UKU BALA'I
NA.
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
BABI NA SITTIN DA UKU.
Hajiya Layla ce ta dubeshi a karo na ba adadi zuciyarta na mikata wani mataki na tausayi amma so take yi ta kwace kanta domin sam Dr.Erena ba abin tausayi bane ba abin ma a tsaya ana sauraron batutuwan da yake yi bane na rashin hanyyaci.
sosai zuciyarta take kuna gami da suya kwanyarta take ji tana kokarin kamawa da wuta laɓɓanta ta shiga motsawa tana kokarin yin magana amma ta kasa sai ma wani tari da ya zo mata da sauri ta koma gefe nesa da inda Dr.Erena yake a kwance saman gadon asibiti yana ta faman numfarfashi gabadaya ya sauya daga kamanininsa yayi wani irin baki ga idanuwansa da sukayi jajir sunyo waje sosai bakinsa ya karkace ya koma ɓarin dama fuskarsa gabadaya duk ta mokaɗe.
Tari take yi sosai wanda har sai da ya kaita zaunawa tana dafe da kirjinta hannu daya kuma ta rufe bakinta dashi sosai tarin take jinsa yana mata ciwo daga cikinta har zuwa kirjinta da take ji kamar zai fashe.
Areefa dake zaune can gefe daya takure gabadaya ita kanta tayi zuru-zuru kamar wacce ta tashi daga amai da gudawa mikewa tayi da sauri gami da daukar gorar ruwa ta nufi wajanta gami da riko mata hannu sai dai me? Abin da ta gani ya sanyata saurin ja da baya tana duban hannun Hajiya Layla da ta cire daga bakinta
sosai idanuwanta sukayo waje wani bakin abu ne mai kauri gami da yauk'i yake zubowa daga bakinta runtse idanu Areefa tayi sannan ta buÉ—e mikar da Hajiya Layla tayi ta kai ta Toilet ta wanke mata baki sannan suka fito.
Gefe guda ta zauna tana ta faman mai da numfashi kamar wacce tayi gudun ceton rai.
Sosai zuciyar Areefa ta karye sosai take jin wani irin abu nayi mata ciwo a zuciyarta tsoro na kara bayyana yanayin da take ganin Hajiya Layla a ciki ba karamin tashin hankali yake saka bata ba tun yau ba ta lura da ita tana cikin matsala amma take boye mata ko tayi mata magana su je asibiti a dubata cewa take yi a,a ta barshi akwai maganin da take sha a da can baya tana dadewa bata yi ba amma yanzu a wuni sai tayi tari yafi a lissafa.
Motsin buÉ—e kofa ne ya katse mata tunanin zucin da take yi da sauri ta dubi kofar Alhaji Abdulwahaab ne ya shigo fuskarsa a tanke kamar ba a taba halittar fara'a fuskar ta shi ba duban su yayi su duka ganin yanayin da Hajiya Layla ke ciki ya sanya shi tsaida kallonsa a kanta.
"Hajiya Layla ya ya dai na ganki cikin wannan yanayin?".
Girgiza kai tayi ba tare da tace dashi komai ba can gefe yayi ya dauko Remote dake kan loka din gadon asibitin ya shiga Control din Tv bango da yake a kusurwar dakin na dama a can sama a hankali ya shiga canza tasha har ya zo kan tashar NSTV MINNA sannan ya tsaya yana mai maida hannayensa duka baya ya juyo ya dubesu suma shi suke duba bai ce musu komai ba har illa nuni da yayi musu su mai da hankalin su kan labaran da ake yi cikin harshen turanci.
A hankali ka shiga labarai hankalin su na kai har aka zo in da ya kusan kashe su a zaune Areefa ce ta mike da sauri tana nuna Tv da dan yatsarta dake ta faman rawa Company din Dr.Erena na ne aka nuna yan kwana kwana na ta aikin kokarin kashe wutar da take ta faman ci akan sa kamar WUTAR DAJI sosai mutane suka cika wajan sai faman kallo ake yi yan kwanakwana na ta aikin su amma ina kamar kara rura wutar ake yi.
Dr.Erena da yake cikin halin rashin hayyaci da yake Tv din na saitin sa idanuwansa na kan Tv din ganin abin da ake haskowa ya kara rikita masa jiki da sauri ya shiga mutsu-mutsu yana faman kakari yana kokarin daga yatsarsa amma ya kasa dukkan su duban sa suka shiga yi ba wanda ya motsa suka cigaba da kallon su ihun da yake kurmawa ne da wani irin kuka kamar na kare ya kara rikita dakin da sauri Alhaji Abdulwahaab ya kashe TV din tare da komawa gefe ya harÉ—e hannayensa yana duban su Areefa da hankalin su ya gama tashi.
