rikita shi yayi don sosai ya ji marin hannu ya saka da sauri ya shafi kuncin nasa sannan ya dubi hannun nasa mamaki ya turnuke shi tare da bakin ciki da takaici yau karo na biyu kenan a duniyar nan 'YA MACE na daga hannunta ta na marin sa bai san mai ya sa ba kuma abin takaici kananan yara kamar wadannan kuma yan gida daya runtse idanu yayi zuciyarsa na shiga wani irin kunci hannunsa ya sake kai wa fuskarsa ya shafi wajan da ya ji marin kafin ya buɗe lokaci guda ya cafko wuyan ta ba tare da tayi zato ba sosai ya rike mata makoshi ta shiga kakari idanunta sukayo waje sosai dukansa tashiga yi amma ina ko a jikinsa sai ma idanunsa da ya saka cikin nata cikin tsantsar bakin ciki da jin haushi.
Sai da ya ga numfashin ta na kokarin kufce mata sannan ya watsar da ita akasa ta baje tana faman rike wuyanta sai murkususu take yi da sauri ya fada cikin motarsa ya ja ya bar layin.
Izuwa lokacin sosai mutanan layin sukayi cincirindo suna kallon ikon Allah ba wanda yayi kokarin zuwa ya kwace ta domin sun jima da sanin halin rashin kirki irin na Hafsat kuma akan idanunsa mafiya yawan lokaci Huzaif yake zuwa ya dauke ta ya fita da ita ba irin bakin halin da ba su sani ba da rashin mutunci da suke yi ita da Huzaif.
Mariya dake tsaye tun dazu bakin kofa idanuwanta na faman tsiyayar da hawaye takaici duniya duk ya gama cika mata zuciya hawaye sai faman safa da marwa suke yi takaici take yi yarda ɗa namiji yake wulakanta mata yar'uwa a gaban idanunta girgiza kai ta shiga yi abin na ci mata rai ba ta son abin da zai sake daga mata hankali a wannan matakin wanda take ciki ma ya ishe.
Ba tayi mamakin abin da Huzaif yayi ba don kadan daga aikin sa sosai take tuna kalamansa a ranar farko da suka fara haduwa sosai take tuna yaudararsa da yayi mata baza ta taba mantawa ba hannu ta sa ta shafe fuskar ta a hankali ta shiga takowa zuciyarta na kara curewa waje guda har ta iso wajan da Hafsat take durkushe tana ta faman rusar kuka dafa kafaɗar tayi.
"Bai kama ta ki zauna kan layi kina kuka ba wannnan ba mutuncin ki bane sannan bai kamata ki zauna kina fada da namijin da kika san yafi karfin ki ba...".
Wata irin tsawa ta daka mata gami da bige mata hannu da sauri Mariya ta ja baya tana dubanta cikin mamaki dago idanuwanta tayi wanda suka gama kaɗawa sukayi jajir ta watsa mata wani mugun kallo.
"Ina ruwan ki ko gayyarki nayi tsohuwar munafuka duk ba dake aka hada baki aka kashe mani rayuwa ba kuma wallahi ki rubuta ki ajje yarda na gamu da bala'in nan ke ma ki tsumayi naki don ba zan shiga duniyar takaici ni kadai ba".
Da sauri Mariya ta waro idanuwa waje tana ambatar 'Innalillahi wa inna ilair raji'un'. juyawa tayi ta dubi mutanan da sukayi cirko-cirko suna kallonsu wani takaicin ya sake kular da ita da sauri ta bar wajan idanuwanta na zubda hawaye ta fada cikin gida sai faman jan numfashi take yi kamar ranta zai fita.
Umma dake zaune ta dube ta ganin yanayin da ta shigo ya sanyata mikewa ta nufi cikin dakin zube ta hangeta saman katifa sai faman numfarfashi take yi.
"Lafiyar ki kuwa Mariya me ke damun ki ne haka?".
Dago jajanyen idanuwanta tayi ta dubi Umma tana faman cizon laɓɓa.
"Hafsat ga ta can a waje suna dambe da namiji Umma mutane sun hadu sai kallon su suke yi".
Gaban Umma ne ya yanke ya fadi tana ambato innalillahi gami dafe kirji idanuwanta a waje.
"Fada fa kika ce?".
Kai ta daga mata gami da komawa ta kwanta zuciyarta sai nukurkusa take yi kanta na faman juya mata.
Jikin Umma sosai yayi sanyi a hankali taja jiki ta koma ta zauna gefe guda gami da zabga tagumi abin duniya duk ya damu yayi mata yawa tausayin Hafsat take yi tun lokacin da ta lura da halin da take ciki duk da Goggo bata fada mata ba amma ita ta gane ai irin wannan abun ba ya buya koman daren dadewa sai ya bayya abu daya take gudu shine Abulle ta sani don sai ta fi kowa shiga tashin hankali.