"Ajiya cikin dare Company ya kama da wuta ba tare da kowa ya sani ba tun misalin karfe biyu na dare a halin da ake yanzu duk masu gadin Company din sun mutu wajajen Asuba ne aka ankara da wutar nan aka sanar da yan kwana-kwana suka iso to dai har zuwa wannan lokacin ba suyi nasarar kashe wutar ba kuma sai kara ci take yi yanzu haka fitar da nayi can na nufa manaja din ne ya kira ni yake sanar dani abin da ke faruwa".
Ya karashe cikin nuna halin-ko-in-kula yana duban Dr.Erena da ya gama ficewa daga hayyacinsa gabadaya ya muttsuke jikinsa yana ta faman kartar fuskarsa.
Jinin da yake zuba a bakinsa ne bakinkirin ga hannayensa da ya saka ya shake wuyansa a hankali ya dinga ihu mai tsananin kara lokaci guda ya tiko kasa yana numfashi kirjinsa na faman dagawa lokaci guda kuma ya tsagaita ya daina motsi gabadaya.
"Kun ga ku tashi mu bar asibitin nan tun kafin wahalar mutumin nan ta kashe mu ai mun yi masa na Allah tunda har muka kawo shi asibiti mukayi jinyarsa ta kwanaki".
Ya fadi yana duban su kafin ya shiga toshe hancinsa wani irin warine yaji ya karaÉ—e dakin gabadaya da sauri ya juya ya fice ji yayi kan sa na juyawa Hajiya Layla ce ta dubi Areefa da tayi tsaye cikin tsananin tashin hankali ganin yarda Dr.Erena ya koma kamar bashi ba wani irin tsoro da fargaba suka shige ta ta daga hannu tana kokarin nuna shi da sauri Hajiya Layla ta riko mata hannu suka fice daga cikin dakin.
Alhaji Abdulwahaab suka hango tafe da wani likita cikin hanzari ya iso garesu gami da duban su kafin yasaka kai cikin dakin runtse idanu yayi ganin yarda Dr.Erena suffar ta juye ta koma kamar ta kare a hankali ya taka hannunsa toshe da hancinsa jin warin da yake yi dubansa ya shiga yi kafun ya tabo wuyansa sannan ya shiga auna shi sosai ya tsorata ganin baya numfashi sake auna shi yayi domin tabbatar da abin da yake zargi mikewa yayi kan kafafuwansa.
Yana kokarin fita ya ji wani kuka mai kama dana kare ya karaÉ—e dakin shi kansa sai da ya tsora ta da sauri ya juya ya dube shi gani yayi ya dawo hayyacinsa yana numfashi kusa dashi likitan ya karasa bakinsa ya gani yana motsi magana yake yi amma bata fita sai da yayi tari gami da watso wani bakin jini sannan sunan Areefa ya fito daga bakinsa yana faman nuna kofar waje jikinsa sai karkarwa yake yi juyawa likita yayi ya dubi kofar gami da mikewa ya fita can ya hango su har sun kusan barin bangaren kwala musu kira yayi gabadayan su suka juyo yayi musu nuni da hannu da su dawo.
Ko kallon arzuki ba suyi masa ba sai da yayi musu magiya sannan Areefa da Hajiya Layla suka dawo jan su yayi cikin daki suna shiga suka tadda Dr.Erena magashiyan likita ne ya isa gareshi gami da dago hannunsa ya saki ya fadi ragwaf da dauri ya sake duba sa saidai ina tuni lokaci yayi.
Numfashi ya ja mai karfi gami da mikewa kan kafafuwansa yana duban su gyaÉ—a kai ya shiga yi.
"Allah yayi masa cikawa".
Zaro idanu sukayi waje gabadayan su kafun Hajiya Layla ta dubi Dr.Erena wani irin yanayi ta ji ta a ciki zuciyarta na kara tsorata wata irin nadama da kaicon wannan rayuwar tayi sosai take jin zuciyarta na mikata wani mataki na tsoro wai yau Dr.Erena ne haka cikin wulakantaccen yanayi cikin yanayin da ko kallonsa ba za ayi ba batare da an kau da kai ba wai yau Dr.Erena na ne haka duniya kenan mai yayi duniya kenan wacce ba ma tabbata ba kuma ba aljanna ba.
Da sauri ta dubi Areefa wacce jikinta ya gama yin sanyi sosai idanuwanta du cika da kwalla hannunta ta kama tana kokarin fidda su daga cikin dakin likitan ne ya tsaida su yana mai fadin.
"Sai ku zo ku dauki gawar ko domin yi mata suttura".
Ko ta kan sa ba su bi ma shima bai damu ba duk a nasa tunanin mutuwarce duk ta ruÉ—a su haka shimfiÉ—ar gadon ya janyo ya lullube gawar gami da ficewa daga cikin dakin yana jan kofar.
******
Kwance take tayi ruf! da ciki tunanin duniya duk yabi ya dame ta gaɓadaya duniyar take ji ta tsana komai na cikinta ya daina burgeta zuciyarta sosai ta tsorata ba abin da take tunawa sai yarda ta ga Dr.Erena ya koma kamar bashi ba halittarsa gabadaya ta sauya kamar ba ta DAN'ADAM ba Company din sa take tunawa yarda taga yana ci da wuta tunda take a rayuwarta bata taba ganin harshen wuta na tashi kamar igiya ba sai ranar wuta har kore-kore take yi yarda taga ana watsa ruwa amma kamar ana kara rura wutar hakan yayi matukar daure mata kai.
Dafa kafadar da ta ji anyi ne ya sanya ta saurin jan numfashi gami da dawowa hayyacinta mikewa tayi ta zauna tana duban fuskar Hajiya Layla da murmushin yak'e zama tayi bakin gadon itama tana dubanta cikin wani irin yanayi kafun ta ja numfashi ita ma.
"KHAIRIYYA!".
Ta fadi da wata kwantacciyar murya da sauri Areefa ta dubeta jin ta kira sunanta na asali.
"Ya kamata ace kin ajje komai a gefe na sani batun Dr.Erena na ne ke damun ki ba wani abu ba kuma ya kamata ki ajje batun sa agefe shi ai duniyarsa ta kare".
GyaÉ—a kai Areefa tayi gami da goge kwallar da ta zubo masa.
"Maama zuciyata nake jin wani iri wallahi babu dadi tsoro nake ji yanayin da na ganshi a ciki".
"Khairiyya kenan ai duk wanda yace zai kauce hanyar Allah yana aikata abin da ransa ke so aiko ba zai taba ganin daidai a rayuwarsa ba kin ga dai Dr.Erena kin ga yarda rayuwarsa ta kare a duniyar nan baki daya kamar ba a taba yin mai sunansa ba kina dai ganin dukiyar da ya tara da kadarori amma ba su yi masa amfani ba kin ga kenan duniyar ma bakidayanta ba komai bane wajan Allah balle kuma bawa da yake a cikinta yake abin da ransa ke so".
GyaÉ—a kai Kawai take yi tana jin wani tsoro na kara ratsa mata zuciya da duk wani sashi na jikinta sosai ta firgita da yanayin wannan rayuwa a wannan duniyar.
"in har son zuciya zai zama ado ga dan'adam to tabbas yana cikin gagarin rayuwa in har dan'adam zai daura wa kansa buri na son abun duniya to yana tare da tashin hankali".
ta sake fadi tana riko hannayen Khairiyya idanuwanta na kawo kwalla.
"Khairiyya ki yafe mani na san nayi miki laifi mai girman gaske a filin duniyarki ina da hannu dumu-dumu wajan fadawarki wannan bala'in da kika fuskarta ina mai rokon afuwarki a karo na ba a dadi Khairiyya nayi dana sanin mu'amala da Dr.Erena nayi nadama nayi kaico in da nasan wannan rayuwar zan zaba miki wallahi ba zan taba amincewa da bukatarsa ba...".
Da sauri Khairiyya ta kai hannunta saitin bakinta tana rufewa.
"A,a Maama ki daina fadin haka dama can tun fil'azal ALKALAMIN ƘADDARA ya rubuto min hakan sai ya faru a gareni ba laifin ki a ciki".
Wani kuka ne ya kwacewa Hajiya Layla sake damke hannun Khairiyya tayi tana jin wani irin kauna da sonta na kara ratsa mata zuciya da dukkan gangar jikinta sosai take jin Khairiyya kamar ita ta haife ta.
"Ban san iyaye na ba san nan na rayuwa cikin kazamar rayuwa gashi ni ba aure nayi ba bare na samu wata zuri'a da za su jibance ni ina cikin UKU BALA'I a rayuwa ta Khairiyya...".
Da sauri ta sake rufe mata baki hawaye na wanke mata fuska itama.
"Ki daina fadin haka Maama kina da dangi kina da zuri'a ni duk zan zame miki duk wadannan abubuwan da kika rasa a rayuwa ki dauke ni a matsayin 'Ya Maama ki rikeni har karshen rayuwa mu rayu tare cikin MARAICI da ALKALAMIN ƘADDARA ya zano mana a rayuwar nan tamu".
Sosai ta rungumeta ta matse ta a jikinta wani kuka ne sukeyi gabadayan su mai taba zuciya da ruhi kuka suke yi gabadaya sun fice daga hayyacin su an rasa mai rarrashin dan'uwansa a tsakaninsu sai da sukayi mai isar su sannan Khairiyya ta kokarta tayi shiru tana rarrashin Hajiya Layla wacce kukan nata ya kasa tsagaitawa sai yinsa take yi mai hade da tari kamar ranta zai fita...
*KAMALA MINNA*😘😘😘