"Wai Umma me ke damun Hafsat ne yanayin da naji suna hayaniya da Huzaif kamar akwai abin da ya shiga tsakanin su ne wanda shi kuma bai yarda shine mai laifi ba...ko dai Hafsat...".
Sai kuma tayi shiru ta kasa fadin abin da tayi niyya ganin irin kallon da Umma ta watsa mata na gargaɗi.
"Ba ruwanki Mariya ki kame bakin ki ban son abin tashin hankali wanda nake ciki ma ya ishe ni kin san dai halin Goggo yanzun nan ta sauke miki laifin..."..
Dago labulan da akayi ne ya sanya Umma saurin tsuke bakin ta Goggo ce ta fado dakin tana zuwa ta damki Mariya ta shiga jibga sai da tayi mata duka sosai Umma na kallo ba tare da ta ce da ita komai ba itama Mariya bata ko motsa ba.
"Wato ke saboda kin dauki mugun abu irin na dangin uwarki shine zaki saka saurayi yayi wa Hafsat cin mutunci akan titi haka ko to wallahi ba ki isa ba yarda kika sanya aka ci mata mutunci to wallahi ke ma sai kin samu daidai dake...".
"A,a kam Allah ba zai taba daura mata laifin da bata san dashi ba ai duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan dako".
Kamar daga sama suka jiyo muryar gabadaya suka juya da sauri Abulle ce tsaye idanuwanta sun kaɗa sun yi jajir kallo daya zaka yi mata ka gane tashin hankalin da take ciki mai girman gaske duban su tayi daya bayan daya kafun ta ja wani numfashi mai zafi ta dubi Goggo.
"Meye laifinta Goggo akan me zaki dake ta ai ba ita ce sanadi ba komai ya faru ita waccen maras hankalin wacce bata san darajar kanta da kimar ta ba ita zaki je ki daka saboda tsakaninku ne ku kukayi kidin ku kuma ku zakuyi rawar ku".
Hawayen da take makalewa suka zubo zuciyarta take ji tana harbawa kamar zata faso kirjin ta ta fito ga wani irin nauyin da kanta yayi idanuwanta suna lumshewa a hankali taji duniyar na juya mata kokarin juya tayi domin fice wa amma ina lokaci guda kafafuwanta suka lauye suka watsar da ita akasa da hanzari umma ta isa gareta cikin tashin hankali bata san lokacin da ta fashe da kuka ba dama ta san za ayi haka.
Jinjigata ta shiga yi amma ina ba alamun motsi a jikinta da sauri Mariya ta mike tayi waje da gudu ta kamfato ruwa ta kawo Umma ta watsa mata amma ina ba alamun motsawa duban Goggo tayi dake tsaye kamar wacce aka dasa sosai jikin ta yayi sanyi amma ta kasa tabuka komai.
Sake sheka mata ruwanta yi sosai wani numfashi ta ja kirjinta yayi wata irin harbawa da sauri Umma ta dagota idanuwanta da suke rufe ta buɗe su kadan hawaye masu tsananin zafi suka zubo mata laɓɓanta taa ciza cikin yanayi na takaicin zuci da ciwon rai ta shiga fadin.
"Allah na tuba Allah ka yafe mani laifinukana in har sanadin haka ka jarabe ni da wannan kaddara na gode Allah ka yafe mani".
Wani kuka ne ya kwace mata ciki karfin hali ta shiga kokarin mikewa amma ina ta kasa komawa tayi ta zauna gami da jingina da bango tana mai runtse idanu zuciyarta take ji tana kartawa kanta na sarawa cikin wani irin tashin hankali wai ita ce yau 'yar cikinta ta dauko mata abin magana abin da za ayi tur! da ita da zuri'arta abin da zai bi duk wani nata ana tsine musu ita kam! ya zatayi da wannna rayuwar Hafsat ta gama da ita ta gama kashe mata rayuwa.
"Kiyi Hakuri Zainabu ki dauki komai a matsayin rubutun ALKALAMIN KADDARA a gareki".
Wani murmushi tayi mai ciwo tare da duban Goggo da tayi wuki-wuki kamar wacce tayi wa sarki karya ta kau da kai.
"Umman Mariya in ban yi hakuri ba ya zan yi cuta ce an gama cuta ta ba yarda zan yi wai ace ni ce yau 'yar cikina ta dauko min magana ni dai na san ban yiwa iyaye na haka ba sannan ban cutar da 'ya'yan wasu ba ban zalunci mijina ba".
Girgiza kai ta ke yi domin ita kadai ta san tashin hankalin da take ciki ji take yi kamar ta hadiyi zuciya ta bar duniyar nan..
*Kamala Minna*😘😘😘